← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 127

Sashe 69

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 7 min read

haka y'an gidan ko kasancewar sunsan Aira gwanar zaman dakice ta kulle kanta ya sanya basu damu da Rashin ganin nata ba Alhaji Yusuf ko lokacin daman dakin Hajiya saude yake kuma fushi yake da Airar ya sanya baibi ko ta kanta ba washegari Aira cikin farinciki ta tashi Wanda har Laila saida ta gane hakan tambayar ta tayi ta ce " wai Sis ya akayi yau naganki cikin farinciki Dariya Aira tayi ta ce "kawai Hakanan nima najini cikin farinciki" Dariya Laila tayi ta ce "kodai Anfara son dadynmune" Harara Aira ta galla mata tare da tilla mata Pillow ta ce y'ar air kawai"Murmushi tayi tukwana sukaci gaba hira Arman ko Alhaji Yusuf ne ya kawo mashi wasu kaya Zasukai kala shida ya ce "ga shi ya dinga sawa Ya daina shigar buzayen" Godiya yayi mishi a yana fita ya ja tsaki tare da Wulli da kayan wai yau shine ARMAN har wani banza zai bashi jace"Saikuma yayi murmushi ya ce "a saboda so ne Ai " Hakan ya karamai kwarin gwuiwar Dan bayajin ciwon kome zaiyi kome zai sameshi indai a soyayyar Aira ne daga kayan yayi yaga suna da tsafta kuma basu sha jikiba kamar sabbi Tsaki yaja Dan daman ya gaji da kayan buzayen koda yayi wanka shiryawa yayi cikin wani black yadi da yasha d'inkin Kufta sosai ya fito yayi kyau ya dawo asalin Arman d'inshi koda ya fito domin kai Laila school kasa Daina Kallonshi yayi Wanda har saida yaja tsaki shiyadawo da ita daga duniyar tunanin data Lula sosai ya tafi da imaninta Dan ita a yanda ta ganshi baiyi mata kama da driver ba kwata kwata ya koma kamar wani basarake ko kuma hamshak'i Dan yanayin fatarshima daka gani kasan Hutu ya zauna a ciki da wannan tunanin har ya kaita school koda ya maido da ita d'akin Aira ta nufa a lokacin tana linke kayanta kamo hannunta tayi ta ce "Sis wai kinsan wani abun mamaki kuwa wlh sabon driver d'innan kwata kwata baiyi kama da kaskantacce ba Karkiga yau da yasa kayan hausawa yanda yayi masifar kyau har tuntube nasoyi Dan Kallonshi Gaskiya guy din ya had'u wlh tunda nake bantab'a ganin guy me kyanshi ba sis Kinga kuwa fatarshima kuwa Yanda take shining Gaskiya guy d'innan ya had'u iya had'uwa Dan a ko novel da nake karantawa yanda ake zuzuta mazan novels to zan iya ce maki wannan yafi Namijin novels kyau tak'amaimai dai in fad'a maki sis Ki kirashi da mijin novel kawai (lol😝)Dan yakai duk Inda baki tunani.Sosai Aira taji wani wutar kishi na taso mata wai Arman dintane wata mace ke yabawa haka lokaci guda taji tsanar Laila tatsargu cikin zuciyarta Danne b'acin ranta tayi da zafin da takejin cikin zuciyarta ta ce " Uhm su Laila manya"Harararta Laila tayi ta ce "haka ma zakice wai meyasa jiyama na kawo maki maganarsa kin shareni" Tab'e baki Aira tayi ta ce "To me kikeson nace maki Laila" Bata fuska tayi ta ce "Tayani zakiyi ko zanji dadi sannan ki bani shawara Dan wlh sonshi nake" A matuk'ar zabure Aira ta mik'e ta ce "so so fa kika ce Laila" Da mamaki Laila take kallonta ta ce "Meye naga kin tada jijiyoyin wuya saikace wacce ta ce tana son mijinki"ko saurayinki ?Rumtse ido Aira tayi ganin zatayi baram baramma ya sanyata saurin gyarawa ta ce "Amma dai Laila baki da hankali ki rasa Wanda zakiso sai Wanda yake K'ark'ashin mahaifinki driver d'inki ne fa Haba Is not your class ke ai Matar manyace" Ajiyar zuciya Laila ta sauke ta ce "Daman a saboda wannan ne ni har kin tsoratani Ai ba wani Abu bane Dan kaso Wanda yake k'asa dakai Sai Abba ya mayar dashi mai kud'in wannan ba wani Abu bane tunda dai ina sonshi nasan shima zai soni ta fad'a tare da tashi tace “Kinga bari naje na watsa ruwa na Shawo rana" Tana fita Aira taja dogon tsaki tare da Wulli da Kayan linkin ta ce "Chabd'i wlh bazai yuba Kujimun wani sabon iskancin Tama rasa Wanda zataso sai Arman d'ina Wanda mallakin nawa ni kad'ai sosai ta karajin tsanar Laila a ranta kasa daurewa tayi cike da jin Haushi tana cika tana batsewa ta fito farfajiyar gidan Hangoshi tayi a wajen parking space Shima ita yake kallo yana mamakin yanda ta wani had'e rai wajenshi ta k'arasa yana ganin haka yayi saurin janta wajen lambu Dan kar a gansu kallonta yayi cike da kulawa ya ce " Yadai naganki haka my prince's me ya faru"Kama k'ugu tayi tare da turo baki ta ce "Nidai Gaskiya Yaya daga yau karka k'ara kai Laila school banason ganinka da ita cewafa tayi tana sonka dan iskanci" Shi maganar ma dariya taso ba Arman saida ya d'an dara tukwana ya ce "Ummm cutie manya Wannan kishi haka kamar zaki tashi sama" Harara ta galla mai ta ce "wasa ka d'auka ko?Kama hannunta yayi ya ce " inbanda abunki cutie ina ruwana da ita keda kikasan halina ai Saidai kiba wani labarina Me zanyi da wata Gaki kalloma ni bata isheni ba haryau bazan iya ce miki ga kalartaba saboda ko kallonta ban tab'a yiba calm down ki nutsu karki damu da wannan kisa a ranki danke kad'ai akayini " Ajiyar zuciya Aira ta sauke tare da turo baki ta ce "To nidai na k'agara mu tafi mu bar garin nan yaya" gyara mata gashin kanta yayi da ya bazo ya ce "Karki damu akwai lokaci ai" Sun tab'a Hira sosai a nan Saida Aira ta Hango Motar Daddy Ya sanyata tashi cikin Sauri ta bar wajen shikuma Arman ya koma BQ. Kullum Arman da Aira saisun kebe sun zuba love d'insu kamar saurayi da budurwa Dan Arman mancewa ma yake da Akwai Aure a kanta itako Aira daman bata daukin Auren da komai ba Dan bata tabajin kanta a Matar Aure ba Satin Arman guda kenan Kullum saisun had'u batare da wani ya tab'a ganinsuba Dan Daddy yayi tafiya kwana huduma bare ya takurawa Aira ranar da ya dawo Aira Sun shirya fita da Arman Ta rasa yanda zata tambayi Daddy haka nan tayi shahada ta je palourn da yake yana zaune yana shan fruit nesa dashi ta tsaya tana wasa da zoben hannunta shiko tunda ta shigo ya zuba mata Idanu ba ko k'iftawa sun kai minti biyar ba Wanda ya ce uffan da kyal Aira ta iya d'ago baki ta ce "Ina yini Daddy andawo lafiya" Ajiyar zuciya tajo ya sauke Tare da cewa "Alhamdulilla my Beauty kin fara hankali ko" Tsaki Aira taja a ranta a fili kuwa murmushi tayi Wanda baikai cikiba sosai Alh Yusuf yayi farinciki ya ce "Inaga beauty ta hakura " Cikin y'ar in ina ta ce "Uhm Uhm Daddy Daman fita nake so nayi tunda nazo banje ko ina ba gashi ina son naga gari" Cikin fara a ya ce "Ai ba matsala Beauty gashi na gaji ai dani da kaina ma zan kaiki Na kaiki ko ina amma ba matsala Bari nayiwa driver magana saiya kaiki duk Inda kikeso Ko" Hamdala Aira tayi a cikin ranta Murmushi tayi tare da mik'ewa ta ce "Thnks Daddy Bari naje na shirya" murmushi yayi ya ce "Bazaki daina Cemun wannan daddyn ba ko" k'asa da kanta tayi tare da barin D'akin cikin Sauri ta shirya cikin Abaya doguwar Riga black da tayi mugun amsarta ta yafa belt din rigar sosai yayi mata kyau Ga gaban lallausan gashin kanta da ya kwanta ya fito Tunda ta fito Alhaji ya kafeta da idanu bako k'iftawa sosai yake godewa Allah daya bashi zuk'ek'iyar mata kama hannunta yayi ya ce "kinyi kyau my baby" Sosai Aira taji haushin rik'e mata hannu da tayi Dan ba yanda zatayi a tare suka fito shida ita hannunsu rik'e Dana juna Arman dake cikin mota tunda ya hangosu yaji wani irin bak'inciki Ya mamayeshi Ji yake kamar yaje ya fisge Aira daga hannun Alhaji Yusuf Rumtse idanunshi yayi da karfi Dan bai buk'atar Kara ganinsu har mota Alhaji ya kai Aira tare da bude mata back sit ya sanyata Tare da rufewa zagayawa yayi ya kalli Arman ya ce "Ka bimun ita a hankali kaji Dan daman ya fad'a mashi Inda zai kaita sannan ya bashi kudade dan ya mata sayayyar abunda take buk'ata Dak'yal Arman ya iya d'aga baki ya ce " To tare da Jan motar Horn yayi mai gadi yazo ya bud'e masu a guje sukabar gidan........✍🏿
Chapter 69 · 0% Book details