Sashe 126
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 5 min read
sosai ta shiga tarbarsu Dan sun kwan biyu basu zoba a lokacin twins na school Bayan an cika musu gabansu da Abinci Suna cikin Hira Mummy Ce ta ce "Wai ni Daughter ya maganar makarantarki Anfa fara registration Jamb tun last week" shiru Aira tayi tare da Kallon Arman saikuma tayi k'asa da kanta "Kallonsu Mummy tayi ta ce " bakicemun komai ba "Dagowa Aira tayi kamar me shirin yin kuka ta ce " Ya hana Mummy ya ce bazanyi ba wai "lallaima Aiko bai isa ba wlh Mummy ta fad'a tana Hararar Arman ta ce "wannan ne baka isa ba wlh saitayi karatunta kamar kowa " Amma Mummy Cikin maza fa "ya fad'a yana marairaicewa " Eh cikin mazan Matarka ce kad'ai cikin mazan kuma ma ina ruwanta dasu ita da karatu taje Kuma Bana shakkar Aira a ko ina Yarinyace mai kamun kai da nutsuwa Koda tana budurwa batayi Shiririta ba bare da Aurenta Dan haka wlh karatu zata jona barima ka gani na kira Suje tayi registration Jamb "Shiru Arman yayi jin Mummy ta fara fad'a Aira ko sosai tayi farinciki taji dad'in zuwansu Gwalo tayiwa Arman dake hade rai " wara idanu yayi tare da nuna kanshi"gyada mishi kai Tayi tana Dariya "Cije baki yayi tare da karkada hannu Alamun zata gane kuranta Gwalo ta k'ara masa Hada yi da hannu Marairaicewa yayi tare da Kallon Mummy ya ce " Mummy Kinga gwalo take yimun"Harararshi Mummy tayi ta ce "Tayi maka d'in " Dariya Ayra tayi Ganin haka ya sanya Arman tashi zai chafkota tayi saurin Mikewa tare da zuwa ta lafe jikin Mamy tana Dariya "Kudai bazaku daina shiriritaba wlh kun girma harda yara amma Abunda yaran suke Shi kuke Allah shiryeku ta fad'a tana Kiran Wanda zai fara yiwa Aira registeration din cikin sa a ko ta sameshi A ranar Aka je da Aira tayi registration din jamb sai murna take Daga nan gidansu ta wuce Bayan sun gaisa da y'an gidan Ta wuce gidan Amma Inda aka shiga Firar yaushe gamo cikin y'an uwanta Ranar suna yaro yaci suna Sani ana ce masa Sultan Haka akayi taron suna Lafiya aka gama lafiya Inda Aira ta koma gidansu a lokacin twins Sunje suna ganinta da gudu Suka ruga suka Rungumeta suna oyoyoy cutie D'aya Bayan d'aya ta daddagasu ta ce " oyoyoy my Angels "I miss you mom Suka fad'a a tare " Miss you tooo "ta fad'a tana sama da Haidar dake Dariya ya ce " Mom amma dai Kindawo nan ko"Dariya tayi ta ce "Sarkin wayau nufinka na dawo nan ku bazakujeba Chan kenan Saidai ku ku koma Chan badai ni ba " Mak'ale kafada yayi yayi ya ce "um um nidai bazan koma ba Saidai ke ki dawo" Dariya Ayra tayi ta ce "nak'i wayan " dak'yal Aira ta samu ta zauna saboda yanda suka yayyabeta Mamy da Mama ta Gaida suka Amsa cikin mutuntawa Mamy ta ce "Y'an suna sai yau ake ganinki tun Randa kikazo" Dariya Aira tayi ta ce "Wlhko Mamy hidima ta boyemu Ina su Sadeq da shureim " sai yanzu ma kike Tambayarsu Dan gidanku Kawai daga zuwa ki tafi kibar yara suta Rafkawa mutane kuka saidai babansu na kira Yazo ya d'aukesu kinsan k'iyiwa ce dasu daman zaki barsu ke raguwa Biyun ma kin kasa kula dasu tsabar ragwanci ai wlh naso ace Biyar d'innan hannunki suke muga ta tsiya"Dariya Ayra tayi ta ce "Chab Mamy Ai bazan iya dasu ba Kuma kunsani shiyasa kuka amshesu ina ni ina Iyawa da Yaran nan Ai Saisu ida doramun hawan jini Kinga idan sukaje Hutu suka had'u Su Biyar d'innan Kullum da ciwon kai nake yini Dan B'arna da Irin tijarar da suke mun kare baici wancen hutun fa k'atuwar plasma d'inmu ta palour wlh Suna fad'a suka fasata saida tayi ragwa ragwa kuma Da gangan Wancen uban zuciyar ya fara fasata ta fad'a tana nuna Haidar saida muka sake sabuwa"girgiza kai Mamy tayi ta ce " Sun aika Wlh Shiyasa da na gansu kaffa kaffa nake da kayana b'arna yaran nan garesu Allah dai ya kyauta "Ameen Aira ta fad'a ranar ta kwana gidansu tukwana tayi musu bankwana Ta wuce gidan Mummy Dan yau zasu wuce tana zuwa ta samu Arman da Twins suna ganinta suka Ruga suka Tareta daukarsu tayi tare da zaunawa ta ce " Shine kukayi tayiwa Mamy kuka ko"Dariya sukayi suna wasa da Sarkar gold din jikinta shureim ya ce "Mom mu chafi(tafi)Dariya Mummy tayi ta ce " bagwaran nan Baisan mutane ja iri tunda sukazo saidai babansu wai dole.sai an tafi gida"Dariya Aira tayi ta ce "Wlh Mamy sarkafa garesu shiyasa Na gudu ba dasu ba " Harararta Arman yayi ya ce "Ai wlh sa a kikaci ina y'an mutuncin da kaimiki su zanyi kawai kika tafi kika barmun yara Suna kuka Kika kashe wayarki saini Mamy ta kira " Dariya Aira tayi ta ce "To ayi hakuri ai gwara da kake a y'an mutunci ba y'an tsiyarba ta fad'a tana Dariya" Shima dariyar Arman yayi ya ce "Mummy zamu wuce " Okay Allah ya kiyaye Amma bamu minti biyu ta fad'a tana kama hannun Ayra bedroom d'inta ta nufa da ita Bayan ta rufe kallonta tayi ta ce "Shawarace nayi akan karatun da zaki Fara idan kika samu wani cikin zakusha wahala Shiyasa na sayo Allurar planning zanyi maki ta shekara Ukku Kina ganin ba matsala?Ajiyar zuciya Ayra ta sauke Dan daman a tsorace take karta kuma samun wani cikin Dan data samu ko tasan ko giyar wake Tasha Arman bazai barta tayi karatu ba cikin farinciki ta ce " Mummy kawai kiyimun nima inaso"To Mummy ta fad'a tare da had'a allurar ta ce "Karki kuskura ya sani nima bazan fad'a masa ba " Insha Allahu Ayra ta fad'a Nan Mummy tayi mata allurar A tare suka fito Arman bai damuba Dan Mummy da Aira An saba sirri har parking space Mummy ta rakasu tare da musu bye bye.