Sashe 111
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 3 min read
ta girma ma amma ban iya barinta ta tafi da kwana daya ma ai bazan iya bacci ba" Dariya Aira tayi ta ce "nikam Kinga banajin komai Saidai ma wani Karin ne nakejin kewarsu " Ai Dan kunsamu wannan shiyasa da ace ba kowa zakiji fin kadaici"eh kuma hakane noor ma Dan ita kad'aice shiyasa "Mik'a mata Haidar Mom noor tayi tare da Aje mata 20k ta ce " gashi mom twins ba yawa Ai bansaniba da har suna munje Allah ya raya"amsar Haidar tayi tare da ajeshi kan gadon shi Dan yayi bacci ta ce "Haba mom noor Dan Allah ki barshi sunyi yawa" Girgiza mata kai tayi ta ce "a a a kawata baza ayi haka ba sainaga kamar bakison kyauta daga waje na ne Ai anzama daya Dan Allah ki amsa" Badan Aira tasoba ta amsa ta ce "Angode har bakin get Inda tayi parking motarta Ta rakata tana mata Godiya sannan ta ce " insha Allahu duk ranar da su twins sukazo zasuzo tare "Bayan ta koma Daga mata rakiya ta samu missed call d'in mamy a sabon layinta na 9ja dayake suna waya " kiranta tayi Inda suka sha hirarsu sosai nan Mamy take fad'a mata irin fad'an da Inna tayi murmushi Aira tayi ta ce "Allahsrk my Inna inasonta sosai wlh Allah yabar mana Ita inason ganinta amma ba hali". Washegari Aira na yiwa Haidar wasa yana y'ar dariyar k'uda Arman ya shigo da Fara a fuskarsa " Mikewa tayi tare da tarbarsa ta ce "Yadai honey yau ka shigo cikin fara'a kama hannunta yayi ya ce " kin tuna promise d'in da nayi maki na haihuwar twins ?jujjuya idanu tayi sai Chan kuma ta ce "Na tuna hero " yawwa to muje ga tukucinki na farko "suna fita Aira taga dalleliyar mota Ja mai masifar kyau da d'aukar hankali wacce a k'alla zata haura 10 millions"batagama santin motar ba Taji ya mik'o mata makullin mota a hannu ya ce " ga motarki cutie ta iso"wara idanu Aira tayi ta ce "Hero kana nufin motar nan tawace " Gyara mata kai yayi yana murmushi "tsallen murna Aira ta daka tare da Rungumeshi Ta fashe da kukan farinciki ta ce " Thnks yo hero Thnks you so much ka gamayimun komai a rayuwa Allah ya saka da alkhairi ya k'ara budi"murmushi kawai Arman yake ya ce "Komai nayi maki ban isa na biyaki kwatar abunda kikayimun ba cutie kece kika gamayimun komai a rayuwa kika bani farincikin da babu wanda ya tababan kwatankwacinshi Komai nayi maki kin chanchanci fiye da hakan banason Godiya Da ni da duk abunda na mallaka naki ne keda yaranki ko kin manta" murmushi Aira tayi tana farinciki ta ce "Hakika kaid'in haskene a cikin duhu Mijina Da babu kamarsa a fad'in duniyar koda ina cikin bakincikin wani abun idan na tuna Da baiwar da Allah yayimun na mallakamun mijin da yafi na kowa so da k'auna da tattalina uwa uba kyauwun hali da kyawun fuska sai Naji dadi a raina Naji waccen damuwar ta gushe nagode mijina aljannata Allah ya barmu tare har a badan Abadan....✍🏿