Sashe 31
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike da firgici Aira ta juya ta saki jakar hannunta bin jakar Abba yayi da kallo Mamy ce daga palour tajiyosu cikin Sauri ta fito ta na fitowa kallon Aira tayi cikin basarwa ta ce "Harkin dawo kenan Kinko kyauta baki wuce magribar ba bani sak'on ta fad'a ta na amsa jakar hannunta kallon Abba tayi ta ce " Ni na aike ta" Ajiyar zuciya Aira ta sauke a zuciyarta ta ce "Amma Mamy ba k'aramun ceto na ba kikayi tayi saurin daidaita nutsuwarta ta ce "Eh Mamy na dawo" Abba ne ya kalli Mamy ya ce "Da izininwa kika aiketa ba gabanki na yanke hukuncin hana ta fita ba shine zaki aiketa Raini ne ko me" Danne zuciyarta Mamy tayi cikin ladabi ta ce "Kayi hakuri D'an aike na rasa ita kad'aice gidan shiyasa banjima da aikenta ba " Shiru Abba yayi saikuma ya ce "Daga wannan ya zama first and last ko kin rasa d'an aike duk Mahimmancin abun ki jira wani yazo ko ki kira driver kika sake Aikenta ranki zai b'aci" Ikon Allah Mamy ta fad'a a cikin zuciyarta a fili kuma cewa ta yi "To Allah huci zuciyarka" tana gama fad'a ta kama hannun Aira ta jata sukayi ciki suna Zuwa bedroom d'in Mamy ta saki hannunta Tare da d'aure fuska ta ce "Daga ina kike?" Gidan....saikuma tayi shiru"Bansan k'arya kinsan kikamun ganeki nake ki fad'amun Gaskiya kai tsaye Daga ina kike"Aira ba yanda ta iya tasan dole ta fad'awa Mamy tunda ma harta taimaketa a wajen Abba k'asa tayi da kanta ta ce "Mamy yaya Arman ne yazo shine.." shine me"Mamy ta fad'a a tsawace"Shine naje muka gaisa kuma wlh ba Inda mukaje gidansu kawai mukaje Kuma daga Chan ya maidoni wlh kingama abunda Mamanshi ta bada na kawo maki "ta fad'a tana nunawa Mamy jakar" shine ke har kin iya dabarar fita kiyi mana wayau ki fita kodan kinga na daina matsa maki shine kike nema ki rainani To yanzu da babanki ya kamaki kice Ubanme inbanda na taimakeki ke kinfison kullum ke kad'ai akejin kanki Da mahaifinki Aira"Cikin hawaye Aira ta ce "Bazan sake ba Allah Daga yau kiyi hakuri mamy Allah ban rainakiba " Hmmm ai hakurinki da bazan sake d'inki ba Inda sabo mun saba Allah ya shiryeki "Sannan ta d'aga jakar ta fiddo kayan ciki Turamen atamfofi ne Ukku sai Turare da sabululluka masu kyau " kallonta tayi ta ce "Ai da ina da number ta da nayi mata Godiya Angode" Murmushi Aira tayi ta ce "Wlhko mamy Ai tana da kirki sosai Mummy ba ruwanta kuma karkiga yanda take sona har cewa tayi na koma nayi mata kwana" hmmmm naga alamu ni da zan samu numberta ma akwai maganar da mukeso muyi"Cikin Sauri Aira ta ce "Ko nace yaya Ya turo maki" Ta ina zakice ya turo Makin keda ba waya kukeba sannan Mamy ta kama hab'a ta ce "Ke wai ko har yanzu wayar nan na cikin gidan nan taya ma akayi kikasan yazo har kika fita inba kuna communication ba " cikin tsurewa Aira ta ce "Na janyowa kaina garin ilata Cikin Sauri ta ce " a a wlh Mamy na mayar mashi da Wayarshi a wayar Inna yakirani shine fa dazu da tazo take fad'amun"kindai tabbata kin maidamai wayar"cikin basarwa tace "Haba Mamy tun yaushe idan baki yarda ba Kuma ki tambayi innar" a a ni ba saina tambayeta ba jeki"Ajiyar zuciya Aira ta sauke ta ce "Na sila" cikin Sauri ta bar d'akin a palour ta tarar da Amma na salla zama tayi Dan fashin Sallah take saida Amma ta gama ta tambayeta ta ce "Y'an makaranta kenan sai yanzu" Wlhko ai yau munsha wahala Kinsan sai six muke fitowa daga lecture to yau driver baizo da wuri ba shiyasa nakai magriba"Amma ta fad'a tana cire hijab tab'e baki Aira tayi ta ce "Tofa Allah takaita wahala" Kamarya Allah takaita wahala Amma ta fad'a tana Harararta "Dariya Aira tayi ta ce " To me zance inba Allah takaita wahala ba to Allah k'aro wahala shikenan"girgiza kai Amma tayi ta ce "Kede kika sani Ai zaki shiga University d'in zakiji yanda mukeji kema" Tab'e baki Aira tayi ta ce "Uhm Aiko kina ruwa inkinganni lahira kaini a kayi karatu ba shine gaba na ba" Mama ce da ta fito tayi charaf ta ce "To meye gaban naki" Rufe baki Aira tayi tare da zare idanu ta ce "Kai Mama waida kinajina Sannan ta tashi tayi dariya ta ce " Ina nufin ba yanzu ba sai Abba ya huce tukwana"girgiza kai Mama tayi ta ce "Ai nazata ko Aure kike nufi keda sahibin naki" Rufe fuska Aira tayi tare da rugawa bedroom d'insu tana Dariya Itama Mama Dariya tayi ta girgiza kai. Tana shiga Aira wanka tayi ta sauya kaya ta haye Gado Arman ne ya kirata tana d'auka ta fad'a mashi cewa "Mamy ta ce yayiwa Mummy Godiya sannan ta bashi labarin taimakonta da Mamy tayi a wurin Abba" cikin jin dad'i ya ce Allah sarki Mamynmu Allah mata albarka Gaskiya ta taimakemu yanzu dai Matsalarmu tayi sauki tunda Mamy ,Mummy, Mama Halima, Inna duk sun goya mana baya Saura Abba da Daddy kawai suma kuma muyi ta addu'a Insha Allahu Zasu amince kinsan ni fa harna k'agara Dan wlh bansan Aurenmu ya wuce nan da 3Months a k'agare nake "wara idanu Aira tayi kamar yana gabanta ta ce " 3months kuma yaya"Eh mana ai yamayi kusa ai kwanciyar hankali ace ranar da aka daura aranmu gani Gak.....cikin Sauri Aira ta katse wayar tana Dariya ta ce "Kai yaya wlh yanzu baida kunya yanzu da magana tayi nisa sai ya saki layi ta fad'a tare da yimai text da cewa " Good Night ka kwanta kayi bacci saida safe"tana turamai tayi saurin kashe wayar Dan karyayi ma ta kira Kwanciya tayi Bayan tayi Addua Dan bacci take ji Ba b'ata lokaci bacci mai dad'i yayi awon gaba da ita cike da mafarkin sahibin ta.washegari Bayan tayi Sallar asuba komawa bacci tayi Dan bai isheta ba ita ce bata tashi ba sai 10 da wata muguwar yunwa ta tashi da ita brush kawai tayi cikin Sauri ko wanka bata tarka ba ta fito palour bata tarar da kowa ba Alamun amma da Haidar suna School Dining ta nufa ta bud'e cooler soyayyar Doya da kwai ta gani a plate ta zuba da yaji ta fara ci dukda ta fara sanyi tadanji dad'in ta tana cikin ci taga fitowar Mamy da hijab Tare da Amer a hannunta "ina kwana Mamy ina zaki naga kinfito kamar kina shirin fita" Aira ta fad'a tana cin doyarta "Wlh ko wai Aysha ce suke Asibiti tun jiya da dare bamu saniba sai dazu mijin ya kira tayi miscarriage ne Wai harma anyi mata wankin ciki Su Mama sunyi gaba shine zan bisu " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Aira ta fad'a tana hawaye sannan ta ce "Kaico Aunty Aysha Allah bata lafiya Mamy Dan Allah inzo mu tafi" Ta fad'a tana hawaye ganin yanda ta damu ya sanya Mamy cewa sanya hijab d'inki tare da Abbanku ai zamu idan ya yarda saimuje "cikin Sauri Aira taje ta sanyo hijab da takalmi suna fitowa farfajiyar gidan Abba na mota harsun fiddo mota Zagayawa Ta glass Mamy tayi ta ce " Abbansu wai Aira tace itama zataje ta dubata da naga a mota ne kuma tare zamu ta bimu ko ?Ba Inda zata ta koma tayi mata addu'a a gida ke kuma kiyi Sauri ki shigo mu tafi Sauri nake"Kallon ta Mamy tayi ta ce "Kinji abunda ya ce " ki koma"Goge hawayenta Aira tayi ta ce "To Mamy Allah bata lafiya barmun Amer Dan Allah ya tayani zama tunda ni kad'aice"Mik'a mata shi Mamy tayi ta ce " idan yaji yunwa ki had'a mashi abincinshi ki bashi saboda zamu jima"Amsarshi tayi daga hannun Mamy ta ce "To Allah kiyaye kice ina duba ta Dan Allah Mamy" Su Mamy na tafiya Aira ta koma ciki tare da Amer dake mata gwalamgwamtu sosai ta damu da Rashin lafiyar Aunty Aisha taso taje ta ganta Amma ba dama a gida tayi mata addu'a ta ce "Allah baki lafiya Aunty" tana komawa Aje Amer tayi da niyyar taje tayi wanka Amma fir ya k'iya ya fara kuka ba yanda ta iya sai daukarshi tayi ta fara jijjigashi Dabara tayi ta goyashi ba b'ata lokaci ko bacci ya daukeshi saukeshi tayi a hankali ta shinfid'ar dashi gadonta taje tayi wanka tana fitowa ta shirya cikin Doguwar Riga Atamfa ta d'aura kallabin atamfar Wayartace tayi ringing d'auka tayi Daga bangarenshi Arman ya ce "Shine jiya kika gudu kika barni ko" Dariya tayi ta ce "Ai kai dinne yaya Naji kana neman sako wata maganar yanxu dai ya kake ka tashi lafiya" Alhmdllh sai kewarki kawai"Zaro idanu tayi ta ce "Jiya fa muka rabu" Eh mana ai nafison koda yaushe muna tare da juna"Murmushi tayi ta ce "Nima da so samune hakan amma ya zamuyi" me kike Arman ya fad'a "Bakomai ni kad'aice ma a gidan sai Amer Duka sun tafi duba Aunty Aysha " Subhanalla Me ya sameta"miscarriage tayi"wayyo Allah ya bata lafiya ya musanya musu da mai amfani "Ameen yaya" kince ke kad'aice ko"Eh yaya"To ganinan zanzo mu gaisa "gabantane ya fad'i ta ce Yaya ai mai gadi bazai bari na fita ba" eh na sani lek'owa zanyi daga bakin gate ganinki kawai zanyi na koma"murmushi Aira tayi gabanta na fad'uwa ta ce To yaya saika zo"ganin ana kiran Sallar Azahar ya sanyata tashi taje kitchen ta dafa indomie Da egg cikin 30 minutes ta gama komi ta fito a palour ta Aje jiyo kukan Amer ya sanyata tashi tana zuwa Taga ya tashi yana shirin fadowa kasa ta tareshi tare da daddaukarshi ta jijjigashi ta ce "To yi shiru" Kuka ya cigaba dayi dafe kai tayi ta ce "Nima naga ta kaina fitowa tayi dashi palour dakin Mamy taje ta had'o mashi custard da madara cikin Sauri ta dawo palour Tana fara bashi yayi shiru Ajiyar zuciya ta sauke taci gaba da bashi saida ya koshi har yana kauda kai tukwana ta rabu dashi abun wasa ta Aje mishi nan yahau wasanshi yana dariya"(Nikam nace Aira ashe an iya raino😂) sai sannan ta samu damar cin nata