Sashe 5
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda Mamy ta fara maganar Aira take sauraranta saida ta gama ta ce "Insha Allah Mamy bazaki sameni da matsala ba " Sannan ta tashi ta ce "Bari naje nayi sallah naga ana kiran Sallar la'asr " Koda ta fita da Kallo Mamy ta bita Tayi mata maganar nan ne badan komai ba "Saidan zargin da take na Aira Soyayya suke da Arman a zuciyarta ta ce " Allah yasa ma tunanina karya zama Gaskiya muddin Aira da Arman soyayya suke akwai matsala batason yanda ta zama farin silar raba wannan y'an uwan y'arta ma tazo ta k'ara zama silar k'ara rugujewar zumuncin iyayensu tasan Arman baida wani Aibu amma kuma soyayyarsu da Aira k'ara ruguza abubuwa zatayi da dama ta jima ta na tunanin AL amarin nan kafin ta tashi ta shiga toilet Dan dauro tata alwalar.
Aira Bayan tayi salla Kwanciya ta yi palourn inna tana kallon wani series inna ta fito daga d'akinta kare da waya a hannunta ta mik'awa Aira ta ce "Amshi inji Mujahid " Cikin Sauri ta Amsa ta gaisheshi ya amsa tare da tambayar ya take"tukwana ya ce ki shirya nan da 30 minutes ina nan zuwa zamu fita amma Bazan shigo ba Dan sauri nake Zan kiraki wayar Inna zaiki fito" To yaya ta fad'a cikin Sauri kafin ta kalli inna ta ce "Inna fa kasan Abba ya fad'a mata ta daina bari na fita " Lost phone" yafad’a mik'awa inna wayar Tai daga bangarenshi ya cewa inna "Inna Dan Allah Anjima zanzo mu fita da Aira zan yo maki sayayyar kayan marmari ta kawo maki " Washe baki Inna tayi ta ce "To d'an albarka Saikazo kai nidai nayi sa ar jikoki wlh " Dariya Aira Tai Dan ita da Arman sunsan logar kashe bakin inna Dan tana da saukin kai indai akwai kayan makulesshe.
Kafin lokacin da yace harta shirya sosai tayi kyau cikin blue din Abaya Jikinta duk stones ne Sosai tayi mata kyau kunsan yanda blue din abun ke karb'ar farar fata flat takalmi tasa batai make up ba sai hoda da kwalli kawai da tasa Sosai tayi kyau ta fito kamar wata balarabiya Tana gama shiri inna ta kawo mata waya ya kira ta amsa mai da gata nan fitowa.
Ta na fita ta Hango motarshi Dan nesa da gidan ta na zuwa ta bud'e front sit ta shiga a hankali ya ce "wow my cutie kece kuwa" Murmushi ta yi tare da rufe fuska "Yau kuma ni akejin kunya " cikin Sweet voice d'inta ta ce "Yaya ai Kaine kamar yau kafara gani na " Murmushi yayi ya ce "kinyi kyau ne shiyasa" Kallonshi tayi Sosai yayi kyau cikin Dakakkiyar shaddarshi milk Tasha aikin da shi kanshi abun kallone hularshi ya hada matching colour ga Agogon gold d'inshi da take ta walkiya sosai yayi mata kyau kamar wani ango "A hankali ta ce " Wow Yaya kaima Kayi kyau Kamar Wanda zaije Zance .
"murmushi yayi ya ce " Ai zancen nazo ki rakani"yafada ya na tada mota"lokaci guda ta chanza fuska Tare da cewa hmmm"Dadi yaji a zuciyarshi na ganin kishinshi a kwayar idonta dukansu sukayi shiru na d'an wani lokaci kafin ya juyo ya Kalleta ya ce "My cutie ya kikayi shiru ko bazaki rakani zancen ba " Kallonshi tayi tare da turo baki ta ce "Ni bazanje ba Daman kasan wajen budurwarka zakaje shine kacemun shan ice cream za ka kaini" cike da so da k'auna yake kallonta Dan sosai kuruciyarta take burgeshi ya ce "To saboda me bazaki rakaniba" Saboda bana sonta"Dariya yayi sosai kamar bashi ba ya ce "Ina kika Santa da zakice bakya sonta" turo baki tayi ta kauda kai gefe Sosai ta bashi Dariya ganin yanda take kishin ido bud'e ko wannan alamar kadai ta tabbatar mai da Airanshi itama tana sonshi.
Wuraren shakatawa sosai ya kaita saida ya fara kaita Tasha Ice cream Sukasha hotuna a Wayarshi mutanen da suka sanshi sai mamakin ganinshi da budurwa suke Dan sunsa Arman mutum ne mai kamun kai ba kowace mace ce zata iya tunkararshima ta ce ta na sonshi bare shi karan kanshi yace yana sonta sosai Arman yake burge mutane saboda bashi da girman kai inba saninshi kayi ba baka tab'a cewa d'an Governor ne Dan ko Security bai fiya yawo dasu ba.
Saida ya kaita wuraren shakatawa da shan iska sosai ya kashe mata kudi Inda ya kaita shopping mall ta zaba abunda takeso yawaici duk turarruka ta zab'a da choculate da ta jibgo kamar ba gobe shiko sai karo mata yake inbata ga wata ba ya ce "Cutie ga wata Bayan sun gama ya wuce da ita wani makaken Shagon saida iPhone's lokacin har Angama kiran Sallar magrib suna shiga masu shagon suka gaisheshi cikin mutuntawa ya amsa " Kallon Aira yayi ya ce "Baby tayani zab'e Waya zan chanza wacce kikaga ta dace dani"murmushi tayi ta ce .
" Tohm yaya "Nan suka fiddo mata wayoyin tundaga 5× har zuwa iphone13 Ana dauko 13 Din tace yaya wannan tayi kaga itace ake yayi yanzu"tambayarsu yayi kudinta suka fadamashi 720k nan take yayi musu transfer yasa aka sanya mata cover mai kyau tare da Yin register sabon layi tukwana suka fito a hanya sai zud'in wayar take har suka iso bakin gate " ganin bai fito ba yasanya ta cewa "Bazaka shiga ba" Eh cutie Sauri nake"Kindai iya d'aukar kayan naki ko na shigar miki dasu"Murmushi tayi ta ce.
"Haba yaya kamar wasu da yawa zan iya " to shikenan "tana niyyar fita yace " Zaki mance wayarki"Zaro idanu tayi ta ce "waya ta kuma?nida banda waya yaya ka manta" Wadda muka sayo nake nufi takice "Yaya tawa kuma ta fad'a cikin nuna mamaki" mik'a mata yayi ya ce "zakiga number ta a ciki nayi miki save zan dinga Kiranki ta nan idan zamuyi waya" Farincikin da take ciki bai musaltuwa tazo rungumeshi ya kauce ya na Dariya Ya ce "Cutie kin girma fa" Cikin murna ta ce "Thnks you yaya bansan da wani irin baki zan gode Maka ba nagode Allah saka da alkhairi ya k'ara budi Sai jujjuya wayar take wai tata ce "ameen Cutie na bansan godiyar nan haka Kinfi k'arfin komai a wajena " .
Murmshi ta sakar mashi kafin ta ce "Yaya to ya zan fad'awa y'an gida Kar Abba ya kwace kasan bai fara barinmu rik'e waya ba musamman Na yaji kai ka bani"Ashe baki da wayau Baby karki sake ko da wasa wani ya ganta bare har ma asan ni nasai maki nima nasai maki ita ne badan komai ba saidan nadinga jin muryarki koda na koma Wajen aiki amma kinsan nima banason Abunda zai dinga Zame maki matsala a gida ni zan wuce yanzu sai gobe Idan na leko" .
Thnks yaya insha Allah ba Wanda zai ganta ta fad'a cikin murna tukwana ta dauki sayayyar da sukayi tayi cikin gida sai murna take wai yau itace da waya wayarma y'ar yayi Koda tashiga tayi sa a ba kowa Sai inna Nan ta bawa inna Sayayyar da Arman yayi mata tukwana tayi ciki Sai tsallen murna take nan take ta jona ta chaji saida ta cika tukwana ta bud'e tana budeta taga ya turo mata 10gb cikin zumudi ta shiga Ta dinga d'akko apps har su what's app da Instagrams su tiktok saida ta d'auko a ranar ta fara setting d'in komai a Daren ranar ma saida suka kusan raba dare suna shan hira da Arman Saida yaga ta fara jin bacci tukwana yayi mata saida safe .
Washegari tunda safe Bayan tayi Sallar asuba harta koma saiga kiranshi saida ya tambaya lafiyarta Daga nan bata koma ba da d'auko numbobin class mates d'inta Wanda take dasu a Littafi duk ta Kwafe ta bud'e what's App duk tayi musu sallama zumudin wayar ya hanata komawa bacci ta shiga nan ta shiga Chan sai wajen 12 ta fito Bayan tayi wanka ta saka Riga marar nauyi gaishe da Inna taje tayi tukwana ta wuce bangarensu.
A Babban palour ta tarar da Abba ta duk'ursa ta gaishe da shi ya amsa mata cikin sakin fuska taa cewa "lafiya qalau Mamana ya exams din yau bakuyi ko?" Alhmdllh Abba sai gobe zamu fara neco din "Masha Allah Allah taimaka ku dage kinji Allah muku Albarka" Cikin jin dad'in Addu'ar Abba ta amsa da Ameen tukwana ta wuce cikin bedroom d'in Mamy ta gaisheta tare da yi mata ya jiki ta amsa da sauki.
"Mamy ba abunda za a miki bakya buk'atar komai? Eh Aira ba abunda nake buk'ata mai aiki tagama komai Saidai zan aikeki gidan Maman Zarah kawar tau nan dake d'orayi kingane gidan ko?Eh Mamy na gane ta Ai muna zuwa tare " yawwa to Chan zaki da kinje kice Nina aikoki ta baki sak'on ki kawomun ki gaisheta "Sannan ta zaro dubu d'aya a Jakarta tace " gashi kihau napep "to Mamy saina dawo ta fad'a saida taje ta d'auko doguwar Hijab d'inta har k'asa tukwana ta tafi.
Ta na zuwa bata jima sosai ba ta amsowa Mamy sak'on ta fito ta na tsaye ta na jiran mai napep wata dalleliyar mota ta faka a gabanta Gaba tayi mai motar ya bita yana mata magiya Dan girman Allah ta tsaya ta saurareshi jin ya had'ata da girman Allah ya sanyata ta tsaya saida ta k'are mai kallo ta ganshi baida laifi dogone baki cike da magiya ya ce " ki shigo na rage maki hanya bai kamata mace kyakyawa kamarki rana na gallarta ba.
"Yi tayi kamar bada ita yakeba " Saida ta yi ta had'ata da Allah tukwana ta shiga Dan ta lura zatasha wahalar samun abun hawa nan tayi mai kwatancen Inda zai kaita har kofar gida ya kaita ta fito ta ce Nagode "Me kyau baki bani number ki kuma ba?Kamar ta shakeshi Dan Haushi ta ce.