← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 127

Sashe 66

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 10 min read

Zaune yake akan Kujera k'aramun littafin Alquran a hannunshi yana karantawa sosai yakejin dad'in iskan farfajiyar hotel d'in Musa ne yazo mik'a mashi Hannu yayi suka gaisa tare da cewa Ya bak'unta" Bayan sun gama gaisawa nan musa Shima yaja tashi kujerar ya zauna "yawwa Abokina inajinka ina son sanin labarin nan da kace zaka bani yau Dan a k'age na kwana da sonjin labarin" kamar bazaiyi magana ba saikuma ya fara bashi labarin soyayyarsu da Aira da abunda ya had'a mahaifansu rigima har suka rabasu haryakai karshen labarin Inda ya d'ora da cewa "Ina buk'atar taimakon Abokina wajen gano gidan da Airata take Dan Allah patan zaka bani Had'in kai" Sosai musa ya tausayawa abokin nashi Tabbas akwai abun tausayi a labarin "Numfasawa musa yayi ya ce " a Gaskiya Kunga jarabawa Abokina Allah baku ikon cinyeta Saidai abunda ban fahimta ba a nan me ya kawoka garin nan me zakayi idan ka gano gidan da take"a saboda Aira nazo garin nan ina son sanin Inda take ne bazan iya cigaba da rayuwa batare da ita a kusa dani ba tayi nesa da idanuwa na Amma har yanzu kusa take da zuciyata bazaka gane irin son da nake mata abokina ba hakan yasa na yanke shawarar zuwa Inda take Dan na nemu gidan da take Na nemu Aiki a gidan hakan ne kawai zaisa naci gaba da arba da ita "da mamaki Musa ya Mike ya ce " kana da hankali kuwa Abokina Aikifa kace Haba impossible wlh kamarkai da darajarka da komai ka kaskantar da kanka a saboda mace kana d'an governor guda kace zakayi aiki a k'ark'ashin wani Gaskiya shawarar nan da ka yanke batayi ba so hauka ne aka gaya maka"so yafi hauka Abokina Son da nakeyiwa Aira ya wuce duk yanda kake tunani kada ka kashemun kwarin guiwa inason ka karfafamun hakan yasan ban nemu taimakon kowaba ba na nemu naka Saidai idan bazata taimakamunba kawai ka fad'amun"ya fad'a cikin daga murya "kwantar da murya musa yayi yana mamakin wani irin sone wannan ya ce " ba haka bane Abokina amma Ina mamakinkane Shawarar da ka yanke ce nake ganin bata dace ba Kadubafa matsayinfa maid house zakayi Haba Abokina da iliminka da kyanka da kudi ga mulki ga matsayi ka duba fa "Numfasawa Arman yayi ya ce " Tabbas hakan ya shaidamun baka San meye so ba musa so babu ruwanshi da mulki,kud'i,sarauta,matsayi da sauransu Zan iya komai a saboda Soyayyata so ba Karya bane karka k'ara katseni akan Abunda nayi niyya idan zaka Taimakeni ka tayani neman gidan if bazaka iya ba kawai ka fad'amun bazaka iya ba na nemu taimakon wani "Sorry Abokina kayi hakuri idan ranka ya b'aci yanxu shikenan yaushe zamu fara neman Gidan" Mikewa Arman yayi ya ce "For now" Girgiza kai musa yayi Dan yalura abokin nashi yayi mugun nisa a soyayya A mota musa ya Kalleshi ya ce "kasan sunan mijin nata" Harara Arman ya maka mai tare da Jan tsaki ya ce "Wlh ka k'ara ambatarmun sunan wai mijinta a nan zakayi mamakina" Dariya musa yayi k'asa k'asa ya ce "Allah huci zuciyar manya to ya sunan shi mutumin" Tsaki Arman yaja yanajin tsanar sunan ya ce "Wai Madugu? ai Madugu suna da yawa a garin nan wanne kenan Real name d'inshi zaka fad'a" Tab'e baki Arman yayi ya ce "Bansan asalin sunanshiba nasan dai ana ce mashi Madugu " Aiki ja Kace aikin namu babba ne Aiko nemoshi a garin nan akwai aiki "bincikawa zamu tayi har Allah yasa a dace " Ganin yanda Arman ya had'e rai ya sanya musa Jan bakinshi a haka sukayi da Yawata gari suna neman mai suna Madugu amma duk kwatancen da akayi musu sai suga bashi bane Sai magriba suka Koma gida cike da gajiya musamman musa da aka tada mashi aiki tun daga ranar nan kullum Arman da musa sai sun fita neman Gidan amma sun kasa samowa saida sukayi kwana biyar suna Abu d'aya sosai sukeshan wahala ba karama ba Dan Duk Inda suka tambaya Sai ace su dai fad'i lak'anin yaudai musa ya fara gajiya Dan sun gama yawatawa amma Ba nasara kallon Arman yayi yace Gaskiya Abokina na fara gajiya haka fa zamuyi ta gararanba a gari batare da mungano gidan ba"Kayi hakuri nasan ina sanyaka wahala insha Allahu jikina na bani yau za a dace "to waikai bazaka iya tuno sunan ba?wlh bansan sunansa ba amma me zai hana mu zagaya unguwowin masu kud'in garin nan tunda Shima yana da kud'i" na am da wannan shawarar musa yayi nan suka zagayawa unguwowin masu duk Inda sukaje su tambaya Dan Allah Ko sunsan gidan Alhaji Madugu sai ace musu basu saniba a haka har Allah ya kaisu Arkilla quarters Inda suka hangi wani wajen chaji Musa duk ya gaji a tare suka fito Dan tambayar mai chajin ko Allah yasa a dace Dan haka suke duk Inda suka samu tambaya suke Suna isa mik'a mishi hannu sukayi musabaha musa ya ce "Dan Allah Abokina tambaya muke ko Allah zaisa a dace" To inajinku Allah yasa na sani"mai chajin ya fad'a yana fuskantarsu"Dan Allah gidan wani Alhaji Madugu muke nema ko ka sanshi" Ciza yatsa Mai chajin yayi ya ce Madugu,Madugu,Madugu To mudai Madugu anan Unguwar Biyu ne akwai Alhaji Yusuf da kuma Alhaji bukar" Cikin Sauri Arman ya ce "Eh shine Alhaji Yusuf sai sannan ya tuno da sunanshi da aka fad'a a lokacin da Aka fad'a a gidan television " Kallonshi mai chajin yayi ya ce "Wanda ya auri wace Yarinya k'arama kwanaki Y'ar kano shi kake nufi kuwa"Eh shine Dan Allah gidan mukeso ka nuna mana" ya fad'a cike da zak'uwa "Kallonshi musa yayi ya ce " Daman kasan sunan ka bari muke ta shan wahala"mancewa nayi sai yanzu da aka fad'a na tuna da sunan"Kallon mai chajin musa yayi ya ce "Dan Allah Abokina zo zaka gwada mana gidan" Badamuwa me chajin ya fad'a tare da rufe wajen chajin ya ce "da y'ar tazara Saidai muje Tare na muku rakiya" Cike da farinciki suka yi mashi Godiya suka shiga mota Shima ya shiga A baya ya dinga nuna musu hanyar gidan Har yakaisu daidai kofar gidan tukwana ya ce "nan yayi ga gidan nan ya fad'a yana nuna musu kofar gate d'in " a tare suka kalli kofar Wani farinciki na shiga zuciyar Arman wai yau shine a kofar gidan da Cutie d'inshi take hamdala yayi a zuciyarshi ya godewa Allah Kallon musa yayi ya ce "Ka gane gidan daiko" Eh ai nama San unguwar muke ta shan wahala ya fad'a su suka maida mai chajin Inda suka daukoshi sosai sukayi mashi Godiya Inda Arman ya rubuta mishi check d'in Dubu d'ari biyar ai mai chajin nan godiyar da ya shiga kwararawa Arman bata lissafuwa harda kukan farinciki yayi wai yau shine akayiwa kyautar har Rabin million.kudin da ko kwatarsu bai tab'a kamawaba sosai ya shiga kwararawa Arman addua shi arman har gajiyawa ma yayi da amsawa a hanya musa ya Kalleshi ya ce "to mungama me wahalar yanzu meye shirin ka na gaba"shirina na gaba daga gobe zai fara kaidai abunda nakeso dakai inason ka nema mun irin abun nan na nad'in buzaye tare da kayan buzaye wad'anda suka d'an sha wahala " Dariya musa yayi ya ce "kace buzu kuma zaka koma" tsaki Arman yaja ya ce "matsalata dakai Maida serious magana wasa" washegari wajen 4 PM musa ya kawowa Arman abunda ya buk'ata Suka d'auki Hanya Suka nufi Arkilla quarters nesa da gidan sosai Arman ya ce "ya tsaya nan ya isa" Sannan ya amshi kayan ya ce Ka fita zan sanya a cikin mota"musa na mak'e dariyarshi ya fita kasancewar motar mai tinted ce hakan yasa cikin Sauri Arman ya cire kayan jikinshi ya mayar da kayan buzaye nan Duk da a k'yamace ya sanyasu amma idan ya tuna da A saboda masoyiyarshine saiyaji ma ya daina kamar kayan yana gama sanyawa tare da nad'in Buzaye bud'e motar yayi ya fito ai musa tunda ya Kalleshi yake kakkabewa da dariya hada rik'e ciki ,tsaki Arman ya ce "da yake mahaukacine ni da zaka dinga mun Dariya" Cikin Dariya musa ya ce "Sorry Abokina wlh shigarkace taban Dariya Sak ka fito wani buzu" tsaki ARMAN yaja ya ce "Bansan wulakanci lokaci na kurewa muje kawai ka rakani saida ya rakashi Har kofar get d'in sannan kuma ya juya da niyyar zasuyi waya duk yanda sukayi" Arman ya jima tsaye yana karewa unguwar kallo kafin ya fara knocking d'in get d'in gidan mai gadi ne ya fito tare da bud'ewa Karewa ARMAN kallo yayi ya ce "Malam lafiya" lafiya qalau Mai gidan yana ciki"Arman ya bashi amsa cikin muryar buzaye daya kirkira "eh yana ciki wa yake nemanshi"? ni nake nemanshi Dan Allah Ko zakamun iso da shi" Tsaf me gadin ya k'ara karewa Arman kallo ya ce "Ikon Allah yau kuma buzu ne a gidan Ya fad'a tare da shiga cikin gidan a lokacin Alhaji na palour yana Danna lapton mai gadi ya shigo ya shaida mashi yana da bako Okay ina zuwa ka shigo dashi Alh yafada tare da mik'ewa mai gadin na komawa yabawa Arman hanya ya ce " ka shigo"a hankali Arman ya shigo gidan daidai lokacin da Alhaji magudu ya fito da Kallon tsana Arman ya bishi dashi yana jin dama da dama da saiya kashe mutumin Chan da ya rabashi da masoyiyarshi Karasowa Alh yayi da mamaki yake kallon Buzun mutumin Tare da cewa "Malam lafiya" Dagowa da idanunshi Arman yayi ya sauke a na Madugu dak'yal ya iya yak'i da zuciyarshi yanda yakejin kamar ya Fard'o mutumin cikin muryar buzanci ya ce "Ina wuni Alhaji ni bak'one a garin nan ina neman Aiki ne ko da gadi ne indai zansamu inci insha shine kawai burina koda bansamu albashi ba" Kallonshi kasa da sama Alh yayi kafin ya ce "to nidai Gaskiya nan ina da ma aikata ina da mai gadi da masu bawa flowers ruwa driver ne kawai nake nema Wanda zai dinga kai iyalaina unguwa kai kuma banjin ka iya tuk'i " Cikin Sauri Arman ya d'ago ya ce "Alhaji ai na iya tuk'i" Kallon rainin wayau Alhaji yayimai ya ce "Kai dinne ka iya tuk'i ina ganinka a haka" wallahi Alhaji na iya tuk'i a aikace aikacen da nayi nayi driver kuma idan kana kokonto zaka iya gwadawa"Shidai Alhaji mamaki yake yaza ayi Ace buzu dayazo daga rugage ya iya tuk'i Dan son tabbatarwa mik'awa Arman key d'in motarshi yayi ya ce "Amshi ga mota ta Chan a parking space fiddomun ita ka kawo ta nan" Amsa ARMAN yayi yana hamdalar ya taka nasarar matakin farko cikin Sauk'i haka ko akayi yanda Alhaji ya fad'a haka ya fito da motar"Cike da farinciki Madugu ya ce "Eh Gaskiya ka iya tuk'i gashi cikin nutsuwa daga yau na d'aukeka Aiki duk wata zan dinga biyanka dubu talatin " Kasa da kanshi ARMAN yayi ya ce "Saidai wani hanzari ba gudu ba Alhaji bani da wajen kwana " karka damu akwai BQ zansa a share maka d'aki nan zaka dinga kwana"to nagode Alhaji Allah Kara budi"Arman ya fad'a zuciyarshi na mashi zafi "Karka damu yaro ai na yaba da hankalinka yanzu bari naje na fito da mutanen gidan na gabatar musu dakai sosai gaban Arman ya fad'i amma ya fisge Alh Yusuf na shiga gida ya shaidama su Hajiya saude ya d'aukar musu driver suje su ganshi Laila hada tsallen murna a lokacin Aira na mata kalaba Mikewa tayi ta ce " Sis taho muje Tare"B'ata fuska Aira tayi ta ce "kuje kawai ni basainajiba" Mama saude ce ta ce "a a a kema fa saikinje ai hakkin kine " Saude Da Alhaji saida suka fita tukwana Laila ta mik'ar da Aira suka fito Hakanan Aira tajita yanayinta ya sauya kallon Arman Hajiya saude ta yi ta ce "Alhaji ai wannan yayi nutsuwa Saidai naga kamar ba buzu ba kamar yafi kama da bafullatani" Gaban Arman ne ya bada daram Alhaji ne ya ce "inbanda abunki saude meye maraban buzu da Fulani sannan ya kalli Arman ya ce " wannan itace uwargina "Juyawa yayi ya kalli su Aira dake Tunkarosu tare da cewa " wad'anchan kuma Y'ata ce tare da Amarya"gabanshine ya bada daram daidai lokacin da ya d'ago idonshi ya sauka akan na Aira da itama shid'in take kallo karaf idanunsa suka sartse Dana juna" Rumtse idonshi Arman tare da budesu ya k'ara saukesu a nata jin abun yake tamkar mafarki sosai yaga ta k'ara mishi kyau Saidai kuma ta rame Aira ja tayi turus ta tsaya Inda take bugawar zuciyarta ya tsananta Ji take kodai mafarkine idan ba idon tane ya gane mata ba daidai ba Arman take gani da shigar buzaye gabanta Nunashi tayi da yatsa tana son magana mamaki ya gama cikata Duk kallonta suka tsayayi da mamaki sukace kin sanshi daman "Rumtse idonshi Arman yayi ya ce " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un shikenan Aira zaki ruguzamun plane da na jima ina shiryawa............✍🏿
Chapter 66 · 0% Book details