Sashe 64
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 6 min read
bata labarin soyayyarsu da Arman har hawaye take batare da ta sani ba daddab'ata tayi ta ce " Kiyi Hakuri sister Allah yana tare daku nasan zafi da rad'ad'in so ba abune mai sauk'i ba a Gaskiya ko a labarai bantab'a ganin masoyan Asali masu k'aunar junansu da zuciya daya ba sama da yanda kikebani labarin soyayyar da kike yiwa wannan bawan Allahn Amma ina mai baki shawara da Kibi komai a Sannu ki daina yawan tunanin wani a cikin ranki saboda yanzu kina matsayin Matar wani ce Karki bari shaid'an yayi galaba a kanki Allah babu ruwanshi da Rashin son Auren da bakiyi zai iya kamaki da laifin hakkin Daddy please sis ki rage wannnan soyayyar da kikeyiwa bawan Allahn nan tunda kinyi Aure"Numfasawa Aira tayi da kukan da take tare da gyadawa Laila kai Alamun to amma batajin daidai da second d'aya zata iya daina tunani da soyayyar Arman murmushi Laila ta sakar mata ta ce "ko kefa sis niko zanso naga Arman d'innan da ya zuzutar mana da Amarayr daddynmu guda " Hararar wasa Aira ta galla mata tare da turo baki ta ce "bako zaki ganshiba " Dariya Laila tayi sosai ta ce "Maida wuk'ar naga har kin fara kishi Daga ambatar sunanshi" Dariyar da bata shiryaba Aira tayi ta ce "Hada sharri ko sis" ba wani sharrri Amaryan daddynmu "Tilla mata Pillow Aira tayi tana turo baki.. Zuhura ce ta shigo Tare da yaranta Sakato tayi tana kallon yanda Laila da Aira suke wasa kamar wasu y'an uwa ko aminai kasa shiru tayi cike da fad'a ta ce " me Zan gani haka Laila keko wani Rashin sanin ciwon kan ne ya kaiki mu'amula da yarinyar nan harda Dariya"Sai sannan suka Kalleta Mikewa Laila tayi tare da zuwa ta amshi boy din dake hannunta ta ce "oyoyoy my Aunty kece da Yammar nan " Harararta Zuhura tayi ta ce "Amsa nace kiban ka wani iyayi ba " Murmushi Laila tayi tare da kama hannunta ta ce "Aunty jarabatu kenan muje ciki saina baki Amsar sannan ta kalli Aira ta ce " ina dawowa sis yanzu karki tafi akwai labari"murmushi kawai Aira tayi ta ce "To saikin fito" Bata gaishe da Zuhura ba saboda taga yanda take aiko mata da harara"Suna zuwa daki Zuhura Cike da fad'a tacewa su mama me yasa suke sakewa waccen Banzar yarinyar fuska Mama da kanta ta bawa Zuhura labarin da Aira ta basu sannan ta d'ora da cewa "ki kwantar da hankalinki ai yarinyar Chan da kike gani ba ma saimun bata lokacinmu wajen fitar da ita ba mu daukarwa Kanmu zunubi a banza da kanta zata fitar da kanta idan muka zuba musu ido " Tabe baki Zuhura tayi ta ce "ku dai daina sake mata da yawa haka " Itako Laila har ranta yanzu son Aira take Dan sun shaku sosai cikin y'ar abutar da suka k'ulla ta kwanannan gashi ta lura Aira bata da matsalar rayuwa D'aukar Junior K'aramun Dan Zuhura tayi tare da ficewa Zuhura ta bita da harara Laila na komawa Inda ta bar Aira ta sameta Zama tayi nan suka cigaba da Hira Bayan Aira ta amshi junior tanayi mashi wasa a yanzu Saukin Aira daya yanda Daddy Ya shareta hakan ko yayi mata bala'in dad'i yanzu ko kokarin rik'e mata hannu bayayi hakan ya sanyata yanzu fara sakewa ta daina Yawan zaman d'aki Saidai idan kwanciya zatayi rufe d'akinta ne ko yanzu koda mistake bata mantawaba saita rufe tabar key d'in jiki yanzu ta fara sakin jikinta da y'an gidan Sadiq ne dai saitayi ma sati bata ganshi ba mubarak ko harta mance rabon da ta ganshi hakan ko yayi mata dadi Dan daman Duka gidan tafijin nauyinshi har yanzu bata bar kukan Rashin Arman ba Dan daidai da rana d'aya bata tab'a fashin kukan Rashin shiba musamman idan tazo kwanciyar bacci.. Arman koda ya kwanta mafarke mafarken Aira kawai ya dingayi Inda mafarkin yake yimai nuni da tana buk'atar shi a kusa da ita hakan yasa tunda ya tashi ya shiga damuwa yinin ranar bai samu ya leko ko palour ba saboda azabar ciwon da kanshi ke mashi Sosai ya zurfafa tunanin Aira Inda daga karshe ya yanke shawarar da yake tunanin indai yabita idan yaci sa a zata b'ulleshi a lokacin karfe Tara na dare Mikewa yayi kamar Wanda aka zabura cikin Sauri ya d'aga locker Kayanshi Tare da bude k'aramar had'ad'd'iyar box dinshi Kala hud'u ya sanya cikin Kayanshi Tare da saka abunda yake ganin zai buk'ata na yau da kullum Yana gamawa ya ja akwatin ya rufe takarta da biro ya ciro tare da zaunawa ya fara rubutun doguwar wasik'a yana gamawa ya linke sannan ya k'ara bud'e wata ya sake wani rubutun Wanda baikai na wancen ba Shima ya linke saida ya lek'o palour yaga ba kowa Ajiyar zuciya ya sauke tare da saurin komawa yaje ya janyo akwatinshi harya fita daga Part d'insu bai hadu da koawaba saida ya fito ne yaci karo da securities D'aya daga cikinsu ta nufa wajenshi Wanda yasan Daddy Ya aminta dashi fuskarshi a daure danma kar wani cikinsu yayi mashi wata tambayar rainin hankali cike da gadara ya je ya mik'awa security d'in tare da mik'a mashi takaddun nan guda biyu ya ce "Gashi gobe da safe ka bawa Daddy d'ayar kuma Mummy zaka bawa"to ranka ya dad'e zan kai musu amma ina kake shirin zuwa da Daren nan na ganka kamar kana shirin tafiya" wani banzan kallo Arman ya watsa mashi tare da cewa "is not your business " yana gama fad'ar haka ya kira d'aya daga cikin driver d'in gidan umartarshi yayi da ya sanya mishi akwatinshi cikin boot din motar sannan ya bud'ewa Arman back sit ya shiga Shima ya shiga ya tada mota cike da girmamawa ya ce "ranka ya dad'e ina muka nufa" Airport zaka kaini"Koda suka isa airport Bayan driver ya fitowa da Arman da akwatinshi Kallon Arman yayi ya ce "Allah ya tsare hanya ranka ya dad'e " Ameen Arman ya fad'a tare da cewa"duk Wanda ya tambayeka Inda ka kaini kada ka bashi amsa a Daren nan ka fad'awa wani ka kawoni Airport kaima kasan sauran"insha Allahu hakan bazata faru ba ranka ya dad'e a dawo lafiya"Arman bai Kara cewa komai ba ya bar wajen cikin k'ank'anin lokaci aka shirya mishi tafiya sokoto kamar yanda ya umarta Dan a lokacin ma babu jirgin da zaije sokoto mak'udan Kud'i Arman ya kashe Dan bayason ya k'ara kwana d'aya a garin nan ba tare da ya isa garin da masoyiyarshi take ba ba ayi 1 hour ba jirginsu ya d'aga sokoto Wanda cikin k'ank'anin lokaci suka isa a lokacin kusan 11pm saura Koda suka isa a hankali Arman ya dinga Saukowa Daga benen jirgin Wani farinciki da annashuwa ya mamayeshi harya gama Saukowa k'ayaitaccen murmushi ya saki ya ce "Yau Gani a garin da ban tab'a mafarkin zuwa ba Amma soyayya ta kawo ni Alhmdllh yau gani garin da masoyiyata Take cikinshi a halin yanzu nima ina cikinshi Tabbas Gaskiya ne da y'an magana sukace Garin masoyi baya nisa..........✍🏿