← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 127

Sashe 2

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan yayi wanka ya sake shiri ya huta mahaifiyarshi da kanta ta dinga feeding d'an nata kamar wani yaro shi kuma sai shagwaba yake mata kamar zaiyi kuka ya ce "Uhm mummy na k'oshi please ki barni haka cikina ya cike"mummy na k'ara d'auko wani spoon din ta ce " Haba son Bafa kaci da yawa ba nasan a can ba wani cin abinci kake sosaiba ha a d'aga bakin saika cinye na plate d'innan".

"Murmushi kawai yayi a haka dak'yal har ya ida cinyewa Dan shi ba mutum bane mai fiyason cin abinci ba ya na gamawa ya Mike tare da kallon Mummy ya ce Mummy zan d'an fita please karki hana" Haba son ko fa hutawa bakai ba daga dawowarka ka ce zaka fita "cikin shagwaba ya ce Mummy ba jimawa zanyiba yanzu zan dawo " To bazaka bari sai ka kara huta wanna"Mummy please" yafada yana hade hannaye,To shikenan Allah ya kiyaye ka kulamun da kanka kuma karka jima"Hug d'inta yayi ya ce "Don't mention my dear mom saina dawo.

Driver kadai ya tuk'ashi Dan bayason yawo da Security wannan Karin ma yayi kyau sai baza k'amshi yake Dan shigar da yayi ta yanzu ma tafi ta d'azu kyau murmushi kawai yake shi d'aya.

Aira suna zazzaune a palourn inna Ita da su Amma,Haidar sai Ummy duk suna shan labari wajen inna sai kwasar Dariya suke banda Aira da tayi jugum Dan yau ko abincin kirki bataci ba Suka jiyo knocking Haidar ne ya tashi ya je ya bud'e Aira da hankalinta na kan k'ofa ganin mai shigowarne ya sanyata mik'ewa a matuk'ar rud'e ba k'aramun surprise d'inta yayi ba shima tsaye yayi ya na K'are mata kallo sanye take cikin wasu English wears Riga da wando red and black kanta bako kallabi sai gashinta da yake a parke Sosai yaga ta k'ara yimashi kyau da girma A d'an kwanakin da yayi bai ganta ba murmushinshi kawai mai tsada yake sakar mata Ai bata San Lokacin da ta Ruga a guje ba tare da Rungumeshi Farincikin da take ciki tama kasa musaltashi da komai Kuka ta fashe dashi cikin muryar kuka ta ce ..........✍🏿

```Hmmmm ya kukaji salon Fans kudai muje zuwa ai ba afara komai ba salon na musamman ne Kudai kawai Had'in kanku nake buk'ata ta hanyar comment da zazzafan sharhi ni kuma zan datse damtse wannan Karin ba wasa a zafafe na dawo kamar yanda littafin yake zazzafa Idan Naji comment da sharhi zaku jini idan kuma Naji shiru nima zaku jini shiru ta hanyar yawan comment ne zan gane labarin zai muku dadi ko akasin haka more comment more typing ``` 💪🏼🤷🏼‍♀️🙅🏻‍♀️

_*Miss Hajo ce*_
[5/23, 18:16] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️...............3&4

“My Yaya why did you turn off your phone for two days i could not find you’’ dad dab’a bayanta yafara cikin sigar lallashi ya ce “ I’m sorry my cutie Babe bansan zaki tashi hankalinki haka ba I did this to surprise you shiyasa “sakinshi tayi tare da turo baki ta ce ‘’uhm My Yaya ni nayi fushi ma tunda da gangan kayimun haka ‘’ta turo baki ta koma kan Kujera ta Zauna ta na turo baki ita ala dole anyi mata laifi”Murmushi yayi tare da binta dan yasan ya tab’o y’ar rigimar tashi kamar zaiyi mata rad’a ya ce.

“Sorry my cutie bazan sakeba kinsan fa duk saboda naganki na dawo kiyi hakuri ki janye fushin kinji little sis”Turo baki gaba tayi ta ce “Ni bazan hak’ura ba “kamar zaiyi kuka ya ce “Too na koma chan kenan “juyowa tayi cikin sigar shagwab’a tace “nayi missing din naka shine zakace zaka koma “ta fad’a ta na aika mashi da hararar wasa lakutar kumatunta yayi yace “Nima kewarki ce ta dawo dani I was joking dan ki hakura “To ai nahakura karka sake “murmushinshi mai tsada ya sakar mata ya ce insha Allah bazan sakeba smile mana kinsan kinfi kyau da murmushi “Dariya tayi tare da rufe fuska ta kwance kanta saman kafadarshi sai sannan yayi ajiyar zuciya yace”fatan dai na sameki lfy”gyada mashi kai ta yi tace “Alhmdllh saidai rashin lafiyar kewarka kuma yanzu na warke hope kazo lafiya ya hanya “murmushi yayi yace Nima lfy nadawo sai dai cutar kewarki kuma yanzu na warke ya fada yana shafar kanta ya ce “kinga yanda kika kara girma kuwa cutie Meye sirrin ko dai inna wani abun take baki “.

Dariya tayi tare da rufe fuska tace “Kai yaya ai kaine ma ka kara girma “Tsinkayi murnar inna sukayi “To fa jarabar ta dawo yanzu za a faramun manne manne da tab’e-tab’e a daki ta karasa fada ta na jan tsaki “Dariya duka sukayi Banda Arman da baifiya dariyaba murmusawa kawai yayi ya ce .

“Haba y’ar tsohuwas daga zuwana bako sannu da zuwa bakiyiwa angon naki ba zaki fara halin “tabe baki tayi ta ce “Akai kasuwa indai kaine sannan daka shigo ko gaisheni bakayiba bama ka ganni a wajenba ka tafi wajen fitsararriyar y’ar lelen naka “murmushi yayi yana kallon Aira yanda take aikawa da inna harara yace “afuwan hajjaju Nina isa na kyale uwar gida ran gida Allah huci zuciyarki ran ki ya dad’e kiyi shekaru irin na dabino “lokaci guda inna ta saki rai ta ce “sannu da zuwa Mujahid ya kasar turawan andawo lafiya “lafiya qlau inna fatan kuma mun sameku lafiya “su Amma ne da Haidar suka gaisheshi ya amsa a tak’aice basu damuba saboda daman sunsan duk gidan nan ba wanda yake sakewa ko doguwar magana ta hadasu sai Aira.

Aira ce ta ce “Yaya ka rabu da inna Neman fitina ne kawai irin nata kaga tashi ma mu fita na baka labarin abubuwan da Akayi Baka nan ta fada ta na mikewa tare da kama hannunshi sukayi farfajiyar gidan Sunajin inna na sababi suka kyaleta.

Sun jima a waje suna ta Hira ta bashi labari na dariya yayi itama haka har akai margriba suna nan saida Mummy ta kirashi ya Sanyashi tunawa da ta ce kar ya jima yace mata yanzu zai dawo kallon Aira yayi ya ce “Baby zanwuce Gida Mummy na kirana “nan ta fara shagwaba ita bata gaji da ganinshi ba dakyal ya samu ya lallabata ya tafi gida da niyyar washegari zai dawo yakaita shan ice cream kuma zai taho mata da tsarabarta.

Daren ranar kowannensu Kwanan farinciki yayi Washegari Aira koda ta dawo daga school Lokacin Tahfex nayi langwabewa tayi tace batada lafiya bazataje ba saboda kar Yaya Arman yazo ta tafi.

Da misalin karfe biyar na yamma ya shigo gidan sosai yayi mata kyau cikin riga ash da black din jeans itama tayi kyau cikin atamfarta doguwar riga ta sa malha tayi daurin dankwalinta tare da fito da gashinta baya sosai tayi kyau Arman ko kasa daina kallonta yayi dan ba karamun kyau tayi mashi ba bayan ta shigo gaban Motar ta ce “Yaya na shirya muje ko”Harararta yayi yace a haka zakije gashin kanki duk waje kuma wannan miririn mayafin zaki yafa jeki ki sanyo hijab “kamar zatayi kuka tace “Dan Allah yaya ka bari muje harfa na shirya kuma idan na koma inna ganewa zatai da inda zamu bakaga gyalenma a jaka na sanyashiba “zakija a fasa fitar wlh muddin haka zaki fita gardawa na gane maki gashi ke ko kishin kanki bakyayi “Yafa gyalan tayi ta saman ka tace “to yaya na rufe kan please karka kara cewa wani abu “badan ranshi yasoba suka tafi dan yana bakin cikin mutane su dinga ganemishi surar Airar shi ba danshi kad’ai yasan kalar so da kishinta da yake “.

Wuraren shakatawa sosai yakaita sai murna da farinciki take tabbas farincikinta yadawo rabon da tashiga farinciki haka tun tafiyarshi london kimanin wata biyu kenan.

A hanyar su ta dawowa a mota ya bata kyautar hadaddiyar zoben gold din daya sayo mata sosai tayi farinciki da murna sai godiya takemai shidai murmushi kawai yake yana kare mata kallo.

Suna isa suka fito Hannunsu makale da na juna sai Dariya take ta farinciki tana zabgamai godiya daidai zasu shiga palourn inna Abba na fitowa Sosai gabanta ya fadi cikin dabarbarcewa ta fara kokarin kwace hannunta ya rike gam tare da galla mata harara kamar zatai kuka tace ka sakeni kara rike hannunta yayi ma .

kallon zaki gane kuranta Abba yayi mata tare da wucewarshi sosai nayi mamakin ganin Arman baiko gaishe da Abba ba saima kauda kai da yayi Abba na wucewa Arman ya gallawa Aira harara yace “ita kuma wannan rikicewar da kikayi ta mecece kamar kinga mala’ikan mutuwa “cikin muryar in ina tace yaya ab ba tsaki yaja tare da sakin hannunta ya wuce ya fasa shiga gidan inna durkushewa tayi ta fashe da kuka tasan ba karamun hukunci zata fuskanta a wajen Abba ba ga kuma shima yaya Arman din yatafi kamar fushi ma yayi da ita tana cikin kuka haidar yazo tare da daddabata ya ce “ya Aira Abba yace kizo yanzu yanzunnan ki sameshi a babban palour kika wuce minti biyar kinsan sauran..........✍🏿

Tofa meye dalilin da yasa Aira ta rikice ganin Abba ya ganta tare da Arman ????

Meye dalilin da yasa Arman bai gaishe da Abba ba????

Tukunnama wace Alakace ke tsakaninsu????

Zaku samu amsarkune ta hanyar bibiyata cikin wannan zazzafan labari

* Ta hanyar comment da sharhi tare da sharing shine abunda zaisa na gane labarin yana muku dadi ko akasin haka kuma shine babbar kwarin gwiwar da zaku bani idan kun karanta ku dinga comment tare da sharing sauran grps masoyan asali* 🤗

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[5/25, 00:17] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE* 📔
🅿️...............5&6
Chapter 2 · 0% Book details