← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 127

Sashe 100

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 4 min read

babu wasa ya ce " wacece Rahama Lemart Jannat?tana shashekar kuka ta ce "Kawayenane ?tsaki yaja ya ce " zoki amsa ki kirasu kice su sauke abubuwan yarana da suka d'ora yanzunnan"cikin Sauri taje ta amshi wayar tana kuka Rahama ta fara kira tana d'auka ta ce "Mom twins yau wata sabon gani kece hada kirana" Cikin muryar mai kuka Aira ta ce "Momcy Dan Allah hotunan su twins da kika D'aura ki sauke Yanzu Dan Allah a tiktok" lafiya mom twins nagama kamar kuka kike"Da sauki dai ki sauke Yanzu Tana gama fad'ar haka ta kashe kiran kallon Arman tayi d'aya kafeta da idanu Jannat ta dannawa kira itama ta fad'a mata haka A na lemart ne gabanta ya dinga fad'uwa karta ganeta Harararta yayi ganin takasa kiran d'ayar ya ce "jiran me kike" Goge hawayenta tai tare da Danna mata kira lemart na na d'auka sosai tayi mamakin ganin kiran Muryar da ba tataba Aira ta ara ta ce "Sis Dan Allah hotunan su twins da kika d'ora zaki hau yanzu ki sauke plx" subhanalla lafiya"da sauki ki sauke Dan Allah"too yanzu kuwa Amma meya faru Naji kina kuka"Bata bata amsa ba Aira ta katse kiran mik'awa Arman Wayar tayi da ya mik'o hannu amsa yayi tare da Kara shiga yana shiga Yaga Rahama. Da Jannat harsun sauke nasu tsaye tayi yaga saukewar na lemart itama tana nan yaga ta sauke ajiyar zuciya ya sauke Tare da shiga daman shi ya kware a computer a take ya lalata account din nata yayi harking dinsa yana gamawa Ya goge tiktok din gaba d'aya Tare da kashe wayar yasa a Aljihu D'aukar twins d'inshi yayi da suka fara bacci yayi ya wuce Bedroom d'insu Aira dai ta zama hoto dak'yal ta iya Jan kafarta ta shiga dayan bedroom d'in Sallar itama tayi har isha i da taji ankira Tana gamawa itama Sosai tayiwa yaran nata addu'ar neman tsari Tana nan zaune har 12 duk daukarta Arman zai huce da wuri Kodan susha abincinsu ai ya kawo mata su Amma taji shiru tunowa da bak'ar zuciyar Arman tayi ya sanyata saurin Mikewa ta fito d'akin ta shiga a hankali Inda ta samesu kwance akan Gado Arman a lokacin ba bacci yakeba yanajinta ya rufe idonshi Kamar mai bacci Ajiyar zuciya Ta sauke tare da Yin sanda a hankali taje ta d'auko Nihal tare da zama Gefen gadon Zage zif din rigarta tayi ta fito da Mamanta tare da sanya mata abaki Nihal da daman abunda take buk'ata kenan a take ta tashi tare da kamawa ta dinga tsotsa Dukda duhune hakan bai hana Aira yi mata wasa ba Takai 15 minutes tana sha tukwana taji ta saki Alamun tayi bacci a hankali ta yunkura Ta maida ita makwancinta tare da rufa mata bargo Arman duk yanajinta yana kallonta ta wutsiyar ido sosai yaji tausayinta Allah sarki y'a da uwa kenan ya fad'a yana jinjina kai Aira ko a hankali ta d'auko Naila Tana daukarta Ta yage baki zatayi kuka Cikin Sauri ta sanya mata abaki Wanda hakan yasa tayi shiru Ajiyar zuciya ta sauke daman yunwa Naila takeji nan tashiga tsotsa Sosai saida tayi 30 minutes tana tsotsa Aira harta fara gyangyadi Chan kuma taji ta saki Alamun tamayi bacci Daman Naila tafi Nihal tsotsa a hankali ta maida abunta tare da kwantar da ita Tana shirin Mikewa tabar dakin taji Arman ya janyota tare da rungumeta jikinshi Dan tuni zuciyarshi ta karye Yama fasa horata din da yace zaiyi Aira jin Haka kamar me jira ta sanyata sanya mishi kukan shagwaba ta ce "Yaya Dan Allah kayi hakuri Allah bazan sakeba nima nayi nadama dan Allah karkayi fushi dani bazan iya jurar fushinkaba yaya please ka yafemun"Rungumeta yayi ya ce " Na hakura my cutie nima ai bazan iya fushin dakeba ta maza ce nayi na daure amma kin b'atamun Raine Kinga yanzu inbanda Allah ya taimaka malamin nan yazo dafa zamu iya rasa yaranmu"Cikin kuka ta ce Bazan sakeba yaya "to my cutie na hakura ya fara yana fara romance d'inta Kamar basu tab'a fada ba daganan suka Lula wata duniyar ta daban. Twins Nada shekara daya da Rabi sosai suka Tashi da baki magana rai rai ga shegen wayau ga gudu ko ina Komai aka fad'a saisun maimaita A lokacin ne kuma Aira ta fara wani irin zazzabi da amai ga tashin zuciya arman yayida ita suje Asibiti ta kiya yauma tana kwance jikinshi Tana sauke ajiyar zuciya twins na tsaye suna wasa su biyu da teddy Shafa cikinta arman yayi ya ce " Cutie kodai nayi ajiya ne a cikin nan yake sanyaki amai da tashin zuciya"cikin shagwaba ta ce "Hero ka manta wancen cikin na twins banyi wani lauyayi ba sai nakega kawai ciwo ne fa " Naila ce ta rugo da gudu ta fad'a jikin Aira nihal kuma ta fad'a jikin Arman cigaba da hirarsu sukayi ARMAN ya ce "Amma ai saikanakega baizama lalle Duka biyun ya zama iri daya d'aukar cikinsu sainakega kowanne da banbancinsa nidai ban yarda ba cikine dake cutie" Uhm Nidai ka daina cewa haka hero ciwone kawai"Naila ce dake tsotsar yatsa Duka sunajinsu ta kalli Aira ta ce "Cuty(Cutie) itakuma Nihal ta kama Sajen Arman ta ce " Helo(Hero) Wara idanu a tare Aira da Arman sukayi Arman ya ce.....✍🏿
Chapter 100 · 0% Book details