← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 127

Sashe 68

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

...Ruguzamun plane d'in dana jima ina shiryawa "sauke hannunta Aira tayi tare da rumtse idonta ta ce " wai meyake neman damuna karfa na haukace Yaya Arman gizau yake mun mema zai kawo Arman gidan nan meya had'ashi da buzanci kuma "duk cikin zuciyarta take maganar nan" Laila ce ta dafata ta ce "Yadai ko kinsanshi ne" Bud'e idonta Aira ta sakar mata murmushi ta ce "a a a bansanshiba Yadai yimun kama da wani Wanda na tab'a ganine sai yanzu na lura bashi bane" tana gama fad'a ta Juya Dan batason k'ara had'a ido da Buzun mutumin nan zuciyarta neman tarwastewa take "Da kallo suka bita har ta wuce" Arman ko wata nauyayyar Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Alhamdulilla Allah na gode Maka Amma yayi mamakin yanda Aira ta kasa ganeshi gashi da farko dai Ta nuna ta ganeshi ko meyasa kuma ta nuna bata sanshiba " Aira tana komawa d'akinta ta nufa saboda tsananin sara mata da kanta yayi Gado ta haye tare da rumtse idonta ta ce "Ya Allah Arman harya faramun gizau to meyasa da Chan bana kallon mutane a matsayinshi sai wannan buzun da sak yaya Arman d'ina nake gani,tsaki taja ta ce " Lallai na fara haukacewa Ma me zai kawo Arman gidan nan " a haka tayi ta sake sake akan buzun nan a cewarta. BQ aka sharewa Arman tare da samashi Katifa a ciki da niyyar gobe zai fara aikinshi Koda Ya kwanta bacci k'auracewa idanunshi yayi Kallon d'akin yayi tare da Inda yake kwana Wanda gaba d'aya gidanma yana da dukiyar da zai rabawa sama da mutum d'ari irinshi ba tare da dukiyarshi ga girgiza ba "Murmushi Yayi tare da sanya hannunshi a baya ya had'esu ya d'ora kanshi ya ce " So kenan" washegari tunda Safe ya tashi Ya kai Laila school ya dawo a lokacin Aira ta lek'o kenan ta window shi kuma yana fitowa murza idanunta Aira tayi ta k'ara budesu tsorata tayi da ganin shi d'inne da gudu ta Ruga ta koma d'akinta tana ta karanto duk addu'ar da tazo bakinta Kardai Gamo ne take tayi. Arman ko sosai yaso had'uwa da Aira A lokacin amma ya gagara da Yamma yaje ya d'auko Laila daga school Wanda tun a hanya sai iyayi take yimashi shidai shiru yayi yanajin haushin ta da tsananta Dan Duk abinda ya shafi mutumin nan ya tsaneshi musamman yarinyar da yaga sai shishige mai take Laila ko tana dawowa bata iske Aira ba A palour bedroom d'in Aira ta nufa tana zuwa ta isketa tana salla saida ta jira ta gama da zumud'i ta ce "Wai kinsan Me sis?A a saikin fad'a " Lumshe idanunta tayi tare da murmushi ta ce "Wlh sabon driver d'in nan ya had'u ke saima kinji muryarshi zazzak'a da ita har so nake yayi magana saboda karkiga yanda muryarshi ke rikitani" Gaban Aira ne ya fad'i saurin fisgewa tayi ta ce "Uhm Laila kenan to ya school d'in kunyi text d'in kuma" Dan son barin wancen zancen "tab'e baki tayi ta ce 'wlhko munyi Ai lecturer nan baida mutunci Da banjeba fa da na fad'i " Daga nan suka cigaba da hirar makaranta Wanda Aira Duka hankalinta na kan buzun nan Da daddare Bayan isha'i Aira kasa daurewa tayi Dan so take ta tunkari buzun nan Dukda fargabar da take Dan a zatonta Aljanine yake mata suffar Arman d'inta Hakanan tayi shahada ta fito saida ta lek'a ko ina taga bamai ganinta kuma taci sa a palourn ba kowa cikin Sauri ta nufi BQ d'in gidan Dan Laila ta fad'a mata Chan aka saukeshi tana sanda haka harta isa d'akin da tagani bud'e da labule ya tabbatar mata da nan yake a hankali ta tura kofar tare da Yin bismilla tana shiga ta ganshi kwance yana d'an latsa waya Arman jin shigowartata kawai yayi cikin Sauri ya Mike daga kwancen da take Da mamaki yake kallonta Cike da farinciki ya ce "My Cutie" Wara idanu Aira tayi jin ya ambaceta da sunan da Arman d'inta kad'ai yake kiranta dashi cike da tsoro ta ce "Dan Allah kai D'in mutum ne ba aljaniba meyasa kakemun suffar mutumin danafi k'auna a rayuwata " murmushi Arman yayi tare da wara mata hannu Alamun tazo gareshi ya ce "Ba aljabi bane my cutie nid'in ne dai Arman d'inki" Cike da mamaki Aira ta ce "Yaya Arman Me ya kawoka nan kuma" Murmushi yayi mata tare k'ara wara mata hannuwanshi ya ce "So my cutie soyayyarki ta kawoni" Da gudu Aira ta Ruga tare da Fad'awa jikinshi ta fashe da kuka mai cin Rai"wace nutsuwace ta dirarwa Arman Ajiyar zuciya ya sauke "Jin abar K'aunar tashi a jikinshi Dadddabata ya fara kamar yanda yake mata a baya ya ce " is okay my Cutie ba kuka ya kamata kiyi ba farinciki ya kamata kiyi"Lafewa Aira tayi tana shakar daddad'an k'amshin turarenshi da bazata tab'a mantawaba dashi a rayuwarta ba Irin salon yanda yake daddab'a Bayan nata ya k'ara tabbatar mata da shi d'inne lumshe idanunta tayi ta ce "Yaya da gaske Kaine please Idan mafarkine nake ya Allah kada ka tasheni daga wannan mafarkin Ka dawwanar dani a cikinsa har k'arshen rayuwata" Shafa bayanta yake a hankali ya ce "Ba mafarki bane cutie a zahirance d'in nine dai yaya Arman d'inki da Abba ya rabamu Allah ya sake had'amu" Tashi Aira tayi tare da Kallonshi Kamo hannunshi tayi cike da farinciki ta ce "my yaya da gaske Kaine dai na kasa gaskata mafarkinnan"murmushin da ya mance yaushe rabon da yayishi yayi tare da shafa mata fuska ya ce "nid'inne dai Arman yayanki kuma mijinki insha Allahu mai k'aunarki na har abada"Wara idanu Aira tayi cikin fara a ta ce " yaya Ya akai kazo wajen nan me yakawota nan gidan matsayin driver kuma ?murmushin gefen baki yayi ya ce "a saboda soyayya ba abunda bazan tab'ayiba a rayuwa Aira a saboda son da nake maki banajin bazan iya afkama ko wani hatsari ba a saboda ke soyayyarki daga Allah ne ked'in a jinin jikina kike Bazan tab'a iya jurewa rashinkiba a tare dani hakan yasa Bayan Naji sauk'i na yanke shawarar nemoki a duk Inda kike Wannan ce kawai nayi tunanin mafitar da zan samawa kaina ta hanyar aiki a k'ark'ashin mijinki...rumtse idonshi yayi yanajin kamar wani dutse ya tokare mashi zuciyarshi " Tuni hawaye sun gama wankewa Aira fuska Shafa fuskarshi tayi ta ce "Hak’ik’a aya kaid'in ka cika masoyi na Gaskiya Wanda babu kamarsa a duk fad'in duniya Allah nagode maka daka had'ani da masoyin da babu kamarsa mai yimun soyayyar da babu irinta mai sona saboda kai ya Allah Sannan ta fad'a Jikinshi ta fashe da kuka ta ce " I love you yaya bansan irin kalar adadin Kaunarka a cikin zuciyata please yaya wannan dama ce muka sake samu please ka tashi kawai mu gudu muje muyi Auren mu?Shafa bayanta yayi yana goge hawayen da suka so zubo mata ya ce "Bazamu gudu ba cutie " Da mamaki ta d'ago hawaye jab'e jab'e a fuskarta ta ce "saboda me.yaya Bayan mun sake samun dama" Saboda da igiyar Auren banzan Chan a kanki ya sanya bazamu gudu ba harsai Ya sakeki"Cikin kuka Aira ta ce "Ni yaya Banajin a jikina ina da wani Aure ni ban daukeshi matsayin mijina ba kawai mugudu yaya" shafa kanta yayi cikin sigar lallashi ya ce "Komai ba ayinshi cikin gaggawa my cutie ba yanzu ba" Lafewa jikinshi tayi tare da turo baki ta ce "To sai yaushe" Lakutar kumatunta yayi cikin sigar zolaya ya ce "Sai sanda kika zama jawar da kud'in yaro" Bugunshi a k'irji Aira tayi tare da turo baki cikin shagwaba ta ce "Allah yaya zan sanya maka kuka " Murmushi yayi ya ce "I m sorrry my prince's d'ina ayi hakuri kar ayi kukan nan wasa nake" Murmushi tayi tare da kafesshi da idanu ta ce "I love you so much My buzuna" Murmushi yayi ya ce "I love too Matar buzu" Duka Dariya sukasa a lokacin jinsu suke cikin farinciki da annashuwa marar musaltuwa harsun manta da damuwar da suka shiga a baya Arman ne ya ce "Had'in kanki nake buk'ata cutie wajan ganin mun cimma burinmu karki sake ki nunawa kowa kin Sanni zamu dinga mu'amula da juna a sirri kingane "Gyad'a kanta tayi ta ce " to my yaya"Jinjina mata hannu yayi ya ce "Good girl " Amma wai ya akayi jiya kad'an ya hana ki kwafsamun"Murmushi tayi ta ce "Na d'auka gizau ne kakemun Ko kuma Aljanine ya kemun siffarka Dan Yaga ina mugun sonka zai tsoratani da kai" Dariya yayi ya ce "Lallai My cutie Aljanin nan da bai kyauta ba kice har yanzu ina ranki alk'awarinmu bai tafi a banza ba" Murmushi tayi tare da kama hannunshi ta murza hannunshi ta ce "Kar Allah ya kawo ranar da zan manta dakai my yaya da ranar tazo gwara mutuwa ta Alk'awarin mu bazaije ko ina ba ya na nan har abada" Sun tab'a Hira sosai Cike da farincikin da sun manta yaushe rabon da su shiga irinshi Wanda basu sani ba har sha d'aya tayi saida Arman ya duba agogo wara idanu yayi ya ce "Maza cutie tashi ki koma kalli agogo " Turo baki tayi ta ce "Ni nan zan kwana" wara idanu yayi sai kuma yayi murmushi ya ce "Kiyi hakuri ki koma ciki ai koda yaushe muna tare banason a fara samun matsala tun ba Aje ko ina ba" tana gunguni Aira ta mik'e Shidai lallab'ata yake Shi ya rakota har wajen Haske tukwana ya juya tana waiwayen shi Harta k'arasa part d'insu Arman tun a hanya ya fara istighfari Dan yasan a yanzu Aira da Auren wani a kanta amma babu yanda zai iya da zuciyarshi D'aga hannu yayi ya ce "ya Allah ina neman gafara da yafiyarka ya Allah na kasa jurewa ne a kanta koda ya koma ya kwanta bacci mai dadine yayi awon gaba dashi saboda tsananin farincikin da yake ciki Airako koda ta koma cikin sand'a ta shiga gidan Allah ya taimaketa ba kowa kowa yana Dakinsu cikin sand'a ta nufi part d'inta tana shiga ta sauke ajiyar zuciya Cike da farinciki ranar tayi baccin da har ta manta rabon da tayi bacci cikin kwanciyar hankali
Chapter 68 · 0% Book details