Sashe 78
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
a haka ba kasan da hakan banason ne Mama Safina tayi fad'a " Sakin hannunta yayi ya ce "to shikenan hakan ma nagode my prince's Ki kulamun da kanki kinji" Murmushi ta sakar mai ta ce "kaima haka " I love you "I love you 2 ta fad'a tare da barin motar Dan karya Kara tsareta Dan ta lura baida niyyar barinta Murmushi Arman yayi tare da barin Wajen koba komai yaji sassauci a ranshi Aira ko cikin sand'a ta shiga gidan Mama Safina da ta fito Harararta tayi ta ce " Ja irai Watau Murja Ni tayiwa wayau zata dawo ta sameni ke kuma hada biyeta"k'asa da kanta Aira tayi tana wasa da zoben hannunta ta ce 'Mama nima bansan shi bane "Kudai kuka sani yanzu ki maza.kije Ummu Rumah ta gama had'a ruwan wanka ki maza kije Tund'azu itama ke take jira 'to Aira tace " tare da sauke ajiyar zuciya bata mata fad'a ba "D'akin da ake mata gyaran Jikin ta nufa. Biki ya rage sati guda Mummy ta dawo daga Dubai tare da lefen Aira saida ta had'o akwatina set goma Wanda ko wani set mai guda biyar ne akwatina hamsin kuma dukansu shak'e suke da abun duniya na ban mamaki Dan akwatin gold ma daban A gidansu aka baje akwatinan saikuma Sayayyar kayan D'akin Maryam hadaddu y'an daure Mummy ko hutawa bata gama ba ta ce " A kaita taga y'arta"Hafiz d'an kaninta Umar shi ya d'auketa ya kaita gidan Baba Nasir Tana shiga a palour ta tarar da Aira tana shan fruit "Aira na Dagowa ta kalli Mummy wara mata hannu Mummy tayi da gudu ta ruga tare da Fad'awa jikinta cike da farinciki ta ce " Oyoyoy Mummynah Sannu da zuwa"Murmushi Mummy tayi tanajin k'aunar Aira har ranta ta ce "Lafiya qalau Daugher ta Ai dak'yal na ganeki" Murmushi Aira tayi tare da kama hannun mummy suka zauna "Kallon ummu Rumah Mummy tayi ta ce " Ammafa Gaskiya Ummu Rumah kinfitomun da y'a nesa ba kusa ba Jifa irin kyan da tayi Godiya nake dole na k'ara had'a maki da tukuici "Dariya Ummu Rumah tayi cikin hausarta da bata gama.nuna ba ta ce "Ai aikienane Hajiya Nema nagode" Matar yaya Nasir taje ta cikawa Mummy gaba da kayan makuleshi itama Sosai Mummy tayi mata Godiya akan kula da y'arta da take ta ce "ba komai ai d'a na kowa ne" Maryam ce ta fito itama ta gaishe da Mummy"Amsawa Mummy tayi cikin fara a ta ce "Ahh masha Allah Amaren namu dai ba karya" Murmushi Maryam tayi tare da kama hannun Aira zasu bar wajen"rik'e Aira mummy tayi ta ce "a a barmun d'iyata bata gama Jin gumin mamantaba" Bata fuska Maryam tayi ta ce "Kai Mummy yanzu komai Aira kindaina yina ma" Murmushi tayi tare da janyo ta itama ta zaunar da ita gefenta ta ce "Ai ku yanzu na yayeku" Itakuma Kinga jaririyace"Duk Dariya sukayi yayinda Aira tayiwa Maryam gwalo ta lafe jikin Mummy tana tunanin ko Mamy yanzu tana wani hali Hakanan kawai taji tausayin mahaifiyartata tana jin kamar batayi mata adalci ba saurin Goge hawayenta tayi Dan kar kowa ya Gani ta ce "Ku yafemun please mamy Abba nasan banyi muku adalci ba. Juma'a a aka sanya Ranar D'aurin Auren Bayan anyi gayyar mutanen Arziki ranar laraba su Aira sukaje Saloon sosai gyaran kan nata yafi na kowa yin kyau wanda su kansu masu gyaran kan sai santin yanda kan yayi suke ga wani k'amshin ni'ima da gashin yake Dan a lullubeshi da manyan mayuyyuka masu kyau da tsada Wanda Mummy ta sayosu daga Dubai Sosai Aira ta k'ara fitinannen kyau Daga wajen saloon kai tsaye gidan kunshi suka wuce Inda fitacciyar mai K'unshin ta Zane Aira tasss sosai tayi mata kunshi mai bala in kyau abunka ga farar fata sosai K'unshin ya k'ara fito da ita a lokacin daka kalli Aira dole kayi sha awar Kara kallonta saboda kyan da tayi Saidai kawai a tofeta da wala haula su Murja ma da su Maryam sai santin lallan Aira suke a gajiya suka koma gida Suna komawa kuma aka dasa da gyaran jiki akan Inda aka tsaye ciki da bai tsaf ake gyara Aira. Washegari aka shirya walima Wanda aka kira manyan manyan malaman sunna Dan suyi wa azin mata A wani Babban Hall Wanda wannan shirin Mummy ne Dan ta ce Batason ayi bidi'a a bikin yaron nata Dan yayi albarka Aira sosai tayi kyau cikin tsadaddar doguwar Riga pink wacce ta Cikin lefentane da Mummy ta sayo a k'alla Rigar zatayi Sama sa dubu d'ari biyar banmayi k'arya ba Ba make up fuskarta sai ainahin kyaun da Allah ya bata Sosai rigar tayi mata bala in kyau a haka malamai mata suka shiga wa azi ba kama hannun yaro Wanda yawaici duk akan aurene da hakkin mace akan mijinta da hakkin miji akan matarsa da azabar da Allah ya tanadarwa Wanda basa yiwa mazajensu biyayya sosai aka shiga wa azi mai ratsa jiki Wanda jikin kowa saida yayi sanyi hatta iyaye Aira ko saida tayi hawaye haka aka k'are walima lafiya aka k'are Inda aka raba kyaututtuka na ban mamaki sosai wajen yayi mutane ni da Yaya Arman fans ma ba abarsu a baya ba dan sosai suka cika wajen wanda bama zan iya Gane wasu ba Dukda naga cikinsu wasu na gunguni akan mummy ta kwafsa musu da bata Bari suka chasheba sunajin haushin duk training din rawar da sukayi ya tafi a banza suna shirin yin warrrrr kawai an warware su (🤣)tukwana kowa ya koma gidanshi Wanda mota d'aya Mummy da Aira suka shiga Gidan Baba Nasir aka wuce da Aira Dan Chan y'an matan suke Hidimominsu. Washegari da misalin k'arfe 1:PM Aka d'aura Auren *Hajara Abubakar Umar* tare da Angonta *Muhajed Kabir Umar* Akan sadaki Naira Dubu d'ari Dan ance sadaki Kad'an yafi Albarka bayan nan aka daura na Maryam da angonta Salis Baffa shi ya zama wakilin Auren Aira shikuma Arman maimartaba Sarkin Adamawa shi ya zama wakilin shi d'aurin Auren da ya samu halartar manyan mutane Sosai wajen d'aurin Auren ya cika da mutane Saidai kuma an hana koda a waya ne a d'auki hoto ko vedion d'aurin Auren Arman sosai yayi kyau cikin Farar shaddarshi da Tasha surfani na ban mamaki sai kyalli yake duk Inda ya gitta zaka gane shine Angon saboda ya fita da kowa a wajen koda yaji an d'aura Auren rasa Inda zai sanya kanshi yayi saboda Farinciki A wajen yayi sujjada Ya jima yana kwararo yabo da Godiya ga ubangiji cousin d'inshi duk Dariya suke mai yayi minti goma yana sujjada tukwana ya d'ago cikin fara a ya ce "Alhamdulilla Allah na gode Maka daka nuna mana wannan rana daga hannunshi yayi sama sosai ya ce " Alhamdulilla Allah nagode nagode nagode Ka gamamun komai ya Allah Alhamdulilla "murna saida ta kusan zautar da Arman Y'an uwanshi sai Dariya suke mai cikin Sauri ya ja hannun Suleman ya ce " ta Ho mu wuce gida ". Aira sosai tayi kyau cikin tsatsadan white material Fitet gown da yayi mugun amsarta yayi Mata das a jiki Anyi mata nad'in headgolden wuyanta ko da hannayenta duk gold ne masu matukar tsada sosai tafito tayi wani irin masifar kyau ga make up da akayi mata tayi mugun mata kyau kasancewar bata make up A palourn Aunty Safina Y'an matan cousins din Arman duk suka baje sai tsiya suke yiwa Aira Itadai tayi shiru tayi sanyi Maryam ma sosai tayi kyau su biyun aka hadu aka dinga kashewa Hotuna Bayan anyi mata ita kadai a waya da kuma photograper wanda daya gama zai tura musu ya goge a haka sukayi dashi kuma Mummy ta ce Kar ayi posting koda a what's app ne kawai ayi saboda tarihi Itama Mummy sosai tayi kyau cikin lace d'inta mai mugun tsada hannuwanta da wuyanta shake yake da gwagwalai daka ganta zakaga asalin bafullatanar Yola Dan Mummy itama badai kyau da gayu ba shiyasa Arman yayi masifar kyau saboda biyu ya had'a ga kyan Mummy ga na Daddy Mummy na gefen Aira Ta kama hannunta nan aka shiga musu hotuna masu masifar kyau kamar y'a da uwa(kodan ai sune) ana cikin hotuna sai ganin Arman sukayi kamar daga sama ya fad'o kai tsaye wajensu Mummy ya nufa Tare da Rungumesu ita. Da Aira kamar k'aramun yaro saiji sukayi ya sanya kuka y'an palourn duk Dariya sukasa yayinda wasu suka fara musu video Aunty Safina ta ce "Haba ya haka ango da kuka kuma" wata kanwar mamy ta ce "kukan farincikine" Sosai Arman yake kuka jikin Mummy Danne zuciyarta tayi ta fara Lallashinshi Itama Airar kuka ta fara a jikin Mummy"Ikon Allah Mummy ta fad'a ta ce "To nima kukan kukeso nayi" Zaunawa tayi suna jikinta suna kuka Dak'yal Arman ya sassauta ya ce "Thnks you Mummy mungode mungode Allah saka maki da gidan Aljanna hak'ika kin cika uwa ta gari da kowani d'a zaiso ki kasance uwa a gareshi Mummy kingama mana komai Allah ya biyaki da gidan Aljanna Allah ya baki farinciki Fiye da yanda kika bamu" murmushi Mummy tayi ta shafa kanshi ta ce "Ameeen Ameen Allah yayi muku Albarka ya sanya Albarka a cikin aurenku ya baku zuri'a Dayyiba " Ameen Mummy"Arman ya fad'a yana Goge hawayen shi "murmushi Mummy tayi ta ce " Kazo ka rikitamun y'a kaga ka sanyata kuka"Dagowa Arman yayi ya kalli Aira dake jikin Mummy tana shashekar Kuka "Tashi yayi tare da zagawa gefenta Ya Rungumeta sosai tare da shafa bayanta ya rankwafar da kanshi yana sinsinar wuyanta a hankali ya ce " Alhamdulilla My beautiful wife finally dai An daura mana Aure kin zama mata ta Cutie ji nake kamar mafarkine nake Tabbas yau rana ce da bazan tab'a mancewa da ita a rayuwa ta ba"Lafewa Aira tayi jikinshi Tare da Yin shiru tana sauraran Kalamanshi itama d'in ji take tamkar a mafarki wai yau itace Matar Arman Bayan gwagwarmayar da aka sha a baya shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya Tare da Yin luff a jikinshi "Y'an palourn sim sim kowa ya dinga Zamewa yana fita Dan bazasu iyaga wannan Rashin kunyar ba Mummy girgiza kai tayi tare da barin Wajen Dan tasan Arman gaban kowa zai iyayin komai indai akan Aira ne ta