← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 127

Sashe 7

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari jiki ba kwari ya tashi koda mumy ta tambayeshi lafiyanshi qlau kawai yace mata nan take fad'a mashi Daddynshi jirginsu ya taso tun d'azu sun kusa isowa sai sannan ya d'anji sanyi sanyi a ranshi Dan sosai yakeson ganin Daddy Mummy tace yaje ya shirya nan da 30 minutes zai k'arasa.

Arman da kanshi shida Mummy suka taryo Daddy daga Airport Hannun Daddy rik'e da na Arman Dan ko Wanda bai saniba yasan irin tsananin son da Daddy ke yiwa Arman kasancewarshi shi d'aya tilon d'anshi a duniya.

Bayan Daddy ya huta yaci abinci Mummy sai Nan nan take da mijin nata Kallon Arman yayi ya ce "Son ya London d'in Fatan ka dawo lafiya" Lfyqlau Daddy "Masha Allah yaushe kuma zaka koma wajen Aikin naka" ran Monday sukace Daddy nama zata zasu d'an bani Hutu tunda kaga su suka turani London d'in nadawo na zata sunbani ko hutun 2weeks ne amma jiya sun kirani suke ceman Monday suke Son na koma"Dafa kanshi Dady yayi ya ce "Toh nan kusa kenan Kaga yau muna Friday to Allah ya kaimu Monday din Ai nasan d'ana jarumine Shiyasa basason suyi missing d'in aikishi ".

Murmushi Arman yayi Dan sosai yakejin dad'in yanda Daddy kullum ke kod'ashi shi d'anshi jarumine jajirtaccene tun yana yaro haka yake cemashi shi jarumine Ranar Yini sukayi suna Hira da Daddy Dan ko gidan Inna bai lek'a ba Yau cikin hirar ne yake cewa "Daddy Inna na ta nemanka" murmushi yayi ya ce "Insha Allahu gobe idan na huta zanje na gaisheta.

Washegari Daddy da Arman su kaje ya gaishe da Inna shida Security d'inshi Wanda koda yaushe suna biye dashi Arman bai samu ganin Aira ba dan Inna tace mai suna makaranta kasancewar da safe sukaje daga Chan suka wuce asibitoci Dan duba marassa lafiya sannan yayi musu alheri sosai wannan na Daga cikin abunda yasa mutanen jahar suke tsananin sonshi da son mulkinshi danshi mutum ne mai kirki da kuma tausayi ga Gaskiya da rukon amana.

Ran Sunday da dare Arman ya je gidan Inna Dan bankwana da Airanshi koda ya fad'a mata zai koma wajen Aiki kuka ta sanya mashi ita batason yake nesa da ita dak'yal ya lallab'ata yace zasu dinga Video call kullum kuma suna waya duk saiyaji bayason ma Tafiyar Dan dai ya zama dole Amma shi Zama da Airan shi ya fiye da mashi komai.

Tunda Arman ya tafi kullum cikin waya suke da video call kamar ma suna tare Aira suncigaba da Jarabawarsu ta neco ita da Amma sosai suka maida hankalinsu ga karatunsu har yanzu babu Wanda yasan da wayar Aira a cikin gidan Bayan Amma koda yaushe son Arman Kara ninkuwa yake a cikin Zuciyarta.

Ranar da Arman ya cika sati Biyu da tafiya Ranar Su Aira suka gama neco d'insu sai farinciki suke suda class mate d'insu ana tashan hotuna a wayar Aira nan Duk wasu suka amshi numbobinta ranar ji suke kamar karsu rabu daga karshe suka sha kuka musamman Aira ita da frnds d'inta Khady bestynta sosai suka shaku koda yaushe a school tare suke yawo nan sukayiwa juna Alk'awarin ziyartar juna akai akai Sai wajejen 6 suka gama hotuna da bankwana suka fito Bakin gate domin tafiya gida Suna fitowa Wata wulfefiyar Mota Fara me masifar kyau Aira ta gani parke .

Ganin mai fitowar ne ya sanyata wara idanu sosai yayi cikin sky blue din shadda ta tasha Aiki hular kanshi hadaddiya wadda a k'alla zata kai 100k Rungume yake da hannayenshi da suke sanye da Wrist din zinare kara wara idanu tayi Dan tabbatarwa da shi d'inne koko Gizau ne shiko kafeta yayi da idanu murmushi kawai yake sakar mata sosai tayi mashi kyau cikin unifoam dinta Light blue Hijab da Dark blue din wando y'ar k'aramar hijab dinta tare da rafar rigarta da ta sauko har gwuiya anyi mata hular hijab d'in da yadin wandon jelar rigarma haka ji yake Kamar ya je ya rungumota Aira ganin da gaske shi d'inne de gabanta ai batasan lokacin da ta saki Hannun Khady ba ta ruga a guje tayi wajenshi tare da Rungumeshi tama mance ta tsiraran mutanen class d'insu dake wajen Cike da murna da farincikin ganinshi ta ce My yaya........✍🏿

*Share fisabilillah*

*_Miss Hajo ce*_🤙🏿
[5/30, 23:01] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️...............13&14

Cikin zazzak'ar muryarshi Mai cike da kassala a hankali ya ce "My Cutie baki girma har yanzu ko kin manta gaban mutane muke kike rungumeni " ya fada kamar bashi yayi maganar ba murmushi tayi tare da sakinshi ta ce "Sorry yaya murnar ganin kace ta sa na ma manta da mutane a gurin" Aike gimbiyace bakya laifi my cutie "Uhm My yaya ammafa Gaskiya kayi surprise Dina da yawa bantab'a tunanin zaka zoba" Ranar graduation d'in Cutie na guda ace banzoba ai Abu baiyi dad'iba yanzu dai ki shigo mu tafi gida ma ida maganar a hanya ko"to my yaya bari naje nakira Amma Tana barin wajen ya zagaya ya shiga mota.

Aira na komawa khady tayi mata Dariya tace “ummm kwt har anfara love kenan kice mu fara shiri kece bikin farko a mate “harara ta galla mata tace “sa’idinawa kawai yaya nane to sannan tace muntafi sai mun had’e online “tukwana sukayi hug din juna suka rabu Amma na baya Aira na gaba haka suka tafi a hanya sai satar kallonta yake harsuka isa ba mai cewa uffan sunzo daidai bakin gate din inna sukaga fitowar motar Abba ta gate d’in gidansu cikin faduwar gaba Aira tayi k’asa da kanta dan kar Abba yaganta abunda bata saniba tuni yaganta saida taga wucewarsu tukwana ta dago tana sauke ajiyar zuciya Shidai Arman girgiza kai kawai nan ya gyara parking a waje Amma ta fita tare da cewa thnks Aira zata bude motar taji kulle juyowa tayi ta kalleshi saita sakar mai murmushi shima ya mayar mata tare da cewa.

“Ina kika saka wayarki jiya nayi ta kira a kashe”uhm yaya wlh wayarce kasan boyeta nake bana yawo da ita ko tsakar gida dan kar wani yagani shiyasa tana locker d’ita tun jiya sai da zamu sch nadaukota dan muyi hotuna “.

“Ajiyar zuciya ya sauke ya ce “nazata ba lafiya shiyasa na taho saida nazo nan nake tambayar haidar a bangaren inna yacemun kuna sch yau kuke last paper “wayyo yaya wai saboda baka sameni ba a waya kawai ka taho i’m sorry “ta fad’a ta na langabar da kai”Shitttt Kin manta bakya laifi komai kikayi daidaine my cutie “sannan ya dauko wata karamar waya daga cikin kwali tana gani ya daga ya saka wani sabon sim card tukwana ya bude ta yace “amshi wannan karamace saikidinga yawo da ita yanda duk sanda na kira zan sameki “murmushin jin dadi tayi tace Thnks my yaya”banson godiyarnan fa daman kinsan yau kuke graduation shine baki sanar daniba “uhm yaya na manta shiyasa “Allah bada sa a Ya fitar da sakamako me kyau kawai yace sannan yace “zan wuce dear baki bukatar komai”Eh yaya bana bukatar komai ganinka ma ya wayadas Bazaka shiga ku gaisa da inna ba “dazu mungaisa ai zanje na hutane kafin gobe na wuce “kamar zatai kuka tace “yaya gobe kuma yayi kusa ai”Zandawo soon yanzun akwai aikin da na baro shiyasa I am sorry gobe idan ba jirgin Safe zanhau ba zanbiyo muyi bankwana idan kuma na samu na safe na wuce kawai “hawaye ne suka fara zubar mata tace “shikenan yaya Allah ya kiyaye ya tsaremun kai “handkerchief ya d’auko ya fara share mata hawayen ya ce “Idan nazo kinamun kuka idan zan koma zandaina yawan zuwa dan bakisan yanda nakejin kukanki a cikin zuciyata ba “cikin sauri ta had’iye kukanta da take shirin cashews’

“sorry yaya bazan sakeba banson kana nesa dani ne shiyasa idan ka tafi yaushe zaka dawo “shima ji yake kamar yayi kukan yace “nafi kowa bukatarki a kusa dani dan bayanda zanyine next week insha Allah zanshigo na kwana biyu “to my yaya Allah ya maidoka lafiya “ki kulamun da kanki kinji my cutie “murmushi tayi tace “kaima ka kulamun da kanka sun dan taba hira kadan tukwana yayi mata bankwana ya wuce ji suke kamar karsu rabu da juna.

Aira koda ta shiga gida bata iske kowaba sai Ummy da Haidar da amma da suka dawo tare “Ya Ummy ina y’an gidan naga ba kowa bangaren inna ma bata nan”ta fad’a tana Waige waige “Suntafi kai Mamy asibiti “wara idanu tayi tace “Asibiti kuma me ya sameta “Haihuwa zatai “langabar dakai tai tace “wayyo Allah sauketa lafiya ranar bangarensu ta kwana sai addua take Allah sauke mamy lafiya dakyal bacci b’arawo yayi awon gaba da ita.

************

Arman kai tsaye guest house dinshi ya wuce dan yasan ya biya ta gida Mummy saisunji dalilin da yazo to yace musu saboda Aira ko me hakan yasa ya wuce chan bayan yayi wanka t-shirt kawai ya sanya da gajeran wando fresh milk kad’ai yasha tukwana yabi lafiyar gado dan akwai gajiya sosai tattare dashi yau jinshi yake cikin farinciki saboda ya hadu da Airanshi lumshe ido yayi a hankali ya ce “I love her so much Cox she’s beautiful “tunowa lokacin da yaganta cikin unifoam yake kyakkyawar fuskarta kawai yake ta hangowa da yanda take sakar mai murmushinta mai narkar da zuciya tuno lokacin da ta rungumeshi yayi ji yayi tsikar jikinshi ta tashi kamar wanda aka tsunkula haka ya zabura rumtse idonshi yayi sosai kafin ya bude su mikewa yayi ya dauko wani hotonta sosai tayi kyau cikin Wata black laffaya daga gani hoton bai jima ba kafe hoton yayi da idanu bako kiftawa kafin ya fara shafa hoton yana murmushi shi kad’ai yace “I love you my Aira ina sonki sosai Airata ki soni please ko kadan ne yafada yana marairaicewa (🤣nikam nace Arman karfa ka haukace)rungume hoton yayi a haka baccci me dad’i ya daukeshi cike da mafarkin Airanshi.
Chapter 7 · 0% Book details