← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 127

Sashe 113

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har Abadan Abadan sosai Aira ta shiga Jerawa mijin nata adduo i Dan sosai ya sanyata farinciki marar musaltuwa a ranar Ta shiga ta tuk'a mota Inda yana gaba Rike da Haidar Dan yaga yanayin tukin nata kuma masha Allah komai na tafiya normal Saidai Sam barka sosai masoyan nan suke rayuwarsu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Sai fargabar su d'aya kawai Rashin daidaaito tsakaninsu da mahaifansu Anyi hutun school Wanda Mummy ta sanya aka kawo twins Dan suyima iyayen nasu Hutu da misalin Sha biyun rana Arman na wajen Aiki Aira na d'akinta tana gyara kayan Haidar da twins suka lalata shi kuma ta barshi a palour cikin net Twins da suka gaji da wasansu Wajen Haidar suka nufa tare da Fara liliyarshi suna mashi wasa Nihal ce ta ce "Naila bari kiga na iya d'aukar Haidar yalinya " Wara idanu Naila tayi ta ce "Mu daukeshi mom bazatayi fad'a ba " Eh mana ai bata nan "a tare suka had'u suka Chunkumeshi Jin damkar manya yaro ya kwala Kuka Wanda shi ya fito da Aira daidai suna shirin kadashi da gudu da ruga ta warceshi Cikin fad'a ta ce "Dan gidanku ban hanaku Tab'amun yaro ba kashemunshi kukeso Kuyi mugaye waye ya ce Ku daukarmunshi " ta fad'a tana jijjigashi tsuru tsuru sukayi Naila ta ce "Cutie Nihal ce ta ce Mu daukeshi" Cikin masifa Naila ta hayayyakowa Nihal ta ce "Munafuka Ba ke kikace mu daukeshi ba shine zakimun sharri" Harararta Nihal tayi ta ce "kece dai Munafuka muguwa kawai " Kallon Aira Naila tayi ta ce "Mom kinganta ko "? harararsu Aira tayi tana danna wayarta tana chat ta ce " Kuka k'ara sako suna na ma zakuyi mamakin abunda zan muku koba fad'a ba ku kashe kanku"sosai Naila ta kulu Aiko shako Nihal tayi nan suka hau Dambe Aira na jinsu ta musu banza ganin ihunsu ya isheta ma earpiece ta sanya Arman ne yashigo Ya ga twins na fad'a D'aya ta hau kan d'aya cikin Sauri ya shigo Tare da rabasu nihal dake Kuka tana saita rama Dakyal ya samu ya raba su Kallon Aira yayi da Hankalinta na kan waya ya ce "Ke yanzu Kina ganinsu suna fad'a bazaki raba su ba Saima zama kikayi kina Danna waya to idan d'aya ta jiwa d'aya ciwo fa kice me?Dagowa Aira tayi tare da turo baki ta ce " To Hero Akanme zan damu kaina Kaida kasan halinsu sarai barinsu nayi su gwada karfi nan gaba wacce taji jiki bata yarda su Kara fad'an ba Dan basu isa su doramun hawan jini da yarintataba "tana gama fad'ar haka ta sab'i Haidar tayi ciki girgiza kai yayi tare da d'aukar Nihal dake birgima take kuka ya ce " sorry my angel kiyi shiru idan ba haka ba Kuma na fasa kaiku wajen wasa"Lokaci guda ta Goge hawayen tace "hero da gaske" eh mana kuje Yanzu mom ta shiryaku anjima zamu fita sannan kice itama ta shirya kafin na shirya "Cikin Sauri Nihal tahau tsalle tare da Kallon Naila ta ce " Naila taho muje muyi Sauri mu shirya kinji dad zai kaimu wajen wasa"kama hannunta Naila tayi Ta ce "Nihal kiyi hakuri Bazan sake Dukanki ba kinji kema ki daina Jana" Gyada mata kai tayi ta ce "Nima nadaina" tukwana suka Ruga a tare d'akin Aira "murmushi Arman yayi yana jin soyayyar iyalan nashi tun suna yarinta ya lura zasu taso cikin Had'in kai da k'aunar juna danma Mummy Sun kwafsa musu sun amshe Su Gashi bazai iya amsar su daga wajen iyayen nashi ba Suna zuwa Suka samu Aira kan Gado Naila ta dareta ta ce " Cutie mom dad yace ki shiryamu kema da my boy ku shirya zamu fita unguwa Shima shiryawa yake"To aku sarkin surutu ta fad'a tana Mikewa "Dariya Nihal tayi ta ce " Mom yaushe zamuje naga takwarata"Harararta Naila tayi kamar wata babba ta ce "Ke baki da zuciya me zamuje muyi a wannan gidan Ai dad en Cutie mugu ne bazamu sake zuwa ba" Ta fad'a tana murguda baki"kallonta Aira tayi tare da hade rai Ta ce "magulmaciya Abban nawane mugu na k'arajin kin fad'a haka saina Bata maki rai Munafuka" Turo baki Naila tayi ta ce "To ai mugun ne tunda baya sonki nima bana sonshi kuma bazan sake zuwa gidan ba Har mom En takima bazanje naganta ba Tunda bata tab'a zuwa gidan muba shi kuma dad enki da bindigata zanje na harbe sa" Sakato Aira Tayi tana kallonta ji take kamar ta shakota Ja mata kunne tayi ta ce "Uban kine mugun ba uba na Dan Ubanki ubana sa ankine karki Kara zuwa gidan mana wani yace yanason ganinki yarinya sai shegen surutu to gobe_goben nan zaku tattara kubar mana gida Tunda Isgilallu ne ku munafukai" ta fad’a tana Kara ja mata kunne k'ara ta saki tare da fashewa da kuka Arman da ya shigo yaji suna dramar nan Dariya yayi tare da saurin zuwa ya d'auki Naila da take rafka ihu ya ce "Sorry momcy Yaudai kinjawa babanki zagi Kiyi shiru karna karajin maganar nan a bakinki"tana ihu tana kuka ta ce " Ance mugu ne "Tasowa Aira tayi da niyyar bugunta Arman ya ja gefe yana Dariya ya ce " Sorry mana my beautiful wife ayi mana hakuri bazamu sakeba "Naila dake Kuka ta ce " Dad saina sake mugu ne Ai "Cikin fad'a Aira ta ce " ka bari hero na daki yarinyar nan wlh ta rainani Kanaji ina fad'a tana fad'a ga sa'arta(Ohni su Aira manya)Dariya Arman yayi sosai Ya ce "To ai halinkine tayo na kafiya kinga ko idan ka tashi Gado ai linkawa kake" harararshi Tayi ta ce "Ni ba hali na ba tayo wannan ai gulmace take kuma Zakisan ni kika Zagarwa uba daga yau ba ruwana dake" Ta na gama fad'a ta zauna Kan Gado tana girgiza k'afa "girgiza kai Arman yayi ya ce " Yanzu dai yi hakuri tashi ki shiryasu mu fita"Turo baki tayi ta ce "Allah wlh kaji na rantse bazan shiryata ba Saidai kai ka shiryata" Dariya yayi ya ce "ta turo maki baki kema kinturomun kinga an fanshe 1-1 kenan to ni bari naje na shiryata kafin na shiryata kishirya sauran" Bata ko kallesu ba harya fita sai Haushi takeji a haka ta shirya Nihal da Haidar itama ta shirya sosai sukayi kyau gwanin burgewa nan d'akin Arman yazo ya shirya Naila dake like dashi kar Aira ta daketa A tare suka fito gwanin ban sha awa kai tsaye wani katafaran mall suka wuce Inda kowa ya jibgi abunda yakeso daga nan ya wuce dasu ya kaisu park sosai ya nishad'antar da iyalin nashi suka ci sukasha sannan sukasha hotuna sai wajen isha i suka koma gida har lkcn Aira zafin maganar Naila takeji ko magana bata mata abun ne ya isheta suna zaune a palour Naila da Nihal na Game a tab d'in d'insu suna gefen Arman Haidar ko na hannunshi yana masa wasa yana Dariya janyo wayarta Aira tayi ta lalubo number Mamy tana d'auka ta fashe da kuka sosai hankalin Mamy ya tashi ta ce "Lafiya Aira meya faru" Su Arman ma da twins duk kallonta suka tsayayi cikin kuka Aira ta ce "Mamy Dan Allah yaushe zakizo kinganninan har yara sun fara yimun gori wai iyayena bakwa sona ta k'arasa fad'a tana rushewa da kuka " Arman sosai yayi mamakin maganganunta ya k'ara tabbatarmai da airantashi dai har yanzu ta da d'ince dai "mamy ko cewa tayi wasu yaran ne suka maki gorin" Mamy Naila ce Hada cewa wai babana mugu ne "Tsaki Mummy taja ta ce " nazata ma wacen macen arzikice akan jariran yaran nan kikemun wannan kukan Allah ya shiryeki ni ban iya shiririta ba sanda kika dawo daidai munyi waya "tana gama fad'ar haka ta katse kiran " Fashewa da kuka Aira tayi sosai "Arman ne yaje tare da Rungumeta ya Ce " Haba Aira akan Naila ne duk zaki d'aga hankalinki kiyi shiru kinsan ba abunda na tsana sama da kukanki bazata sakeba daga yau"To ba kaibane ka goyi Bayan ta rainani ba kuma ko Ka bani hakuri"Murmushi yayi tare da "Goge mata hawayen ya ce " to yi hakuri bazamu sakeba"Nihal ce tazo tare da hayewa kan Aira tana Goge mata hawaye ta ce "Sorry mom " Goge hawayenta Aira tayi tare da d'aukar nilah ta ce "Na hakura yarinyar kirki Allah miki albarka" Amen Nihal ta fad'a tana Lafewa jikin Aira Naila ce ta taho tana Hawaye ta ce "Sorry mom bajan zakeba" Harararta Aira tayi tare da d'aukar Nihal tayi sama da ita ta ce "Muje mu kwanta my Beloved Daughter kuma Mummynah " Dariya Nihal tayi tana yiwa Naila gwalo Suna barin Wajen Naila ta fashe da kuka Lallashinta Arman ya dingayi amma ta tubure Dak'yal ya samu bacci ya d'auketa tana bacci Dakinsu yaje ya kwantar da ita Shikuma ya wuce d'akin cutie d'inshi . Washegari ayra Tarairaiyar Naila ta dingayi Dan Naila taji Haushi yanzu ma tana cinyarta tana bata choculate ta kunna mata game a wayarta tanayi Naila na gefe tana hawaye Ganin Haka ya sanya naila fashewa da kuka tare da zuwa taje ta haye Aira ta ce "Dan Allah mom kiyi hakuri Allah na daina bazan sakeba" Shafa kanta Aira tayi ta ce "Na hakura Amma kika sake me zan maki" Dagowa tayi tana Hawaye ta ce "Ki dakeni Mom Allah bazan sakeba " Murmushi Aira tayi tare da Rungumeta Itama ta ce "To yi shiru my prince's d'ina " Sosai Naila taji dad'i . Washegari Aira ta shiryasu sukaje gidan maman noor Bayan ta turo mata address din gidan Sosai Taji dad'in zuwansu a motarta Aira ta tuk'a sukaje Twins da noor kuwa Sai wasa suke Sai magriba sukayi mata bankwana Bayan ta cika twins da abun arziki Washegari kuma kawarta Jannat ta kawo mata ziyara itama ganin twins tazo. Hutunsu na karewa na makaranta Mummy ta aiko Aka tafi dasu Suka koma Inda Aira gidan yayi mata ba dad'i haka rayuwa taci gaba duk Hutu ana kawo twins suyo Hutu su koma A haka har Haidar yayi wata Bakwai Wanda yaron yayi wayau sosai ga kyau da shiga rai . Yau Aira tunda Arman ya tafi Wajen aiki takejin fad'uwar gaba Hakanan kawai
Chapter 113 · 0% Book details