Sashe 43
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
......Wara idanu Aira tayi cike da firgice ganin Abba tsaye bayansu yana tab'i tare da jami'an tsaro Sosai ta firgita ba itaba hatta Arman saida ya tsorata Rugawa Bayan Arman Zatayi Abba yayi Saurin Fard'o hannunta Tare da d'auketa da gigitaccen mari rumtse ido Arman yayi ji yayi kamarshi Aka Mara cike da b'acin rai Abba ya k'ara wanketa da wani Marin Wanda yafi na d'azu durk'ushewa a wajen tayi tare da fashewa da kuka Kamar Wanda aka tsunkula haka ARMAN ya zabura tare da Fard'o Aira ya boyeta bayanshi idanunshi harsun fara sauya launi tsabar masifa cike da b'acin rai Abba ya ce "Kai harka isa ina yiwa y'ata hukunci ka boyeta Dan ban waiwayo kankaba "cike da b'acin rai Arman yace " na b'oye ta d'in wannan ai zalinci ne Idan ka daketa a Bayan idona wannan ban ganiba amma gaban ido na baka isa ka daketa na zuba ido ina kallo ba "cike da b'acin rai Abba yace " Tabbas ka haifu kome kamun bazanji ciwo ba saboda baka da tarbiya bacin b'atawa y'ata tarbiya da kayi shine har zaka nuna mata hanyar da zaku gudu to Allah ya Toni asirinku y'an iskan banza y'an iskan hofi sannan ya nuna Aira dake mak'ale a bayan Arman ba abunda take inba kuka ba ya ce "Ke kuma zaki gani zakisan ja da iyaye ba Abu bane me kyau y'an sandan ya juya yace " ku kama mun ita "Daya daga cikinsu yazo Zai kama Aira dake Bayan Arman wani irin bak'inciki da ya tunkarowa Arman Ai baisan sanda ya d'aukeshi da Mari ba cike da masifa ya ce " zanga ubanda ya isa ya D'auketa wlh duk Wanda ya k'ara attempting tab'ata zaku San asalin waye ni stupid kawai mararsa Aikinyi"Sosai y'an sandan sukayi luk'ui ba Wanda ya k'ara yunkurin tab'ata cike da b'acin rai Abba ya nunashi da yatsa ya ce "Harni ubanta?Harkai d'in Arman ya fad'a cikin k'unar rai" D'aukeshi Da mari Abba yayi Dagowa Arman yayi tare da rik'e kumcinshi yace "Ni ka Mara?An mareka d'in marar mutunci ko ramawa zakayi" Suka tsinkayi Muryar Mummy"duk kallonta sukayi musamman Arman dake mamakin me ya kawota wajen nan "Abba ko sosai ranshi ya b'aci cike da b'acin rai Mummy ta ce " ka basu y'arsu Arman kafin ka fuskanci fushina"Mummy Auren dole fa yake shirin yi mata mutumin nan baida tausayi ki barmu Mummy babu ruwanku munason junanmu koma ina zamu babu ruwanku"cike da b'acin rai Mummy ta ce "Arman Yayan mahaifin naka kake fad'awa haka?Shima Arman d'in cikin b'acin rai ya ce " shi Mummy baisan da hakan ba baisan da wannan alak'arba abunda yakemun ko Wanda bamu had'a komai dashi ba bazaiyi ba me yasa bazaku ganeba Mummy munason junanmu amma mutumin nan ya tsaneni baku tunanin irin halin da zamu shiga rabamu ba alkhairi bane"Cikin b'acin rai Mummy ta ce "nace ka basu y'arsu kai wani irin mutum ne y'ar ko ta gwal ce baka hak'ura da ita ba na fad'a maka ka rabu da ita me yasa baka da zuciya Arman " Kallon Mummy Aira tayi cikin kuka ta ce "Mummy please karkice haka Allah inasonshi Karku rabamu" Hawaye ne suka zubowa Mummy tamaza ta Goge ta ce "Kiyi hakuri Kibi umarnin mahaifinki zakifi ganin da kyau Aira ku hakura Da juna sannan ta dakawa Arman Tsawa ta ce " bazaka saketa ba baka ganin hankalin mutane duk yana Kanmu ko so kake sai mutane sun fara daukarmu "Cikin b'acin rai Arman ya saki Aira tare da kama hannunta ya wullata wurin Abba ya ce " ga y'ar taka nan idan ka tashi ka kasheta Sannan baka burgeba idan baka Aura mata Duka mazan duniyar nan ba"Rik'e hannunshi Aira tayi tana kuka Ya fisge hannunshi tare da barin wajen kamar zai tashi sama cikin Sauri Mummy ta bishi Dan tasan halinshi idan yana cikin wannan halin kome zai iyayi ruk'oshi tayi dak'yal ta samu ya shiga motar da sukazo da ita tare da escort d'inta Suka bar wajen Aira ko cikin b'acin Rai Abba Shima ya kama hannunta Tare da wullata cikin mota ya zagaya ya shiga ya tada motar Mutane harsun fara taruwa wajen danma y'an sanda sun rufe ba kowa ya fahimci abunda ake ba Aira harsuka isa gida tana kuka kamar ranta zai fita suna isa Zagayowa Abba yayi tare da Fiddota ya wullota nan ya hau ball da ita tsakar gida cikin b'acin rai masifa kawai yake ya ce "kin nunamun ban isa dake ba ,ni zaki wulakanta a idon duniya Kibi namiji hotel ku shirya guduwa Y'ar iska wulak'antatta marar mutunci biye biyen maza ne kika fara hotel hotel koshi D’an iskan naki nafi karfinshi bare ke " Sosai Aira ke kuka y'an ciki ne duk suka fito Jin hayaniyar Abba da kukan Aira dak'yal manya suka kwaci Aira daga hannun Abba ba k'aramun Duka yayi mata ba Mummy ko ko lek'owa batayi ba tana ciki ta na kuka Yayyinta da d’iyan yayyinta da suka zo daga agadez su suka dinga Lallashinta akan tayi hakuri ta fawwalawa Allah komai Aira ko Bayan ankwaceta d'akinta Mama a kayi da ita ba abunda take In banda kuka tana cewa "Dan Allah ku barshi ya kasheni wlh bana k'aunar rayuwar nan mutuwa ta kawai nake buk'ata Duk Wanda yaganta saiyayi mata kuka Cikin kuka Aysha taje ta duk'ursa gaban Abba tace " Dan Allah Abba kayi hakuri ka janye Auren nan wlh Aira na cikin wani hali"D'auketa da Mari Abba yayi ya ce "kika Kara zomun da makamanciyar maganar nan sainayi miki lilis bar ganin kinyi aure cikin y'ay'ana babu Wanda yafi k'arfina" Cikin kuka Aysha ta koma ciki rik'e da kumcinta da tasha Mari wajen Aira ta nufa ta Rungumeta Itama ta fashe da kuka cikinsu bamai Lallashin wani itama amma rungumesu tayi tana kuka Dak'yal aka samu suma wata yayar Mamy ta rabasu Ta dinga basu hakuri a ranar za ayi walima walimar da ba ayita ba kenan Dan gidan ya koma kamar gidan makoki wajen isha'i Abba ya shigo ya cewa Aunty Maryam a palour maza na baki minti goma kije ki amsomun wayar da suke communication dashi idan ta Bari kuma naje na amsa da kaina tasan sauran" "To Abba" Aunty Maryam na zuwa tace "Aira ki kawo wayarki idan akwaita a kaiwa Abba yace ya shigo ranki zai b'aci " cikin kuka Aira tace tana d'akinmu cikin kayana dukansu ki kaimai"ta k'arasa fad'a tana kuka"Aunty Maryam na zuwa Inda Aira ta fad'a mata nan ta samu wayoyin tana zuwa a palour tace "ga su Abba" Kallon wayoyin Abba yayi tare da amsa ya kalli Mamy ya ce "kalli wayoyin da take rikewa a boye ke da kike d'aure mata dukanku harke zanyi maganinku" Sannan ya tarwatse wayoyin sukayi ratsa ratsa "Mummy ko tsaki taja batare da tayi magana ba abun duniya duk ya ishi Mamy Abba na fita ta tashi ta dauki mayafinta tare da ficewa ta dauki mota kai tsaye gidan Yayanta Wanda ya rik'eta ta nufa tana kuka ta ce "Dan Allah Yaya kaje ka samu Alhaji ka mashi magana kila kai yaji maganarka Dan Allah kar a d'aura Auren nan " Yayanta Alhaji Safiyanu dattijone Shima Dan zai wuce sa annin su Abba ba kamarsu daya da mamy shima dukda ya fara manyanta ya ce "Gaskiya zan fad'a maki Rahama kiyi hakuri mijinki ya dau zafi baki saniba ni kaina na sameshi munyi magana dashi ta fahimta Duka ya fad'amun abubuwan da take da kuma dalilinshi na Aurar da ita a Gaskiya ko nine iya hukuncin da zan yanke mata kenan Aurar da ita y'arki batajin magana Rahama Duka abubuwan da tayi bana kyalewa bane kawai dai Auren tsohon ne ba dad'i amma tunda shi mahaifinta ya yanke hukuncin da ya yanke me zaisa bazaku hakura ba Kuyi mashi biyayya tunda dai shine mahaifinta ku mata kuna da matsala wlh ku kuke d'aurewa y'ay'anku gindi suke lalacewa sai abu yazo yafi k'arfinku kuzo kuna kuka da idanunku kuna sharrin shed'anne bayan y'ay'annakune shaid'anun kuzo ana lik'awa k'addara tabbas akwai k'addara amma kaddara tana tarda hali Allah yace tashi in taimakeka ko saikije ki aje kud'inki a kasuwa ki tafi ki barsu kice Allah zai tsare to kamar hakane ku da kanku ya dace ku dinga tsawatarwa y'ay'anku idan sunyi ba daidai ba yana da kyau y'ay'anku ya kasance suna shakkarku to nidai indai na isa dake karki k'ara daga maganar nan ki sanyawa Auren nan Albarka kawai kinji abunda na fad'a maki" cikin kuka ta ce "Yaya ni ban d'aurewa y'ata gindi ba maganar gaskiya ce yaya tana da wanda takeso suna san junansu kuma d'an uwanta ne yaya kasan komai fa yanzu haka fa yau inbanda Allah ya taimaka dafa sun gudu wani hali kake tunanin zasu jefa kansu da ace sun gudu d'in" d'aga mata hannu yayi ya ce "duka nasan komai Ya fad'amun ba a hotel aka gansu ba ni kaina na so ace d’in wanda take so d’in aka bata amma tunda mahaifinta yace bayason alak'arta dashi me yasa bazasu hakuraba tayiwa mahaifinta biyayya kika sani kila sanadin biyayyar da tayi mashi Allah ya daidaita tsakaninshi da d'an uwanshi ko kuma ya sanya ya hakura kinsan dai ba ayiwa iyaye biyayya a tab'e Bansan ki k'aramun maganar komai Rahama y'arki bata da gaskiya abubuwan da take ba daidai bane ga al'adar mu mu hausawa harma a musulunce dan haka Aure shi yafi dacewa da ita Tsohonma idan yaro ya gagareka wanda ya fishima saika Auramai da dai d'a ya daukomun magana hukuncin mahaifinta yayimun daidai kawai inda bai Kyauta ba da baya bin komai a hankali fushi ne kawai matsalarshi ‘’Goge hawayenta Mamy tayi tare da tashi Ta ce " saida safe yaya " Kinji Haushi na dan na fad'a maki Gaskiya ko Rahama"girgiza kai tayi ta ce "a a yaya zantafi ne nabar bak'i "girgiza kai yayi ya ce" sannan itama Hajarar ki yi mata nasiha kinji gobe idan an d'aura Auren zanshigo na ganta"To"tafada tare da saurin ficewa daga palour duk Haushi ya kamata yayannata ma da take tunanin zai huce mata takaici shima ga abunda yake fad'a Cike da takaici Mamy ta koma gida sannan kuma tana nazarin maganganun Yayan nata. Arman har suka isa gida