Sashe 77
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
.....Finally dai Kin kusa zama real Mrs Arman "Dariya Aira tayi tare da rufe fuska nan suka shiga yi mata tsiya itadai bata tankasu Dan yau jinta take kamar salla Abu kamar wasa. Bayan barin Aira wajen Bappa ya kalli Mummy ya ce" to yanzu sai mu jira lokacin da zata gama idda sai a daura Auren "Dagowa Mummy tayi ta ce " Bappa ai a tunani na babu iddar wancen mijin a kanta bai d'ora mata idda ba"Kallonta yayi ya ce "kun tabbatar kuwa Fatima" Eh Baffa haka maganar take"Ajiyar zuciya Baffa ya sauke ya ce "masha Allahu abu yazo cikin sauki To ke yanzu Fatima ya kike ganin Abun zai kasance zuwa yaushe kikaga za a D'aura Auren Dan banson abun yad'au nisa " Bappa duk yanda ka yanke Amma ni yanda naso a had'e da bikin Maryam tunda kaga saura wata guda sai a game ayi sannan an kikkimtsa komai "Hakan yayi to Allah ya kaimu lokacin yanzu sai a fara shirye shirye har zuwa lokacin" Cewar Bappa "Arman ne ya kalli Mummy tare da marairaicewa ya ce " Mummy Wata guda baiyi nisa ba"Jefa mishi Mafirfici Mummy tayi tare da cewa "tashi ka bamu waje marar Kunya" Gwaggo ko kama hab'a tayi ta ce "nikam inaga ikon Allah" Murmushi Bappa yayi ya ce "Yaran zamani ne sai hakuri" Barin d'akin Arman yayi yana murmushi ga kuma haushinshi na Wata guda da akasa shi yaxaci ma cewa za ai gobe kawai a daura musu Aure ya tafi da Cutie d'inshi Nan dai su Baffa sukaci gaba da tattaunawarsu Inda daga karshe magana ta tsaya akan wata guda mai zuwa Za a daura D'akin su Maryam Mummy ta nufa Inda ta tarar sun sanya Aira tsakiya sai tsokanarta suke"Murmushi tayi ta ce "Dan Allah ku barmun y'a haka Karku takura mata Bata da lafiya " ta fad'a tare da zama Gefen Aira ta tab'a jikinta taji da d'an zafi"Aira ko duk kunyar Mummy ta kamata kasa tayi da kanta "ya jikin daughter me kikeji yanzu" Cikin k'asa da murya ta ce "Bakomai mummy" Kama hannunta Mummy tayi ta ce "ki saki jikinki dani Banson d'ari_d'ari matsayin uwa zaki d'aukeni ba suruka ba keda Arman Duka d'aya na daukeku ban daukeki a suruka ba ki saki jikinki dani kinji " Gyada mata Kai Aira tayi ta ce "To mummy" Murja Mummy ta sanya taje ta zubo abinci da kanta ta dinga bawa Aira a baki gwanin sha awa har saida ta tabbatar ta koshi tukwana ta d'auko Ledar maganin da Dr ya rubuto musu ita ta dinga b'alla mata tana bata tana sha tana Yatsine fuska tare da rumtse ido a haka harta Shanye magungunan Mummy ta mik'awa Maryam ta ce "Amshi kinfi wad'anchan nutsuwa da lokacin shansu yayi ki tabbatar kin bata Tasha Sannan ki kula da cin abincin ta kinji" Dariya Maryam tayi tace "To mummynmu" Hasina ce ta ce "Kai Mummy kenan mu bamu da nutsuwa" Zadai Kuyi nan gaba Idan na Aurar daku "Dariya sukayi nan suka cigaba da barkwanci da Mummy Wanda har Aira Dan Mummy mace ce mai sakin fuska Duka d'iyan k'annenta da yayyunta d'aukarsu take tamkar nata ga bata girman kan Wasa da dariya dasu wani lokacin. Cikin kwana Ukku Aira ta warke garas kamar bata tab'a ciwo ba saboda kula da shan maganinta da Mummy suke gashi biyu aka had'asu hada na hausa ake bata tana sha ganin taji sauk'i ya sanya hankalin Mummy kwanciya Fitacciyar mai gyaran jikin Amare tundaga dilka k'amshin jiki Da sauransu Mummy ta daukota daga Sudan akan ta gyara mata y'arta na wata guda Bayan ta biyata mak'udan kudade gidan yaya Nasir Mummy ta sanya Aira ta koma Dan a gyarata a nutse Matar yaya Nasir d'in Daman itama gwanar gyaran jikice Gata tana da kirki mahaifiyar Hasina da Maryam " Ita kuma Murjanatu d'iyar kanwar Mummy ce mai biya mata Amina ita tana aure ne a gombe Su kuma suna zaune ne a gidan kakanninsu Su ukkun Sosai Aka shiga yiwa Aira gyara na musamman Wanda cikin kwana biyu tuni harta sauya ganin komai ya fara daidaita ya sanya Mummy bankwana da Yola Ta koma katsina Daddy tayima dabara ta ce "zataje Dubai domin sayowa Maryam kayan daki bikin yanzu saura sati ukku" Cikin sauki Daddy Ya amince mata saboda daman duk bikin da za ayi yawaici na family d'insu itake d'aukar nauyin Kayan daki Hakan yasa Shima ya k'ara mata da 15 million akan ga gudummawarshi Godiya Mummy tayi mashi Bayan ta ce mashi daga Chan Yola zata wuce Har sai Angama bikin nan ne ma dak'yal ta samu daga karshe ya yarda washegari Mummy ta wuce Dubai domin hadoma Tilon d'an nata Lefe tare kuma da kayan d'akin Aira da Maryam. Arman duk ya shiga busy saboda Rashin samun ganin Aira da bayayi Dan tunda aka fara mata gyaran jiki ya daina ganinta Wanda Mummy Ce ta sanya a hanashi ganinta hakan sosai yake damunshi itama Airar sosai take son taga sahibin nata yanzu sati guda kenan ana mata gyara Wanda idan ka ganta saika rantse ba ita bace Saboda wani fitinannen kyau da Haske data Kara ga duk Inda ta gitta tabar wajen Sai Ya bide da k'amshin ni ima da dad'i ga k'iba data fara ta murmure tayi kyau saboda kullum Safina Matar yaya Nasir saita dafa mata farfesun kaji Wanda take hadashi da magunguna kuma ta tsare Aira dolenta saitaci kuma ta Shanye romon dukda ba jin dad'inshi take ba ga kuma lafiyayyen tuk'ud'i da ake dama mata mai dad'in gaske kullum hakan yasa tuni ta cicciko ramar nan Duka babu"Yau Arman ya gaji hakan ya sanyashi zuwa gidan Goggo saboda gidanshi dake Yola ya koma Dan bayason zaman hayaniya gidan Baffa ko baya rabuwa da mutane yana zuwa ya sanya yaro.ya kira mashi murja Dan yanzu daga husina sai Murja saboda Maryam tare ake musu gyara da Aira Bayan ta fito kallonta yayi yace "jeki sanyo hijab ki rakani Wani waje" Cikin Sauri taje ta sanyo hijab d'inta Ya shiga mota itama ta shiga yaja sukabar gidan batare da ya kalletaba ya ce "Gidan Baba Nasir zamu dabara zakiyi ki fitomun da Aira" To yaya "ta fad'a suna isa Arman yayi parking a waje ita kuma Murja ta shiga koda taga Aira dak'yal ta ganeta " Ya subhanalla Ta fad'a tana wara idanu"Dariya Mai gyaran jikin tayi "Zaunawa Murja tayi tare da kama hannun Aira ta ce " Sis Kinga kuwa yanda kika koma wlh kin zama sak baturiya wlh bame kallonki ya ce "a k'asar hausa aka haifeki ke Kinga yanda kika koma kamar baki tab'a ganin rana ba jifa jikinki laushi kamar Auduga yo ko Auduga wannan kin fita laushi yacin"Dariya Aira tayi ta ce " kai sis kin iya zuga fa"Ai ba zuga bace Gaskiya Ce wannan yaya Arman ya ganki ai susucewa zaiyi ya ce "Sai an d'aura yau” Dariya Aira tayi tare da K'asa da kanta Sosai tayi missing habibyn nata "kama hannunta tayi tare da janyo mata gyale ta yafa mata ta ce " zo kiji wani abu"Kallonta mama Safina tayi ta ce "Ina kuma zaku da ita Bata fita Ai in ana gyaran jiki ba ashiga rana" Marairaicewa Murja tayi ta ce "Aunty wata magana ce fa kawai zan fad'a mata ba waje ba zamu fita muna bakin Barrander " bata Kara cewa komai ba Yayinda cikin saurin Murja taja hannun Aira bata direta ko ina ba sai Gaban motar Arman ta bud'e mata tashiga ita dai Aira ta zama hoto "murmushi tayi ta ce " yaya na gama aikina saura kuma tukuici"Bandir d'in y'an Dubu_Dubu ya mik'a mata tare da cewa "ga tukuicinki Ya fad'a yana jinjina mata hannu Rufo musu kofar Murja tayi tana Dariya ta maza ta tari taxi saboda tasan ta koma ciki Aunty Safina Masifa zatayi mata "" Wow"Arman ya furta lokacin da ya juyo ya kalli Aira da yaga ta sauya mashi ta k'ara wani fitinannen kyau Ga k'amshin dake tashi daga jikinta tunda ta shigo motar ta turnuke da k'amshi "murmushi Aira tayi tare da d'aga idanunta a hankali ta saukesu akan na Arman daya kafeta da idanu bako k'iftawa " Murmushinshi mai tsada ya sakar mata ya ce "Kinga kuwa Yanda kika koma cutie ai da har zance kodai sauyamun Matar akai bakigaba yanda kikayi kyau" Dariya Aira tayi tare da rufe fuska"yau kuma kunyata akeji "Murmushi tayi tare da sauke hannun langabar da kai tayi A hankali cikin zazzak'ar muryarta mai sanyaya zuciyar mai sauraro ta ce i really miss you my Yaya "Kama.lallausan hannunta yayi Wanda yakejinshi tamkar auduga take taji wani abu ya tsargarmasa tundaga samar kansa Saurin rumtse ido yayi tareda bud'ewa ya Kalleta a hankali ya ce " miss you too my cutie nakasa daurewa jure rashin ganinki ke naga kamarma bakiyi missing d'ina ba"Wara idanu tayi ta ce "injiwa yaya ai nafiyinma missing d'inka yana rik'e da hannunta yana murzawa ya ce " Uhm Gaskiya Mummy na gyaramunke tanason d'anta ya shana da yawa"rufe fuska Aira tayi ta ce "Uhm kai yaya" Murmushi yayi tare da cire hannun data rufe fuskar dashi ya ce "Kinsan bansan kunyar nan Please kidaina Zata Takuramun da yawa karkijemun da ita gida ki barta ma tun anan " kasa da kanta Aira tayi batare da tace uffan ba"Zaki daina jin kunyartawa ko cutie"?Dagowa tayi tare da marairaicewa ta ce "My yaya ai kunya wazibi ce ga kowace y'a mace ka manta manzon Allah S A w ya ce duk... Rufe mata baki yayi tare dayin Dariya ya ce " ya isa malamata shine za a janyo mun hadisi Naji "Dariya tayi Kad'an ta ce " yaya kenan"b'ata fuska yayi ya ce "Daga Ranar Da aka daura ki tanadi sunan da zaki dinga kirana dashi Dan bazan k'ara Amsa yaya ba" murmushi kawai tayi tare da girgiza kai ta ce "Uhm " Uhm "Shima ya maimaita a tare sukayi Dariya sun.kwashi awa biyu a motar suna shan hira Airace ta Kalleshi ta ce " Yaya bari na koma ciki karsu zaci wani wajen naje"Harkin gaji da ganin Yayan naki "ya fada yana langabar da kai" marairaicewa tayi ta ce "Nina isa na gaji da ganin yayana abun alfahari na bank'i mu Dawwama