← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 127

Sashe 94

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ganikwa dak'au kamar ban haihuba ko yanzu sai a dasa daga Inda aka tsaya"Dariya yayi ya ce "Au to bari na yi taste naji da gaskene zai chafkota ta ruga da gudu tayi palour "Rufamun asiri karki kadamun y'a ya fad'a yana binta a palour Kallon Aira da ta shigo da gudu Mummy tayi ta ce " Subhanallahi meye haka Aira Da yarinyar zaki dinga gudu Dan shirme jaririyar saikin kada ita kodai harkin manta zafin nakudar da kikasha ?Sosa kai Aira tayi ta ce "Yi hakuri Mummy bazan sakeba " Hararar Arman d'aya biyo bayanta Mummy tayi ta ce "Kaikuma Dan shirme na meye zaka biyota Wlh indai wannan shiririta zakuyi bazan yardaba wannan kunma iya kula da Yaran har yanzu baku Aje shirmeba" Sorry Mummy Arman ya fad'a tare da Kallon Aira ya kashe mata ido Alamun zasu hade gwalo tayi mishi tare da zaunawa gefen Mummy duk tana kallonsu girgiza kai kawai tayi Ywwa Mummy Sun zaba musu Nick name takwararki Naila za akirata dashi takwarar Mamy kuma Nihal sunan yayi ko?Masha Allah eh sunan yayi kam Allah ya raya"Mikewa Arman yayi tare da Kallon Aira ya ce "Jeki fito musu da kaya masu kyau mai hoton na waje zai shigo ya d'aukesu Ki fito musu da Kamar kala biyar biyar?to Aira ta fad'a tare da mik'ewa ta shiga d'akinta drawer da aka jera kayan Yaran ta fiddo Inda ta zaba musu masu kyau iri daidai ta fito dasu palour a lokacin har mai hoton ya shigo Mik'awa Mummy kayan tayi tare da zaunawa gefe Nan Mummy ta shiga shiryasu da anyi musu hoton su sauya musu wasu kuma sosai hotunan sukeyin kyau a haka har aka gama Mai hoton ya tafi sosai Mummy ta shiga tofe yaran da Addua Dan yaran nan a kyansu sai an dage da addu'a saboda bakin mutane Kallon Aira da Arman tayi ta ce " Karku sake Kuyi sake da Addu'ar nan Safe dare ko fita zakuyi dasu Karku kuskura ku tab'a mancewa Ta zauna a bakinku ku dinga Tofa musu "A'uzu bikalmatillahi tammati min sharrima halak'a " ku tofa musu a kansu sau Ukku ko sau Bakwai insha Allahu babu abunda zai samu Yaranku tundaga kan sharrin mutum da aljan ba abunda zai samu Yaranku sannan Karku dinga Dorasu a social media bakin mutane idan kasan wani bakusan wani dukda idan kun rik'e addu'ar nan babu Wanda ya isa yataba Yaranku koda maye ne kuwa Amma ance hanyar lafiya a bita da shekara Karku dinga d'ora Yaranku a social media Ya wuce what's app a barshi kunjidai na fad'a maku"To Mummy insha Allahu suka fad'a Sannan ta k'ara kallon Aira ta ja mata kunne cikin sigar wasa"Dan Kara Aira tayi ta ce "Auch mummy" Sannan ta d'an dankwasheta aka ta ce "kekuma na k'araga kina gudu da su a hannu Ko shan ruwan sanyi ko zaki ko yaji na hana" Dariya Arman yayi ya ce "Mummy kamar kinsan ta da shegen shan choculate gwara ki mata warning" Shima dankwashinshi Mummy tayi a ka ta ce "Kaikuma ina ruwanka d'an sa ido" Dariya Aira tayi mai tare da mashi gwalo Marairaicewa yayi ya kalli Mummy ya ce "Kinganta ko Mummy gwalo takemunfa" tayi maka d'in Mummy ta fad'a tana Kara masa dankwashi"Dariya Aira tayi sosai hada rik'e ciki Tare da Kara mashi gwalo ganin ya Mike Ya sanyata saurin Aje Nihal kan sopa tare da rugawa tayi ciki ya Mara mata baya"Girgiza kai Mummy tayi ta ce "Ana magani kai yana k'aba Allah ya shiryeku yaran nan kuma zakusha renon mashiriritan iyaye ta fad'a tana Dorasu kan kekensu na kwanciya Dan sunyi bacci tukwana ta mik'e ta shiga bedroom d'in da ta sauka tayi wanka ta shirya.tana tunanin yanda zata kankare da Daddy idan ta koma. Ana jibi suna y'an Yola suka tattaho sunfi su sha biyar hada Gwaggo Sosai Aira tayi farincikin ganinsu ita dasu Hasina tsalle sukayi suka Rungume juna suna farincikin had'uwa da juna Sosai suka tahowa da Aira dinkuna Wanda Mummy ta sanya a kai mata d'inkin a tafo dasu kala goma kuma Duka masu masifar kyau nanfa kowa ya shiga d'aukar yaran da riritarsu kowa ji yake inama nasune musamman su Hasina da suke zuba musu hotuna a wayar Aira saboda wayar badai camera ba idan ka kalli yaran saika rude kaji inama nakane (lol). Yau ta kama Friday ranar sunan twins manyan manyan raguna tirka tirka saida aka yanke takwas uwar jego Aira sosai tayi masifar kyau ita da yaranta Haka uban gayya Arman sosai aka shiga musu hotuna masu masifar kyau Mummy ma anmata hotuna masu kyau ita da y'an jikokin nata da takejin kaunarsu kamar ita ta haifesu sosai akayi bishasha a bikin sunan nan Anci ansha Sannan aka raba su calendar, bags kala kala na hotunan Yaran da sunansu jiki,su cups,memo,littatafai manya da hoton yaran jiki,sannan da kayan yara da aka buga da hotonsu jiki Babban Hall Aka kama Inda akayi lunch Akaci aka sha akayi hani an Hall din sosai ya cika da mutanen Arziki Dan abokanan Mamy dake nan London hada Wanda suke Dubai da aminanta dake 9ja manyan masu kudi saida sukazo sannan kowannensu saida ya cika jariran da kayan arziki Sosai na dinga kyalla idona naga ko zanga Ni da yaya Arman fans a bikin sunan nan amma shiru kakeji nace kaico Nasan kila jirgi suka rasa hakan yasa na d'auko musu rahoto yanda ya kamata anyi taro lafiya ankwashe lafiya kowa sai dai Sam barka........✍🏿
Chapter 94 · 0% Book details