← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 127

Sashe 20

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aira ko Arman har gida ya maida ita kullum saisun had'u idan basu hadu ba idan zata tahfex to sun hadu idan ta dawo Innace ta fito Cikin masifa Kallon Aira tayi tare da mik'a mata wayar ta ce " kiramun Mujahid laifin me nayi mishi da ya daina zuwa wajena "Aira ta kira mata Mujahid yana ganin kiran Inna murmushi yayi ya kira cikin Masifa Inna ta ce "

Mujahid ko d'an fari na kashe maka ai sai haka watanka nawa rabonka da gidana "Hakuri Arman ya dinga bawa Inna tare da cewa gashinan zuwa yanzu Lokacin da yazo Aira na zaune akan sopa tana kallon wani series a Bollywood Hankalinta na wajen ya shigo tana ganinshi itama ita yake kallo kashe mata ido yayi girgiza kai tayi ta na murmushi inna ko washe baki tayi ta ce ""

" Ko kaifa mai gidan Har hankali na ya kwanta ashe ma kana garin shine Ko kazo ka gaishe ni ko"To yanzu ba nazo ba y'ar tsohuwa sai a rufe chapter ya fad'a yana zama kan sopa K'asa Inna ta zauna Suka shiga gaisawa da Arman sai zolayanta yake dayake tana son ganinshi yau ko fad'an Babu Kallon Aira tayi da take kallo ta ce .

"Hajara bakiga Mujahid ba ne Kika wani kauda kai" Juyowa Aira tayi ta ce "Na ganshi Inna ta fad'a tana kauda kai" Hakan da tayi duk cikin shirinsune "Salati Inna ta farka ta kalli Arman ta kalli Aira ta ce " Nashiga Ukku ni Halima ba dai Iyayenku sunyi nasarar raba ku ba.

Kallon Inna Aira tayi ta kalli Arman dake satar kallonta tashi Inna tayi Ta kamo hannun Aira ta janyota ta had'a da na Arman ta fashe da kuka ta ce "Karku sake Iyayenku su zama sanadiyar lalacewar daddaddiyar Tarayyarku mai cike da Albarka Na tabbata Allah da abunda ya gani ya had'aku Karku sake ko dad'i ko wuya suyi nasarar rabaku koda bana numfashi Duk sanda alak'arku ta lalace to ina da tabbacin komai ya Riga da ya lalace Iyayenku bazasu tab'a Shiryuwa ba muddin bakwa tare da junanku Kune nake fatan ku zama silar Daidaituwar Iyayenku kuyimun Alkawari Dan Allah bazaku rabu ba kodan ni ko da bana raye" .

Aira tunda Inna ta fara jawabin nan take kuka Rungume Inna tayi Cikin kuka Ta ce "Insha Allahu Inna munmuki Alkawari sannan ma kina raye insha Allahu" Arman ma Rungume Inna yayi cikin k'arfin hali ya ce "da yardar Allah Inna zamu sanyaki Farincikin da kike buk'ata da ranki insha Allahu" Allah yayi muku albarka Ya nunamun Ranar da nake ta tsumayen jira da raina da lafiya"Kallon juna Arman da Aira sukayi sai kuma Aira ta sadda kai.

Washegari Aira na bangarensu ta na Wanki A washing machine Mamy ta lek'o ta ce "Aira idan kin gama ki shirya zaki rakani Gidan Safiya zanyi mata barka" To Mamy Ai na gama ma bari naje na shirya Cikin kankanin lokaci ta shirya a parking space ta tarar da Mamy "Mamy ta ce duk'ursa na goya maki shi " Cikin marairaicewa Aira ta ce "Goyo kuma Mamy ki bari na daukeshi wlh d'annan naki nauyi garai Yaro wata shidda ai Yama wuce goyo ni banma iya goyon ba" Hararta Mamy ta yi ta ce "To yau saiki koya idan dankine wazai goya miki " Dariya Aira tayi ya ce "Maid house mana Mamy yanzu Dan Allah taimaka ki bari na rikeshi a hannu" to Naji raguwa muje Motarta Mamy da dauko tayi mata key suka bar gidan Aira na gaba da Amer a hannunta.

Suna isa gidan Safiya Mamy tayi mata barka Hjy Safiya ce ta ce "Wai Rahama y'armuce ta zama Haka Allah mai iko kice kin kusa Taramu" Dariya Mamy tayi ta ce "Aikodai ku iyaye saiku fara shiri Fita Aira tayi ta basu waje Arman ta kira tayi mashi kwatancen Inda Take cikin k'ank'anin lokaci ya kira ya shaida mata yazo.

tsayuwar Hijab d'inta ta gyara tukwana ta fita A mota ta tarar dashi ciki ta shiga Arman ya ce " kindai maidani bita zaizai ko My cutie duk Inda kikayi ina binki"Dariya Aira tayi ta ce "Yaya kenan ni kuma a kirani da me da duk Inda naje ina kiranka" Sun tab'a Hira Kad'an cikin nishad'i Sun kwashi wajen minti Talatin Mamy koda suka gama fira da Hjy Safiya suka fito sosai tayi mamakin k'in ganin Aira da batayi ba Tana fitowa waje bata ganta ba Aira ko ta cikin mota ta Hango Mamy sosai gabanta ya fad'i ta ce "Na shiga ukku '"

'Kallon Inda take kallo ARMAN yayi ya ce " Daman tare kuke da Mamy"Eh wlh yaya wlh banzaci har zata fito yanzu ba"To yanzu yi Sauri ki fita danma Mamy ce Ai da sauki "Kamar wacce kwai ya fashewa haka Aira ta fito daga motar Sosai Mamy ta kafeta da idanu ganin Fitowarta daga mota Aira ko dukta tsure bin motar da Kallo Mamy tayi Bayan ya tafi Kallon Aira tayi da ta kasa motsi ta daka mata tsawa ta ce " Saikizo mu wuce gida ko"

"Cike da tsoro Aira ta shiga Mota Mamy ta zagaya ta tada Ranta na matuk'ar k'una tama rasa ita ina zata saka ranta game da Lamarin Aira daman basu rabu ba kenan Aira ko duk ta tsure jira take taji zagi ko saukar dukan Mamy amma bataji ba harsuka isa Mamy Saidai ta Kalleta ta girgiza kai ta ma rasa abunda zatace " Suna isa Aira ta ce "Mamy Dan Allah kiyi hakuri" girgiza kai kawai Mamy ta yi ta ce "Allah ya shiryeki Allah ya shiryeki ita kad'aice Addu'ar da zan dinga maki ta fad'a tare da shigewa ciki Aira ko kamar wacce kwai ya fashewa Haka ta shiga part d'in Inna idan ta tuno kuma da karfafa gwuiwar da Inna tayi musu saitaji sanyi A ranta.

Bayan Sati Biyu Da misalin k'arfe goma Na dare Aira na kwance wayarta tayi ringing d'auka tayi Dan tasan Arman ne kad'ai ke kiranta " ki shirya yanzu ina palourn inna zamuje wani wuri,Cike da mamaki Aira ta ce fita kuma Yaya ?ina zamuje a Daren nan "kede kiyi abunda nace kinsan dai bazanyi Abunda zai cutar dake ba Kuma kinfi kowa sanin bansan gardama " Badan Aira ta lamunta ba ta ce To yaya Doguwar Hijab Ta d'auko tare da sanya flat takalmi ta fesa turare d'an Kad'an ta fito a palour ta tarar dashi shida Inna tana fitowa Inna ta ce.

"To kumaza kuje Allah kiyaye" Kallon Mamaki Aira takebin Inna Dashi to ina zasu a Daren nan Arman ko har yayi gaba binshi baya Aira tayi Tana zuwa harya tada Mota da yake ciki ya shigo da ita Aira na shiga suka ja suka bar gidan daman get man ya bud'e musu kofa.

Aira dai zuciyarta cike take ta tunannika kala_Kala"A wani katoton shagon make up taga yayi parking Kallonshi tayi murmushi yayi mata ya ce "muje ko" Itama mayar mashi da murmushin tayi"Ta bishi suna shiga Shagon y'an mata biyu Aira ta tarar Duka sun girmeta Cikin girmamawa suka dinga gaishe da ARMAN ya amsa sama sama Mai kwalliyar ta ce .

"yallab'ai ko ita ce " Gyad'a mata kai yayi ya ce "ita ce so nake kiyi mata kwalliyar da Baki tab'a yiwa wata irinta ba ko nawane zan biyaki" Dariya Zey tayi ta ce "Angama yallab'ai kai kanka dak'yal zaka ganeta" Haka nakeso Rafar y'an dubu ya bata guda biyu Zey sai Godiya take dan yau ta warke Kallonshi Aira tayi Shima ita yake kallo murmushi ya sakar mata bata samu damar mayar mashi ba saboda a tsorace take saikuma ta tuna Ai Arman bazai tab'a abunda zai chutar da ita ba hakan yasa ta saki jikinta.

Fita Arman yayi ya ce zaije ya dawo itadai tana zaune mai make up ta sanyata tayi wanka a toilet d'in Shagon tana fitowa ta bata wata had'ad'd'iyar gown Fara ita kanta Aira saida ta tsorata da ganin rigar Dan bama zata iya kwatanta Misalin kud'inta ba irin rigunan Amaren nan ce Amaren ma sai d'an waye da wane Bayan Aira ta sanya rigar sosai tayi chif a jikinta kamar a jikinta aka d'inka rigar.

Ba b'ata lokaci aka shiga tsansarawa Aira kwalliya ta ban Mamaki saida suka shafe sama da Awa d'aya tukwana aka gama ya subhanalla Ai Ni kaina kasa gane Aira nayi ta sani sauya kamar ba ita ba tayi wata irin masifar kyau Wanda ko mace ta ganta saita yaba da kyan da tayi mai make up cewa take masha Allah a Gaskiya bantaba make up mai kyan wannan ba kodan nayi a jikin me kyau ne kanwata ki godewa Allah Gaskiya yayi miki kyau da baiwa kala kala"

"murmushi Aira tayi ta ce "Nagode hotuna Sosai Zey da abokiyar aikinta suka dinga wa Aira 11:30 Zey wayarta tayi ringing itadai Aira bataji me akace ba daga dayan bangaren Taji dai ita ta ce " Eh Angama Yallabai yanzu haka muna shirin Tahowa da ita ne bada jimawa ba "tana gama wayar itama ita da d'ayar suka shirya cikin wasu Riga da sicket pink rigar siket din bak'i

rigar Anyi rubutu a jiki an rubuta *A & A* k'asar rubutun kuma anrubuta HBD MRS..sauran rubutun taga An rufe da wani Abu ita dai bata tambayesuba har suka gama shiryawa suka fito a wata dalleliyar mota suka shiga Aka jasu suka tafi Basuyi wata diguwar tafiya ba motar ta tsaya Alamun sunzo wajen da zasu Kallon Aira sukayi tare da kama hannunta Zey ta d'auko wani Farin kyalle sai kamshi yake Duka zanan heart ne jikinshi zagayawa sukai suka rufewa Aira idanu dashi itadai kawai binsu take taga ikon Allah.
Chapter 20 · 0% Book details