← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 127

Sashe 37

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai Arman baisan lokacin da wayar ta sulale a hannunshi ba Sakinta yayi Tim a k'asa "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un kawai yake maimaitawa dafe kanshi yayi kamar Wanda Aka tsikara haka ya tashi ya ce " no bazaiyu ba wlh impossible wlh duk abunda yake kusa dashi ya hau wullawa cikin tashin hankali ya kwashi wayoyinshi yayi waje yana zuwa ya kwalawa mai gadi kira ya ce "Ka maza second biyu na baka ka budemun get yana gama fad'ar haka ya tafi ya d'auki motarshi 360 ya jata yana zuwa bakin gate har mai gadi ya bud'e a guje ya figi motar ikon Allah ne kawai ya kaishi Airport lafiya cikin k'ank'anin lokaci ya yanki ticket zuciyarshi ba abunda take In banda zafi kamar zata fashe kowa ya Kalleshi lokacin zakasan yana cikin tsananin b'acin rai idanunshi sunyi jawur kamar garwashin wuta k'arfe bakwai da wani Abu jirginsu ya d'aga zuwa kano.Aira ko ganin Arman shiru tayi ta magana shiru ya sanyata fashewa da kuka jikin kofa ta durkushe kuka kawai take gwanin ban tausayi Bangarensu Abba ko sosai ranshi ya b'aci matan da suka kawo kaya suda aka batawa rai saiyadawo su sukebawa Abba hakuri sukace ai d'ane ka haifeshi baka haifi halinshi ba ba yanda ba suyiba akan a janye maganar Auren nan tunda bata so suka kira Alh Yusuf sukayi mashi bayani shi ko da yake Allah ya d'ora mai son Aira cewa yayi ba abunda za a fasa idan an d'aura Auren zata soshi Ai Abba ma ko haka yace shi da Mama Halima suka basu hakuri akan Abunda Aira tayi musu sukace ba komai sosai akayi musu sha Tara da arziki Da zasu tafi Mama Halima ce Bayan Tafiyarsu ta je ta samu Mamy Tagumi ta iske tayi ta na hawaye dafa ta Mama Halima tayi ta ce "a Gaskiya zan fad'a maki Rahama kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki ki fawwalawa Allah komai wannan damuwar da kike bata sa komai bata hana komai kila Allah ya nufa matarshi ce ba abunda za a fasa kiyi hakuri sannan kiba y'arki hakuri kiyi mata fatan Alkhairi kawai ki bari tayiwa mahaifinta biyayya tunda Kinga ya kafe idan kika nuna Rashin sonki kamar kina k'ara zuga tane ki mata fad'a ta nutsu ta rabu da mahaifinta lafiya sannan ta cire Mujahid a ranta tunda Allah ya nufa kila bashi bane mijin dukda dukanmu ba haka muka so ba ki saki jikinki ayi hidimar biki dake naga ko gayya bakiyiba dan Allah Rahama ki kwantar da hankalinki ki kwantar da na y'arki hakuri zamuyi mu barwa Allah sauran tunda munyi abunda zamu iya" Haba Halima taya zan kwantar da hankali na bama wannan ba yanzu abunda yafi tadamun hankali idan na tuna gidan kishiya za a kaita da y'ay'a ta yaya Aira a y'an shekarunta zata iya da kishiyar da ta haife tamayi kusan jika da ita ina zataji da d'iyan miji ki duba fa kiga nisan sokoto Halima nifa gani nake kamar sayarmun da y'a ne wannan Abun Sokoto fa ina zata iya kishi da sokkwatawa me ta sani game da kishi "Ajiyar zuciya Mama Halima ta sauke ta ce " ai akwai Allah shi zai tsareta insha Allahu ki daina damuwa da wannan nima Inajin wannan din amma Addua zamuyi tayi mata sannan muyi mata nasiha ta zauna da kowa lafiya"Sosai Mama Halima ta dinga bawa Mamy baki.Arman koda ya Iso kai tsaye Gida ya wuce cikin tashin hankali Mamy ta tareshi tace Lafiya son na ganka da dare tsaka Baka sanarmun kuma zaka zoba naga kamar ma baka cikin nutsuwa Arman bai iya magana ba Dan in yana irin cikin wannan tashin hankali bai iya magana lura da haka ya sanya mummy shiga damuwa kamo hannunshi tayi kamar yaro tare da zaunar dashi itama ta zauna kwantar dashi tayi saman cinyarta tare da Daddab'a bayanshi ta ce "Calm down my son yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi " Dan haka take mashi idan ya shiga damuwa Arman huci kawai yake tare da lumshe ido yanason yayi control d'in zuciyarshi Sosai Mummy take Abu d'aya dukda batasan meya sanyashi cikin wannan halin ba ta kwashi kusan Awa guda yana kan cinyarta tana lallaashinshi sai Chan taji ya na sauke ajiyar zuciya hamdala tayi azuciyarta alamun ya dawo daidai kenan cike da damuwa ta ce "me yake damunka Arman ka fad'aman please" Arman yana daga kan cinyarta ya lumshe idanunshi tare da bud'esu a hankali kamar mai koyan magana ya ce "Mummy wai Aure zasuyi mata" Wacece za a yiwa Auren "Aira Mummy wlh Mummy inasonta sosai please karki bari a rabamu itad'in rayuwa ta ce Bazan iya cigaba da rayuwa babu itaba " Sosai gaban Mummy ya fad'i tasan abunda Arman yake fad'a Gaskiya Dan son da ya ke yiwa Aira ya zarce misali sosai ta shiga damuwa cikin damuwa ta ce "Aure kuma son Waza a aura mata Bayan sunsan kuna son junanku" Arman baisan lokacin da wasu zazzafan hawaye suka zubo mashi ba ya ce " wani ne Abokin Abbanta Ranar Friday Auren Mummy Dan Allah karki bari ayi Auren nan wlh ni nake sonta nasanke uwace ki tausaya mun nasan Daddy bazai saurareniba ammake zaki saurareni Yin Auren nan daidai yake da rasa rayuwata idan ba so kuke ku rasa ni ba to kusa a hana auran nan please ya k'arasa fad'a tare da mik'ewa ya rik'e hannayenta biyu "Rufe mashi baki Mummy tayi karo na farko kenan da ta tab'a ganin hawayen d'an nata da girmanshi Sosai itama ta shiga damuwa Dan a duniya ba abunda take so sama da Arman d'a daya tilo da Allah ya bata girgiza mashi kai tayi tare da Goge mashi hawaye ta ce " ka kwantar da hankalinka kaji Arman d'ina Insha Allahu Aira taka ce zansamu Daddynku yanzu yaje suyi magana da d'an uwanshi fatan mudai ya yarda"yawwa Mummy Dan Allah kuyimun kokarin wannan "Mummy duk yanda taso da Arman yaci abinci kasawa yayi har a baki ta bashi amma ya cije sosai ya bata tausayi lokaci guda ya zama wani so silent A Daren ta samu Daddy ba irin magiyar da batayimai ba akan yaje wajen Abba suyi magana Dan Allah a janye Auren nan Ya nemawa Arman Auren Aira amma Daddy fir yaki cikin hawaye Mummy ta ce " Ammafa kasan d'anmu zai shiga cikin wani hali me yasa kuke zafafa Abu ne ku bari yaran nan su Auri junansu tunda suna so za a sanya rayuwarsu cikin wani hali"ko zai mutu wlh bazanje ba akanshi wace irin Maganace mahaifinta bai fad'amun ba shine kukeso na je a k'ara fad'amun maganar da zan kwana ban rintsa ba to badaniba bazanje ba idan ke kin matsu kije "Daddy na gama maganar ya fice daga d'akin sosai Mummy ta shiga damuwa Mama Halima ce ta fad'o mata a rai ita ta kira ko zata samu ta taimaka mata amma maganar da taji daga bakin Halima ma ya sanyata Kara shiga damuwa Dan labarin komai Mama Halima ta bata akan ba yanda basuyi da Abba ba Amma ya kafe hatta Inna ta kasa tankwarashi Saidai kawai mu barwa Allah zab'i"washegari Arman har ya fad'a sosai ya shiga tashin hankali da Mummy ta fad'a mashi yanda sukayi da Daddy da kuma yanda sukayi da Mama Halima kamar wani zaki haka ya mik'e kamar Wanda aka zabura ya ce " impossible wlh Mummy bazaiyuba Aira tawace Dan ni kad'ai aka yita bazan tab'a zuba ido ta zama mallakin waniba itadin rayuwata ce munyiwa juna Alk'awarin bazamu tab'a rabuwa ba muddin na bari ta auri wani Tabbas munci Amanar soyayya Yana gama Fad'ar haka ya figi makullin mota kamar zai tashi sama ya fice Mummy ba binshi baiko saurare ta ba mota ya figa a tamanin a lokacin wajen karfe Takwas na dare ranar Aira a d'aki ta yini taci kuka kamar ba gobe masu Lallashinta harsun gaji ga Arman tayi ta kiranshi kashe Wayarshi tana kwance tana hawaye ga k'aramar wayarta dake hannunta taji tayi ringing cikin Sauri ta d'auka kuka ta fashe dashi ta ce "Yaya kai kadaine nakejin muryarshi a yanzu Naji sanyi a raina plx karkayi fushi dani wlh babu masaniyata " Daga bangaren Arman taji muryarshi ya ce "bana fushi dake Aira bantaba fushiba tashin hankalin da na shigane yasa ban waiwayi waya ba ki kwantar da hankalinki rabuwa ta dake abunda bazai yu bane kisa a ranki Auren nan babushi muddin ina numfashi alk'awarinmu bazai tafi a banza ba" Cikin kuka Aira tace "taya zan kwantar da hankalina yaya Bayan baka tare dani" kisa a ranki a ko ina ako wani hali ina tare dake my Aira ked'in jinin jikina ce taya za ayi na samu ganinki yanzu"Wlh yaya yanzu babu ta yanda zaka ganni Abba ya sanya mai gadi tsaro sosai babu ta yanda zan fito "Sosai Arman ya shiga damuwa cikin zuciyarshi Dan son kwantar da hankalinta ya ce " karki damu dole ne ki baro gidannan muddin munason cigaba da rayuwa kamar kowa Duk yanda zakiyi gobe kiyi ki gudo kina kub'utowa daga gidan ki fito da waya kiyi saurin Kirana "Goge hawayenta Aira tayi Dan tasan kaso ashirin na damuwarta ya ragu tunda Arman yana nan bazai bari Auren nan ya faru ba a tunaninta " To yaya zan kokarta na gani saurin kashe wayar tayi ganin Amma na nufowa k'ofar maza tayi ta boye wayar tare da kwanciya "Amma tace sis bazakije kici abinci ba " bazanciba ta fad'a tana juya mata baya.washegari ta kama laraba kuma ranar ne za a fara hidimar biki ba yanda ba ayi da Aira ba akan ayi mata lalle da saloon Amma fir tak'i su Ummy da sukazo ana musu lalle su sukace itama sai anyi mata taga zasu takura mata hauka tayi ta ce "Bazanyiba d'in nace Bazanyiba dole ne ku rabu dani mana wlh kuka Takuramun zanyiwa mutum abunda bai tunani ta fad'a tana girgiza kai " Allah baki hakuri Ummy ta fad'a Hafsa ce ta ce "kuma ku rabu da ita tunda bataso ai ba dole bane " tsaki Aira taja tare da komawa daki Ta dinga risgar kuka Aunty Maryam lokacin tazo da yaranta daga Lagos cewa tayi ina Airar akace mata tana daki tana sana'ar kukan d'akin ta nufa
Chapter 37 · 0% Book details