← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 127

Sashe 6

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Bani da waya"Ta juya kenan ta Hango Motar Arman yayi tsaye jikin mota Rungume da hannayensu ya na kallonta "Cikinta ne ya duri ruwa Dan idan bata mance ba yaya Arman ya jima da mata kashedin akan karta yarda ta kula samari ko ya ganta da wani Wanda hartayi mashi alkawarin bazata kula kowa ba gashi idan ma tayi mashi bayanin rage mata hanya kawai yayi ba fahimtar ta xaiyiba .

Taku Biyu Arman yayi kamar wani Zaki haka ya nufosu Fuskarnan tashi murtuke kamar bai tab'a Dariya ba ita kanta saida ta tsorata da ganinshi haka wani irin kallo ya watsa mata tare da data mata tsawa ya ce wuce ciki" A firgice ta wuce hada gudunta Dan sosai ta tsorata da yanayinshi "Arman ko kallon saurayin yayi ya ce.............✍🏿

*Share fisabilillah *

*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[5/28, 21:04] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️...............11&12

....." Malam wa ya baka izinin d'aukar yarinyar Chan a mota?cikin gaskiyarshi saurayin ya ce "Kayi hakuri na ganta ne a hanya ta rasa abun hawa shine na rage mata hanya kuma sonta nake ba son yaudara ba so na Aure Dan tunda na ganta Naji ta tafi da imani na " Wani irin wawan kallo ARMAN ya gallamai ji yake kamar ya shakeshi ta maza kawai yayi ya ce "Matar Aure ce Dan haka karka k'ara bibiyarta ko kaji a ranka kana sonta Wata alaka ta k'ara shiga tsakaninku zan kulleka hope ka gane ya na gama fad'ar haka ya juya ya shige ciki shiko saurayin sosai yayi mamakin jin cewar Matar Aure ce har yana murna yayi Babban kamu cike da jin haushi ya juya.

Aira ko ta na shiga Bangaren inna ta yi sai rarraba idanu take kamar wata marar Gaskiya Daga Amma sai inna a palourn Amma nayiwa Inna Karin karatu tsaye tayi jikin Bango ta kasa ko motsawa ta na haka ARMAN ya shigo daga ganinshi.kasan ranshi yayi mugun b'aci kanta yayi gadan gadan kafin ta juya ya chafkota Cikin zafin nama ya murde mata kunne k'ara ta saki Dan taji zafi sosai Karanta ta jawo da hankalinsu Amma cike da masifa ya ce " Uban waye wancen d'in Wanda ya saukeki a mota "Cikin kuka Aira ta ce " Yaya nima bansanshiba Dan Allah kayi hakuri Bazan sakeba ka sakarmun kunne da zafi"

"ke harkinyi girman da zakishiga motar wani k'ato ko ?ina alkawarinmu dake daman idan bana nan irin abunda kike ko?k'ara fashewa tayi da kuka ta ce "a a yaya wlh yau dinma tsautsayine" Sakin murdewar yayi tare da wurgata ta durkushe ta fasa kuka mai tab'a zuciya har cikin ranshi yake jin kukan nata ganin irin kukan da take ya sanyashi sanyaya zuciyarshi dan ba abunda ya tsana sama da kukan Aira Shima durkusawar yayi cikin kwantar da murya ya ruko hannunta ya ce "Sorry " Bama ta saurareshi ba saici gaba da kukanta da tayi murza hannayenta ya fara ya ce "Sorry my cutie bazan sakeba kema karki sake kinji kinsan banason ganinki da kowani d'a namiji shiyasa na kasa control d'in zcyta please karki sake in baso kike zuciyata ta tarwatse ba " Rungumeshi tayi cikin kuka ta ce "Bazan sake ba yaya kayi hakuri " Shafa bayanta yafara nan ya fara Lallashinta kamar ba shine ya gama zafutartaba.

Inna ko da Amma suna nan suna kallon Ikon Allah "Murmushin jin dad'i inna ta yi ta ce " Allah nagode maka Tabbas mafarkina ya kusa zama Gaskiya Allah cikamun burina na ganin Auren Hajara da Muhajid Tabbas nasan ta silar hakan ne kad'ai za a iya samun sulhu tsakanin iyayensu.

Da misalin k'arfe 10 na dare Aira sanye take cikin kayan bacci Nan ta d'auko wayarta ta ta boye cikin locker ta fiddota ta bud'e data nan tayi ta ganin message d'in mutane na shigowa frnds d'inta na mata congrats Number yaya Arman da tayi save da "My yaya ta shiga taga rabonshi da online one.week kenan Hakanan kawai tayi mai slm Dan daman ya fad'a mata shi chat bai dameshiba gwarama Twitter yana shiga yaga labarai.

Amma ce ta shigo d'akin Aira bata lura ba maza tayi zata boye wayar da sosai ta tsorata Ta ce " Amma Me kikazo yi"Cikin in ina take maganar murmushi kawai amma tayi ta zauna ta ce "hmm Aira kenan ni bantaba tunanin akwai abunda zaki iya b'oye munba Kinsan tun muna yara bama boyewa junanmu komai kuma muna rik'ewa junanmu sirrikanmu to me yasa kwanannan kike neman chanzamun kinsan dai ko mutum muka kashe bamaiji" Ajiyar zuciya Aira ta sauke tasan hakane tun suna yara basa b'oyewa junansu komai a hankali ta ce "Sorry sis "ya wuce amma ta ce sannan ta Amsa wayar hannun Aira ta ce " Wow Sis 13 ce fa "Dariya Aira tayi ta ce " Kina mamaki ne "Sannan taje ta rufo kofar Dan kar Wanda ya shigo " Amma ta ce wa ya baki 13 Aira "yaya Arman ta bata amsa kai tsare dare da dawowa ta zauna" Arman "Amma ta fada sannan ta ce "Kai amma Allah yiwa Yaya Arman albarka Gaskiya Yaya ARMAN ba k'aramun sonki yake ba Aira" wara idanu Aira tayi ta ce "So fa kikace sis" So kuwa sis Arman ya jima da fara sonki fahimta ce kawai bakiyiba amma Arman ba k'aramun so yake maki ba ko ince kuke yiwa junanku.

"kamo hannunta Aira ta yi ta ce " sis kina nufin yaya Arman sona yake"kwarai kuwa Ke wace irice Aira da baki gane so ,baki ganin kishinki b'arob'aro a idanunshi Abunda ya faru dazu ma Kad'ai ya isa ya k'ara tabbatar maki da irin son da Arman yake maki Bayan nan ma alamomin soyayyarki da yake gwada maki a fili suke ba a boye ba Aira ko k'aramun yaro zai iya fahimtar soyayyar dake tsakaninku ni a zato na kinjima da ganewa kiyi tunani ki gani".

Ajiyar zuciya Aira ta sauke tare da lulawa duniyar tunani tun daga rayuwarsu ta baya har zuwa yanzu ,me yasa a cikin gidan ita kadai yake sakewa,me yasa ita kadai yake farantawa,ita kadai ya damu da ita,ita kadai yake kishinta ita kadai da dama Tabbas sai yanzu ta gane Yaya Arman sonta yake sosai gabanta ya fad'i kallon Amma tayi tace "To sis ni kuma ina sonshi? Ta k'arasa fad'a cikin sigar shagwaba Dariya Amma tayi sosai ta ce .

" ke sis wlh baki rabo da abun Dariya ni zaki tambaya ai zuciyarki zaki tambaya"Turo baki tayi ta ce "To fad'amun menene alamomin so?Alamomin so suna da yawa Aira Amma zanfada maki Kad'an daga cikinsu saiki duba kiga idan kina daga cikinsu " Shak'uwa tayi yawa tana daga cikin Alamun so,damuwa da halin da dayan ku yake ciki "Damuwa da rashinshi a kusa dake koda kuwa na y'an dak'ik'a ne,kishi,shine babbar alamar Zurmiya a cikin soyayya,kyautatawa,ko da yaushe idan kika kalleshi kiji farinciki ya mamaye zuciyarki koda kuwa a waya Ne,jin bazaki iya rabuwa dashi ba duk rintsi duk wuya " ga sunan da yawa Aira kiyi tunani.

Shiru tayi tare da Zurmiyawa duniyar tunani Tabbas inko hakane so ta jima da afkawa kogin soyayyar yaya Arman soyayyarma ba ta wasaba cike da damuwa ta ce "Tabbas sis najima da Fara son yaya Arman koma Ince da soyayyarshi na ginu tun bansan kaina ba nakejin Duka abubuwan nan da kika lissafo game dashi ina tsananin sonshi son ma bana wasa ba a da haukana na d'auka duk wannan din shakuwa ce saida kika lissafo nagane Abunda ake nufi da so da Chan shirmen banza na kawai nake sannan ta kamo hannun ta tace.

" Sis ya zanyi help me please ina sonshi sosai ya zanyi kin tabbata shima yana sona"Cike da tausayin y'ar uwar tata ta ce "Karki damu sis son da yake maki ya linka son da kike mashi Wanda na gani a idanuna kedai kawai ki bari har zuwa lokacin da zai furta miki" Hakika indai kika samu Yaya Arman sis kingama samun wani jin dad'i a duniya Dan nasan zaiyi wuya a samu Wanda zai kula dake ya nuna maki tsantsar k'auna da soyayya Bayan yaya Arman Dan Arman mutum ne da kowace mace ta sameshi ta more ,Abu d'aya kawai nake Tsoro kuma nake jiye muku Iyayenmu na tabbata Abba Da Daddy bazasu tab'a yarda Kuyi Aure ba inba wani ikon na ubangiji ba shine Babban abunda yake tsoratani"Hawaye sosai Aira take ta ce "Ina sonshi sis Bazan yarda a rabamu dashi ba Abba bazai iya rabamu ba Inajin da sonshi aka halicceni a yanzu bana jin tsoro ko shakkun komai da zan tunkara indai akan a rabamu da yaya Arman ne na gwammace Ranar na mutu".

ta fad'a tana fashewa da kuka " Sosai Amma ta tausayawa y'ar uwar tata Rungumeta tayi ta ce "Insha Allahu sis babu mai rabaku sai mutuwa nan tayi ta Lallashinta ranar daki daya suka kwana Wanda Aira baccci kauracewa idanunta yayi sakat tunanin Arman ya hanata bacci da kalaman y'ar uwarta Tabbas tasan indai hakane so to baiyi mata kamun wasa ba yayi mata kamun da ita kanta bazata iya control d'in zuciyarta ba sai Bayan asuba bacci ya d'auketa hakan yasa washegari tayi ranar bacci sai 12 ta tashi.

©©©©©©©©©©©©©

B'angaren Arman Shima hakan ta kasance Dan Sosai yakejin son Aira a ranshi Wanda shi kanshi bazai iya kwatanta shi da komai ba Sosai yakejin Haushi idan ya tuno ganinta da yayi da wani a tsaye tunani yake akan ya fito ya furtawa Aira abunda ke ranshi koko ?zata amince dani ko akasin haka? Ta na sona kamar yanda nake sonta ko har yanzu Kallon yaya takemun?Daren ranar bacci kauracewa Idanunshi yayi Yasan son Da yakewa Aira daga Allah ne Dan koda bai shiga zuciyar zukatan masoya ba yaji yanda sukejiba ya tabbata son da yake yiwa Airanshi babu wani mahaluk'in masoyin da zai iya yiwa masoyiyarshi kalarshi ba.
Chapter 6 · 0% Book details