Sashe 104
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 7 min read
Arman ta ce " yaya ina muka nufa"gida cutie muje ki huta tukwana"Kasa tayi da kanta "Kai tsaye gidan Arman dake GRA suka nufa Bayan sunyi wanka sun huta Twins ne suka damu Arman da cewa " Hero ka kaimu muga mummy"Lallashinsu yayi ya ce "Sorry my twins ku bari sai gobe " Tuburewa sukayi hakan yasa ya kira Mummy wayarta kashe batamason zuwansu ba kallonsu yayi ya ce "Kunga wayarta a kashe ku kwanta ku huta Wanda ya Riga bacci shi zan fara kaiwa Wajenta " cikin saurin suka Haye kan sopa Tare da rumtse ido wai bacci yazo"Dariya Aira tayi kasa_kasa ta ce "Ai gwara da kayi mana maganinsu Dandananko baccin gaske ya kwashesu a lokacin ana isha I Aira salla tayi Bayan ta ciccibi twins ta kaisu bedroom Gado ta kwantar dasu Bayan tayi musu addua itama ta kwanta dandanan baccin gajiya ya kwashesu Arman koda ya dawo ya samesu Gado daya addua yayi musu tare da wucewa d'ayan bedroom d'in ya kwana. Washegari wajen 12 na rana Aira ta shirya ita da twins d'inta sosai tayi musu gayu cikin y'an kanti d'insu Riga da wando da suka matse red ba hula kansu sai Gashin kansu da akayi parking sai shek'i yake Itama shiryawa tayi cikin doguwar riga ta d'ora hijab d'inta mai hannu har k'asa green sosai hijab din tayi mata kyau A harabar gidan suka tsaya Arman ya fito da mota Suka shiga Kallonta yayi ya ce " ina muka nufa mom twins"gabanta na fad'uwa ta ce "Mu fara zuwa gidan Aunty Aysha hero" To ya fad'a tare da kama hanyar gidan Aysha Dan bai manta ba Suna isa suka fiffito da twins Kallonta yayi ya ce "zanshiga gari around 3 zanzo na daukemu" gyada mishi kai tayi a sanyaye tare da kama twins dake shirin nufa wani wajen knoking gidan ta fara minti Ukku taga anbude kallon mamaki Aysha ta dinga binta dashi ji take kamar mafarki itama Airar Kallon y'ar uwar tata ta tsayayi wara idanu Aysha tayi ta ce "Sis kece" Murmushi Aira tayi ta ce "Nice sis" Rungume juna sukayi a tare saikuma suka sanya kuka Aysha ta ce "Aira ina kika tafi kika barmu da kewa tsawon shekara Ukku da rabi" kasa magana Aira tayi sai kuka da take janye jikinta Aysha tayi tare da Kallon cikin jikin Aira wara idanu tayi ta ce "Sis ciki" Bata rufe bakinta ba taga twins Suna kallonsu"janyosu tayi tana mamaki taa ce "tare kuke sis" gyada mata kai tayi "D'aukar d'aya Aysha tayi tare da kama hannun Naila tace taho mu shiga ciki labarin nan sai anzauna kin sanyani a duhu da yawa" murmushin k'arfin hali Aira tayi suka shiga ciki a palour suka tarar da mijinta gaisheshi Aira tayi ya amsa mata cike da mamaki Bayan sun zauna Aysha ta kawo musu abun Tabawa twins ko tuni suka kama wasansu a wajen dining harsuna shirin yiwa Aysha b'arna tashi mijin aysha yayi yabar gidan dan yabarsu su sake kallon Aira tayi tare da kama hannunta ta ce "Sis yaran waye bani labarin abunda ya faru" Goge hawayenta Aira tayi tare da bawa aysha labarin komai da ya faru tundaga rayuwar gidanta ta Alh Yusuf har Zuwan Aurensu da Arman da yaran su Sannan sharrin da Akai musu Tayi mata rantsuwa akan basu tab'a aikata Alfasha ita da ARMAN ba"Aysha na kuka ta Rungume y'ar uwar tata ta ce "Allahsrk sis wlh na tausaya maki Abba mahaifinmune amma baiyi miki adalci ba Abba yana tsananta Abu da yawa fushinshi yana yawa yanzu Kinga ba bincike ba komai ashe haka abun yake"Aira na kuka ta ce " Sis Dan Allah fad'amun Gaskiya Bayan tafiyata Abba da Mamy basu tsinemun ba"Goge hawayenta Aysha tayi ta ce "basu tsine maki ba sis amma Abba ya Ce ya cireki a jerin yaranshi nan Tabawa Aira labarin komai da ya faru har Rashin lafiyar da Mamy ta dingayi a dalilinta" Sosai Aira ke kuka ta ce "Na shiga ukku ni Hajara sis ya zanyi da rayuwata wlh nayi nadama Yanzu kenan Abba ya cireni a yaranshi sannan ya rabaku dani" girgiza mata kai aysha tayi tana Hawaye ta ce "Sis fadarshi ta yarabamu bashi ke nuna zamu rabu dake ba muna tare da ke har gobe ke y'ar uwarmuce babu yanda zamuyi dake sannan koda ace zargin da aka maki Gaskiya ne bazamu rabu dake ba bare sharrine jibi da ikon Allah hada rabon yara Har biyu ga na Ukku " Sosai Aysha ta shiga Lallashin Aira harta samu ta daina kuka suka hirar yaushe gamo Waiwaye Aira ta dingayi ko zataga yaran Aysha amma shiru kasa daurewa tayi ta ce "Sis ina Yaran ko suna makaranta" Murmushi Aysha tayi ta ce "Bani da yara ko d'aya har yanzu sis Gaki k'anwarta ta Ukku hada yara biyu ga na Ukku Kinga ikon Allah Ko" Sosai Aira taji tausayin y'ar uwar tata cewa tayi "Allah ya baki kema me amfani sis"Ameen Aysha ta fad'a " rugowa Nihal tayi wajen Aira tare da hayewa kanta tana boyewa ta ce "Cutie Kinga Naila zata doken " Kallon Naila da ta biyota Da wayar chazar Aysha tayi sai huci take tana hawaye Aira tayi ta ce "naila bansan zalinci y'ar uwar taki zaki doka da abun nan Dan iskanci Ta fad'a a tsawace tare da amshe chazar tace " wuce kiban waje sarkin fad'a"kuka Naila ta fashe dashi tare da durk'ushewa ta fara burgima Aysha ce tayi saurin daukarta tana Dariya wai Aira ce da raba yara fad'a kallon Aira tayi ta ce "Ke kuma haka ake rabon fad'a saikiji me tayi mata kafin ki sasinta" Turo baki Aira tayi ta ce "Allah Aunty fad'ane da ita Dan taga ta fita k'arfi ita kuma sakaran tsorantama take ta fad'a tana dungurarwa Nihal kai data lafe jikinta " Dariya Aysha tayi tana Lallaba Naila harta samu tayi shiru ta ce "Uhm su Aira iyaye Ashe dai twins dinkine amma ta rude a kansu hhh kaji y’an soyayya yarankuma cutie suke cemaki kenan “Dariya Aira tayi ta ce "Ai har yanzu batasan ni bace sai ta ganmu k'watsam amma Aunty kina ganin naje gida ba matsala?Ajiyar zuciya Aysha ta sauke ta ce " bazance kije ko karkije ba sis amma zaki iya zuwa kidai je a b'oye kar Abba ya ganki firstly "Gyada mata kai Aira tayi wajen 3 Sukaji order Arman Bankwana Aira tayima Aysha Wanda twins harsun saba da ita suka fito Inda ta basu choculate sannan tacewa Aira Dan Allah ta dawo bayanin sanya mata number ta" da to Aira ta amsa mata cike da kewar y'ar uwar tata ta bar gidan suka shiga mota sosai gabanta ya fad'i koda suka shiga layin gidansu sosai gabanta ya shiga fad'uwa ta shiga jero duk addu'ar da tazo bakinta kallonta Arman yayi da suka kusa get d'in gidan ya ce "Kisa a ranki akwai nasara insha Allahu kinji my cutie" Cikin k'arfin hali ta gyad'a masa kai tare da bude kofar zata fita kallonta yayi ya ce "Da yaushe zanzo na daukeku "? Wajen 5 ko 6 ko?gyada mata kai yayi ya ce " ki kulamun da kanki Da my unborn nd my twins"murmushi ta sakar masa ta ce "kaima ka kulaman da kanka my hero a tare da twins suka fito da suke daka tsalle yau zasuga mom d'in Cutie Kallonsu tayi tayi murmushi ta kauda kai " Kallonsu yayi ya ce "My angels ba a yiwa hero bye bye" Dariya sukayi tare da d'aga masa hannu suka ce bye bye hero bakache mu gaishe maka da mom En cutie ba Kuma ma har dad enta yau jamu gani suka fada suna tsalle"y'ar Dariya yayi musu tare da cewa "To ku gaishemun da su" kama hannunsu Aira tayi tare da d'aga masa hannu ya wuce Tayi minti biyar tsaye tana tunanin yanda zata tunkari get d'in gidansu haka nan dai tayi shahada tare da nufar bakin get d'in gidan gabanta na tsananta fad'uwa Dak'yal ta iya d'aga hannunta ta yi knoking mai gadi ne ya leko tare da bud'ewa turus yayi ganin Aira gabanshi wara idanu yayi cike da mamaki ya ce "Hajiya kece da gaske" Murmushin K'arfin hali Aira tayi ta ce "Ni ce Baba Su Mamy na ciki?........✍🏿