Sashe 115
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 10 min read
*Allahsrk rayuwa kulli nafsin za ikatul maut Mutuwa kenan mai yankan kauna Allah jikan musulmanmu da suka rigamu gidan gaskiya idan tamu tazo yasa mu cika da imani Allah ya sa muyi kyakyawan karshe*😭😭😭
*Ni da Yaya Arman it’s not free it’s for sale #200 for more information contact me on my phone number as follows 07026166536*
_*Miss Hajo ce_*🤙🏿
[7/22, 19:54] Hajo hajo: 🅿️.........*121&122*
Summammiya su Mamy da su Aunty Aysha su ummy amma da Mummy da twins da sukazo Sosai Suka shiga kuka mutuwar Inna ta girgiza mutane da dama musamman Arman Daddy da Abba ko ba a magana Babban bakincikinsu da Inna ta mutu Da Jimamin Rashin jituwarsu A bakinta Tabbas basuyi mata adalci ba Mummy ce tayi k'arfin halin Daga Aira taji ta sume ruwa ta yayyafa mata amma bata kawoba Kallonsu tayi cikin k'arfin hali ta ce "Addu'a ya kamata muyi mata ba wai kuka ba Ta rigamu ne Saidai muyi fatan samun Rahama Inda taje dole kowa zaijeshi muma jiran tamu muke Allah sa mucika da imani Inna kuma yayi mata Rahama yasa ta huta mala'ikun Rahama su San da zuwanta" Ameeen duk suka fad'a "nan aka shirya tafiya domin ayi Jana izar inna itakuma Aira aka wuce da ita emergency Arman ko baka iya Tantance yanayin da yake ciki ba a tab'a yimasa mutuwar da ta shigeshi irin mutuwar Inna ba zuciyarshi ji yake kamar zata rabe gida biyu " Wajen ya samu ya zauna a waje yanajin zuciyarshi na masa zafi da zaiyi kuka ma shi da ya ji sassauci akan Abunda yakeji idan ya kalli masu kukan sai yaji inama shine ya samu kukan irin nasu Sosai yayi mamaki jin Daddy Ya dafoshi ya ce "Addu'a zamuyi mata Mujahid tashi mu tafi ayi mata Sutura" Kallon Daddy Arman yayi sai kuma zuciyarshi ta karye Ya fashe da kuka tare da Fad'awa jikin Daddy Ya ce "Daddy Inna ta rasu Daddy shikenan ta mutu" Rungume dan nashi dad yayi yanajin nadamar abubuwa da dama da yayi a rayuwa ya Ce"Adduarmu take buk'ata namiji da jarumta aka sanshi muje kaga antafi da ita muje ayi mata Sutura da wuri"Dak'yal Arman ya iya daidaita kanshi A tare da Dad suka shiga mota Cikin k'ank'anin lokaci aka shirya Inna Bayan anyi mata salla aka wuce da ita gidanta na Gaskiya( Inda kai da ni da ita da su da kowa zaije Saidai muyi fatan Allah ya sa mu cika da imani Wanda suka rigamu Allah ya jikansu yasa sun huta Mu dake raye kuma Allah bamu guzirin taddasu )Bayan an dawo daga Sutura Wanda dumbin mutane da dama suka Je suturar Dan kafin kace me labarin mutuwar Inna ya baza gari saboda d'iyan zumunta Mama Halima ma ta tarar da suturar Inda ta sha kuka kamar ba gobe Abba ko sosai daka Kalleshi shida dad zakasan mutuwar tana nukurkusarsu cikin gidan ma ansha kuka Inda daga karshe kuma duk aaka bita da addua sai Bayan magriba sai Sannan Mamy ta kawo a kanta Aira Na Asibiti Kallon Aysha tayi ta ce "Dawa aka bar Aira a Asibiti "Aysha da cikinta da ya fara girma ta ce " Wlh Mamy bansaniba duk nan muka taho "Mikewa Mamy tayi ta ce " Bari naje naga jikin nata "Mikewa itama Aysha tayi Ta ce " muje Tare Mamy a tare suka fito harabar gidan Daidai lokacin Abba ya dawo daga salla Kallonsu yayi da mamaki ya ce "Ina zaku" Aysha ce tayi k'arfin halin cewa "Aira ce zamuje mu gano a Asibiti ba a barta Da kowaba" ku jira na d'auko mota mu tafi tare suka tsinkayi Muryar Abba "Sosai sukayi mamaki da AL ajabi musamman Mamy Sakato tayi a wajen har Abba ya fito da mota har suka iso asibitin Mamy na.mamaki suna fitowa suka samu Amma rik'e da Haidar din Aira tayi jugum idanunta jawur a waje " Kallonta sukayi a tare sukace "Kina nan daman kenan to ya jikin nata" Juyowa Amma tayi tana jijjiga Haidar ta ce "Har yanzu basu bamu wani bayani ba Tunda suka shiga har yanzu shiru Kuma sunki barina na shiga na ganta" sosai suka damu musamman Abba da a fuskarsa zakaga tsananin damuwar da yayi Kallonta yayi ya ce "Dr din bai fito ba har yanzu" Gyada musu kai tayi "Suna nan tsaye Mummy da Arman sukazo suma daga wajen makokin sukayo nan Dan suga jikin nata Arman daka Kalleshi zakasan yana cikin tsananin tashin hankali ga mutuwar Inna ga kuma Aira ba asanma halin da take ciki ba nan suka zazzauna jiran Fitowar likitan aji halin da ake ciki " sai wajen 9 pm tukwana dr din ya fito yana shafce zufa duk wajenshi suka nufa tare da tambayar halin da take ciki"Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Alhamdulilla munyi nasarar ceto rayuwata da d'an dake cikinta ta so ta samu heart attack ne Allah ya kiyaye Amma dai bata farka ba zata iya farkawa zuwa gobe haka Allah ya bata lafiya" Duk hamdala sukayi ga mamakin su na jin Aira wani cikin gareta Arman ne yayi k'arfin halin cewa "yanzu zamu iya ganinta" Eh ba damuwa zaku iya ganinta amma kar ayi hayaniya a kanta Dan Allah"Arman shi ya fara shiga d'akin Inda ya sameta kwance tana numfashi sama sama "Kama hannunta yayi ya ce " Allah ya baki lafiya my cutie"Duk shigowa sukayi suka duba jikin nata Har Abba Haidar ne da ke kuka hannun Amma Mamy ta amshe shi ta ce "Ko yunwa yakeji " Eh kila ai yanama da hakuri Tun dazu ruwa kawai na basa "Arman ne cikin k'arfin hali ya mik'awa Amma makullin mota ya ce " Ki bud'e Motar da mukazo da ita zakiga Madararshi a Pida"To ta fad'a tare da amsa ta fita Abba ne ya fita daga d'akin Bayan Amma ta dawo ta bawa Mamy Madarar Inda ta shiga bashi yana sha "Mamy kawai ta kwana wajen Aira Inda suaran suka koma gida Washegari Tun safe Arman a asibitin ya tare Dan jiran farkawartata Mummy Wajen 11 tazo tare da twins Suna ganin mamansu cikin wannan halin suka hau kuka Dak'yal aka dinga lallashinsu Haidar ko bawan Allah sai madara Mamy ta dinga bashi yanzuma yana bayanta ta goyashi yayi bacci suna nan zaune jugum jugum Sukaji farkawar Aira Cikin Sauri Arman yaje tare da kamata ya ce " Sannu Mom twins"Kallonshi Aira ta tsayayi tare da Kallon mutanen wajen da kuma Inda take abubuwan da suka faru ne suka shiga dawo mata Kuka ta fashe dashi tare da d'ora hannu a ka ta ce "Na shiga ukku yaya Dan Allah ka Cemun mafarki nake ba Inna bace ta mutu" Rungumeta Arman yayi ya ce "ki nutsu Aira baki da lfy Dukkan mai rai Mamacine Addua zakiyi mata Inna ta rigamu gidan Gaskiya" basuyi aune ba saiji sukayi ta buga uban k'ara tare da Kara sulalewa a wajen Duk rudewa sukayi Inda suka kira dr nan ya k'ara dubata Kallonsu yayi ya ce "Gaskiya mutuwar nan ta girgiza ta da yawa Ta Kara suma Allah ya kiyaye karta samu wata matsalar Allah Ya bata lfy ya fad’a tare da sanya mata Karin ruwa " sosai kowa hankalinshi ya tashi twins kuka suka sanya tare da hayewa kanta suna jijjigata sukace"Cutie mom ki tashi mom ki tashi mu tafi gida"Janye su Mamy tayi tare da Kallon Mummy ta ce "Ko Aysha ta wuce dasu gida" Mummy da duk tayi sanyi cewa Tayi Eh to a wuce da su din"Arman ne yayi saurin cewa "Mummy bari na kaisu gidan aboki na nan kusa ba nisa" Duk kallon mamaki suka bishi dashi "Mamy ta girgiza kai Mummy Ce ta harareshi ta ce " gidan abokin naka har yafi gidansu"Kiyi hakuri Mummy gwara na kaisu Chan saboda Chan din za a iya korosu Nan ko damun gama abunda muke zanje na d'aukesu "Duk Kallonshi suka tsayayi cikin b'acin rai Mummy ta ce " to ba Inda zaka kaisu"Mamy ce ta ce "Ki barshi ya kaisu Chan din Hajiya Ai yana da Gaskiya Abban su baida Tabbas ka kaisu Inda yafi maka kwanciyar hankali" Girgiza kai Mummy tayi Arman ko d'aukar yaranshi yayi ya fita dasu Dan bazai lamunta ba a wulakanta mai yara tunda baisan last time abunda Abba yayi musu ba har suke ce masa mugu Saida ya biya yayi musu sayayyar kayan ciye ciye Dan su kwantar da hankalinsu tukwana ya wuce dasu gidan wani abokinshi kasancewar akwai yara a gidan Tuni suka wartsake suka hau wasanninsu yinin ranar Aira Haka ta yini a sume.
Washe gari ma.koda ta farka bata iya tuna komai saidae tabi mutane da ido ganin Abun nata Yana neman zama tab'in hankali ya sanya Mamy buk'atar a basu sallama Dan Aje kawai a dinga mata rokon Allah likitan bai musa ba ya basu sallama ranar Suka wuce gida Da ita Sosai Mamy tayi mamakin Abba da bai ce komai ba A.lokacin Aira bata ma cikin hayyacinta Abu saiya Zamewa mutanen gidan biyu da Jimamin mutuwar Inna ga Rashin lafiyar Aira Arman kasancewar bayanan aka bada sallamar koda Mummy ta fad'a masa an sallamesu an Wuce gidansu da ita sosai ya shiga f'ada Inda ya shiga ba tanan ya ke fita ba Ya ce "Akanme za a kaimun mata Chan bada izini na ba sanadin a kara bata mata rai ne Me yasa ba a kiraniba Ko so ake sai an k'ara wulakantamun ita tukwana hankali zai kwanta" Cikin fad'a Mummy ta ce "Kai baka da hankali ma to tatafi chandin kainan gani kake har kafi iyayenta sonta to ko su da kaga suna mata haka ba Dan basa sonta ba koshi mahaifin nata Yana son y'arshi daurewa ce yake ka duba kai soyayyar da kakeyiwa yaranka to haka ko wani uba yake yiwa y'ay'ansa Dan an kaita gidansu shine zakazo ba kunya kana kumfan baki to ankaita din kuma bazata dawo ba sai ta samu lfy" Shiru Arman yayi batare da ya k'ara cewa uffan ba Daga asibitin Mummy gida ta wuce ita da twins shi kuma Arman ya wuce Guest house d'inshi ko ya rage haushin da yakeji har a ranshi yaji haushin tafiya da Aira akayi gidan su Dan Ko kare ya cinye zuciyarshi bazai tab'a taka gidansu ba Dan ko zaman makokin Inna da akayi a Farfajiyar gidanta akayi bai lek'a ko bangarensu ba to shi yanzu ya zaiyi sun tafar mai da mata gashi baya ma da tabbacin Abbanta zai amsheta Da wannan tunanin ya yini zuciyarshi chunkushe duk ba dadi Aira ko bangarensu Sosai Aka baza malamai aka dinga mata rokon Allah Dan ta firgice ta zama kamar wata mahaukaciya a haka Aka samu take shan rubutu ko magana batayi Yayinda Mamy ta yaye Haidar ganin halin da mahaifiyarshi ke ciki Ga kuma ciki da Dr yace tana dashi madara da Abinciccikan yara aka shiga bashi y'an gidan sosai suke Son yaron lokaci guda suka shaku dashi abun tausayi Aysha Da Ummy ko kullum suna gidan Mama Halima da Aunty Maryam Bayan anyi sadakar Bakwai suka tafi gidajensu Yaya Omar ma ya koma wajen aikinshi Bayan Kwana goma da rasuwar yan uwan mummy ma da na mamy duk sun zazzzo gaisuwar daga garuruwansu har bappa da goggo sunzo sunyi gaisuwa ranar suka juya gidan ya rage sauran yasu yasu Aira ko har yanzu sauki Saidai na Allah Arman Kullum da damuwar abun yake kwana yake tashi gashi idan ya kira wayarta Saidai Amma ta d'auka a wajen amma nema yake sanin halin da ake ciki yau yana zaune a daki kadaici duk ya isheshi gana Aira ga na kewar twins ga mutuwar Inna duk ya rame kiran Daddy ne yaji ya shigo Wayarshi da mamaki ya d'auka "Nan Daddy Ya shaida masa yana nemansa a gidansa yanzu" Cikin Sauri Arman ya Mike tare da d'aukar key bai zarce ko ina ba sai gida Inda yana zuwa ya samu twins Gefen Daddy Alamun Kuka ma suka gama suna ganinshi suka Ruga da gudu tare da Fad'awa jikinshi suka sanya kuka Lallashinsu yayi tare da zaunawa kan sopa Ya ce "Ina yini Daddy " Lafiya qalau Daddy Ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya "Shiru Arman yayi Ya rasa abun cewa ga twins dake masa kuka Jin Shima Daddy yayi shiru ya sanyashi Dagowa a hankali ya Kalleshi tare da Kallon Mummy da itama shid'n take kallo Da ido tayi masa sing da yaba Daddy hakuri Kallon Daddy yayi tare da Saukowa daga kan kujera ya Dirar da gwiwowinshi har k'asa cikin ladabi ya ce " Daddy Dan Allah ina neman yafiyarka akan abubuwan da nayi maka Kayi hakuri ka yafe mun badan niba Dan girman Allah"Ajiyar zuciya Daddy Ya sauke ya ce "Ka tashi Arman na jima da yafe maka Allah yayi maka albarka ya yafe mana baki d'aya Arman wani sanyi yaji cikin zuciyarshi Mikewa yayi tare da zuwa kujerar da Daddy yake ya ce " Nagode Daddy Allah ya saka Alkhairi ya k'ara girma hakika kaid'in ka cika uba na gari mai mahimtar iyalanshi Allah ya k'ara maka lafiya da nisan kwana"Cikin murmushinshi na manya daddy ya ce "Ameen my son Tare da Rungumeshi yanajin soyayyar yaron nashi na k'ara ratsa shi ta bangaren Arman ma haka yaji sosai soyayyar mahaifin nashi na k'ara fisgarsa.........✍🏿