← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 127

Sashe 118

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

samu mu warware matsalolin nan Inajin a jikina komai yazo karshe" Ajiyar zuciya Arman ya sauke Tabbas maganar Mummy Gaskiya Ce soyayyar da zai nunawa Aira a yanzu ita ce Ta sasinta da mahaifanta da dare Mummy ta samu Daddy da maganar zataje taga jikin Aira cewa yayi zata iya zuwa amma akayi mata wulakanci ba ruwanshi cewa Mummy tayi ta yarda tunda dai ya amince taje din da sauki. Washegari kamar yanda Dr ya fada tunda safe y'an gidan suka sanya Aira gaba Suna jiran farkawartata har Naila dake jikin Mamy Suna wajen Abba ma yana d'akin Nihal na jikinshi Dan tun jiya ta like mai A hankali ta fara bud'e idonta da sukayi mata nauyi harta k'arasa budesu saukesu tayi akan y'an gidansu kowa Ajiyar zuciya ya sauke Sukace alhmdllh Naila da Nihal da gudu sukaje suka Fad'a kanta sukace "Mom kin tashi" Kallonsu Aira tayi d'aya Bayan daga abubuwan da suka faru suka dinga dawo mata a kwalwa rumtse idonta tayi tare da budesu wasu zazzafan hawaye ne suka shiga zubo mata kallon Mamy tayi ta ce "Mamy wai da gaske ne Inna ta mutu?Kama hannunta Mamy tayi ta ce " Hakan da kikayi ayra ba soyayya bace kike nuna mata Shi mamaci a koda yaushe addua yake buk'ata bawai Dan anyi mutuwa ka shiga tashin hankaliba Wannan din kamar Rashin tawakkaline karfa ki manta mutuwa na wuyan kowa kuma muma bamu wuce ta d'auke muba a kowani lokaci kema Da mu jiranta muke addua zaki mata ba kuka ba kinji"hawaye ne suka zubowa Aira ta Goge ta ce "Allah ya jikanki Inna yasa kin huta ked'in kinyimun komai a rayuwa halinki na gari ya biki Tabbas nayi Babban rashi Inna shakuwarmu da mukayi shekara da shekaru shikenan yanzu kin tafi kin barni" Rungumeta Mamy tayi ta ce "Is okay kukan ya isa Haka kiyi mata addu'a kinji" Saida Aira tayi kuka sosai jikin Mamy kafin ta hakura tayi shiru Dagowa tayi ta kalli Mamy ta ce "har an binneta mamy"?,Yanzu watan Inna Biyu da rabi Ayra tunda ta mutu kika zautu sai yau Kika dawo hankalinki " Sosai Ayra tayi mamaki Ace wata biyu kenan da rasuwar Inna ji take kamar yau ne duba jikinta tayi taga ciki jikinta ya fara girma sosai tayi mamaki ita dai ko lokacin nan bata San tana da ciki ba "Nihal da Naila ne sukaje Wajenta suka Rungumeta suka Ce "Sannu mom " Rungumesu Aira tayi tare da Kallon Mamy Dan bata lura da Abba dake dakinba ta ce "Mamy bari muyi Sauri mu tafi kar Abba ya dawo ya samemu Ta fad'a tana yunkurawa tacewa twins ku taho mu tafi" Ba Inda zaki koma ki zauna Mamana "Suka tsinkayi Muryar Abba " Sosai Ayra tayi mamakin jin kalaman Abba da batayi tsammani ba Bama ta San yana wajenba Kallonshi tayi hawaye na zubowa daga idonta sai kuma tayi k'asa da kanta ta ce "Dan Allah Abba kayi hak....shit Abba ya fad'a tare da cewa " banason jin komai ki huta Sannan ya kalli Mama ya ce "A bata abinci taci sannan Tasha magani " To Mama ta fad'a Abba na gama fad'ar haka yabar palour kowa saida yaji dadin ganin saukowar ta Abba Bayan fitarsa Ajiyar zuciya Aira ta sauke tare da Kallon Mama ta ce "Allah yasa Abba ya yafemun" murmushi kawai ta mata nan kowa ya shiga yi mata Sannu Inda Amma Cikin farinciki ta kira Aysha Da Ummy ta fad'a musu samun lafiyar ta Ayra A lokacin da Aysha Tazo sosai Ayra tayi farincikin ganinta da tsohon ciki nan suka Rungume suna suna murna Ummy ma tana da wani k'aramun cikin Dan d'anta harya girma Itadai Aira shiru tayi tana son ta tambaya ina Haidar d'inta tana jin nauyi ga ARMAN da takeson taji yana ina Dan bata gansa ba Da dare Suna daki ita da Amma suna ta hira Ta ce "Sis wai ina Haidar " yana wajen babanshi jiya da ya kawo twins Ya tafi dashi gobe zai maidosa ya ce Ai kullum saiya kira ta wayarki ni nake d'auka yaji halin da kike ciki"Shiru Aira tayi tana nazari kenan Arman wata biyu bai ganta ba kenan Tasan Tabbas daman indai tana gidansu ne bazai tab'a taka kafarshi gidan ba yanda yake da bak'ar zuciya Shiru tayi bata Kara cewa komai ba washegari tunda Safe Abba ya sanya Driver ha kaisu Aira Asibiti Wanda Mama tayi mata rakiya Inda akai checking lafiyarta da abunda ke cikinta Alhmdllh komai normal Jikinta yanzu watanshi biyar Ya shiga na shidda nan aka rubuta musu magunguna suka dawo gida Suna zazzaune twins na bangaren Abba Suka jiyo sallama Amsawa sukayi Haidar babba ya je ya bud'e Mummy ce ta shigo Tare da Haidar A hannunta sosai Su Mamy suka tarbeta cikin girmamawa da mutuntawa Nan aka shiga gaisawa sosai Mummy tayi farincikin samun lafiyar na surukar tata Sosai tayi hamdala nan suka Rungume juna ita da Aira Haidar ko Amma ta amsheshi Dan tayi kewarshi sosai Nan aka shiga jajinta abunda ya faru Aira dai na like da Mummy Arman ko yana kawo Mummy yajuya ya koma A hankali Aira take kallon Haidar d'inta taga Ya girma masha Allah ga ya k'ara wayau ganin Yanda ya lafe jikin Amma kamar itace mamansa "Murmushi tayi musu Tana kallonsu Shima ita d'in yake kallo" Amma ce ta nuna masa ta ce "Ga Mom je ku gaisa" Lafewa yayi jikin Amma yana tsotsar yatsa Alamun bazaijeba "Murmushi Aira tayi sosai taji dad'in yanda taga y'ar uwar tata tana kula mata da d'anta Dan yanda taga ya like mata to Ta tabbata ba k'aramar kula ta bashiba a kwanciyarta. Da Mummy zata tafi Bayan ta Aje sayayyar da tayo Sosai tayi wa su Mamy Godiya sannan ta ce a rakata su gaisa da Abba Mamy ita ta rakata har part din Abba Suna tafe Mamy nayi mata Godiya akan Abubuwan da Aira ta bata labarin ta dinga mata cewa tayi ba komai ai Ayra da Arman duk d'aya suke a waje na " Suna isa palourn Abba Inda suka tarar twins Na cinyarsa suna Danna laptop suna ganin Mummy da gudu Suka tashi tare da Rungumeta "daukarsu d'aya Bayan daya tayi ta ce " Oyoyoy yaran Mummy ya weekend din "Alhmdllh suka fada a tare da tsallen murnar ganinta Mamy ta Ce " to ku bar mummyn taku ta zauna ko "Sai sannan suka bar Mummy ta zauna " Kallon Abba tayi da ita yake kallo ta ce "Ina yini Yaya munsameku lafiya" Lafiya qalau Fatima ya Gida"Alhmdllh Abba Mummy ta fad'a tana sauke ajiyar zuciya jin ga Alamun Abba zai saurareta "Madalla " ya fad'a Mamy ce ta fita tare da twins Dan su basu wuri su tattauna "Bayan fitarsu cikin ladabi Mummy ta ce " Daman hakuri muka zo baka yaya akan laifin da mukayi maka ni da yarana Dan Allah kayi hakuri ka gafartamana "shiru Abba yayi kamar mai nazari sai kuma ya ce " ai babu abunda zance kin tab'ayimun na b'acin rai Fatima tsakani na dake Sai mutunci da mutuntawa bakiyimun komai ba Allah yafe mana tare"a a a yaya Munyi maka laifi babba Wanda nice mai laifin ma dai a Gaskiya Dan ni na had'a Auren yaran nan bada saninku ba ?Aure!!!!Abba ya fad'a mamaki k'arara a fuskarsa "Shiru Mummy tayi Chan kuma ta ce " Eh Yaya Aure.....tas ta basa labarin abunda ya faru a yola Har zuwa yanzu "Sosai Abba ya shiga kogin tunani kenan yaran nan yaran sunna ne " a fuska bata iya Tantance yanayin da yake ciki b'acin rai ko akasin haka amma a fili cewa yayi "Allah yasa haka shi yafi zama alkhairi " Ameeeen Mummy ta fad'a tare da Yin shiru ganin Abba bai sake cewa komai ba ya sanyata rasa abun cewa Mikewa tayi ta ce "To zan wuce Yaya mungode Allah Kara girma zan wuce da twins Gobe za a koma makaranta" Ai nazata zasu kwanan mana biyu to shikenan Allah tsare hanya "Ameen Mummy ta fad'a tare da fitowa bata gane dai abunda Abba yake nufi ba Tana fitowa Mamy ta kira a waya ta ce " Twins su fito mu wuce ?To gasunan Mamy ta fad'a tare da Kallon Aira ta ce "Zata tafi da su Naila saboda Makaranta daman weekend ne suka zo mana " To Mamy Ayra ta fad'a tare da mik'ewa ta sanya k'atuwar hijab d'inta ta kama su Suka fito a harabar gidan ta tarar da mummy na jiransu Murmushi ta sakar mata tare da dafa Aira ta ce "Ke kika fito da kanki kenan daughter Aida kin huta saboda yanajin jikin naki" Murmushi Ayra tayi tana kasa da kanta ta ce "Ai da sauki Mamy a gaishe da su Dady ta fad'a tana mik'a mata kayan su twins " Ansa tayi ta ce "zasuji me kike buk'ata na bada driver ya kawo maki" Murmushi tayi ta ce "bana buk'atar komai Mummy nagode Allah saka da alkhairi" Duk yanda Mummy tayi Aira ta fad'a abunda take so kin fad'a tayi "To tunda kinki fad'a na bada sako yanzu akawo maki" Mummy ta fad'a tana kama Nihal dake shirin sillewa ta ce "Ku wuce mutafi sarakan wasa" Murmushi Aira tayi tare da musu bye bye "suma bye bye suka mata Naila ta ce " Mom bakice a gaishe da Hero enki ba"Dariya Mummy tayi itama Airar Dariya tayi Tare da girgiza kai ganin sun fita ya sanyata komawa Ciki ta na tunanin sahibitin nata.........✍🏿
Chapter 118 · 0% Book details