← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 127

Sashe 9

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aira tafada ta na nufar d'akin Mama da Mamy duk ta fad'a musu zuwan su ya Umar a tare suka fito su Mamy na musu barka da zuwa Suka amsa cikin sakin fuska har khadija Dan Duk iskancinta bata fiya yiwa su Mama da Mamy ba khadija ce Ta amshi jaririn hannun Mamy tare da yiwa Mamy barka tace " Allah raya "nan Shima ya Umar yayima Mamy barka Daman sunji haihuwar ne yasa suka taho Aira ganin Mamy da Mama sun d'auki hankalinsu ya Umar yasa tayi saurin fita ta nufi part d'in Inna.

bedroom d'inta ta shige tare da rufewa ajiyar zuciya ta sauke ta ce " yau na tsallake rijiya da baibai da Mamy ta fad'awa Abba Aida na shiga ukku"kiran Yaya Arman tayi kamar zatayi kuka ta fad'a mashi komai kuma Mamy ta ce Wai na maido maka wayar ta fad'a kamar zatayi kuka".

Daga bangarenshi ya ce "bana kyauta a maido mun Kuma bana kyauta na amsa ko wani nayiwa bare ke Dan haka karma ki maidomun " To yaya ta ce fa Ta Kara ganinta Fasa ta zatayi kuma ina tsoron karta Fad'awa Abba "Arman duk Haushi ya isheshi yana jin haushin yanda iyayen Aira ke nuna mai kamar ba Wanda bai had'a komai da ita ba kamar ba kanwarshi ba Mamyn ma da yake ganin dama dama a Wajenta itama nema take ta kwatsa" .

Ya fada cikin ranshi a fili ko tsaki yaja baimasan yayi ba ya ce "Kinji dai abunda na fad'a sanin kanki ne bana magana biyu ta rage ruwanki ko ki yadda ita ko kiyi sadaka da ita ko ki fasata komai kikayi taki ce Dan haka karki k'aramun magana akan dukkan wani abu da zan baki ko na baki hope kinfahimta " Cikin sanyi Aira ta ce "Na gane Yaya yi hakuri Bazan sake ba nasan ranka ya b'aci Naji kamar kana fad'a "saiyaji ta d'an bashi tausayi yasan halinta Sarai akan wannan D'an abun saita yini ta na kuka hakan ya sashi kwantar da murya ya ce .

" raina bai b'aci ba my cutie yaya za ayi my Aira ta ta b'atamun rai Y'ar lele na ai bakya laifi "Ajiyar zuciya ta sauke ta ce " Uhm "Shima Uhm" din ya mayar mata yana mata Dariya ita ma dariyar tayi tanajin sanyi Cikin zuciyarta "ARMAN ne ya ce " Naga hoton k'ananmu yayi kyau naga ma kamar yaso ya sato kamannin my cutie d'ina kodan ya samu ya d'anyi farinjini wajen y'an mata ammafa my Cutie d'ina ta fishi kyau nesa ba kusa ba .

"Dariya Aira tayi sosai ta ce " Allah my yaya kace na fishi kyau"Eh mana ki daina hadamun kanki dashi ma "Dariya tayi ta ce " kai yaya Shima fa yana da kyau sosai"idan babu ke ba amma idan Dake musamman kuka Kara fuska mummuna zakiga ya koma kin manta Kyanki dishe kyan wasu yake "Dariya tayi sosai ta ce " to ni da kai kuma wa yafi kyau"Shima murmushi yayi ya ce "Ni mana Aini na taimaka maki da har kyan naki ya fito idan ba haka ba Ai kema kyan naki da baikai haka ba nine na taimaka maki"

Cikin shagwaba ta ce "Kai yaya wlh nafika kyau" Dariya yayi sosai take burgeshi idan tana shagwaba hakan yasa ya biyeta sukayi ta gardama yana mata Dariya saida suka kwashe kusan awa Ukku suna waya batare da sun gaji da Hira ba daga karshe ma Video call suka koma Dan yau Arman baida aiki yana gida Nan Aira tayi tamai labari Dan rufo d'akin ma tayi Dan kar wani ya shigo ko da zasuyi salla kin kashewa sukayi kamar suna tare Ranar haka suka yini Dukansu sai farinciki suke Dan Aira harta manta ma da Maganarta da Mamy koda zasuci abincin dinner tare sukaci Shima ya zubo nashi ita ma ta zubo nata suna ci suna kirga spoon Din da kowa yayi ta waya dukda basu da cin abinci sosai ranar saida sukaci sosai.

har wajen 11pm suna video call idan zatayi wani abun taje tayi ta dawo Shima haka Saida yaga bacci ya d'auketa murmushi yayi yana kallonta ta waya Yajima yana kallon yanda take baccin yana karajin sonta na ratsa kowani sassa na jikinshi saida yaga wayar ta birgima Alamun baccin nata yayi nisa tukwana ya kashe ganin baya ganinta ranar dukansu kwanan farinciki sukayi batare da tunanin wata damuwa ba.

Ana jibi suna Aira na bangaren Inna wajen la asr ta fito ta nufi bangarensu tana shiga taga Yaya Aysha na fitowa daga mota driver na fito mata da akwatinta Aida gudu Aira ta Ruga ta Rungumeta Itama Aysha Rungume kanwar tata tayi cikin muryarta mai cike da iyayi ta ce "I really miss you my Fav sis " Itama cikin murna Aira ta ce Miss uh 2 my Fav Aunty da bakinan gidan ba dad'i nafi kowa rashinki "Murmushi Aysha tayi ta ce " Ai yanzu nadawo Sis mundaina Rashin juna ko"Gyada mata kai tayi ta na amsar hand bag d'inta ta rik'e mata Aysha tabs driver umarni ya shiga da akwatinta ciki tana dafe da Aira suka nufi haryar ciki Sai murnar ganin y'ar uwar tata ta ke Aira ta ce "Aunty Ya malesia d'in wai kina nufin harkun gama karatun gaba d'aya " Alhmdllh sis karatu kam mun kammala sai Kuma bautar Kasa burin Abba yau ya cika "Cikin murna Aira ta ce " Wow congratulations sis ta fad'a tana Kara Rungumeta Itama Rungumeta tayi ta ce "Thnks my sis yanzu kuma saura ku munyi waya da Ummy ai kwanaki take fad'amun kun kammala s s c e d'inku sai jiran result.

" Wlhko Aunty mungama kai wlh Aunty Ummy bata da kirki duk lokacin da nace mata ta had'ani dake ko a waya Ne wlh kiyawa take Dana dame ta ma cewa tayi "karna k'ara damunta tunda ba waya ta bace nima nayi zuciya nasayi wayar kuma wai kinma sauya layi itama bata dashi" Dariya Aysha tayi ta ce "Kai Ummy ta na nan da halin nan nata kenan Wai har yanzu Abba bai baku waya ba ki ce dai har yanzu tsautsatsauran ra ayin nan na Abba na nan na Sai an Je university idan yanzu baku fara rik'e waya ba fisabilillah yaushe zaku rik'e Baku sanin halin da duniya ke ciki Gaskiya Abba yanzu An waye y'an 10 years ma suna rik'e waya bareku ".

murmushi kawai Aira tayi batace komai ba shiyasa duk yayyinta tafi son Aunty Aysha jininsu yazo d'aya sosai ga tana mugun sonta tana tunanin yanda Aysha ta k'ara wayewa Dukda daman a waye ta tafi amma k'asar wajen nan da taje karatu ka k'ara kilewa....✍🏿

*Share plx*

*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[6/1, 22:52] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️...............19&20

Suna isa a palour suka tarar dasu Mamy da gudu Aysha taje tayi hug d'in Mamy da Mummy tana musu iyayin tayi missing d'insu Mamy na murna tana mata oyoyo" Sai sannan Aysha ta lura da mutanen dake palourn wasu baki ta gaishe su Ganin jariri a hannun wata ya sanya ta kalli Aira ta ce "Sis wa ya haihu" .

Mamy Airata bata amsa "wow Kice nazo A daidai Allahsa dai ba ayi suna ba Kuma shine ko a fad'amun sannan taje ta amshi jaririn tace " wow ammafa yaso yayi kama da sis Aira "Haka kowa yakecewa Cewar Mamy Mama ko Kallon Aysha kawai take da shigar dake cikinta K'ank'anin kaya ne jiens da Riga danma bata da jiki hakan yasa basu d'ame ta ba ga wani uban glass da ta dageshi saman goshinta .

Aysha black beauty ce tana da kyau ba fara ba ce Amma bata da bak'i sosai irin choculate colour d'innan amma daga ganinta kasan akwai iyayi da malle " ita Mama duksai kunya ma ta kamata Ganin da mutane itako Aysharma ko a jikinta hakan yasa Mama ta fara aika mata da Harara ganin batasan da ita ba yakeba ya sanya Mama kyaleta saida tagama iyayinta tukwana taja Aira sukayi Bedroom d'insu .

koda su Ummy da Amma suka ganta suma sai murna suke suna daka tsalle suna murnar ganinta Aira tace "Su daina karsu b'alla mata yaya" suna haka Mama ta shigo ta kalli Aysha ta ce "Ke yanzu Aysha ba kunya haka kika ketaro tundaga wata k'asa kikataho a haka kamar ba y'ar musulmi ba " Aysha na tubure fuska ta ce "Haba Mama daga dawowata Ko Sannu da zuwan kirki fa bakimun ba zaki fara mun fad'a me shigar nan tayi kuma" .

Mama ta girgiza kai ta ce "Ai daman Nasan sai Abunda yayi gaba a nan ma ya aka k'are bare anturaki wata k'asar da ba uwa ba uba ba mai tsawatar maki dole likkafa taci gaba shiyasa tun farko banso Alhaji ya tura ki wata k'asa karatu ba to wlh mu nan ba Chan bane Dan haka kar in Kara ganin kinyi wannan shigar kinfito wannan shigar ko tsakar gida Inda kunya kinyita bare waje idan kin gama hutawa kije abincinki na dining Mama ta fad'a tare da barin d'akin.

Aysha gunguni tayi kasa_kasa saida Mama ta fita ta ce " Aifa nadawo wlh su har yanzu sunk'i su waye mu Chan ba ruwan wani da wani ina laifin wannan shigar ta fad'a tana tab'e baki "(nikam hajjo nace ikon Allah Ayshar nan za Aje da ita ).

Bayan ta fito daga wanka ta shirya cikin Wata doguwar Riga (Abaya)mai shegen kyau maron kallonta Aira tayi ta ce " Wow My Aunty kinyi kyau"Lakutar kumatunta tayi ta ce "Thnks kanwa Sannan ta fiddo wata irinta ta mik'awa Aira ta ce " ga taki nan daman tare nayi mana Anko ki shirya kafin na gama cin abinci zamu fita outing ".
Chapter 9 · 0% Book details