← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 127

Sashe 33

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 9 min read

*ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali Naira 200 kachal katin Mtn ta wannan number 07026166536 karku fitarmun da littafi mu rikewa juna amana please*

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[6/17, 10:08] Hajo hajo: 🅿️.......*47&48*

Ta na Jan tsaki ita d'aya Ta na nan zaune har Mamy ta dawo kallonta Mamy tayi ta ce "har yanzu baki gama tsakin ba " Turo baki tayi ta ce Na gama Mamy Dan Allah ban d'ari biyu"Harararta Mamy tayi ta ce "me zakiyi da ita ko wayan da kikamun ne zaki sake" Dariya Aira tayi ya ce "a a wlh Mamy Choculate zanba Haidar ya sayomun " ke bazan bada ba sai shegen shan zak'i zafi duk ya cinyeki"Dariya tayi ta re da tashi ta ce "Ni bani da zafi Mamy bari naje Allah ban iya bacci bansha choculate ba Duka nawa sun k'are " Tana zuwa ta haye Gado ta janyo wayarta kiran yaya Arman tayi yana kira cikin shagwaba ta ce "Yaya choculate d'ina sun k'are " Ba ko gaisuwa cutie ya fad'a cikin husky voice d'inshi"Uhm ai mun gaisa dazu shiyasa to ina yini"Murmushi yayi ya ce "lafiya qlau uwar y'ar shan zak'i " cikin shagwaba ta ce "Kai yaya kaima haka zakace nidai Allah choculate d'ina sun k'are ka kawomun ko na sanya maka kuka" Dariya yayi ya ce "to yi kukan muji " Diddira kafa Aira ta fara ta fara kukan shagwaba na k'irk'ira "ARMAN me zaiyi inba Dariya ba ganin zatayi na gaske ya sanyashi cewa " sorrrry my cutie kiyi shiru yanzu zansa a kawo maki"lokaci guda tayi shiru tana Goge hawaye Dariya ta yi ta ce "da gaske my yaya" gaske mana idan yazo zan kiraki sai mai gadi ya lek'a ya amsa"tsalle ta daka ta ce "yeeeee my yaya thank you so much I love youuu so much I love you with All my heart my sweetheart" murmushi Arman yayi ya ce "I love you too my prince's you deserve more than that Amma ki daina shan zakin nan da yawa karkiga ina biye maki yana da illa Kinga kwanaki ya fara sanyaki ciwon ciki lokacin period "Uhm to yaya ta bashi amsa Yana kashewa ba ayi minti Talatin ba ya kirata ya ce ta lek'a ta amshi sakonta wajen mai gadi cikin Sauri ta mik'e tana murna ta fita palour lokacin Su Amma harsun dawo bata Ko saurare su ba ta fita tana zuwa Baba mai gadi ya mik'a mata k'atuwar Leda har rinjayar ta take tana komawa palour suka ganta da leda Mamy ta ce " wannan Ledar fa "Sosa kai tayi tace " kayan guga ne"dak'uwa Mamy tayi mata ta ce "wannan ne kayan gugar ban mugani" badan Aira taso ba ta mik'awa Mamy zata daga Aira tayi saurin zuwa ta amsa tace Dan Allah Mamy ba saikin daga ba "Saboda baki da Gaskiya ko" a a Mamy to kawo na Daga tana amsa ta shiga dagawa choculate ne manya manya masu tsada sai k'atuwar robar ice cream da juice kala kala gefe kuma an nannade Kaza hada zafinta "kallon tuhuma Mamy tayi mata ta ce " wannan daga gidan ubanwa Aira bansan Rashin ji wlh kodan Kinga ina maki lakwa lakwa "Sosa kai Aira tayi ta ce " Dan Allah Mamy ki bari anjima kinmun fadan Yaya Arman ne fa ya bada a kawoman"Duka a baya Mamy ta kai mata cikin Sauri Aira ta tashi ta kwashi kayanta tayi ciki Tana zuwa ta boye choculate d'inta Haidar ko na ganin Banza ta samu ya biyota shida amma a tare sukaci Wanda suka iya ci sauran Haidar taba ya kaiwa Mamy da Mama mamy ta ce " ta k'oshi"Mama ko ta amsa taci kayanta Ta ce "Ai wlh Rahama indai akan Yaran nan ne kingaji ki bari Koba Aira da Mujahid ba Ai kika bi ta tasu tuni jininki zai hau gwara kawai mu sawa sarautar Allah ido"Wlh yaya nima na sa musu idon ni tsoron Abbansu kawai nake idan ya juyo kanta wannan shirun nashi gani nake ba banza ba baki ganin duk ya zuba mata ido kuma ita sakaran bata sanma Annabi ya k'aura ba" Saidai muce kawai Allah ya kyauta Dan Alhaji bai shiru a banza amma kuma kila ya fara Saukowa"hmmm kawai Mamy tace tacigaba da tunani.
Bayan magriba Har Aiport Abba ya raka amininshi Abba yaso ya kwana Amma alh Yusuf yaki ya ce "Karka damu Abokina ai zan dawo kusa insha Allahu" To shikenan nima zansamu na shigo"cewar Abba"murmushi Alh yusuf yayi ya ce "Allah da gaske abokina gaskiya fa y'arka ta na da kyau Alh Ta burgeni wlh " murmushi Abba yayi tare da girgiza kai ya ce "Madugu kenan Har Alh yusuf ya tafi yana yiwa Abba zancen Aira.
Bayan Kwana biyu da tafiyar Alhaji Yusuf ya kira Abba Bayan sun gaisa Alhaji Yusuf ya ce " Maganace a bakina Abokina amma ta na da nauyin fad'a Inajin nauyi sosai kuma ina fargaba"Wace magana kenan Alh Madugu ka fad'a kawai kai tsaye "Abba ya fad'a " Alh Yusuf ya ce "A Gaskiya Alhaji bazan b'oye maka ba wallahi tun sanda naga y'arka Hajara Zuciyata ta kamu da sonta Mai tsananin gaske Tunda na koma gida wlh alh bana iya bacci da na kwanta ita nake gani kwata_kwata hankalina ya kasa kwanciya sainazo zankiraka na fad'a maka nauyin maganar tasa na kasa Dak'yal yanzu nayi jarumta har na iya fada maka abunda ke zuciyata a Gaskiya na gani Ina so Indai ba ayi mata miji ba ina ciki dukda dai nasan na manyanta shine na kira na nemi amincewarka Allah yasa ba ayi mata miji ba Kuma za a amsheni " Daga bangaren Abba sosai yayi mamakin maganar data fito daga bakin aminin nashi wata zuciyar kuma ta ce "Alhamdulilla wannan babbar dama ce ta zo maka cikin sauk'i " Ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce "To Alhaji maganar Gaskiya banyi mata miji ba Kuma kai ba mutum bane da za ace yana da wani aibu da baza a bashi Aure ba tare muka taso nasan halinka kasan nau maganar Gaskiya kai tsaye zan amsa maka ni mahaifinta na baka ita " Ajiyar zuciya Alhj Yusuf ya sauke sosai yayi mamakin amincewar aminin nashi cikin Sauk'i cike da farinciki ya ce "Nagode nagode Alhaji bansan da wani yare zanyi amfani wajen gode Maka ba Tabbas kayimun babbar kyauta ni kuma insha Allahu bazan baka kunya ba insha Allahu zanriketa da amana Saidai kuma wani hanzari ba gudu ba ka fara tuntub'ar yarinyar kaji ta bakinta Kasan yaran yanzu sai tace Nayi mata tsufa zanso na samu amincewarta tukwana " karka damu Alh Madugu bani da matsala da ita duk umarnin da na bada dashi ake amfani Dan haka indai da gaske kake kana son yarinya Magana ta k'are bayan anyi Aure ka nemi yardartata"Alhamdulilla to shikenan nagode sosai Alh ko ince Abba dan yanzu kuma ka zama uba Allah ya saka da alkhairi "Dariyarsu ta manya Abba yayi ya ce " Madugu kenan Yanzu nan da kwana biyu zanyi shawara sai na fada maka ranar da Zaka turo magabatanka Dan bansan abun ya dau kwanaki sosai Alh Madugu ya shiga Jerawa Abba Godiya shikan kakarshi ta yanke sak'a bai tab'a tunanin Abba zai amince mashi cikin Sauk'i haka ba Abba ko suna gama waya hamdala yayi ya ce "Allah na gode Maka da ka kawomun haryar rabuwa da yarinyar nan cikin Sauk'i bata daukomun magana ba".tundaga ranar Abba da Alh Yusuf suka shiga daidaita maganar ranar da magananta Alh Yusuf zasu turo Babu Wanda Abba ya sanarwa Cikin gidan Aira ko yanzu Hankalinta kwance yake Dan yanzu ba mai takura mata ko sa idon da Abba ke mata ya daina ga sako da Arman yake badawa a kawo mata kullum take amsowa a gurin mai gadi a haka har akai sati guda Ranar Asabar Aira na kwance sai shan love d'inta take da Arman Ta na shan choculate d'in da ya kawo mata Sun kwashi kusan awa Ukku suna waya Arman ne ya ce" Gaskiya cutie na gaji wlh Kawai zanzo na tinkari Abba da magana kai tsaye Ayi mana Aure wlh na gaji "Dariya Aira tayi ta ce " kai my yaya me kake ci na baka na zuba ka bari mana su k'ara hucewa Dan wlh Abba ya fara hucewa yanzu ya daina Takuramun kuma fa rannan har ganina yayi na amso sako amma baice uffan ba Kuma fa ranar nan ma da yaganmu tare ko uffan bai ceba "Allah my Love da gaske kike" wlhko yaya"To Alhmdllh Allahsa ya fara hucewar Dan kinsan ni nafijin Abba wlh Daddy banajinshi sosai yana Saukowa wani time din idan ya hau shikuwa Abba baya Saukowa"murmushi Aira tayi ta ce "Shima zai sauko " daga palour Aira ta jiyo y'an gidan su na oyoyoy ga aysha cikin Sauri ta mik'e ta ce "Yaya sai anjima Aunty Aysha tazo " tafada tana kashe wayar tare da ajeta a guje ta ruga palour Tana zuwa kuwa taga Ayshar ce Ai da gudu ta je ta d'are ta cike da farinciki ta ce "oyoyoyo my Aunty " Rungumeta Aysha tayi ta ce "oyoyoy sis nayi kewarki da yawa" Cike da farinciki Aira ta saketa ta kama hannunta ta ce "Nima nayi kewarki Aunty Gaskiya nayi farincikin ganinki sannan ta bata fuska ta ce " ya jikin naki Aunty Kinji sauki ba abunda ke maki ciwo dai ko"murmushi Aysha tayi tare da lakutar kumatunta ta ce "Na warke sis " Zaunawa sukayi kujera D'aya Aira tana Rungume da Aysha ta gefenta ta ce "Allah ya k'ara sauki Aunty ya kawo mana wani mai amfani Amma dai yini kikazo mana ko aunty" Ameen my Aira eh yau ina nan har magriba "yeyeyeye yawwa my love " Aira sai murna take sai nan nan take da Aysha ta kawo mata wannan ta kawo mata wancen"Mama tayi dariya ta ce "Ai yau kuma Aira ba zama" Mamy ta ce "Ah ina zata zauna K'auna guda na gida " Dariya Aysha tayi ta ce "Ai dole ai zuwan nata ne" Murmushi Aira tayi ta ce "Ai ina mugun sonki sosai wlh Aunty" Abba ne suka ga ya shigo da goro bayanshi Baba mai gadi d'auke da cartoons d'in biscuit da su halawa "a ajjewa sukayi a palourn Abba ya Sallami mai gadi ya fita neman kujera Abba yayi ya zauna tare da sauke ajiyar zuciya Duka d'akin Kallon abubuwan da Abba ya shigo da su suke cike da mamaki Mamy ce ta kasa shiru ta ce " Abbansu wadannan kayanfa naga su goro"Kayan sa Auren y'arki ne"Abba ya fad'a yana Danna waya"Cike da tashin hankali Mamy ta mik'e ta ce "Sa Aure kuma wace y'ar tawa" kina da wace y'ar ne da ta wuce waccen "ya fad'a yana nuna Aira" Cike da Tashin hankali Aira ta mik'e Aysha Da Mamy ne suka hada baki wajen cewa"sa Aure kuma?Aira ko kasa magana tayi sai kallon Abba ta ke jin maganar tashi take kamar a mafarki Mama ce ta ce "Alhaji ka sanyamu cikin duhu ka warware mana Dan Allah " Ai daman warwarewar nazo maku inason dukanku ku bud'e kunnanku ku saurareni da kyau"Wannan kayan da kuke gani na sa Auren Mamana ne Aira Tare da Amini na Alhaji Yusuf Madugu sokoto Tun sanda Yazo ya ganta yarinya tayi mai baiyi kwabron baki ba Ya fad'amun ni kuma na amsamai na bashi ku godewa Allah ma da da kanshi ya ce ya na sonta dan ina shirin bada ita sadaka Yau magabatanshi sukazo da kayan sa auransu da toshi An sanya Auren wata Guda Masu zuwa na fad'a muku ne yanzu Dan kar kuji daga sama Dan haka sai ku fara shirin biki "Kutumar Uban nan Suka tsinkayi Muryar Mamy daga sama cike da Masifa da tashin hankali ta mik'e ta ce........✍🏿
Chapter 33 · 0% Book details