← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 127

Sashe 47

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 5 min read

kuma ta lumshe a hankali ta ce "Yaya Arman ku kaini wajenshi" Hawayen tausayin y'ar uwar tata ne suka zubo mata ta ce "kina lafiya ko sis ba abunda ke damunki" gyad'a mata kai Aira tayi"to ki bud'e idonki ki kalleni"bud'e idon tayi ta Kalleta abubuwan da suka farune suka dinga dawo mata a kwalwa "rufe idonta tayi ta ce " sis yaya Arman yana ina please ku kaini wajenshi"Hawaye kawai Aysha take tama rasa amsar da zata bata "Alh Yusuf ne ya dawo tare da Dr ya ce " duba ta Dr ta farka tare da Dr suka nufi Wajenta likitan ya ce "Tashi ki kalleni kinji " ba musu Aira ta bud'e idonta aysha ta kama ta ta zaunar da ita murmushi Dr yayi mata ya ce "Bakyajin komai kinajin jikin naki normal ko " gyad'a mishi kai Aira tayi ta ce "Ba komai please ku kaini wajen YAya Arman shi nakeson gani" Alh Yusuf sosai yake kishin sunan wani da take Ambata Hakanan ya Danne zuciyarshi kama hannunta yayi tare da cewa "Ya jikin naki baby" wani irin k'ududun bakin ciki ne ya tunkarowa Aira Fisge hannunta tayi tare da Jan tsaki Dan a duniya babu Wanda ta tsana takejin da tana da dama da zata iya kasheshi sama da wannan bak’in mutumin "Sosai Alh Yusuf yaji ba dadi amma kuma yasan dole yayi hakuri da hakan tunda bata sonshi harya samu ya shawo kanta " Kuka Aira ta fashe dashi Tare da Fad'awa jikin Aysha tace "Aunty ku kaini wajenshi please ku taimakeni ku kaini ko ganinshi nayi " Mama Halima ce ta taso Bayan ta Goge hawayenta ta kama hannun Aira tare da mik'ar da ita ta ce "muje ki ganshi sai Kuyi bankwana " Cikin Sauri Aira ta mik'e tana hawaye ta ce "Yawwa Mama Dan Allah ki kaini wajenshi yana ina " cike da b'acin rai Alh Yusuf ya kalli Mama Halima ya ce "da izininwa zaki kaita wajen wani kin manta da igiyar Auren na a kanta to ba Inda zata " Cike da b'acin rai Mama Halima taja tsaki tare da cewa"Wannan kuma baka isa ba D'an uwantane koba alak'ar soyayya tsakaninsu dole zankaita suyi bankwana "tana gama fad'ar haka ta figi hannun Aira sukayi waje suka nufi Inda Arman yake Arman Angama shirin komai har anfito dashi a kan gadon marassa lafiya har lokacin ko motsi bayayi Mummy na Bayan masu turashi sai kuka take dukda tare da ita zasu tafi Nan suka had'e dasu Aira ana shirin fita dashi daga asibitin Kallon Mummy Mama Halima tayi tace Kiyi Hakuri Insha Allahu zai samu lafiya sannan ta kalli Aira ta ce " ga shinan Saidai kiyimai fatan samun lafiya"Cikin rud'u Aira ta fisge hannunta daga na Mama Halima tare da rugawa ta fad'a kan Arman dake kwance ta fashe da wani irin kuka mai shiga rai Sosai take kuka kanta na k'irjinshi tace "Yaya Kaine cikin wannan halin yaya karkamun haka yaya bamuyi haka dakai ba munyiwa juna Alk'awarin rayuwa tare yaya ka mance alk'awarinmu kai da kanka fa kace Mu rik'e alk'awarin juna sannan ta nuna zoben hannunta ta ce " yaya da kanka fa ka bani zoben nan kace ta alkawarinmu ce Karka tafi ka barni karmuci Amanar soyayyar mu I love you yaya kai kad'aine nakeso kaikad'aine mijina ka tashi Airanka ce ba Aira kadai ba hatta mutanen dake wajen kukan tausayi suke sosai Mummy itama take kuka rungumo Aira tayi ta ce "Kiyi hakuri daughter Kiyi mai fatan samun lafiya kinji ke kuma Allah baki zaman lafiya da mijinki" kuka Aira ta fashe dashi tare da kankame Arman gam tace "Mummy ki rabu dani ni yaya Arman ne kad'ai mijina yaya ka tashi Airanka ce fa ta na fad'a tana girgiza shi Bambareta Mummy tasoyi amma ta kasa saboda ba rikon wasa ta mashi ba gashi Dr sai magana yake akan lokaci na kurewa jirgin ya kusa tashi Mama Halima da Mummy sukayi kokarin bambare Aira daga kanshi sai kuka take Dak'yal suka Bambareta suna Bambareta sukaga Arman na motsi cike da mamaki suke Kallonshi " Kungani daman nace maku zai tashi Yaya Ka bud'e idonka Airanka ce "Bud'e idonshi Arman yayi a hankali ya s'aukesu akan Aira Murmushi Aira ta sakar mashi dukda hawayen da yayi jab'e jab'e da fuskarta fad'awa jikinshi tayi tare da Rungumeshi tace " I love you yaya please Karka tafi ka barni ina tare dakai karka mance alk'awarinmu yaya ka manta kaid'in jinin jikina ne "lumshe idonshi Arman yayi dukda zafin ciwon da yakeji a cikin zuciyarshi a hankali ya d'aga hannunshi tare da rik'e hannunta ya murza hannunta daidai kunnanta ya saita bakinshi a hankali kamar mai koyon magana ya ce " My cutie "Cike da farinciki Aira ta ce " My yaya"Lumshe idonshi yayi saikuma ya bud'e a hankali ya rad’a mata ya ce "I Love you my cutie ki rik'emun Amanata Alk'awarinmu ya na nan karki ci Amanata ki rik'emun Amanar Komai dake tattare dake na baki Amanar kanki Da kanki ke tawace ni kad'ai kiyi hakuri kiyiwa mahaifinki biyayya kafin na dawo ina tare dake duk rintsi duk wuya alk'awarin mu na nan i love you .....Duka a hankali yake maganar cikin k'arfin hali Dan a rarrabe yake maganganun " Goge hawayenta Aira tayi tace "I love you too yaya kai nawa ne ni kad'ai nima takace kai d'aya plx ka tashi a ciwon nan meya sameka yaya" tari ne yazowa Arman Cikin Sauri Aira ta Dagashi cike da tashin hankali ta fashe da kuka ganin Arman na tari jini na zubowa daga bakinshi "Dr ne yace " ku maza ku turashi a sakashi mota ciwon yana worse "cikin Sauri aka tura Arman Dan a sakashi mota a tafi Airport Kuka Aira ta fashe dashi tare da Rik'e k'arfen gadon ta ce " ina zaku kaimun shi ku barmunshi zai tashi ba abunda ya sameshi yanzu muka gama magana dashi ku barmun miji na dak'yal wasu nurse tare da Mama Halima suka rik'eta tana fusgewa tana kallo har aka fitar da Arman daga asibitin Sulalewa a wajen Aira tayi summammiya.........✍🏿
Chapter 47 · 0% Book details