← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 127

Sashe 54

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 6 min read

ne ya sanyata tashi ta koma tayo alwala ta tada salla harta gama tana addu'ar Allah yabawa Arman lafiya ta jima tana mashi Addu'ar neman samun lafiya tukwana ta koma Gado ta kwanta yinin ranar a rufe ta yini a d'aki ba tare da taci komai ba yunwar ma batajinta saboda tashin hankalin da take ciki Saidai idan taji kishirwa ta tara ta sha a tap d'in toilet Alh Yusuf ko sosai Rashin fitowar tata ya dameshi sau Ukku yana turawa laila takai mata abinci Saidai ta koma tace mai a rufe shi da kanshi yaje Dan yakai mata amma bata bud'e ba cike da damuwa ya yini Hajiya saude ko mamakin al'amarin nan take Gashi tana son tambayar Alh Saidai kuma tace ba ruwanta idan tayi tsami saji....washegari Aira da azababbiyar yunwa ta tashi ga ciwon kai dak'yal ta iya mik'ewa taje tayi wanka saboda yanda jiri ke d'ibarta shiryawa tayi cikin doguwar rigar lace d'inta black da yasha kyau d'inkin Street gown sosai kayan suka amsheta simple d'aurin dankwali tayi zaunawa tayi bakin Gado tare da tagumi sosai ta Lula duniyar tunani ga yunwa da take ji cikinta banda k'ululu ba abunda yake knoking Tajiyo Hakanan dai ta tashi saboda yunwa a hankali ta bud'e k'ofar Tare da Yin tsaye k'arewa Aira kallo laila ta tsayayi sosai ita kanta ta tsorata da ganin kyau irin na aira kafin ta tab'e baki ta ce "Kije Palour Daddy na nemanki " Sosai gaban Aira ya fad'i idanunta duk sun firfito kamar mai shirin yin kuka ta ce "To gani nan zuwa " Juyawa laila tayi tana Jan tsaki tana komawa Ta zauna kusa da Mamanta sai tsaki take ja "Kallonta mamanta tayi ta ce " Yadai Auta naga kin dawo kina tsaki"Haba Mama wlh Dan bakiga ba yarinyar da Daddy Ya auro ba Duka cikin gidannan ba sa anta hatta ni na girmeta nesa ba kusa ba Duka bata wuce 16to17 ba wannan ai abun Kunya ne Wlh a k'awayena ma sai sumin gori dukga mata nan manya birjik a gari amma ya rasa wacce zai auro sai wannan kamar fara da k'ilama ko fitsarin kwance bata gama ba "Girgiza kai Mama tayi ta ce " Uhm bari dai ta fito nima na ganewa idona takaici"Suna ganin shigowar Daddy sukayi shiru kallon laila yayi ya ce "ta bud'e " Cike da jin Haushi laila ta ce "Eh ta ce gata nan" Cike da farinciki Alh Yusuf ya ce "Bari naje na gani" Cike da takaici Saude ta mik'e ta ce "Ai saika dawo ka zauna ba ankira maka ita ba sai wani rawar k'afa kake gaban yaranka ko kunya" Shidai Alh baice komai ba yadawo ya zauna itama Saude ta zauna tana cika ta na batsewa Laila na wucewa Aira ta saki Ajiyar zuciya tare da Goge hawayen da ya zubo mata ko saboda yunwa yau dole ta fita gyalenta ta janyo tare da d'oroshi a Samar ka flat shues ta sanya sosai tayi kyau a haka ta fito tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki harta Iso katoton palourn gabanta na fad'uwa tana isowa tsaye tayi tare da Kallon Matar da ta tabbatar kishiyartace sosai ta k'ara tsorata Dan girman Matar ya tsorata cike da tsoro tayi k'asa da kanta Daddy ko tunda ta shigo yake kallonta yana Kara godewa Allah da ya bashi wannan zuk'ek'iyar Matar yasan ba k'aramun sa a yayi ba cike da farinciki da annashuwa ya ce "Ki k'arasa ki zauna Baby" sai sannan Aira ta Kalleshi tsaki taja a cikin ranta ta ce "tsohon najadu kawai ba ko kunya wai baby" a hankali ta k'arasa shigowa palourn tare da zaunawa kujerar nesa dashi"baby ki matso mana nan"ya fad'a yana nuna mata Inda yake "bata Kalleshi ba Aira Haka bata matsa daga Inda take ba a hankali ta d'ago ta kalli kishiyartata cikin murya mai shirin yin kuka ta ce " ina kwana"Hajiya saude da tunda ta shigo take kallonta Sosai kyan Aira ya tsoratata amma kuma tayi mamakin yarinya k'arama da kyau da komai ta auri wannan tsohon gashi tasan mahaifinta Shima me kud'i ne bare tace Auren kud'i tayi sosai tashiga kogin tunani jin Aira na gaisheta ya sanyata saurin fusgewa ta ce "Lafiya ya bakunta" k'asa da kanta Aira tayi ta ce "Alhamdulilla" Alh Yusuf ne yayi gyaran murya ya ce "to Alhmdllh ba komai yasa na had'aku anan ba sai Dan kusan juna sannan ku had'e kanku Nunawa Aira Hajiya saude yayi ya ce " wannan ita ce Saudatu matata ce uwar gidanki kenan Ki girmamata sannan kiyi mata biyayya "Sannan ya kalli saude ya ce " ita kuma basai na miki bayanin komai ba kinsan komai abunda nakeso Dan Allah ku had'e kanku sannan ku zauna lafiya sai magana ta k'arshe maganar raba kwana kowa saita fad'a yanda takeso Ayi"cike da gadara Hajiya saude ta ce "Masha Allah yayi kyau Ango Nidai bani da matsala da kwana na bar mata nau da nata Har wata Ukku Asha amarci lafiya tana gama fad'ar haka ta mik'e cike da b'acin rai Ta bar wajen " Aira ko gabanta banda fad'uwa ba abunda take tuni harta Fara hawaye Alh Yusuf ko d'age kafada yayi yayi tare da tashi yaje ya zauna kujerar da Aira take suna gogar juna a hankali ya ce "Beauty na kinajin yunwa ko" Laila ko ganin wannan kayan takaicin ya sanyata tashi cike da b'acin rai tabi mamanta cike da masifa ta ce "Wlh akwai d'anyen aiki a gidan nan Mama Dan waccen Amaryar Area take ko uwar wa wlh wataran saina mata d'an banzan dukan da zata kasa tashi yanzu haka fa Daddy ba ko kunya Yaje kamar zai runguemeta ita kuma y'ar duniyar har wani sissine kai take " Tagumi Hajiya saude tayi ta ce "Duka zanyi maganinsu barni dasu ni nama zaci wace macen kirki ce aka auromun har ina tayar da hankalina Ashe wannan figaggiyar ce yo in tsaya kishi da wannan abar ma ai Naji kunya " Wlhko Mama ai zataci ubanta da mu take zancen Ammafa Mama naga kamar tsoro gareta bakijin yanda take magana kamar zatayi kuka "nima na kula da hakan barni dasu...Saurin tashi Aira tayi cike da tsoro Dan ta lura mutumin nan kwata kwata baida kunya tana zumburo baki " murmushi yayi ya ce "Sorry me zaki ci " Komai ma ta bashi amsa tana kauda kai Alh Yusuf da kanshi ya tashi yaje dining ya hadawa Aira break fast tukwana ya dawo cike da kulawa ya ce "na had'a maki Prince's muje " tana cika tana batsewa Aira ta tashi Bayan ta zauna a dining shi ya zuba mata yana kokarin fara bata ta mik'e tare da zare dara daran idanunta ta ce "Wai meye haka Daddy Nifa har yanzu Kallon uba nake maka meye haka d'in ka bari zanci da kaina idan ba so kake Duka na fasa cin abincin ba wlh kaiko kunyama baka da ita " ta k'arasa fad'a tana hawaye "Sorry sorry beauty kici da yawa bari ma na bar wajen tunda bakyaso yafada yana komawa palour tsaki Aira taja Dan ta tsani mutumin Chan Tare da Fara yin break fast d'inta.........✍🏿
Chapter 54 · 0% Book details