Sashe 91
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 6 min read
cikin wannan halin kici gaba da hakuri da daurewa ankusa rabuwa insha Allahu" Gyada mishi kai tayi ta ce "Bacci nakeji muje ciki" Shiya kamata Dan bazai iya daukartaba tana rik'e da k'ugu suka shiga ciki Suna zuwa ta kwanta Gado Sosai take d'anjin sauyi a tattare da ita amma batason tayarwa da habibyn nata hankali hakan yasa ta yin shiru Dan abun bai matsa mata ba Sosai ba tana daijin bayanta na sarawa Koda ta kwanta Arman toilet ya shiga tare da Dauro alwala Inda ya shiga jera salloli Akan Allah ya sauke cutie d'inshi lafiya Aira ko bacci ne ya kwasheta Chan wajen Ukkun dare taji ciwon na k'ara yawa koda ta bud'e idonta ta ganta jikin Arman Yana bacci cije baki tayi tare da daurewa ta fara adduo I a haka dai har taji kuma abun ya lafa tukwana bacci ya sake daukarta Chan wajen Asuba taji Abu ya dawo sabo Wanda ya linka na d'azu "wayyo Allah na ciki na " ta fad'a yana rik'e kugu "Cikin kid'imewa Arman ya Mike Dan daman baccin baiyi nisaba cikin tashin hankali ya ce " me ya faru cutie "Cikinta ta nunamai tana yarfe hannu Tace " yaya cikina bayana kamar zai balle ta fad'a tana hawaye "Subhanallahi Sannu dia bari mu tafi Asibiti cikin Sauri ya lalubo Wayarshi ya kira Mummy ringing biyu ta daga Dan ta tashi Sallar asuba cikin kid'imewa ya ce " Mummy Aira ce ba lafiya Kingantanan cikinta da bayanta ke ciwo sai kuka take"Ku maza ku tafi Asibiti nak'udarce ku marmaza ganinan tahowa k'asar nima yanzu yanzu"Cikin rud'u Arman ya sanyawa Aira hijab da ta fara hada gumi ya sungumeta Sai mota koda suka isa asibitin har gari ya fara wayewa Labour room aka wuce da ita duk yanda Arman yaso shiga hanashi nurse sukayi zaunawa yayi ya rafka tagumi tare da Fara jera mata adduo I Mummy ko Cikin Sauri ta shirya kayanta akwati Lek'a Daddy tayi ta da mamaki ya Kalleta ya ce Ina zuwa da asubar nan "wata karyace tazo mata ta ce " Wlh habiby yanzu aka kira kanin mahaifinmu dake Yola ya rasu za ayi sutura karfe Tara shiyasa na maza na shirya "Subhanalla Allah ya jikansa Aida kin bari mun tafi tare " a a a dia Basaikajeba na wakilceka ai Sunsan yanayin da kake ciki na gajiyar siyasa "To shikenan Allah jikansa sannan ya mik'a mata check din kudi akan takai sadaka cikin Sauri Mummy tabar gidan duk ta rude koda ta isa airport ba jirgin da zaije London jirgin Lagos tahau Inda tana isa ta samu jirgi mai zuwa London cikin k'ank'anin lokaci ta gama clearing d'in komai jirginsu ya d'aga. Aira sosai take shan azabar da tunda uwarda ta haifeta bata tab'a shan irinta ba Cije baki kawai take tana Salati Tana kiran sunan duk Wanda yazo bakinta gashi likitoci sun duba sunga Haihuwar da saura sosai take Abu d'aya har Mummy ta Iso wajen 1 na rana Aira na Abu d'aya Koda Mummy tazo cikin k'arfin hali Arman yayi mata kwatancen asibitin a waya Tana shigowa cikin rud'u ta ce " Ina take "Arman kamar zaiyi kuka ya ce " Mummy tana ciki tund'azu taki haihuwa"Bata saurareshiba Mummy tayi cikin labour room d'in Inda ta sameta sai yarfewa take Wajenta Mummy ta nufa cike da tausayawa Dan daman tasan yanda Aira batayi laulayin cikiba zata iyashan wahala wajen haihuwa sosai ta tausaya mata Sannu ta shiga jera mata Aira bama tasan da wanzuwarta ba cewa ta ke "Zan mutu yaya kazo ka taimakeni yaya Airanka Ce fa Gashinan ina ganin mutuwa daman haka Zafin d'aukar rai yake bansaniba wayyo ni Aira Mamy ki yafemun na tuba Abba ka yafemun zanmutu yaya Arman kazo"Saida Mummy tayi hawaye kamata tayi ta ce " bazaki mutuba haka kowa yakeji ki daure kinji y'ata"Arman jin Haka bai saurari kowa ba ya Banko k'ofar Tare da zuwa ya Rungumeta Saikuma ya sanya kuka "Ikon Allah Kowa ke fad'a itadai Mummy tana mamakin yanda Arman akan Aira Duka jarumatarshi ta tafi Ada d'an nata ko hawayen shi baka isa ka ganiba" Tasoshi Mummy tayi ta ce "Haba son meye haka ka fita mana zata sauke lafiya insha Allahu" Cikin hawaye ya ce "Mummy bakiga yanda take shan wahala Mummy ba yanda za ayi cutie na sai shan wuya take" Airako jin Arman Sosai ta karawa rakinta volume Ta ce "Yaya karka tafi kaikadai ke sona mutuwa sukeso inyi Yaya Ka taimakeni Cikina" Kama hannunta yayi tare da durk'ushewa ya ce "Zaki sauka lafiya cutie kinji kiyi hakuri ki daure " Dak'yal Aka samu Arman ya fita Inda ya tafi masallaci ya shiga jera Adduo I Aira tana nan tana Abu har magriba Har ana shirin mata Aiki Mummy dukta fita hayyacinta Dan ta tsorata da wuyar da takesha ana shirin Tafiya da ita d'akin theatre ta haifo y'arta Kyakyawa Fara Sol "Hamdala kowa yayi musamman Mummy Bayan nan nakuda ta dawo sabuwa Inda Bayan Mintuna baifi goma ba ta k'ara haifo wata d'iyar itama fara Sol kamarsu d'aya da d'ayar rai da rai ba banbanci Nauyayyar Ajiyar zuciya Aira ta sauke Sai yanzu tajita ta dawo mutum Mummy ko hamdala tayi tare da godewa Allah Bayan anshirya yaran an sanya musu kayansu iri d'aya mik'o wa Mummy su akayi sosai Take farinciki ta ce " Alhamdulilla Allah na gode Maka wai yau nice rik'e da d’iyan Arman shida Aira Allah mai iko"Aira ko Bayan Angama shirayata Aka ajeta gadon hutawa Kallon Mummy tayi da take Ta murmushi tare da Yaran A hannunta Kallon nurse din tayi ta ce "Meye na Haifa Dr " Murmushi tayi ta ce mata "Twins Mata " Ajiyar zuciya Aira ta sauke tare da Yin hamdala Mummy ce ta mik'e tare da Yaran ta ajesu Gefenta ta ce "Daugher Kinga Abunda kika Haifa Ikon Allah kenan Twins lokaci guda kuma Duka mata masu zafin rabo " Kallon Yaran Aira tayi sosai taji wata irin soyayyarsu ta mussaman na shigarta dukda jariraine daka kallesu sak kaga ARMAN Saidai haskensu irin na Aira amma rai da rai Arman ne "Rungumesu tayi batasan lokacin da wasu hawayen farinciki suka zuba mata ba wai yau ita ce Da Yara yaranma har biyu lokaci guda kuma ita da masoyinta Arman suka haifesu Goge hawayenta tayi ta yi a hankali ta ce " Alhamdulilla Allah abun Godiya Allah ya raya munku bisa sunnar ma aiki"Ameeeen Mummy ta fad'a tare da daukarsu ta ce "Son baisan kin haihu ba bari naje na masa albishir Murmushi kawai Aira tayi tana karajin soyayyar Mummy koda ta fita Mummy da Yaran a hannunta daidai lokacin da Arman ya shigo harabar asibitin dawowarshi kenan daga masallaci cikin Sauri ya karaso Inda Mummy take da sai fara a takemai cikin zumudi ya ce " Mummy ta haihu?Mik'a mashi ta farkon Mummy tayi ta ce "Ta haihu congratulations son An samu twins duka mata kagansunan a hannuna.........✍🏿