← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 127

Sashe 60

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

....Saina nemo ki masoyiya ya k'arasa fad'a yana murmusawa ta gefen baki"Daddy ne ya taryoshi Rungumeshi yayi ya ce "highly wellcome my son I m very happy to see you Allah ya k'ara maka lafiya"Ameen Arman ya fad'a Shima yana Rungume Daddy Mummy ta matso cike da farinciki Dan yau jinta take cikin farincikin marar musaltuwa Dan samun lafiyar yaron nata a yanzu ta fiye mata komai cike da farinciki suka bar airport d'in koda suka isa gida sosai goverment house din ta cika da mutane Dan ko a Chan Egypt d'in mutane sundinga tururuwar zuwa y'an uwan Mummy ma dake yola duk sunzo domin duba jikin na Arman gidan saiya kasance kamar ana wani shagali Arman ko dayake baisan damuwa da hayaniya tunda ya shiga katafaran bedroom d'inshi bai lek'oba Dan wasu idan suna son ganinshi Godiya Mummy takeyi musu tace ya samu bacci Dan tana kiyaye dokokin da likita ya dorasu a kansu Arman ko kwance yayi a makeken Royal bed dinsa ya d'ora kanshi bisa hannunshi yana kallon sama tunanin Inda Aira take kawai yake tare da tunanin yanda zai nemo ta dan baitab'ajin ya karaya ba ko sau d'aya indai akan Aira ne lokacin shan maganinshi nayi Mummy tazo da kanta ta b'alla masa ta bashi yasha. Tunda aka Sallamo Arman kullum gidan cike yake da mutanen Arziki masu zuwa dubiya Mama Halima ma tazo daga kaduna ita da Hafsa Dan duba jikin nashi Tunda Mama Halima tazo batayiwa Arman zancen Aira ba haka Shima baiyi mata ba dukda yana son tambayar Inda take Zaune suke a palour ya kwanta saman sopa Mama Halima da Mummy na hira jefi jefi yayinda Hafsat ke waya k'asa k'asa Shidai Arman idonshi rufe ba wacce takeyimai gizau idan ba Aira ba Shi ina ma take?ya tambayi kanshi Bud'e idonshi yayi a hankali ya sauke akan Hafsa dake lumshe ido tana waya bamaijin abunda take cewa "Tsaki yaja Tare da yunkurawa zai tashi cikin Sauri Mummy taje ta taimaka mashi ya mik'e tare da yi mashi Sannu" Gyad'a mata kai yayi a hankali ya ce "Mummy zan iya fa tafiya da kaina kije ki zauna Naji sauk'i fa" Murmushi tayi ta ce "Ka tabbatar dai ba wata matsala" gyad'a mata kai yayi tare da d'an murmusawa kad'an da mahaifiyar tashi taji sanyi"Sosai kwa hakan yayiwa Mummy dad’i ta ce "To shikenan ka kula Allah ya k'ara lafiya" Ameen ya fad'a tare da Fara tafiya ya nufi bedroom d'inshi Yana isa kan bed ya zauna tare da dafe saitin zuciyarshi dake mashi ciwo Dan tunanin Aira da ya zurfafa Kwance yayi wasu siraran hawaye na zubo mashi wace hanyace zai samu ya had'u da Aira tunani yayi Tabbas Hafsa tasan Inda take kuma zata iya fad'a mashi hakan yasanya shi janyo telephone d'in dake gefen gadon ya Danna number Mummy tana d'auka ya ce "Mummy a bawa Hafsa ta kawomun Tea " Daga bangaren Mummy Ajiyar zuciya ta sauke tare da Kallon Hafsa ta ce "Jeki had’awa yayanku tea ki kai mashi d'aki amma karki cika sugar kinji daughter" Katse wayar da suke da yaya Umar tayi tare da mik'ewa ta ce "To Mummy " Bayan tafiyar Hafsa kallon Mama Halima Mummy tayi ta ce "Ni wlh daman Hafsat Arman ya komawa Tunda dai Airar tayi Aure kuma naga Kamar ya d'an fara hakura da ita tunda ko maganarta bayayi" Cike da Rashin nuna jin dad'i Mama Halima ta ce "Aunty kibar wannan Maganar Dan Allah karma ta zame matsala " murmushi Mummy tayi ta ce "Ai daman ceewa nayi daman naga Hafsa d'inma kamar da Wanda takeso tunda na kula tunda tazo kullum tana waya" Wlh ko wai Umar nefa suke soyayya dashi ni farkon d'aukarma wasa nayiwa Abun saidaga baya na lura itama sonshi take "ikon Allah To Allah tabbatar da alkhairi kice tuwo na maina za ayi amma ai yana da mata ko" Eh yana da mata Allahdai tabbatar da alkhairi kawai Amma banson kai y'a gidan mai mata dukda dai d'an uwanta ne "Ameeeen ya Allah ai fatan Alkhairi kawai ake Wani gamin saikiga Auren mai Matar ma yafi na saurayin kwanciyar hankali Yanzu barin Kasu d'in da ta shiga zatayi kenan idan Auren ya taso" a a. Gaskiya banjin Abbanta zai cireta tunda Shima ak'ida garai cewa yayi saitagama karatu ko yana mata Aure "Nan dai sukaci gaba da tattaunawarsu Hafsat ko Bayan ta had'a tea d'in d'akin Arman ta nufa knoking tayi ya bata izinin shigowa tana shiga Ta duk'ursa ta ce " Sannu yaya ga tea d'in"yunkurawa Arman yayi ya tashi zaune tare da cewa "Ajeshi kan center Table " Nan ta Aje harzata juya ya ce "zo muyi magana Hafsa " Juyowa tayi tare da zaunawa Kujerar dake gefen gadon ta ce "Gani yaya" Numfasawa yayi kamar bazaiyi magana ba kallonta yayi ya ce "Kinsan Inda Aira take tana gidansu har yanzu kuwa ?"Sosai Hafsa tayi mamakin tambayar da Arman yayi mata cewa tayi "a a a ta na sokoto " what sokoto kuma?Arman yafada cike da mamaki"Gabanta na fad'uwa Dan tsoro take kar wani abun ya kuma samunshi ta ce "Kayi hakuri Yaya Yanzu Aira ai tafi wata guda a gidan mijinta Ammafa har yanzu tana sonka yaya dukda yanzu bama tare A dalilin Auren har kokarin kashe kanta tayi Tasha fiya fiya" Kashe kanta fa kikace Hafsa yanzu dai fatan tana lafiya ba abunda ya sameta "gyada mashi kai tayi ta ce " Eh taji sauki tun lokacin ta warke"nauyayyar Ajiyar zuciya Arman ya sauke Sosai yaji zafi da kishi da rad'ad'in jin wai Aira na gidan mijinta mijin ma bashiba "Ya sunan mijin nata?ya fad'a cikin k'arfin hali" Kamar mai nazari Hafsa tayi Dan sunan ya shige mata saikuma ta ce "Inajin dai akwai Madugu a sunan nashi Amma na manta ainahin sunan"Kallon Hafsa yayi ya ce " okay thnks u can go but don't tell anyone munyi wannan Maganar dake "gyada mashi kai tayi ta ce " Insha Allahu "tare da barin d'akin tana tunanin me Arman zaiyi da sunan mijin Aira Arman ko tana fita Sosai ya k'ara shiga damuwa wai Aira ce Ke gidan wani har tsawon wata guda Sosai wani irin kishi ke taso mashi shikenan kenan Wani banza sakarai ya rigashi sanin Airarshi sosai zuciyarshi ta dinga tafarfasa. Da misalin tara na dare Zaune suke a palour ita da Laila suna Hira Laila na bata labari har Dariya take Sadiq ne ya shigo da sallama a bakinshi Kallo d'aya Aira tayi mai tayi kasa da kanta Dan nauyin had'a ido dashi ta ke " Zaunawa yayi yana sauke ajiyar zuciya Laila ce ta ce "Sannu da zuwa yaya Ga alamu kashayo gajiya" Yawwa Sadiq ya fad'a ya ce"wlhko na kwaso gajiya jeki d'auko mun ruwa"To yaya Laila ta fad'a tare da tashi tabar palourn Kallon Aira yayi da tayi kasa da kanta tana wasa zobe yayi ya ce "Auntynmu ba magana to ina yini " D'agowa Aira tayi ta Kalleshi tare da turo baki ta kauda kai"Murmushi yayi ya ce "Baza a amsa gaisuwarta tawa ba kenan Mamanmu" Dagowa Aira tayi ta Kalleshi tare da Fara hawaye Cikin shagwaba ta ce "Ni ba mamanka bace ina nazama mamanka please mai sunan Abba ka daina "Dariya Sadiq yayi ya ce " sorry to na daina Auntynmu zance kenan"Turo baki Tayi ta kauda kai"Wai ina Aunty Aysha kuwa kun bani ita tunda dai Ke yanzu kin zama mamanmu "ya fad'a cikin sigar zolaya " Murmushi tayi ta ce "Tana Chan kano Ai tayima Aure tafi 5 moths ina tunani" Cike da nuna Rashin jin dad'i Sadiq ya ce "Ayya to Allah ya basu zaman lafiya"Ameen Aira tafada" Laila ce ta dawo tare da mik'awa Sadiq ruwan kallon Aira tayi tare da mik'a mata wayarta ta ce "Natafi kuma sai Mamy ta kira zan kawo maki kuma saita katse amshi ki kirata...kafin Aira ta amsa ta sake kira" yawwa ma gashi ta sake kira Laila ta fad'a tana mik'awa Aira amsa Aira tayi tare da d'aga wayar daga d'ayan b'angaren Mummy tayi sallama "Aira ta amsa tare da cewa " Ina yini Mamy"Lafiya qlau Aira ya sokoto kindai zama basakwakwaciya"tashi Aira tayi tare da barin palourn tayi d'akinta ta ce "Haba Mamy ni har yanzu bakaniya ce Sokoton da ko ganinta bantaba ba Tunda nazo banje ko ina ba"Haba dai to ai gwara haka daman Banason yawo amma naga kamar kuna zaman lafiya da mutanen gidan ko Aira " Eh Mamy yanzu lafiya qlau muke zaune da dai suka bani wahala Amma yanzu Alhamdulilla "To masha Allah haka nakesonji daman ki hakura kiyi zaman aurenki kinji Aira tunda Allah ya kaddara miki" hawaye ne suka zubowa Aira ta maidasu "Uhm kawai tacewa Mamy" Sannan ta ce "Mamy ban Amer mu gaisa" Murmushi Mamy tayi ya ce "shidai bai magana Saidai yayi miki gwalamgwamtu ta fad'a tana Kara mishi Wayar a kunne" My boy Aira ta fad'a jin gwalamgwalamtun Amer nan ta biyeshi suka yi ta shiririta tukwana ta ce "a bata Haidar kiran Haidar Mamy tayi Shima ta bashi Sosai yaji dadi cikin farinciki suka shiga gaisawa da y'ar uwartashi ya ce " ya Aira munyi missing d'inki wlh gidan duk ba dad'i inna ma kullum saitayi kukan rashinki"Goge hawayenta Aira Tayi ta ce "Nima nayi missing naku sosai bro Kaico my Inna kenan ta dawo nima nayi kewarta"Amsar wayar Mamy tayi ta ce " "ba abunda kike buk'ata inbada ko mota ne a kawo maki...Dariya Kad'an Aira tayi ta ce " Kai Mamy yanzu ko nace inason wani Abu saiki bada a kawomun tundaga kano a a bana buk'atar komai ganinku kawai nake buk'at....kasa k'arasa maganar tayi sakamakon ganin shigowar Alh Yusuf da tayi a murtuke Ihu ta fasa tare da wulli da wayar ta ce "Na shiga ukku Daddy Dan Allah fita" k'arasa shigowa Daddy yayi ya ce "Bazan fita ba ke nifa ba haka nan na auroki Dan na dinga kallonkiba ba biyan buk'ata shine kuka hademun kai keda saude ko to yau zanga ta Had'in kai saitazo ta kwaceki" ya fad'a yana rufo d'akin tashin hankali ba a gwada maka rana da gudu Aira Ta Ruga ta shige toilet tare da sanya key ta ciki ta rufe durk'ushewa tayi jikin kofar tare da fashewa
Chapter 60 · 0% Book details