Sashe 63
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
....Ranar Aurenka kai da "Asma'u husna y'ar gidan Alhaji Zakari Commissioner of Sport kuma bikin bazai d'auki lokaci ba Dan sati biyu zamu sanya saikaje ka fara shirye shirye" Tunda Daddy Ya fara maganar Arman yake mamaki Harsaida yakai k'arshe d'agowa yayi tare da had'e rai fuskar nan tashi murtuke ba alamar Dariya ya ce "Wai Daddy ni kake nufi zakayiwa Aure ?Eh kai nake nufi ko ban isa da kaiba " A a Daddy ka isa dani amma dai kasan ni ba mace bace bare kace Auren dole zakamun Gaskiya ka janye maganar nan bamai yiwa bace "cike da b'acin rai Daddy Ya ce " Zaka San bamai yuwa bane Indai nine mahaifinka Auren nan ba fashi kamar yanda ita wacce ka so din tayiwa mahaifinta biyayya ya Aurar da ita ta zauna d'akin mijinta to haka nima Idan har na isa dakai zan Aurar dakai "shi Arman mamakima ya gama cikamai kai ya ce " Amma Daddy ai ita macece Nifa namijine ina aka tab'ayi"Za a fara a kanka ko Rashin kunya zakayimun"Tunda suka fara maganar Mummy batace uffan ba sai yanzu Kallon Arman tayi ta ce "Karka sake magana Son" Kallon Mummy Arman yayi sai kuma ya koma ya kwanta kan sopa tare da lumshe idonshi Kamar mai bacci a ranshi ya ce "Lallaima Daddy wai ni zai duba yace zaiyiwa Aure murmushi yayi danshi abun ma Dariya ya bashi shiyasa ko a kanshi bai damuba" Kallon Daddy Mummy tayi cike da damuwa ta ce "Dear maimakon ka bari jikin Nashi ya k'ara sauk'i yanzu kuma kazo da maganar Aure ko shiri babu two weeks fa" d'aga mata hannu Daddy yayi tare da mik'ewa ya ce "Na Riga na yanke hukunci ba neman shawarar wani cikinku nazo ba umarni ne na bada ba shawara ba" Jan bakinta Mummy tayi shiru ita tsoranta d'aya kar Arman ya kuma shiga wani hali Kallonshi tayi taga hankalinshi kwance kamar ma ba a kanshi ake magana ba Bayan Daddy Ya bar palourn Mummy ta matsa kusa da Arman cike da nuna Rashin jin dad'i ta ce "Kayi hakuri karka sanyawa kanka damuwa kasan ba abunda na tsana sama da b'acin ranka kar wannan ya dameka kaji son please Karka k'ara jefa kanka cikin halin da ka shiga a baya ba bazan jureba kai d'aya garan Arman ina sonka sosai" ta k'arasa fad'a hawaye na zubowa daga idanunta " Lumshe idonshi Arman yayi ya budesu a hankali tare da yunkurawa zai mik'e Mummy ta rikeshi ta ida mik'ar dashi kamo hannayenta biyu yayi tare da Goge mata hawayen da suka zubo mata sosai Mummy take bashi tausayi iirin son da ta ke mashi Shima sosai yake so da k'aunar mummyntashi ya ce "Karki damu Mummy bazan k'ara shiga Cikin wani hali ba kidaina damun kanki kinji my first love " Rungumeshi tayi ta ce "Nagode my son Allah maka albarka" Murmushin k'arfin hali Arman yayi ya ce "Ameen mom" koda Arman yaje kwanciyar bacci da Tunanin Yanda zai yi ya samu Aira kawai ya ke dukda tayi Aure amma bayajin karaya a kanta tunaninshi Duka yana kan mafitar da zai samu harya isa gareta kwata kwata shi maganar Daddy ma bata dameshi ba saboda yasan ba abune mai yuwa ba washegari aka sanya Ranar Auren Arman tare da husna wacce sai d'auki da farinciki take Dan bata tab'a tunanin zata auri Arman ba mutum maiji da kyau,kud'i,mulki,Dan kwalisa tuni harta fara rawar kai tana jin tazama big girl Arman ko yinin Ranar a guest house d'inshi yayishi Saida dare ya koma gida Nan ya samu labarin sanya ranar Auren wajen Mummy d'age kafad'a yayi ba tare da nuna damuwa ba ya ce "yayi kyau" Sosai Mummy tayi mamaki ta ce "Wai Arman Yanaga baka damu da Auren nan Daddynka zaiyi maka ba Kodai da abunda kake shiryawane " murmushin yak'e yayi ya ce "bakomai Mom Good night ina buk'atar hutawa" daren ranar Arman ya samu bacci sosai Dan shawarar da ya yanke akan mafitar da yake tunanin zai gamu da muradin ran nashi Haka aka fara shirye shiryen biki Wanda Arman kosa hannu baiyiba sannan ya ce karma Mummy ta shirya shagaalin komai sannan karta gayyaci kowa nata"Sosai Mummy ta damu ta ce "Son me kake nufi kenan da karnayi gayya " Mummy nadai fad'a maki karki gayyaci kowa hakan ne zaisa na kwantar da hankalin da kikeso nayi amma idan kikamun gayya zan shiga damuwa"Ya fad'a mata hakane Dan yasan ta hakan ne kawai zata yarda Dan abunda yake shiryawa bayason ya kunyata Mummy cikin mutane"Girgiza kai Mummy tayi ta ce "To zanyi yanda kace son indai hakan zai sama maka farinciki" murmushi yayi tare da Rungumeta ya ce "I love you so much My dear mom d'aya tamkar da trilillion" Love you too my one nd only Dan lelen mummynshi"Murmushi Arman yayi yana shafa sajenshi.Bangaren Daddy sosai suka shiga shirye_Shiryen biki Mama Halima ya sanya takanas taje ta had'o Lefe a Dubai dukda itama batajin farincikin Auren amma ba yanda za ayi tunda Airar tayi Aure Shima Arman d'in gwara yayi tunda shekarunshi ja suke shidai Arman ya sanya musu ido ba um ba umm umm.duk yanda Daddy yayi dashi akan Yaje su gana da Asma'u kin zuwa yayi rabuwa dashi Daddy Ya ce "Ai idan Akai Auren dole kaje ka ganta Arman dai ganin gadan gadan Daddy da gaske yake Aure zai mashi gashi a yanda yaji suna lissafi Saura sati bikin Ranar da Aunty Halima ta dawo laifen ya k'ara tabbatar mai da Daddy da gaske yake fezar da iska mai zafi yayi ya ce " Impossible wlh bama zan yarda a d'aura Auren nan ba kamar naci amanarki cutie da kuma Amanar soyayyar mu ke kanki Auren da Akayi miki fin k'arfinki akayi kuma ke macece mai rauni ni kuma namiji ne Wanda zan iya gwagwaarmaya akan komai Zaunawa yayi bakin Gado tare da dafe kanshi Duka biyun dake Sara mashi soyayyarshi da Aira ta shiga dawo mashi cikin kwalwa mik'ewawa yayi tare da zuwa daidai saitin Inda hoton ta yake manne jikin Bango d'akinshi Tsaye yayi tare da Fara shafa hoton sosai tayi kyau cikin Rigar sanyi Red mai shegen kyau da black d'in wando ta kyalkyale da dariya a daidai bitch akayi hoton "Sosai Arman ya kafe hoton da idanu bako k'iftawa soyayyya da k'aunar Aira na k'ara fisgarsa yanajin wata sabuwar k'aunarta na ratsa ko wani sassa na ilahirin jikinsa baisan lokacin da wasu zazzafan hawaye suka zubo daga idanuwanshi ba k'ara shafa hoton yayi tare da lumshe ido ya ce " I love you you my cutie bazan iya rayuwa ba tare dake ba kiyi hakuri tsawon lokacin da Na d'auka batare da na cika alk'awarin da muka d'aukarma junanmuba ki sani a duk Inda kike gangar jikinmuce kawai tayi nesa da y'ar uwarta amma zuciyoyinmu suna Tare a waje guda for ever and ever har gaba da abada bazan tab'a daina sonki ba sannan bazan tab'a karaya a soyayyarki ba Sannan yayi kayataccen murmushin da ke karawa kyakyawar fuskarshi kyau da haiba ya ce "Ki shirya ina nan zuwa gareki yake sahibata" Wani Frame d'in hotonta dake gefe ya ciro shi kuma sanye take cikin Abaya Tasha nad'in larabawa sak ta yi kamar balarabiya komawa yayi kan bed d'inshi tare da Rungume hoton ya kwanta yanajin kamar ita ya Rungume shauk'in kaunarta na k'ara ratsashi sosai ya matse hoton a jikinshi yana sakin smiling a haka bacci mai dad'i yayi awon gaba da shi. Aira na zaune a kan sopa suna kallon wani serries a Bollywood sosai ta maida hankalinta ga kallon da take Laila kuma na chat Alhaji Yusuf ne ya shigo saida gaban Aira ya fad'i Dan rabon da ta yarda sun had'u tun ranar nan ya yaso Fad'a mata amma bata nunaba a fuska saici gaba da kallonta da tayi Kallo d'aya Daddy yayi mata ya kauda kai Dan fushi yake da ita dukta jagula mai lissafi kullum da tunaninta da sha'awarta yake bacci cike da girmamawa Laila ta ce "Sannu da zuwa Abba " Yawwa Auta ina mamantaki"Tana ciki ta bashi Amsa Barin palourn daddy yayi tare da nufar d'akin uwar gidanshi cike da jin haushin Rashin ladabin da Aira ke mashi dukda dai Shi ya ja ya aurota batasonshi amma wata biyu ai yaci ta hakura kallon Aira Laila tayi tare da b'ata rai Ta ce "mijinki ya dawo ba ko Sannu da zuwa bare gaisuwa " ta fad'a da sigar zolaya "Harara Aira ta maka mata tare da cewa " Allah yarinyar nan ki kiyayeni ke duk yanda zaki zolayeni kin iya ko Uhm su miji manya" "Kardai ki fad'a wata maganar daga wannan " Kallonta Aira tayi saikuma ta kauda kai tare da Yin tagumi Ba wanda ya fad'o mata a rai sai Arman batasan lokacin da wasu hawaye masu d'umi suka shiga zubo mata "Shin wani hali Arman yake ciki,ya warke koko har yanzu yana cikin halin da na tardashi,Yaushe zai dawo gareni,yaushe alk'awarin Soyayyarmu zai cika ,yaushene zai dawo gareni kamar yanda ya fad'amun sosai hawaye suka shiga zarya daga idanunta zuwa kumcinta " Da mamaki Laila take kallonta kamar mai iska lokaci guda lafiya yanzu kuma ta fara hawaye "Dafota tayi ta ce " Sis lafiya kuwa?tunanin me kike haka harda su kuka"Hakan ya dawo da Aira daga Duniyar tunanin da ta Lula kallon laila tayi tare da Fara goge hawayenta ta ce "ba komai sis" B'ata rai Laila tayi ta ce "kinn manta mun zama kawaye plz karki b'oyemun fad'amun tunanin da kike kika sani ko zan iya taimaka maki da wani abun" jin hakan cewar ko zata iya taimaka mata da wani abun ya sanya Aira Numfasawa tare da kama hannun Laila ta fuskanceta ta ce "Na rasa ya zanyi da soyayyar Yaya Arman Laila ina sonshi so mafi muni da bazan iya kwatanta maki kalarshi da komaiba a koda yaushe idan na kwanta kyakyawar fuskarshi nake gani murmushin mai narkarmun da zuciya tare da Kalamanshi masu ratsa ko wani sassa na ilahirin jikina a koda yaushe Fuskarshi da Kalamanshi gizo sukemun laila bazan iya rayuwa babushi ba...ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka Rungumeta Laila tayi sosai ta tausayawa Aira halin da ta tsinci kanta Dan kullum idan tana