← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 127

Sashe 119

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 11 min read

*Ni da Yaya Arman it’s not free it’s for sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*

*_Miss Hajo ce_*
[7/24, 12:52] Hajo hajo: 🅿️..........*125&126*

Tana tunanin sahibin nata Koda Mummy ta koma ta fad'awa Arman samun lafiyar Aira zokuga farincikin da ya shiga Kiran wayarta yayi tayi a lokacin wayar na silent bata gani ba Da dare Aira na zaune a palour suna Hira da y'an gidansu Dukda ba wani sakewa take sosai ba Amer yazo ya ce "Ya Ayra Abba yace kije" Saida gaban Ayra ya fad'i cikin dauriya ta mik'e ta sanya hijab d'inta Kallon Mamy tayi Gyada mata kai tayi Alamun ta je gabanta na fad'uwa ta isa part din da Sallama ta yi knoking ya bata izinin shigowa tana shigowa kasa ta samu ta zauna nesa dashi tare da Yin kasa da kanta ta ce "Ina yini Abba" Lafiya qalau ya jikin naki"Alhmdllh "ta fad'a masa kasa-kasa" Jim yayi kamar bazaiyi magana ba saikuma ya ce "d'ago ki kalleni zamuyi magana dake kuma kika kuskura kikamun karya kinsan zanganeki Gaskiya nake so ki fad'amun Dazu Hajiya Fatima tazo munyi magana da ita ta fad'amun komai na shirya aurenku Da tayi to ni wannan bai daman ba Sosai Saidai Annunamun ban isa dake ba Wanda ke kika bada kofar yin haka to wannan ya wuce tunda Allah ya kadarta auren ba wanda ya isa ya Hana tunda gashi hada rabon yara Maganar da zamuyi akan Aurenki Da Alh Madugu tun lokacin da abun ya faru Ya kirani yake sanarmun Sunje Asibiti Anga ciki Jikinki Bayan nan sun kamaki keda Mujahid daki daya " To abun nan har yanzu shi yafi mun ciwo Gaskiya nakeson ki fad'amun shin maganar Gaskiya Ce haka take ko Ko?Tuni Idon Aira harya cika da k'walla ta ce "Wlh tallahi Abba ko da Al'kur ani zan iya rantse maka wlh ban tab'a zina ba Da kowa ba bare kuma *NI DA YAYA ARMAN* sharri ne kawai suka mana sannan babu wani ciki a lokacin Typord ne ke damuna suka mun sharri sukace ciki" ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka"Shiru Abba yayi na d'an wani lokaci yana nazarin maganganunta A yanda tayi maganar yasan Tabbas Gaskiya take fada Cewa yayi "Kin tabbatar maganar haka take" Tana kuka ta ce "Wallahi Abba idan akwai karya a maganar nan kar Allah ya maidani Cikin gida lfy" Sosai ran Abba ya b'aci kenan sharri ne Madugu yayiwa y'arshi kenan shiyasa bai Kara kiranshi akan maganar ba Aiko cikin b'acin rai ya lalubo wayarsa tare da dannawa Alh Madugu kira Ring biyu ya d'auka tare da cewa "Alhaji Abubakar kana lafiya " Cikin fushi Abba ya fara magana da cewa "Daman kai ba mutumin kirki bane na d'auke ka na baka y'a saboda yarda da kuma amintar mu da na duba ka rasa Dame zaka sakamun saida b'acin suna Ka k'ullawa y'ata sharrin zina da kuma sharrin ciki to bari kaji wlh baka isa kaci lilis ba Saina makaka a kotu ka kawo shaidun Inda ka kamata mutumin banza da wofi kawai"Sosai Alh Yusuf ya rikice cikin waya ya fara cewa " Dan girma Allah ka tsaya ka saurare Alhaji Duka abunne yazo a wani iri Rashin bincike da zurfafa bincike yasa aka samu matsalar wannan wlh banyiwa y'arka sharri ba Daga asibitin ne suka bada result d'in ba daidai ba muma saidaga baya suke shaida mana mistake ne aka samu aka bata result d'in wata ita waccen Aka bata nata ashe typord ke damunta sannan ni bani da shaidar da zance na kama yarka tana iskanci duk Rashin bincike ne ya kawo haka har yanzu nima ina nadamar abunda na aikata Inajin kunyar zuwa na baka hakuri sannan nayi bikonta Dan wlh inason mata ta har yanzu”sosai ran Abba ya k'ara b'aci ashe Gaskiya ne kenan Aiko cikin fad'a ya ce "Zaka maimaita Duka wannan bayanan a gaban alkali mutumin banza Sannan Kai bakaji kunyar na k'ara maido maka y'a ba a karo na biyu to idan baka sani ba ka sani tun sanda ka saketa tayi Aure yanzu haka Yaranta Ukku Dan haka kaida ita har abada sannan saina nema mata hakkinta na b'ata mata suna da kayi ka jirayi sammaci Abba na gama fad'ar haka ya katse kiran sai huci yake saboda b'acin rai Aira Duka taji abunda Alh Madugu ya fad'a Dan a hands free Wayar take sosai taji dad'in yanda Abba yayi mishi kuma ya nuna zai nemo mata y'ancinta bata gama wannan tunanin ba ta tsinkayi Muryar Abba da cewa " tashi zaki iya tafiya gobe kiyi sammako Mu tafi court saina maka Dan iskan mutumin nan a gaban hukuma "Mikewa Ayra tayi ta ce " To Abba Tare da dukursawa ta ce "Dan Allah Abba ka yafemun irin Abubuwan da nayi maka a baya nayi nadama Kuma na tuba na shirya yi maka biyaya akan duk abunda ka bani umarni a kansa amma Dan Allah ka yafe mun"Taso da ita Abba yayi ya ce " Na jima da yafe maki Mamana Allah yayi maki albarka ya shirya miki yaranki Na yafe maki duniya da lahira ko yanzu kika mutu baki mutu Da hakkin mahaifi a kanki ba sannan nima ki yafemun irin abubuwan da nayi miki na rashin Adalci zafin zuciya ne da fushi ya rudeni harna dinga maki abubuwan da namaki ki yafemun nima na yafe maki duniya da lahira Allah maki albarka mamana "Ayra harta ta manta yaushe rabon da tashiga cikin farincikin da ta shiga ba irin na yau Ai batasan lokacin data Rungume Abba ba ta ce " Nagode Abba Allah ya saka da alkhairi Tabbas kaid'in ka cika uba na gari bakayimun komai da zan yafe maka ba duka laifi nane na rashin maka biyayya da nayi nagode Abba “ta k'arasa fad'a tana hawayen farinciki Sosai Abba yakejin ninkin soyayyar yaratshi na shigarshi Dan har yanzu Aira ta daban ce a cikin yaranshi son da yake mata na daban ne"Da gudu Aira ta saki Abba Tare da rugawa part d'insu Dan tayiwa y'an uwanta da Mamy albishir tana zuwa Cikin farinciki ta Ruga ta Rungume Mamy daka Kalleta kasan tana cikin farinciki " Kallonta duk sukayi tare da cewa "Lafiya Ayra cikin " Tsananin farinciki ta d'ago ta ce "ku tayani murna Abba ya yafemun duk abunda nayi masa da bakinsa yanzu ya fad'a ya ce ya yafemun duniya da lahira" Cikinsu babu Wanda baiyi farinciki ba duk hamdala sukayi "Nan Aira ta basu labarin yanda sukayi Da Alh Madugu Dariya Mamy ta yi ta ce " Ai gwara da suka k'are a hakan shi aminta dadi hada d'aukar Y'a sukutum ka aurawa tsoho ai yanzu an k'are. Tsiya tsiya wani kotu kuma Bayan Allah ya bayyana Gaskiya "Dariya Ayra tayi Jin maganar da Mamy tayi ta ce " ai gwara a kwatomun hakkina na b'atamun suna da yayi ta fad'a tana Mikewa taja hannun Amma suka nufi daki Dan su Kara labatarwa "Mamy ko da Mama tattaunawa suka dingayi akan Lamarin Sannan sukaje suka samu Abba dak'yal suka samu suka shawo kanshi akan yayi hakuri ya barsu da Allah sakayyar Allah tafi ta kotu A haka suka samu harya hakura ya janye maganar Karan .
Aira na komawa daki wayar Ta ta lalubo nan ta shiga kiran y'an uwanta su Aysh,ummy,Aunty Maryam,Mama Halima duk tayi musu albishir da Abba ya yafe mata zokuga farincikin da y'an uwanta sukayi musamman Mama Halima daman Arman Daddy Ya yafe masa yanzu Abu d'aya ya rage Daidaituwar Abba da Daddy Shima kuma suna sa ran insha Allah zasu shirya.
Sai sannan Ayra ta duba wayarta taga missed call d'in da Arman yayi mata Tana cikin liliyar wayar taji yana kira saida taja aji tukwana ta d'auka tana turo baki" Daga bangaren Arman Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "My cutie " Turo baki Ayra tayi ta ce "Uhm ba wani cutie ashe duk Rashin lafiyar nan da nayi bakazo ka ganni ba " Am Sorrry Matar aljanna farincikina Uwar yayana Macen da babu kamarta a fad'in duniyar nan tauraruwa mai Haske a cikin taurari kiyimun Afuwa sannan kiyimun uzuri kinsan dai ason samune bazanso muyi second d'aya batare da juna ba Wlh inason zuwa ganinki ina tsoron Wulakancin da Abba zaiyimun shi ya hanani zuwa Kinsan dai bazai barni na shigo cikin gidansa ba ni kaina kwanakinnan a kaya na yisu"Uhm kawai tace "Cikin damuwa ya ce " Fushi zaki yi dani My nurul khalbi kiyi hakuri Kinsan Gaskiya nake fad'a maki"cikin shagwaba ta ce "Na hakura Hero " Ajiyar zuciya ya sauke har tana ji daga waya ya ce "To ykk ya jikin naki my cutie " Alhmdllh hero "Masha Allah haka nakesonji Allah ya k'ara maki lafiya ya my unborn" Turo baki tayi ta ce "Ameeen wai ashe yaya ciki ne dani bansani ba Gashi harya girma Haidar fa ko shekara baiyi ba Yaya kamar wata kaza" ta fad'a tanajin kamar zatayi kuka "Arman saida yaso yayi Dariya Amma Dan kartaji Haushi ya fusge tare da marairaicewa ya ce " wayyo sorry cutie d'inmu Aike jaruma ce So nake ai ki cikamun gidan da kyawawan yara kamar 30 haka ba yawa"Wara idanu tayi kamar yana ganinta ta ce "Chab Yaya 30 fa saikace wata Akuya" Sosai Arman ya sanya Dariya daman Dan ya dara yayi maganar Ayra ko turo baki tayi ta ce "Dariya ko ai dole kayi Dariya tunda baka tab'a shiga labour room ba kaidai kawai ganinsu kake " daidaita dariyarshi yayi ya ce "Sorrry Oum twins d'inmu kece kika bani Dariya to yanzu dai ayi hakuri a cigaba da kulamun da unborn Allah ya saukeki lafiya Yanzu yaushe zan ganki" ameen ta fad'a tare da cewa "Albishirinnka honey tun d'azu nake son nayi maka Albishir farinciki ya hana " Cike da zak'uwa ya ce "Goro my prince's wannnan wani Babban Albishir ne " Tana murmushi ta ce "Yaya Abba ya yafemun Duniya da lahira " Arman yana daga kwance saida ya Mike ya ce "Da gaske kike cutie " Wlh kuwa yaya nan ta bashi labarin abunda ya faru"Ajiyar zuciya nauyayya ya ce "Alhamdulilla Alhmdll Allah nagode maka Tabbas komai yayi tsanani akwai sauki Nan gaba Ashe muma saukin namu na kusa Amma nayi farinciki marar musaltuwa cutie shikenan yanzu nidake gaba d'aya Bamuda hakkin iyaye a Kanmu Duka sun yafe mana Amma nayi farinciki" tana murmushi Ayra ta ce "Wlh nima nayi farinciki Sosai yaya Inajin a jikina komai yazo karshe yanzu saura Daddy da Abba kawai shiryawarsu ta rage " Insha Allahu suma zasu shirya saboda tundaga mutuwar Inna naga sun yi sanyi Allah ya nuna mana wannan ranar da cikar burin Inna "Ameen Ayra ta fad'a " Sun tab'a Hira sosai cikin so da k'auna Wanda saida bacci ya d'auke Ayra bata ma saniba tukwana Arman ya kashe kiran Washegari aka kira aka shaida musu Aysha ta haihu ta haifi y'arta mace zo kuga farincikin da wannan iyalan suka shiga kodan Aysha ta jima bata haihu ba Musamman Ayra da ta rasa Inda zata sanya ranta saboda Farinciki sati na zagayowa yarinya taci suna Halimatu ana cemata Shukura anyiwa mariganyiya Inna takwara Wanda koda yaushe Ayra da Arman Cikin waya suke da juna ba yanda Arman baiyiba Akan Mummy ko dad suje akan maganar dawowar Ayra dan baigane nufinsu ba Rik'e amsa mata ba Amma Duka sukace bazasu je ba A bari ubanta yayi iko a kanta Kuma Sosai Arman yakejin haushin Dan koda ya koma wajen aikinshima hankalinshi ya raba biyu rabi yana Wajen Ayra Gashi itama ta kiya masa Dan duk lokacin da yace kawai ta shirya ta taho su komawarsu gidansu Sai ta ce "a a a yayi hakuri aga abunda Abba yake nufi A yanzu cikin Ayra ya k'ara girma sosai Inda bikin Hafsat da yaya Omar ya rage wata hud'u kenan tun yanzu amfara shiga busy din hidimar biki Dan su Ayra Abu biyu bangaren ango bangaren Amarya Danma dadinta d'aya Lokacin bikin sannan ta haihu dan yanzu cikinta watanshi Bakwai saura wata biyu ta haihu twins ko duk week end Mummy take badawa akawosu A maidasu Wanda hakan sosai yake yiwa Ayra Dad'i Ana haka Itama Amma aka sanya Aurenta da Wani Saurayinta AL_Ameen tun a B U K suka had'u Wanda aka had'e bikin rana d'aya da na Hafsa zo kuga farinciki wajen Ayra duk ta rasa Inda zata sa ranta Dan murna Yau Arman yazo kano Wanda Hakurinshi ya soma karewa so yake ya had'u da Cutie d'inshi a kofar gidansu yayi parking tare da hade rai irin ba wasa d'innan ya Danna mata kira tana d'auka ya ce " Ki fito ina kofar gidanku"Dariya tayi har yana jinta ta ce "Hero yau kuma zolaya kakeji" ba wasa ba ki fito yanzu karki bata mun lokaci ya fad'a yana katse kiran "Dariya Ayra tayi Jin yanda yayi maganar nan irin ba wasa d'innan hijab d'inta ga zira tare da takalmi Mamy ce ta Kalleta ta ce " Ina zuwa kuma"Sosa kai tayi ya ce "Uhm Dadyn su twins ne yazo zamu gaisa " Mamy batace uffan ba Ganin haka ya sanya Ayra fitowa tana bud'e get d'in gidan ga mamakin ta kuwa ta hangoshi tsaye jikin mota ya Rungume hannayenshi Fuskarnan tashi a had’e"Dariyarta ta Had'iye tare da nufar Inda yake Arman ko tundaga nesa ya k'are mata kallo Sosai ta k'ara masa kyau da kwarjini a y'an kwanakin da yayi bai ganta ba ga cikinta da yaga yayi wani irin girma na ban mamaki baisan lokacin da ya sakar mata murmushi mai narkar da zuciya ba Itama mayar masa tayi da kalar nata murmushin tare da karasawa garesa ta ce.........✍🏿
Chapter 119 · 0% Book details