Sashe 74
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 10 min read
.....Na yafeta a cikin y'ay'ana sannan koda wasa na sameta a cikin gidan nan ta shigo naga akwai sa hannun wani cikinku wlh zakuyi mamakin matakin da zan d'auka kowaye Shima Saidai ya bita hatta mahaifiyarta"kowannensu idan ka kalleshi zakasan yana cikin tsananin tashin hankali musamman Mamy cikin tashin hankali ta ce "Me kuma tayi Alhaji na shiga ukku ni Rahama " Ai zakiji kome tayi "Inna ce ta mik'e ta ce " Amma wlh habu baka kyautaba Kazo ka zauna ka dinga tsinewa y'arka To tukunma me tayi "Ban tsine mata ba Inna na bartane da duniya Sannan Abunda tayi ba abunda Zan d'aukeshi bane ciki taje dashi gidan Aurenta" Cikin tsananin tashin hankali kowa ya mik'e kamar sun had'a baki wajen fad'ar ciki?Tabbas ciki Jiya da Daren mijinta ya kirani yake shaidamun Sunje Asibiti bata da lafiya likita ya shaida musu Cikine da ita harna wata hud'u kuma ba nashi ba saboda ba abunda ya shiga tsakaninsu sannan Bikinsu kowa ya duba invitation yasan wata ukku ne Sannan Yaron nan Arman ashe Had'in baki sukayi ya bita Gidan a matsayin Driver suke cigaba da mu amula dashi karshe dai ya ce sun kamasu a d'aki Wanda Dalilin hakan ya sanya ya saketa saki Ukku Bayan Arman d'in ya tabbatar mashi shi yayi mata Cikin shine ita kuma ta bishi to shiyasa na yanke wannan hukuncin daga yau ko ambatar sunanta kar a k'ara mun a gida "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un kawai suke Ambata sosai kowa dake wajen yayi mamakin irin abunda Aira tayi musamman Mamy da takejin zuciyarta kamar zata rabe gida biyu Aisha ko ba abunda take inbanda kuka haka Amma mamy ko cikin k'arfin hali Ta ce " Sakayyar da Aira zakayimun dashi kenan ta kyauta ta cika y'a tana gama fad'ar haka ta shige cikin d'akinta tayi tagumi sosai take hawaye tanajin zafi da rad'ad'in abun Tabbas Aira ta kunyata k'untatawa.mafi muni kuwa ai yanzu kuma bata da bakin magana a cikin gidannan innako Salati ta rafka ta ce "Na shiga ukku ni Halima cikin Shege a gidannan Amma mujahid Anyi lalatacce daman saida ya lallaba ya kumsawa yarinyar nan Ciki Goge hawayenta tayi tare ciro wayarta cikin Dan tofi Haidar ta mik'awa tace amshi maza maza kiramun Kabir " Amsa Haidar yayi a sanyaye ya kamo mata number Daddy saida yaga ta fara ringing tukwana ya mik'a mata ta k'ara a kunne Daddy na d'auka cikin Masifa ta fara cewa "Kabir ina Mujahid" a lokacin Daddy na tare da Mummy a palour Dan hutawa yau ya ke ya ce "Inna Mujahid kuma ai rabona dashi anfi wata " Eh Mujahid duk Inda yake ka nemo munshi wlh bai isa ba munafuki ina ganinshi kamar mutumin arziki ashe da abunda ya taka Saida ya yi yanda yayi ya kumsawa yarinyar nan Ciki ai wlh bai isa ba ya maidomun jikata duk Inda ya kaita ko inyi rashin mutuncin da na jima banyiba "Cikin tsananin tashin hankali Daddy Ya ce " Inna wace yarinyar kike maganar yayiwa cikin ?yo wa ka sani mana idan ba Hajara ba tunkan ayi Auren ashe da ciki taje bai kyaleta ba a haka ba saida ya bita har gidan Aurenta shiga d'an iska yaje a matsayin matuki yaje ya dinga nanikarta har saida mijin suka kamasu karshe dai ya kashe mata Aure kuma ya gudu da ita to wlh Kaine ubanshi saika nemo munshi Tare da jikata zan nuna masa na fisa iya shak'iyanci "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un kawai Mummy da Daddy ke furtawa Dan hands free Wayar take taji komai kashe wayar Daddy yayi ya ce " Kinji abunda d'anki ya aikata ko?Keda kike d'aure mashi Ga abun kunyar da ya aikata mana to wlh kisani daga yau babuni babushi dukda shi kadaii na Haifa na gwammace nayi rayuwa batare da kowaba sannan duk Inda Yake zansa a kamasu sainasa an rufeshi Su kuma ya maido musu y'arsu sosai Daddy Ya shiga Surfa masifa Mummy ko hawaye kawai take tana Nazarin Arman bazasu aikata haka ba Saidai ance ba a yabon d'an kuturu duk irin masifar da Daddy yayi mata tanka shiba saboda ance d'an goruba mai jawa uwarshi jifa Dan har ita Daddy Ya hada yake surfawa masifa Saida ya gama tukwana ya fara kiraye kirayen Airport tare da tura hoton Arman ya ce da sun ganshi su kamashi sannan ya Ce har gidan nashi na Abuja zansa Aje Duk iskancinshi zan nuna masa k'arshenshi Mummy ko sosai tashiga tashin hankali ta ce "Alhaji karkayi haka karkasa a kama d'anka idan rai ya baci hankali baya gushewa " Daddy baima kulataba sai barin d'akin da yayi cikin tsananin tashin hankali Mummy ta shiga cikin d'akinta Tare da janyota wayarta number Arman kawai take Kira amma a kashe Tana hawaye tayi ta tura mashi text kala kala dukta rude Hankalinta duk ya k'ara tashi Dan bazata juri A rufe mata d'a a banza ba Dan ta lura Daddy da gaske Yake kuma idan yayi irin wannan kafiyar Babu mai tankwarashi hakan yasa hankalinta tashi gashi duk ta kira layukan Arman Amma a kashe zama tayi bakin Gado tare da tafka uban tagumi Tana hawaye.
Arman koda ya dawo bacci ya tarar da ita tanayi Wanda hakan sosai yayi mishi dadi Take away d'in da yayo mata ya Aje tare da maganin ya nufi bedroom d'inshi yaje yayi wanka Bayan ya fito ya shirya sosai yayi kyau cikin Dakakkiyar light blue din shaddarshi sai maiko take d'akin Aira ya koma yaga har lokacin Bacci take zaunawa yayi kan sopar Dake gefen gadon tare da kafeta da idanu bako k'iftawa wutar sonta na k'ara fisgarsa Yakai one hour yana kallonta sai wajen la'asr ta tashi A hankali take bud'e idonta ta saukesu a nashi murmushi tayi mishi Shima ya mayar mata Brush taje tayi shiya taimaka mata taci abinci tukwana tayi Salla maganin da ya sayo ya b'alla mata tana Yatsine fuska ta sha kallonta yayi ya ce "To ya jikin naki? Dasauki yanxu banajin zazzabin Saidai ciwon ciki Kad'an " Insha Allahu Shima zai daina dia Allah ya k'ara miki lafiya"Ameen Aira ta fad'a tana jingina kanta ga jikin gadon Wayarshi Arman ya lalubo ya ce "Kinga Tunda mukazo ban kira musa ba na shaida masa mun Iso lafiya Nasan yana ta nema na bari na kira shi ya fad'a yana bud'e wayar Yana bud'ewa yaji text message na shigowa Rututu daga sama kuma yaga number Mummy ce message d'in farko ya shiga Inda ta rubuto'" Son ka bud'e wayarka zamuyi magana dakai Dan girman Allah"Na biyun kuma ta ce "Arman ka taimakeni indai naci darajar haihuwarka da nayi ka kirani akwai matsala Arman " Na ukkun kuma ta rubuta"Na hadaka da girman Allah Arman idan na kiraka ka amsa kirana nasan duk kiran da nake maka kwanaki kana gani kake kin d'auka wannan Karin muddin baka daukaba zanyi fushin da..bai k'arasa karantawa ba yaji kiranta cikin Sauri Arman ya d'aga cikin damuwa ya ce "Mummy kina Lafiya" nauyayyar Ajiyar zuciya yaji Mummy ta sauke wanda har a waya saida yaji ta ce "Ba lafiya ba Arman kuna ina kaida Aira ?Kallon Aira yayi da hankalinta na kanshi ya ce " Muna Abuja Mummy please karki fad'awa kowa"Cikin Sauri Mummy ta ce "akwai matsala ka maza ka d'auketa Kushiga Mota ku tafi Adamawa Karku sake Kuhau jirgi Daddynka ya sanya a kamaka sannan har nan Abujar ya sanya azo gidanka sannan ka sanya face marks yanzunnan ba sai gobe ba ka maza ku tafi Adamawa gidan Mahaifina Zan sameku a Chan ko zuwa gobe ne" Cikin marairaicewa ya ce "Mummy Dan Allah ba wani shirin kukayi mana ba baso kuke ku Kara rabamu ba"ba Numfasawa Mummy tayi ta ce " Arman ba ka yarda dani ba kenan Babu wani shiri da na shirya wlh ina son kawo karshen matsalar nan ne Kayi abunda nace maka yanzunnan cikin gaggawa"To to Mummy yanzu zamu tafi nagode ya fad'a tare da Kallon Aira ya ce Cutie maza ki shirya Adamawa zamu tafi"Adamawa kuma Yaya wajen me"yanzu Mummy ta kirani ta ce "Muje Chan itama zataje karmu tsaya bata lokaci tashi mu tafi " a sanyaye Aira ta mik'e tare da sanya Hijab d'inta ta ce "Muje Yaya" Makullin motarshi mai tinted ya d'auko Suna zuwa parking space ya bud'e mata gaba tana shiga ya zagaya yaja motar Horn yayi mai gadi ya fito Cikin Sauri ya bud'e Zage glass din motar Arman yayi ya ce "Duk Wanda yazo nemana karka shaida musu nazo garin kace rabona da gidan amfi wata hud'u kuma wlh ka sake ka fad'awa wani nazo gidan nan nadawo a bakin aikinka" Yana gama fad'ar haka ya zuge Glass din baijirama amsar mai gadin ba ya figi motar a guje Sosai Arman ya dinga sharara gudu Suka d'auki hanyar Adamawa a lokacin hud'u Harta gota sosai suke sharara gudu Wanda Aira a lokacin zazzabinta ya dawo sunyi nisa sosai taji Tanajin Amai Kallonshi tayi cikin k'arfin hali tace Yaya "Amai nakeji" tsaida motar yayi tare da bude mata Ta sauke kafafunta waje nan ta shiga Yin aman saida ta gama tukwana ya mik'a mata ruwa ta kuskure bakinta Tare da wanke fuska Kallonta yayi ya ce Sannu Allah baki lafiya"gyad'a mishi kai tayi ta ce "Amen yaya " Fitowa yayi tare da rik'eta ya mayar da ita back sit tare da kwantar da ita saman kurerar ya ce "Ki kwanta ki huta" gyada mishi kai tayi Dan daman hutawar take buk'ata shi kuma ya zagaya ya koma Tare da tada mota ba ayi minti goma ba bacci ya d'auketa tafiyar awa Hud'u sukayi Karfe 8pm tayi musu a garin Adamawa Wanda sai lokacin Aira ta tashi Sannu yayi mata ta amsa da yawwa tare da cewa "Amma yaya munyi Sauri harmun Iso kenan " Murmushi ya sakar mata ya ce "Kina baccinki ai dole kice Munyi Sauri tunfa biyar kike bacci " Wara idanu tayi ta ce "Kaiii Ammafa nasha bacci shiyasa da na tashi Naji ba ciwon kan" Koda suka isa gidan Wazirin Adamawa mahaifin Mummy kenan a bakin get d'in gidan yayi parking Ya fita itama Aira bud'ewa tayi ta fito tare da Kallon get d'in da bangon gidan an kawatashi da zanen sarauta tundaga get d'in gidan Har bangon gidan irin na al'adarsu kama hannun Aira yayi ya ce "Muje ciki" A tare suka shiga cikin gidan Wanda Aira sai kallon gidan take tana kallon yanayin tsarin gidan sosai ya burgeta Kai tsaye bangaren Mahaifiyar Mummy Hajiya Zaituna Arman ya nufa da ita ita dai Aira na biye dashi da Sallama suka Shiga palourn Kallon y'an d'akin Aira tayi tsohuwace d'aya sai y'an mata guda Ukku"Cike da farincikin Ganinshi Hajiya Ta Mike tace "lale marhaban mai Gidan " murmushi Arman yayi ya ce "Tsohuwar daman baki gangara ba har yanzu?Uwaka ce zata mutu bani ba ja iri ta fad'a tana tashi tare da kamo hannun Aira ta ce " Sannu da zuwa kishiyata kunshawo hanya"ta fad'a tana zaunar da Aira gefen ta"K'asa da kanta Aira tayi ta ce "Ina yini Mama" Lafiya qlau y'ar nan ki saki jikinki nan d'in gidankune kinji"gyada mata kai Aira tayi y'an matan dake wajen ne suka gaishe da Arman ya amsa a takaice d'aya daga cikinsu ce ta kalli Aira tare da cewa "Wow waida tare kuke da Auntyn tamu yaya Ita ce ko?Harara Arman ya maka mata bata damuba Dan tasan Halin sauran ne suma suka kalli Aira sukace wow she's beautiful Yaya Gaskiya ta had'u Auntyn tamu ta fad'a Tare da zuwa ta zauna gefen Aira Ta kama hannunta ta ce " Sannu da zuwa Auntynmu ansha Hanya ya gajiya"Murmushi Aira tayi mata cike da kunya ta ce "Alhamdulilla" Sauran biyun ne suka mik'e D'aya ta je ta janyo hannun Aira ta ce "Muje ciki ki huta Karki biyewa tsohuwar nan ta k'ara miki Gajiya " ta fada tana kama hannun Aira dukansu sukayi cikin wani daki da ita Ja irai Hajiya tafada tare da kallon Arman ta ce "oh ni Mujahid yaushe rabonka da garin nan........✍🏿