← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 127

Sashe 125

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce "Alhamdulilla Allah mungode maka da ka nuna mana wannan Rana Allah ubangiji ya k'ara had'a kanku Ya shirya muku zuri arku sannan ya k'ara muku Had'in kai da k'aunar juna" Ameeeen kowa ya fad'a a lokacin da Zaka kalli fuskar kowa zakasan suna cikin farinciki Mama Halima ma zuwa tayi ta Rungume y'an uwan nata ta ce "Alhamdulilla Allah nagode maka Allahsrk Inna da da ranta nasan da zaitafi kowa farincikin wannan Rana Allah ya jikanta Da Rahama nasan ko yanzu ruhinta zai kwanta cikin salama An cika mata burinta dadadde da ta mutu dashi " Duk ameen suka fad'a Bappa ya kalli Ayra da Arman da Murmushi a fuskarsa ya ce "Allah yayi muku Albarka kuma kun sauke nauyin dake kanku Allah shirya muku Yaranku" Ameen suka fad'a "Mama Halima ce ta ce " Bappa bamu gane ba "Murmushi Baffa yayi ya ce " ai sune silar zuwana garin nan Su suka kirani suka yimun bayani akan d'an Allah nazo na taimaka musu nayiwa iyayen nasu nasiha Dan nine kadai Babban da kila idan nayi musu magana za a iya cin nasara gashi kuma alhmdll anci nasara Allah yayiwa kowa Albarka "Sosai kowa yayi farinciki Da abunda Ayra da Arman sukayi Nan aka shiga sanya musu albarka Daddy ko da Abba Hannunsu cikin na juna wani sabuwar soyayyar y'an uwanta ka na fusgarsu Bayan komai ya tsagaita Bappa ya Ce " To saura magana ta gaba Yaushe Hajara zata koma gidanta ?Ya fad'a yana kallon Abba 'murmushi Abba yayi ya ce "Bappa duk sanda kace ai kai mai ikon kowane kuma duk hukuncin da ka zartar ya wadatar" Bappa yanajin dad'in yanda Abba ke girmamasa da kuma daukarsa tamkar uba cewa yayi "to shikenan Idan tayi arba in saita koma gidanta tunda kula dole sai iyaye musamman ita da har yanzu akwai yarinta tattare da ita hakan yayi ko'Duk sunyi na am da hakan Arman ko Haushi yaji ji yake cewa xa ayi ya tafi da matarsa Ganin yana gunguni ya sanya Mummy harararsa tamai nuni da kar yayi magana " Daren ranar kowa kwanan farinciki yayi Daddy ko da Abba daki daya suka kwana su na ta hirar yaushe gamo su kansu sai yanzu sukejinsu cikin nutsuwar da ta jima da tafiyar musu "Washegari su Baffa suka juya Bayan an cikasu da Abubuwan arziki Fly suka hau Ayra Nan tacigaba da samun kulawa a gidan nasu Wanda Arman kullum sai yazo Dan yanzu har palourn gidan yake shigowa Baya da haufi akan komai Bar musu daki ake susha soyayyarshi shida Airanshi a yanzu hankalinsu ya kwanta sosai twins nayin b'ulb'ul abunsu suna samun kulawa sosai Koda Ayra tayi ar ba in a lokacin saura sati Ukku bikin Su Hafsat hakan yasa Taki tafiya nan suka shiga Hidimar biki ba kama hannun yaro gashi Mama Halima ma ta dawo a nan za ayi bikin gaba d'aya saboda kar zaryar tayiwa mutane yawa hakanko sosai yayiwa mutane dadi amarya Amma da Hafsat sosai sukeshan gyara na musamman dan wacce tayiwa ayra gyara Mummy ta d'auko daga Sudan Inda aka hada da Ayra aka shiga musu gyara sosai suka fito musamman Ayra da ta saje dasu baka tab'a cewa ta haihu kamar Budurwa Haka aka fara hidimar biki cikin kwanciyar hankali Arman ma yazo Inda duk Inda zasu suna mak'ale da juna dan twins ma Har jariran Aje su Ayra tayi take shan gayunta Wanda Sosai Arman ya rikice ya rude Dan ta dawo masa kamar amarya Ranar da akayi kamu ma sosai Ayra tayi kyau cikin Ankon lace d'insu da yayi bala in kyau shikuma ARMAN ya shirya cikin dakakkar shaddarsa kalan lace din nata sosai aka shiga Zuba musu hotuna tare da twins Mata mazan bama tasan Inda suke ba (Su Ayra manya anshiga busy an yadda d'iya😂)sosai suke bala in kyau Dan twins ma gayun da sukasha saikunyi mamaki duk Inda suka gitta ana kallonsu Ayra ko Zage jiki tayi ta chashewa a bikin Yayyun nata amma saida taga Arman yabar wajen Dan hanata Yayi haka aka gama kamu lafiya aka k'are washegari ranar Juma a dunbin AL Umma suka shaida d'aurin Auren *Hafsat Zubair Sambo Tare da Angonta Umar Abubakar Umar Saikuma na Halimatu Abubakar Umar tare da Angonta AL_Ameen Sani* Akan sadaki Naira Dubu D'ari d'ari Da yamma angwayen sukayi walima Da dare aka kai kowacce gidan Mijinta Inda Hafsat Aka kaita sabon gidanta Wanda Ya Omar ya Gina Dan bazai had'asu da Khady ba Dan Y'ar jaraba ce a auran nan Ma da zaiyi yajinta hud'u gidansu dandai taga abun yafi karfinta kuma iyayenta sukayi mata fad'a hakan yasa ta zubama sarautar Allah ta dauki hakurin dole Sosai Aka sha kuka Da amaren Aira ko k'in kuka tayi ta ce "ba wani kuka da zatayi Haka aka sha taro lafiya aka k'are lafiya Saidai Fatan nema musu zaman lafiya Ayra ko banda tsiya ba abunda take musu " Bayan biki da kwana biyu Aira suka tafi Ita da Mijinta Abuja Daga su sai twins Dan Haidar ma Mamy ta barwa shi Dan su sake Soyayya Suka dinga zubawa fiye da ta da Ga Aira da kullum sabuwa take komawa Arman har yanzu bata girma jikinta yanda yake Saidai kyau da murjewa da take karayi da wayewa Twins d'insu na samun kulawa sosai Dan Nanny suka d'auka mai kula dasu duk hutu har yanzu Twins nazuwa iyayensu hutu su koma Haidar ma Idan zasuzo hutu tare ake tahowa dashi sai a maidashi dan shi yafi sabawa da gidan Abba saboda yanda Uncle Haidar Da Uncle Amer ke kula dashi da wasa da suke masa danma yanzu Haidar babba yabar kasar yana america yana karatu Makarantarsu d'aya da su twins inda shima Amer chan aka maidashi rabi suna gidan mummy rabi suna gidan Mamy. kwana a tashi ba wuya a wurin Allah a yanxu twins Har an yaye su sun tashi suma da wayau Dan yaran su Aira dukansu masha Allah badai wayau da baki ba (Nikan nace Gado sukayi) Aysha ko ta kara haihuwar y'arta mace inda aka sanya mata Hajara ana ce mata Little Ayra karkuga irin bazan kudi da ayra da arman sukayi a sunan dan sosai yaji dadin yiwa cutie dinshi takwara da aysha tayi ayra ko ba a magana dan akwatinan da tayiwa takwarartata ma b'ata baki ne Hafsat ma ta haihu ta haifi d'anta namiji Sosai yaya omar ya shiga farinciki da kara kaunar matar tasa Khady ko har yanzu shiru danma Mijinta na nuna Mata kulawa Kuma yanzu ta hakura sun hade kansu da Hafsat dukda ba gidansu daya ba amma suna zaman lafiya amma ce dai take da tsohon ciki bata haihu ba. Ayra ganin har an yaye twins Kuma bata samu wani cikinba Ya sanya hankalinta komawa kan karatu Yanzu kuma karatu take so tayi a d'aki ta tarda Arman yana Danna laptop Wajenshi ta rufa tare da D'ora kanta kan kafadarsa ta ce "Sannu da Aiki my hero " Murmushi yayi mata ya ce "Yawwa Ai aiki ya k'are ma tunda Gaki ya fad'a yana linke Laptop din.murmushi tayi ta ce " Dan Allah magana nakeso muyi hero Makaranta nake so na koma kaga duk Sa anni na sunjima da Gama degree d'insu yanzu an kusa fara registration din Jamb "Lokaci guda taga ya had'e fuska ya ce " ba yanzu ba Nifa ina kishin Makarantar nan Me kike nema a karatu turanci dai Kin iya babu Wanda bazaku gagara dashi ba Kina da iliminki daidai gwargwado Arabi da boko kina da wayewarki Kudi Alhmdllh baki da matsalar komai me zakiyi da karatu"Lokaci guda hawaye suka zubowa Aira ta ce "Shikenan yaya tunda bakaso na hakura ta fad'a tana Juyawa tare da kwanciya" Sai yaji ta bashi tausayi amma dukda haka shi dai kishin matarsa ya ke bayason Karatun "Aira ko saida ta Goge hawaye Dan harga Allah yanzu burinta na karshe kuma bai wuce Karatu ba Tunda komai yanzu Alhamdulilla basu da matsalar komai Kenan ita Haka zatayi ta zama ba wani cigaba haka dai tayi ta tunane tunaninta irin abunda taji Arman ya fara mata ne Ya sanya ta fusge dukda barinshi tayi shi d'aya yake rawarshi da tsalle Wanda baiji dadin hakan ba Sosai Ya lura kamar ma fushi take. Washegari cikin sanyi Aira ta tashi Arman ko baice mata komai ba Ganin yanda take fuska Twins Ya Kalla da suke wasa ya kalli Aira ya ce " Cutie kina ganin ba ansanya yaran nan school ba "Yanda ka gani hero amma da anbari sunyi 2yrs tukwana " Hakane kuma ya fad'a wayar Aira ce tayi ringing d'auka tayi tana karawa a kunnanta muryar Hafsat taji cikin d'oki ta ce "Albishirinki Sis" Goro Aira ta fad'a tana sonjin Menene"Amma ta haihu yanzu Ta haifi baby boy Karki ganshi masha Allah "Cikin farincikii Aira ta ce wow masha Allah Kice Kano tayi kira wlh nayi farinciki Allah ya raya ban ammar mu gaisa " nan ta mik'awa Amma wayar Inda Ayra ta mata barka Tana zolayarta ya labour room Dariya tayi ta ce "Kedai bari na azabtu kam har mala iku na dinga ganin sunamun kamar gizau tsabar azaba" Dariya sosai Ayra tayi Ta ce "Amma kinban Dariya wlh to ni me haihuwa Ukku nace me " Dariya Amma tayi ta ce "Ai sai yau na tabbatar ke jaruma ce Wlh " Dariya sosai Aira ta dinga yi hada rik'e ciki Arman na jinsu Ya girgiza kai Bayan sun gama wayar cikin murna ta Kalleshi ta ce "Yaya Amma ta haihu yanzu munyi baby boy " masha Allah na mana murna gsky Allah ya raya sai yawa muke karawa"Dariya Ayra tayi tanajin farinciki ta ce "Wlhko yaya gobe zantafi ko?Hararar wasa yayi mata ya ce " Chab ina zan yarda ki tafi ki barni ai ko kina zuwa sai ana gobe suna"Diddira kafa da kukan shagwaba ta fara ta ce "Uhm Uhm Allah honey ban yarda ba yaushe rabo na Da Kano Shine zakace rayya gobe suna" Dariya Arman ya dinga mata itakuma tana narke masa Dak'yal ta samu ya yarda A jibi suna zata tafi Haka ko akayi ana jibi suna Suka shirya harshi suka taho kano bayan sun jibgarwa mai jego da jariri uwar sayayya Gidan Mummy suka fara sauka Inda
Chapter 125 · 0% Book details