← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 127

Sashe 70

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 10 min read

_*miss hajo_*🤙🏿
[7/5, 22:01] Hajo hajo: 🅿️.........*83&84*

.....A guje suka bar gidan Aira har tsoron gudun da ya sharara tayi Sun d'an bar layin taji ya tsaya ba tare da ya kalletaba ya ce "Dawo gaba" A sanyaye ta fito ta koma gaba tare da rufe k'ofar Kallonshi tayi taga yanda ta had'e girar sama da ta kasa a hankali ta ce "Ina yini Yaya" Ba tare da ya kalletaba ya ce "Lafiya" Cike da nuna Rashin jin dad'i ta ce "Yaya ko nayi maka wanin abun naga kana b'ata rai" Kallonta yayi yaga yanda tayi bala in kyau lokaci guda yaji tsananin kishinta na k'ara ninkuwa cikin zuciyarshi tab'e baki yayi ya ce "Shine Dan ki nunamun kinyi Aure hada Fitowa hannunki mak'ale da nashi ?Cikin marairaicewa ta ce " Yaya nima bani nace ya rik'emun ba Bafa kuma nima banso ya rik'emun hannuba abunda yasama na Kyaleshi Dan Karya hanamu fita"Uhm kawai ya ce Tare da lalubo Wayarshi itadai Aira ta zuba mashi idanu bako k'iftawa Dan idan tana Kallonshi ji take kamar za a kwace mata shi Arman musa ya kira yayi mashi kwatancen Inda suke Ya shaida mashi gashinan yana kashe wayar kallon Aira yayi da ta zuba masa idanu hura mata iska yayi a idanu tare da cewa "wannan kallo haka ai saiki cinyeni" Firgit ta dawo cikin hankalinta tare da turo baki ta ce "Kai yaya saikace mayya" Zan Bugi bakin fa"Dariya tayi ta ce "Sorry my yaya" kinyi kyau cutie"Murmushi tayi tare da K'asa da kanta ta ce "thnks kaima kayi kyau my yaya " sosai suka shiga hira da labarai Wanda har saida ta mantar da Arman haushin da yakeji a haka musa ya samesu Kallon Aira yayi ya ce "Amma fa Gaskiya Kin rikitamun aboki da yawa kin zautashi Kotu ta kamaki ba k'aramun hukunci zata yanke maki ba " murmushi Aira tayi tare da K'asa da kanta "Kallon Arman yayi ya ce " Ammafa Abokina ba k'arya dole ka zauce ko nine na samu wannan zanyi abunda yafi naka"Wata irin harara Arman ya banka masa tare da cewa "ka iya bakinka wlh Wama yasa ka kallemun ita Dan sa ido kawai " Dariya musa yayi ya ce "Maida wukar yanzu dai ina ne za a Naji kiran gaggawa" wajen shakatawa za a kai cutie to kasan bansan ko ina a garin nan ba shine na kiraka ka mana jagora"Musa yayi musu rakiya duk wani wajen shakatawa yayinda Arman yayi wulli da kud'in da Alh Madugu ya bashi akan yayiwa Aira sayayya itadai Aira batace uffan ba Dan Tasan halin kayanta saida lallamo sosai suka shakata suka sha love d'insu kamar saurayi da budurwa Sune basu koma gida ba sai wajen isha'i sosai Aira take nishad'i Suna komawa Aira ta fito tana Dariya Shima Arman ya fito yana fara'a Daidai lokacin da laila ta lek'o da mamaki take kallonsu Sosai gaban Aira ya fad'i Arman ko fusgewa yayi cike da fargaba Aira ta nufi Inda Laila take ta ce "Ina zuwa sis" Bako ina Laila ta bata amsa tare da komawa ciki tana tunanin Me ya maida Aira gidan Gaba ?sannan tunda tazo bataga fara'arta buzu ba (Dan haka suka samai suna saboda basusan sunanshi ba Kuma babu Wanda ya tambayeshi game da sunanshi ko Tarihin shi) amma yanzu shine ta gani yana Dariya sannan tunda aira tazo garin nan bata taba sha'awar fita wani wajeba sai zuwan buzun nan zuciyarta chunkushe da tunani Aira ko tabe baki tayi tashigewarta Takoyi sa a Daddy bayanan tun daga lokacin nan Laila ta sanya musu ido Yayinda su kuma harkar gabansu suke ga kirkirar zuwa shopping ko saloon da Aira take tarka Wanda Daddy yake sanya Arman ya kaita sosai sukeshan love d'insu batare da sanin kowaba amma kuma ko hannunta yanzu arman baya yarda ya taba saboda yasan haramun ne tunda da igiyar wani a kanta ko rungumarsa tazoyi kaucewa yake hakan yasa itama tadaina yunkurin fadawa jikinshi Wanda Laila duk tana ankare da hakan hakan yasa yanzu sama sama takeyiwa Aira itako hakan bai dameta ba saboda yanzu Arman ya maye mata gurbin kowa data rasa hakan yasa hankalinta kwanciya a haka har Arman yayi wata guda a gidan yau Aira tana d'akin Arman suna ta shan Hira har Sha biyun dare tayi batare da sun sani ba saida suka Ankara tukwana Aira ta baro BQ din cikin sand'a ta shiga cikin gidan Kichibus sukayi da Laila dake kokarin shiga kitchen Dan harta kwanta bacci taji yunwa hakan ya sanyata zuwa ta had'a tea Sosai cikin Aira ya d'uri ruwa cike da Kallon tuhuma Laila ta bita ta ce "Daga ina kike da Daren nan ke kuma" Cikin muryar Rashin Gaskiya Aira ta fara in ina saikuma ta ce "Uhm mura ce ta kamani wlh shine na D'an lek'a na ga ko naga Wanda zai sayo man magani" tunda ta fara maganar Laila tasan karya take tab'e baki tayi ta ce "hmmmmmm " Tare da shigewa kitchen Aira ko tsaki taja tare da Wucewa d'akinta Tana zuwa ta iske Alh Yusuf sai safa da marwa yake Sosai ta tsorata Juyowa yayi cikin b'acin rai tare da daka mata Tsawa ya ce "Daga ina kike" Sosai Aira ta rude cikin in ina tace ba ko ina yanzu na fita fa"na kusa awa d'aya a d'akin nan shine zakicemun yanzu kike fita daga gidan ubanwa Kike"Ganin ya na hayayyak'o mata ya sanya ta murgudamai baki tare da Jan tsaki Saurin Juyawa da gudu tayi bedroom d'in Laila kallonta Laila tayi ta ce "Lafiya kuwa" rufo d'akin tayi ta ce "Nan zan kwana tare da nufar gadon ta kwanta" Mamaki duk ya gama cika Laila Tab'e baki tayi tare da Gama shan tea d'inta itama taja ta kwanta a lokacin Bacci har ya d'auki Aira washegari koda ta tashi bataga Laila ba fitowa tayi a palour ta tarar da Mama tare da Daddy da ya kura mata Idanu kasa tayi da kanta ta ce "Ina kwana Mama" ba yabo ba fallasa ta amsa Da lafiya Qalau"Kallonshi tayi ta ce "Ina kwana" Lafiya qalau my Beauty Kintashi lafiya"Harara Mama ta gallamai tare da Jan tsaki Aira ko alhmdll kawai ta ce ta wuce cikin Sauri sosai tayi mamakin yanda bai mata magana akan jiya ina taje,
Da Yamma Aira na zaune a lambu sai Hirarsu sukesha Dan wajen babu kowa Aira hira tayi dad'i ta d'ora kanta saman kafad'arshi duk yanda Arman yayi ta tadashi kiyawa tayi "Aira ce ta ce " wai yaya zaman me muke haka har yanzu kak'i sama mana mafitar da zai sakeni ni wlh nagaji yanzu fa watana ya kusa hud'u gidannan ni wlh na gaji "Nima tunanin hakan kawai nake my cutie Saidai kuma har yanzu na kasa Nemo mana mafitar da zai sakeki din muje muyi Auren mu nafiki damuwa da hakan cutie Dan bakisan yanda nake kishin zamanki a gidan nan ba"Lumshe ido Aira tayi ta ce " Uhm My yaya wai ina Mummy Dan Allah kiramun ita nayi kewarta " cutie kenan so kikema su gane muna tare asirinmu ya tonu Bayan na baki labarin ta yanda na taho ai ko sim d'ina sabo na sauya saboda karma a nemeni a wancen Dan nasan Mummy zata neme ni"dafe goshi Aira tayi ta ce "Kuma fa hakane Amma fa yaya nayi mamakin dabarar nan taka Gaskiya kaid'in na musamman ne basirarka tayi yawa" Murmushi yayi tare da shafa kanta ya ce "Ko my Quen " Murmushi tayi tare da Lafewa jikinshi ta ce "Eh mana my Zuma na" Wara idanu yayi tare da cewa "Wow Yau na samu sabon suna kenan" Dariya tayi tare da rufe fuska Hango Laila Da Aira tayi tana nufo wajen ya sanyata saurin tashi gabanta na fad'uwa duk ta rikice sai sannan Arman ya lura Inda take kallo tsaki yaja tare da saurin barin wajen Laila ko tana isowa da wani irin banzan kallo ta dinga bin Aira dashi Tare da Jan tsaki ta ce "a juri zuwa rafi dai kuma ki sani a tafin hannuna kike yawo zanga gudun ruwanki idiot kawai da Aurenki da komai" Da mamaki Aira take kallonta ta ce "Me kike nufi wai " duk yanda kika d'auka "Tsaki Aira taja ta ce " Kanki akeji "Tare da barin Wajen Laila ko cike da b'acin rai Ta koma ciki tare da zuwa d'akin mamanta ta na hak'i ta ce Wlh Mama akwai matsala gidan nan" wace matsala kenan Laila?"Mama wlh zargin Aira tare da Buzun nan nake nan ta bata labarin duk abubuwan da take gani a tare da su"Dafota Sa a tayi ta ce "Meye abun had'a jijiyoyin wuya Ai wannan babbar dama ce ta samemu da zamu fitar da shegiyar yarinyar nan daurewa kawai kikaga inayi amma babanki yanzu zaman hakuri kawai nake dashi hankalinshi duka yana kan figigiyar yarinyar chan Dan haka ki k'ara sanya musa ido sosai har lokacin da zaki kamasu Turmi da tabarya Kinga daga nan ai ko ta gwal ce ya saketa " Goge hawayenta Laila tayi ta ce "Mama son buzun fa nake " Harara ta galla mata ta ce "Ke bansan shirme ki rasa Wanda zakiso sai na kasa dake wuce kiban waje sannan kiyi abunda nace kinji" gyada mata kai tayi ta ce "Insha Allahu Mama" Tundaga ranar Laila ta k'ara sanya musu ido sosai.
Yau Aira tunda ta tashi ta tashi da zazzabi mai tsananin gaske ga ciwon ciki da ya addabeta ko fitowa ta kasa Haka ta yini a d'aki rufe cikin bargo Koda Alhaji Yusuf ya leko ya sameta a wannan halin sosai ya damu tare da cewa ta shirya ya kaita Asibiti ta ce "a a a taji sauk'i parasitimol ya b'alla mata Tasha wanda saida ta amayoshi A toilet bayan barinshi dakin .
washegari ma haka Aira ta tashi da wannan zazzab'in Dak'yal dai ta samu harta fito palour abincima dak'yal taci saida Alh ya takura mata Mama ko Sannu ita da Laila basu mata ba a palour ta zauna gefen kujerar da Laila take Amai ne taji yazo mata da gudu ta fad'a toilet d'in palour tare da Fara kwarara amai duk abunda taci saida ta amayar Alh Yusuf shi ya taimaka mata ta gyara jikinta sai Sannu yake yi mata harta fito Mama Ce ta Kalleshi ta ce " Gaskiya ya kamata a kaita Asibiti tunda naga Ta fara galabaita "Eh daman asibitin kawai zamu ya fad'a yana Mikewa tare da Kallon Aira ya ce " Jeki sanyo Hijab d'inki "Ba Dan Aira tasoba taje ta sanyo hijab Hajiya saudema Mikewa tayi tace muje Tare Laila ko sai aikawa da Aira harara take har suka fito a lokacin Arman Na wajen mai gadi suna d'an hira Kad'an yana ganinsu Ya taso tare da cewa Alhaji lafiya " nuna mashi Aira yayi data tsugunna Dan ta kasa jurar tsawuyar ya ce "Amarya ce zamu kai Asibiti ba lafiya " Subhanalla Arman ya fad'a tare da cewa Allah ya bata lafiya Aira na jinshi bata d'agoba Arman ya ce "To bari na d'auko motar na kaiku" A a a ka barshi zan tuk'a da kaina Alhaji Yusuf ya fad'a tare da nufar parking space ya d'auko mota Arman ko sai kallon Aira yake tama d'ago taki Dagowa Saida Mama saude ta mik'ar da ita tare da kama hannunta suka shiga mota a lokacin ne Arman ya kalli fuskarta sosai yaga ta fad'a da ka ganta kaga marar lafiya saiyaji daman ciwon ya dawo jikinshi dukda baisan abunda ke damunshi ba a haka har motarsu ta fice daga gidan koda suka isa Asibiti basu bi wani layi ba saboda Dr d'in d'an Yayar Alhaji ne hakan yasa aka amshesu cikin mutuntawa gashi daman private hospital ne "Kallonta Dr Luqman yayi ya ce " Me yake damunki"Cikin k'arfin hali ta ce "Tun shekaranjiya ne nakejin zazzabi to jiya da yau yafi matsamun " Kina amai ko jin tashin zuciya? A a banajin tashin zuciya Amma dai jiya da dazu nayi amai"Kallon nurse Yayi ya ce "Kuje da ita lab ki fara mata gwajin fitsari?A tare da Nurse din Suka nufi lab ta dauki jininta tare da fitsarinta Tukwana Aira ta dawo office d'in Inda ta tarar Alh suna Hira da Dr Jan kujera tayi ta zauna tare da buga tagumi Ba ayi 20 minutes ba Nurse d'in ta dawo tare da Result a hannunta ta mik'awa Dr Amsa yayi tare da fara karantawa Yana gama karantawa cike da Fara'a ya d'ago ya kalli Daddy tare da cewa " Congratulations Alhaji ur Wife she's pregnant for 4 months Allah ya raba lafiya"A tare Alhaji da saude suka Mike sukace " Ciki wata hud'u Luqman"!!!!! Aira ma cikin tsananin tashin hankali ta mik'e ta ce ciki Kuma Dr.........✍🏿
Chapter 70 · 0% Book details