Sashe 110
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya hana Dan ta fad'a masa Aira ta haihu ya ce "bazataje ko ina ba cikin su Duk Wanda yaje a bakin aurenshi Mamy Kad'an Ya hana ta tafi in banda Aunty Ramlat da ta kira ta dinga mata nasiha akan ta zauna ita zasuje gobe ayi komai dasu ta kwantar da hankalinta a haka suka samu Mamy ta zauna Amma taso taje Amma ganin yanda Abba ya hana iyayensu ma zuwa ina ita ina tunkarar zuwa. Yayyun Mamy Duka saida sukaje kd din Har Matar Yayanta ana jibi suna sukaje Wanda hakan sosai yayiwa Aira dad'i koba komai wannan Karin akwai dangin mahaifiyarta da na mahaifinta a sunan y'an uwan mummy ma na yola duk sunzo Ranar suna yaro yaci suna aliyu Haidar k'aton sa Arman ya yankawa d'an nashi sosai a wannan sunanma yayi b'arin kudi Aira ko shigar da tayi ma fad'ar tsadar da kyaun kayan b'ata baki ne Sosai tayi kyau dukda bata da walwala saboda batajin dadi tunda ta haihu k'arfin hali ne kawai take haka akayi taron suna aka gama lafiya Bayan anyi bishshar kudi Mummy ma sosai ta taka rawar gani a sunan Haidar Wanda Daddy ma ya bata gudummawa mai tsoka da zata taho tare da twins sosai suka sha gayunsu nan aka shiga musu hotuna da dare Aira na kwance saboda hayaniyar mutane ya sanya kanta tsananta ciwo Mummy Ce tazo da kanta Tare da mik'ar da ita ta bata magani ta sha su Aysha tayiwa magana akan a barta ita kadai ta huta Haidar ma daukeshi Mummy tayi tare Madarar da aka fara basa ta ce "Shima bari mu kwana dashi Jinin naki ina ganin har yanzu yaki sauka kodai sai mun koma asibiti" girgiza kai Aira tayi ta ce "a a a Mummy ina ga hayaniyar mutane ce zuwa safe na kwanta zai sauka " saida taga kwanciyar ta tukwana Mummy ta mik'e tare da rufo mata dakin. Washegari koda ta tashi ciwon kan da sauki Bayan Angama soye soye y'an uwan Mamy da Mummy duk suka wuce Bayan ancikasu da Abubuwan arziki Arman ko yana Abuja Dan ya koma kan aikinshi Ganin irin jimawar da yayi bayanan kuma lafiya qalau komai nashi a normal ya sameshi hakan yasa bai samu daman lekowaba washegari dukda hankalinshi na kan Aira Cikin kwana biyu su Aysha Da Ummy suka koma Wanda Aira saida suka sha kuka da zasu tafi su Mummy ma sun tafi danma an bar Nihal taki bin Mummy yasa Tadanjin saukin kadaici Da dare tana kwance tana chat Inda Rahama tayi mata voice ta ce "nayi ta Kiranki bata shiga daughter kuma baki hawa online " voice Aira ta tura mata ta ce "Sorry momcy kinsan bani da layin nan Shiyasa bansamu na kira ba kina raina kuma albishirinki muna ma garinku anyima su twins k'ani shekaranjiya akai suna kunyi Aliyu Haidar" kasancewar rahma na online "cikin farinciki ta ce " wow congratulation daughter Allah ya raya kai amma wlh baki kyauta mun ba kina ma garinmu ashe turoman address din Inda kike gobe insha Allah gani nan zuwa "nan Aira ta tura mata address din gidan Wahshegari ko Aira na kwance akan sopa Mama Halima na rigima da Nihal Dan kullum saisun yi rigima Aira na Dariya Haidar ko na hannun Hafsat tana liliyarshi Suka jiyo knoking Mikewa Hafsat tayi da Haidar a hannunta tana bud'ewa turus tayi ganin kawarta Rahama da suka gama KASU tare " wara idanu tayi ta ce "Friendy kece yau a gidan namu ko gizau" itama rahamar mamaki tayi ashe gidansu Hafsat ce ma Aira ta sauka "Dariya tayi ta ce " muje ciki"suna shiga har kasa Ta duk'ursa ta gaishe da Mama ta amsa cikin mutuntawa Rungume juna sukayi da Aira sunajin farincikin had'uwa Barin d'akin Mama tayi Rahama ta kalli Aira ta ce "Kai daughter a fili kinfi kyau kin ganki kuwa" Dariya Aira tayi ta ce "Ai momcy kema a fili kinfi kyau kinganki kuwa " Dariya sukayi "Ganin Nihal Kallon Aira tayi ta ce " Takwarace ko uwar fad'a kinsan bana gane su daban daban "Dariya Aira tayi ta ce " takwararce "Wara mata hannu Rahama tayi ta ce " yaudai gani ga takwara da Oum twins fad'awa jikinta Nihal tayi tana Dariya kamar ta Santa daman"Hafsat ce ta ce "Wai ina kikasan juna nan Aira ta fad'a mata Inda suka had'u tukwana itama Hafsat din ta fad'a mata kawartace " D'aukar Haidar tayi ta ce 'masha Allah shi kuma kama da mom d'inshi yayi kenan Allah ya raya manasu"Ameen Hafsa ta fad'a Bayan an kawo mata kayan makuleshe Nihal ko duk ta hahhayeta Nan ta fito da uwar sayayyar da tayiwa twins hada Haidar sosiau Aira tayi mamakin kirkin Rahama Godiya tayi mata sosai ta ce Bakomai ai ana tare sai yamma Rahama ta tafi Wanda dak'yal Nihal Aka Bambareta jikinta Dan cewa tayi sai ta bita Bayan tafiyar ta Mama Halima taja kunnen Nihal ta ce "Mutane na zuwa kina cewa zaki bisu saina zaneki ko suna baki abu kina amsa ki bisu uwar kwadayi ja'ira a haka idan mugaye ne har a sace ta " Kuka Nihal tasa "Aira ko dariya tayi " Mama ta ce "Gaskefa ku dinga hanata wlh kwanaki haka y'ar wata nan k'asar layin mu Daga ganin wani a hanya ya bata sweet ta like mai Saita bishi a banza mutumin nan ya lalata musu y'a karshe sai gawarta aka kawo musu karkiga ba kyan Gani y'ar shekara shidda " Sosai Aira ta tsorata ta ce "wayyo amma duniya ba Gaskiya wlh insha Allah Mama zamu hanata daman itace Naila bata da likewa mutane " Aira sosai take samun kulawa daga wajen Mama Halima Wanda suke zuwa Asibiti akai akai har aka samu jinin nata ya sauka yanzu ciwon kan ma ta daina sosai Rahama ma kawarta me kirki tana zuwa akai akai Arman ko fashin kwana daya yake yau yazo gobe bai zuwa Mummy ko duk sati sai tazo wannan satin tazo zata tafi Nihal ta ce itama binta zatayi daman ba wasu kaya gareta ananba Mummy tace suje zasu shiga mota juyowa tayi ta dagawa Aira hannu ta ce "Cutie mom bye" Sannan ta kalli Hafsa ta ce "Aunty bye " Dariya Mama Halima tayi ta ce "Ni baza ayimun bye d'inba " Turo baki tayi tare da Harararta ta ce "Ke ai fad'a galeki ba ruwana dake ke da dad en Cutie " sosai kowa dake wajen ya kwashe da Dariya musamman Mummy kama hannunta tayi tana Dariya cikin zolaya ta kalli Mama Halima ta ce "Kinji yarinya k'arama ma tasan halinku na fad'a " Dariya Mama Halima tayi ta ce "y'ar yayatu ce Ai gwara kuje Chan ku karata Wannan iyayen Surutun " duk Dariya sukayi washegari Arman yazo dayake barin musu palourn ake idan yazo Suna mak'ale da juna kamar kullum Haidar na hannunshi yana mashi wasa yana Kallonshi yana Dariya Aira na mak'ale jikinshi marairaicewa yayi ya ce "Cutie yaushe zaki koma gidan ni d'aya ba dadi duk a takure nake "marairaicewa tayi ta ce " Uhm nima bansaniba hero gashi Mama batamayi zancen ba "cikin damuwa ya ce " Yanzu saura kwana nawa ayi arba'in d'in "Juya idanu tayi saikuma ta ce "yau dai satinmu hud'u "Ajiyar zuciya ya sauke ya ce " saura kwana goma kenan"gyada mashi kai tayi "cewa yayi Allah ya kaimu"daganan suka sauya Tasha sunjima suna Abu d'aya kafin Arman ya Mike ya tafi Bayan yayiwa su Mama bankwana Aira ko ciki ta koma tayi wanka tayi alwala tayi sallah Dan tun last week ta fara salla batason Arman ya sanine Dan karya dameta ". Inna koda ta dawo daga kauye aka bata labarin abunda ya faru sosai ta shiga Surfa ruwan masifa a gidan Inda ta shiga ba tanan take fita ba hada kukanta a lokacin Su Abba na wajen a palourn gidan ta ce " y'an jikokin nawa da nafiso su suka tsolewa mutane ido akewa sharri duk wani masifar mutum kansu ake dorawa to ta Allah ba ta mutum ba Kuma abunda akaso suyi din Alhmdllh basuyi ba mutum Saidai ya mutu Sannan kai kuma habu ka jima baka kori Hajara a gidan nan ba Ai ba wajen zama zata rasa ba Aikin banza aikin hofi sosai ta dinga bala I da masifa Shidai Abba bai tanka mata ba haka kowa dake wajen Mamy ko sosai taji dad'in yanda Inna tayiwa Abba Dan ko magana basayi dashi ita kwanciyar hankalinta ma da yanzu aka San Inda y'arta take. Su twins ko sosai suke samun kulawa daga wajen kakannin nasu Dan duk wani meeting da za ayi na manya dasu mummy take tafiya sosai manyan mutane suka San jikokin na excellency Wanda sosai ake musu kyaututtuka ganin Suna zaune a haka ya sanya Daddy nema musu makaranta me kyau wacce tafi ko wacce tsada da koyawa ya sanyasu sannan ya nema musu Tahfex sosai Kuma yaran suke ganewa da fahimta Dan sun tsaida hankalinsu waje d'aya Saidai Rashin ji fa akwaishi musamman Naila da Ake shan fad'a da ita a school y'an ajinsu duk tsoranta suke Nihal cema miskila Dan Yanda take daddagewa yara saikace wata babba wai ita ala dole Jan aji ne kar a rainata Sosai Malaman makarantar keson yaran kasancewarsu masu kyau da kokari gashi kuma jikokin governor guda hakan yasa ake nuna musu kulawa a school kuma hakan yasa sukeson zuwa makarantar har so suke su tafi. Aira ta na gama arba'in da sati Mama Halima ganin irin Rashin kunyar ARMAN tayi yawa yanzu kullum Yana nan kuma ya gwada matarshi yakeso ya sanya hada musu kayansu ta runkutasu ta ce Allah ya raka taki gona hakan ko sosai yayiwa Aira da arman dad'i ranar da ta koma suka bud'e sabon shafin soyayya suka dasa daga Inda suka tsaya Danma yanzu Arman na zuwa wajen Aiki ba kamar Lokacin da suke London ba kawarta maman noor da suka had'u a jirgima Tazo tayima Aira barka Dan jininsu ya had'u ranar yini tayi mata tana tambayar ina twins Noor Kullum saitayi zancensu"murmushi Aira tayi ya ce "Ai suna kano twins ina ma tunanin sun koma Chan da zama wajen kakanninsu " jinjina kai Mom noor tayi ta ce "Amma kinyi kokarifa sis kinganninan noor