← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 127

Sashe 107

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 7 min read

ma tana hawaye ta ce " Kayi hakuri Abbansu Ka yafe mata ka nutsu kaji komai a sannu"Tsawa ya daka mata ya ce "Na karajin bakin wani cikinku yana ban hakuri wlh zakuyi nadamar abunda zanyiwa mutum Sannan ya sakewa Aira Tsawa ya ce " bazaki kwashi rubabbun kafufunki ki barmun gida ba saina sauya maki kamanni y’ar iska a zatonki kingama yawon karuwancin naki zaki dawomun gida na karbeki ai nariga na dade da cireki a jerin yaran da na haifa ki gaggauta barmun gida ko na kira jami’an tsaro su fitarmun dake "Cikin Sauri Aira ta mik'e dak'yal tanajin zuciyarta kamar zata rabe gida biyu ta ce "Abba zan tafi kamar yanda ka koren kuma bazansake dawowaba har saika yafemun amma Bazan gaji da neman yafiyarka ba " Kallon twins tayi da duk sun rude ganin Abba na yiwa mom D'insu Tsawa ta ce "ku taho mu tafi" Da Sauri suka taho Wajenta suna boyewa Dan sun tsorata da Abba hanyar kofa ta nufa tana kuka Suma Duka y'an d'akin kuka suke musamman Mamy cikin kuka ta ce "Alhaji ba Inda zata fushinka bazai rabani da y'ata ba " Saidai ki bita Abba ya fad'a yana nuna mata hanya"Cikin fushi Mamy ta mik'e zuciyarta na zafi ta ce "Aira jirani wannan Karin bazan lamunta irin abubuwan da akayimun a baya ba na Shanye Saidai hakan ya zama silar lalacewar alak'armu tana gama fad'ar haka ta dauki hijab d'inta " Juyowa Aira tayi tare da girgiza mata kai ta ce "Dan Allah Mamy kiyi hakuri ki koma banason na zama silar Mutuwar aurenki kiyi hakuri zantafi ni kad'ai amma Dan Allah ki koma" girgiza mata mai Mamy tayi ta ce "Aira bazan yarda ki tafi cikin halin nan ba Ni uwace zan iya fuskartar ko wani irin Abu amma Bazan barki ki tafi ba " Durk'ushewa Aira tayi tare da fashewa da kuka ta ce"Mamy Dan Allah ki koma ni banason na dinga zama silar rugujewar farincikinku zan tafi kamar yanda Abba ya fad'a duk ranar da ya huce zan dawo tana gama fad'ar haka ta kama hannun twins tana kuka sosai ta fita daga gidan Gaba d'aya Mamy ko binta tayi dak'yal Mama ta lallabeta ta maida ita ciki ta hanata fita Sosai take kuka tanajin haushin Abba Aira ko na fita dakalin kofar gidansu ta zauna tare da fashewa da kuka sosai takejin zafi a cikin zuciyarta twins ma kukan suke sosai a jikinta Naila nacewa "Mom kiyi hakuli Mu tashi mu bal musu gidanchu Tunda Dad enki baya chonki muma I hate him kuma duk sanda na gilma saina rama maki" rufe mata baki Aira tayi tama kasa koda magana sai kuka Yaran abun tausayi suma kukan suke Ganin mamansu na kuka a haka ARMAN yazo ya samesu cikin wannan halin sosai Shima hankalinshi ya tashi a mota ma Aira kuka kawai take ta kasa koda magana Twins ne suka ce"Hero Dad en mom ne ya chanyata kuka sai sannan arman ya gane Dalilin kukan na Aira Lallashinta ya fara amma taki magana sai kuka kai tsaye gov house suka wuce saboda yayi waya da mummy ta ce suzo nan suna isa Bayan sunyi parking a harabar Part d'insu suna fitowa Aira na hawaye har lokacin a harabar gidan suka ci karo da Mummy da Daddy sun fito Da gudu twins suka Ruga suka Rungume Mummy itama rungumesu tayi tana farincikin ganin jikokin nata Daddy ko tsaye yayi yana binsu da Kallon mamaki Kallon Mummy yayi ya ce "me ya kawo wadannan gidana" Ajiyar zuciya ta sauke ganin cikin nutsuwa yayi maganar ta ce "zanyi maka bayani idan ka nutsu Wannan yaran da kake gani jikokinkane yaran Arman ne Wanda suka Haifa da Aira Yaran sunna ne kuma y'an halak "sosai dad yayi mamaki Nihal ce tazo wajenshi tana Dariya ta ce " Dad en hero"Murmushin k'arfin hali yayi mata tare da daukarta Dan yanason yaran sosai tun kafin yasan jinin shine amma hakan bai hanashi tunowa da abunda Arman yayi masa ba Kallonshi yayi ya ce "Fitarmun daga gida karna k'araga kafarka ka tako cikin gidan nan bani bakai na Riga na shafe da labarinki Ubanme ya kawoka gidana" Rumtse ido Arman yayi yanajin zafi a ranshi zuciyarshi na tafarfasa cikin zuciya ya kalli Aira ya ce "Shiga muje " Shiga tayi tana Hawaye Kallon twins yayi dake hannun iyayen nashi ya ce "Ku taho mu tafi" mak'alewa jikin Su sukayi Alamun basu zuwa Cikin fad'a Mummy ta ce "Banson iskanci Arman bazaka bawa mahaifinka hakuri ba kai uban zuciya shine ma zakayi fushi to ka tafi d'in ko warce yaran zakayi a hannumu ka nuna mana kai ka haifesu ba muba" Arman baicewa Mummy komai ba sai Juyawa da tayi tare da bude mota da karfi ya shiga tare da tada motar ya figeta da gudu Tsaki Mummy taja tanajin haushin Arman yanda taga Daddy Ya sauko da ya bashi hakuri zai iya hakura Daddy ko sosai ranshi ya b'aci fasa fitar da yayi yayi ya kalli mom ya ce "Muje ciki " suna shiga Mummy ta bashi labarin abunda ya faru na hada Auren su da tayi sosai Abun ya bashi mamaki yanda ta rik'a boye mai Abubuwa har a zuciyarshi baiji zafin Mummy na hada Auren nan da tayiba tunda gashi hada zuri a da dole dai sai an haifi yaran amma Yaji zafin Arman yanda yayi masa hakan yasa ya karajin zafi a ranshi Idan kuma ya kalli yaran sai yaji soyayyarsu a ranshi ga yanda Nihal ta lafe jikinshi kamar daman ta sanshi sosai Mummy taji dad'in yanda Daddy bai nuna wani b'acin ranshi ba sai shiru da yayi Yana nazarin abubuwa da dama Jin ana kiran Magriba ya sanyashi Aje Nihal zai tafi masallaci taki barin jikinshi murmushi yayi mata ya ce "Amaryar tawa uwar son jikice kenan salla zanje inyi" Dariya Nihal tayi kamar tasan me yake nufi ta ce "Dad en hero kai bazaka dinga yiwa hero fad'a ba shi dad en Cutie mugu ne Kuka ya sanya mom Kuma bama sonshi saina halbeshi da bindigata" Girgiza kai dad yayi tare yimata murmushi ya ce "Eh bari na dawo daga salla saimuyi labarin" Mummy ko girgiza kai tayi gsky abunda Abba yake baya kyautawa gashi har yara kanana zasu kullaceshi Nihal ko dining ta nufa tare da Fara b'arna da abinci Kallon Naila da tayi shiru kamar mai tunani Mummy tayi ta ce "My takwara me ya faru kinyi shiru yau ba surutun kenan" Hawaye Naila ta fara ta ce "Mom ina cutie zataje kuka take dad enta baya chonta ya sata kuka Please kije ki bashi hakuli kice Yadaina sanya mom enmu kuka kuma mu bajamu k'ala juya wajensa ba" Saida zuciyar Mummy ta karye jin yarinya k'arama na irin maganganun nan Gashi damuwa k'arara a fuskarta Goge mata hawayen tayi ta ce "Dad d'inta itama yana sonta Naila laifi tayi mashi shiyasa yayi mata fad'a kuma yanzu ya hakura sunje su dawo muje kici abinci Kinga y'ar uwarki wasanta take ko " ta fad'a tana nuna mata Nihal dake b'arna dak'yal ta samu Naila itama ta waske Inda take ta basu abinci sukaci sosai suka saki jiki da ita suka dinga mata surutu da labarai Wanda tare da Daddy suka dinga musu dimi Saidai suyi Dariya Dan labarin gida kowanne saisun basu. Arman ko cikin fushi kai tsaye hanyar Kaduna ya d'auka ranshi na Mashi mugun zafi shi abunda yafi damunshima irin yanda yaga cutie d'inshi hankalinta ya tashi sun wuce Zaria Aira ta farajin ciwon baya da mara tun tana daurewa har ta kasa cije baki tayi tana Salati da mamaki Arman ya ce "Kina lafiya cutie me ya sameki" Kallonshi tayi yana nukurkusa ta ce "Cikina yaya bayana kamar zai balle" Sosai ya shiga damuwa Cikin kid'imewa ya tsaida motar Mummy ya kira tana d'auka cikin tashin hankali ya ce "Mummy kinganmu nan hanyar Kaduna Aira ba lafiya bayanta da cikinta wai ciwo" Subhanalla Mummy ta fad'a ta ce "ku hanzarta isa Kaduna ka kaita Asibiti zankira Halima ta sameku nakuda ce take" Da mamaki ya ce "Amma Mummy ba watan Haihuwarta bane" Eh inaga tashin hankalin da ta shigane ya turo nakudar ka maza ku tafi karta galabaita"Cikin Sauri yace to mom tukwana ya tada motar harsuka isa Kaduna Aira na Abu d'aya suna isa ya wuce da ita wani private hospital.........✍🏿
Chapter 107 · 0% Book details