← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 127

Sashe 12

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya hafsa tayi ta ce "Ah koda nace wannan show d'in kice love za a sha wannan k'auna keda Yaya Arman har yanzu akwaita kenan" Murmushi Aira tayi tanajin dadi har cikin ranta ta kama hannun Hafsa ta ce "Ai kauna ta na nan Hafsa *NI DA YAYA ARMAN* Mutu ka raba Dariya Hafsa tayi ta ce "

Allah yarda ni daman najima da sanin soyayya kuke wlh"wara idanu Aira tayi ta ce "Rufamun Asiri waya fad'a maki soyayya muke kawai dai k'auna ce muke " Uhm idan tayi tsami dai maji cewar Hafsa suna fita suka tarar dashi a cikin mota back seat driver na gaba Zage glass din motar yayi ya tsaya kallonta sosai ta tafi dashi ba k'aramun masifar kyau tayi mashi ba baisan lokacin da ya sakar mata murmushi ba Itama mayar mashi tayi Dan sosai yayi mata kyau cikin Dakakkiyar shaddarshi da Tasha aiki fara Hafsa ce ta ce

"Ina yini Yaya" Lafiya qlau Hafsa yau a gari"murmushi tayi ta ce "Wlhko Yaya Suna mukazo tare ma muke da Mama " Aira ce ta shagwabe ta ce "Yaya bazaka fito ba wai ka hakimce a cikin mota" Dan murmushi yayi ya ce "So kike na fito a gama kalle maki ni wannan wankan nakine ke kad'ai" Dariya tayi ta ce "Wayau dai kawai cikin shagwaba ta ce " ni fa yunwa nakeji ba abunda naci tun dazu"wara idanu yayi ya ce "Subhanallahi garinya aka barmunke da yuwa" Yaya ban iyacin abincin Taro shiyasa"ai zama bai ganmu ba maza-maza shigo muje restaurant yanzunnan"

ya fad'a yana bud'e mata Kofar da yake ciki Kallon Hafsa tayi ta ce "Sis taho muje" Girgiza kai Hafsa tayi ta ce "A a kije kawai Sis Mama ta ce Zan rakata gidan Daddy su gaisa Dan muna sa ran gobe zamu koma " To shknan saimun dawo Aira ta fad'a tana shigewa batare da shakkar komai ba Restaurant mafi kusa ya kaita saida ta tabbatar da ta koshi tukwana suka fito Suna shiga mota Yaji kiran daddy yana d'agawa nan Daddy ke shaidamai akwai Wani metting da za ayi karfe Tara a Zaria kome yake ya maza ya tafi Zaria yanzu yaje ya wakilceshi da to Arman ya amsa mashi Kallon Aira yayi da take latsa Wayarshi ya ce.

"Cutie
zamuje mu saukeki a gida yanzu Tafiya ta kamani zanje zaria zan wakilci Daddy wani metting " Yaya Dan Allah ka tafi dani Daman bantab'a zuwa Zaria ba Saidai mu wuce ta cikinta in zamu wuce Dan Allah kaje dani"tafada ta na marairaicewa "Rik'e hannunta tayi ya ce " Kiyi Hakuri my cutie Amma bazaiyu na tafi dake Zaria da Daren nan ba Kuma idan munje dinma bamusan tsawon lokacin da za a d'auka ba kiyi hakuri next time idan nazo zan daukeki da kaina na kaiki kiga ko ina da rana "

"nidai Allah yaya ban yarda ba katafi dani kawai " Dafe kanshi yayi ya ce "Aira case Ce " to so kike na tafi dake na ja maki fad'a a gida Kin manta dare ne Zaiyi"Yaya wlh har muje mu dawo ba maiji ni daman b'angaren Inna nake kuma bamai sanin ma Inda naje"Ba yanda Arman baiyi ba Dan kar ya tafi da ita amma ta nace daga karshe ma kuka tasa mai hakan yasa ba yanda ya iya dole suka tafi tare tana ganin an tafi ta sauke ajiyar zuciya sai murna take daman ita tanason tafiyar mota a rayuwarta

karfe takwas da wani Abu tayi musu a Zaria Rasa Inda ma zaikaita yayi hakan yasa ya yanke shawarar kaita gidansu Wani abokinshi kafin su gama metting d'in Abokin nashi ma bai gari mamanshi ta amshesu hannu bibbiyu Daga nan Arman ya wuce wajen metting d'inshi Hankali kwance nan Aira taci abinci sai nan nan y'an gidan suke da ita Dan Arman ya ce Musu kanwar sa ce Aira ganin Har 10Arman baizoba tana ta jiranshi Har bacci yayi awon gaba da ita.

Arman ko metting d'in saida ya jasu Har 11:30 hankalinshi duk ya rabu gida biyu ga tunanin Aira daya baro.

Koda ya koma maman su abokinshi hanashi daukarta yayi ta ce su barwa safiya ba irin yanda bai yiba amma ta hana tace bazasu tunkari hanya da Daren nan ba ga kidnappers da sukayi yawa suyi hakuri su barwa safiya ba yanda Arman ya iya sai hakura yayi yaje ya kama hotel ya kwana Aira ko tana baccinta bata San wainar da ake toyawa ba saida ta farka da asuba Ta ganta a wannan gidan Kan Gado Sosai gabanta ya fad'i ta ce.

"Na shiga ukku ba dai a gidan nan na kwana ba " Sai sannan ta tuno da gida ba Wanda yasan Inda take Cikin firgice ta tashin hankali ta tashi Kanwar Abokinshice ta shigo Dan tada ta tayi salla Tazo ta isketa harta tashi Wanka Aira taje tayi ta mayar da kayan jikinta ta fito suka bata break fast mai rai da lafiya taci tana gamawa Arman yazo Godiya sosai Arman yayi musu tare da alheri Aira ma Godiya tayi musu dukda firgicin da take ciki.

B'angaren gidan su Aira basu lura da Aira bata gida ba sai wajen 11pm Inna ta rikice ta nufi part din su Mamy ta fad'a musu Aira da bata gida Nan aka shiga nemanta lungu da sak'o ba a ganta ba Sosai suka shiga tashin hankali musamman Mamy hada kukanta Har 1 ana neman Aira ba a ganta ba ranar kwanan zaune sukayi Bcci saidai barawo.

Hafsat ce da tasha baccin ta wajen Asuba ta farka Taji kamar ana neman Aira lokacin duk suna palourn Inna sunyi jugum Hankali tashe har Abba daya kasa zaune ya kasa tsaye inna ko inbanda kuka ba abunda take Hafsa dake bacci jikin mamanta ta ce "Mama Wai Aira ce bata dawo ba kowa" Duk kallonta mutanen dake palourn sukayi a tare sukace "ko kinsan Inda take ne Hafsa" Tashi tayi ta ce "Eh jiya dai da Yamma wajen magriba Yaya Arman yazo Nina rakata wajenshi tace yunwa takeji zaikaita joint taci abinci da tare zamuje saina ce Zan raka mama gidan Daddy shiyasa lokacin da muka dawo ni nazaci ma harta dawo"

"Salati dukansu sukasa musamman Mamy kuka ta fashe ta ce " Na shiga ukku Airance tabi Arman suka kwana waje"Abba ko Shi kadai yasan yanda yaji a cikin ranshi safa da marwa kawai yake yama rasa wani irin hukunci zai yanke mata "Inna ko Salati ta rafka ta ce " ku bari sudawo muji dalili Dan nasan Tarbiyar Mujahed da Hajara sarai bazasuyi wani abunda bai kamata ba ni har hankali na ma ya kwanta tunda tare take da d'an uwanta"duk kallon mamaki suka bi inna dashi saikuma suka Jinjina kai Abba ko ya kasa magana sai safa da marwa da yake "Mama Halima ce ta ce

" Dan Allah yaya ka kwantar da hankalinka Tunda dai anji Inda take sai a jirari dawowarta"Cikinsu ba Wanda Abba ya tankawa shi kadai yasan Zafin da yakeji cikin ranshi.

Aira ko tun a mota take yiwa Arman kuka tasan yau Abba yasan bata kwana gida ba ta shiga ukku kasheta zaiyi tun yana Lallashinta har ya rabu da ita 7:20 tayi musu a Kano Kai tsaye gidan Inna suka isa Ba yanda Arman baiyi da ita ta fita ba amma taki sai kuka ta ke "tausasa murya yayi ya ce "

"Kinga irin haka nake guje miki shiyasa Banso kika Bini ba Amma kika dage yanzu ki kwantar da hankalinki ki shiga nasan ma bazasu Gane ba Tunda Bangaren inna kike kuma inna ba d'akinki take shiga ba shiru Aira tayi ta na tunanin kuma hakane k'ilama Allah ya rufa mata asiri basu sani ba Kallonshi tayi cikin sigar shagwaba ta ce.

"To bazaka rakani ba yaya" Idan na rakaki wani zai iya ganinmu Amma idan kikashiga ke kad'ai ba mai ganewa zaisu zaci ma kinfita ne sayan wani Abu Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Hakane Yaya to sai Anjima " Murmushi yayi mata ya ce "kije ki k'ara hutawa saimunyi waya Ko na shigo"

gyad'a mai kai tayi bata samu damar ma mayar mai da murmushinba ta nufi bakin gate a hankali ta kwankwasa mai gadi ya fito ya bud'e yana mata kallon mamaki.

Ajiyar zuciya Aira ta sauke ganin farfajiyar gidan ba kowa Arman ko yana ganin shigarta ya sauke ajiyar zuciya driver ya jashi suka tafi Aira ko gabanta na fad'uwa haka ta tinkari k'ofar d'akin.

saida ta tofa addu'oi tukwana ta yi bismillah ta tura kofar a hankali kamar Munafuka tana bud'ewa tayi turus ganin Duka mutanen Gidansu a palour zata iya cewa a rayuwarta bata tab'a shiga tashin hankali irin na ranar ba baya tayi da Sauri tare da Niyyar Rugawa Kafin tayi taku d'aya Abba ya chafkota cikin zafin nama da b'acin rai yayi mata wani irin
Mahaukacin ruk'o tare da d'auketa da wani gigitaccen mari..............✍🏿

*Kamar yanda na fad’a a page 30 In-Sha-Allah zamu gama book one ma ana free page kenan ku hanzarta biya tun kafin a kammala book one if you want to subscribe pay #200 katin MTN to 07026166536 hoton katin ko transfer masu Vtu suma zasu tura ta number tare da shaidar turowan amma su #300 wanda basu da buk’atar group ma ana ta pc za a tura musu suma #300 zasu biya ta number da na d’ora zasu tura y’an Niger kuma kumin magana ta wannan number +234-7026166536 zan turo muku number da zaku tura katin zain na 200 sai a saka ku Group karku manta book d’innan garab’asa ce babba da na sakeshi a 200 kachal Darajarshi tafi ta 1k Ni da Yaya Arman ba a fara komai ba bama a shiga wasan ba wannan duk somin tab’i ne hmmmmm wasan na nan gaba wannan shi ake kira koda kud’inka saida rabonka wannan salon na musamman ne masoyan asali ku harzarta ku biya nasan babu wanda zaizo ayi doguwar tafiyar nan batare da shiba saina jiku*💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾

*Share fisabilillah*

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[6/4, 22:40] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️...............23&24
Chapter 12 · 0% Book details