Sashe 114
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 4 min read
takejin kamar wani Abu marar dadi zai faru Haidar ne dake Kuka ta hau jijjigashi Bayan ta bashi abincinshi ta samu yayi shiru tana nan zaune Taji shigowar motar Arman Bayan ya shigo cikin shigar kayan aiki ya Kalleta ya ce "My Prince's ya dai naga Sai wani k'ara kyau da k'iba kike kwanannan " murmushi kawai tayi tare da mik'a masa Haidar ta ce Hero.Wlh gaba na ke fad'uwa tun d'az...bata k'arasa fad'a ba sakamakon ruri da wayarta ta fara Duba mai kiran tayi taga bakuwar number d'auka tayi tare da karawa a kunne Muryar amma taji tana kuka ta ce "Sis ki maza duk inda kike ki taho yanzu " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un meke faruwa sis wanine ya mutu "Aira ta fad'a tana dafe k'irji "Inna ce ba lfy muna asibitin Mallam aminu kano sunanki Dana yaya Arman kawai take ta fad'a a kira mata ku" Tuni Aira hankalinta ya tashi cikin kuka ta ce "Na shiga ukku sis gamu nan katse kiran tayi Arman da jira yake ta gama yaji meye cewa yayi " lafiya cutie ?ba lfy ba yaya kana ji Inna ce ba lfy kuma ni dakai take nema "Cikin rudewa Arman ya ce " Subhanalla maza maza sanyo hijab Cikin Sauri Aira ta Ruga ta sanyo hijab Haidar dake hannun arman ta amsa tana hawaye ta ce "Muje yaya muyi Sauri" Kai tsaye Airport suka nufa Cikin kankanin lokaci jirginsu ya tashi zuwa kano minti Talatin me kyau tayi musu a kano Inda Arman ya kira driver d'inshi yazo ya daukeshi Kai tsaye asibitin Mallam aminu kano suka nufa Duk sun rude Suna isa cikin kid'imewa Aira ta fito Inda ta Hango su Mamy ta nufa tana kuka duk kallonsu tayi ta ce "Mamy ina innar " D'akin Da take ta nuna musu itama tana hawaye ganin zata yadda Haidar ya sanya Mamy Amsarshi Tare da cewa "ki nutsu " Cikin Sauri Aira ta nufi d'akin Arman ma d'akin ya nufa batare da ya ma Gaishe da mutanen wajen ba Dan Duk ya rud'e Aira na shiga ta samu Inna Kan gadon marassa lafiya numfashinta na fita sama sama yayinda likita biyu a kanta cikin kid'imewa Aira ta nufi gadon tare da fashewa da kuka ta ce "Inna meya sameki Inna " Arman ma gadon ya isa ya kama hannunta ya ce "Sannu Inna meya sameki" Cikin murya ta marassa lafiya Inna ta murza hannunsu ganin tana motsa bakinta ya sanya su Matsawa saitin kunnansu suka saita bakinta Cikin dauriya ta ce "Allah yayi muku Albarka Allah yayi muku Albarka Ko yau na mutu Alhmdllh tunda burina ya cika na ganin kunzama ma'aurata kuma harda zuri'a Burina na karshe ne har yau ya kasa cika na Daidaituwar Iyayenku Ina fatan ko Bayan raina zaku zama silar Daidaituwar Iyayenku nasan tawa tazo karrshe kuyimun Alk'awarin zama tsintsiya d'aya Ku rik'e juna da amana Allah yayi muku albarka" tari ne yaci k'arfin ta Kuka Aira ta fashe dashi tare da Rungume Inna ta ce "Bazaki mutu ba Inna zaki tashi muci gaba da rayuwarmu zafin ciwo ne ki daina fad'ar zaki mutu Inna bazaki mutu ba " ta Kara'sa fad'a cikin kuka mai ban mamaki Arman ma ji yake kamar yayi kukan girgiza mata kai yayi ya ce "Inna bazaki mutu ba " Bayan tarin ya tsagaita Girgiza musu kai kawai tayi Dan muryarta harta fara chanzawa ta ce "Ina Aliyun yake " Kallon Amma Aira tayi dake tsaya wajen tana hawaye itama ta ce "Amma amso Haidar wajen Mamy" Amso Haidar amma tayi wajen Mamy ta shigo dashi Amsarshi Aira tayi tare da nunawa Inna ta ce "gashinan Inna " Shafa kanshi Inna tayi ta ce "Naganshi daman shine bansaniba Allah musu albarka y'an biyu ma dazu sunzo na gansu Allah ya raya muku zuri arku yayi musu albarka" Ameen Aira ta fad'a tana kuka sosai "kallon amma tayi ta ce “meya sameta sis”Amma na hawaye ta ce “Daga zazzabi kwana biyu yau da safe ana tashi mukaga tana cikin wannan halin shine aka kawota asibiti yanzu da saukima akan dazu tun dazu sunanku kawai take kira tana cewa a kira mata ku shiyasa na kiraku”Girgiza kai aira tayi tana kuka tace “Allah bata lfy”Murmushin karfin hali inna tayiwa aira da arman tare da cewa " Kabir da Abubakar ko bayan raina zanyi alfahari daku idan kuka zama silar daidaituwas....Tari ne Inna ta fara ba kakkautawa Tare da shakuwa sosai duk suka rude har Abba da Daddy da suka shigo tsaye sukayi kanta Aira ko hannunsu gam ta kasa saki kuka kawai take Dr ne ya shigo Tare da sanya mata oxygen ganin numfashita yana daukewa "Chan kuma sukaji shiru Ba motsi ba numfashi Hannunta suka ga ya saki Wanda yake rik'e da na Aira da Arman " A firgice kamar mahaukaciya Aira ta mik'e ta ce "Inna Inna bacci ne kikayi " Dr ne ya matso tare da cire mata na urori ya rufe mata fuska kallonsu yayi ya ce "kuyi hakuri Allah yayi mata cikawa Allah jikanta da Rahama yasa mutuwa Hutu ce yana gama fad'ar haka yabar wajen " Ai Aira jin Abunda Dr ya fad'a batasan lokacin da jinta da ganinta Ya daukeba sai ganinta sukayi a sulale a wajen summammiya......✍🏿