← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 127

Sashe 24

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sosai Zaman Aira gidan Mama Halima yayi mata dadi Hankalinta ya d'an fara kwanciya kayan hafsat take sanyawa Arman ko ya maida kd kamar gida kusan kullum sai yazo sosai yake son fita da ita amma mama halima ta kasa ta tsare tace bazasuyi mata shiriritar yawon da suke a kano ba dan haka kome zasuyi suyi a gidanta yau ma Arman yazo Dagashi sai ita a palour suna zaune kujerar 2siter kamar zasu shige juna Aira sai shagwaba take mai akan ya tafi da ita Abuja shikuma yana biyeta sai Lallashinta yake " da Hira tayi dadi Aira ta ta d'ora kanta kan kafad'arshi tana shak'ar daddad'an k'amshin turarenshi har wani lumshe ido take shiko baiyi kokarin dagata ba dukda duk lokacin da jikinsu suka had'u Dana juna yana cutuwa "Mama Halima ce ta shigo d'akin Salati tayi ta ce " me zan gani haka Mamana"Cike da rud'u Aira ta tashi ita tama manta da d'akin Mama Halima suke "Hararta tayi ta ce " Wuce ciki"cikin sauri Aira ta wuce hada tuntub'e Mama ya zaki korata kuma saboda ita fa nazo ki bari mu gama hira mana "Arman ya fad'a" kai daman nayi maka Ittik'afin kanka marar kunya Kunzo kun wani manne kamar chumgum "Dan murmushi Arman yayi tare da tashi ya ce " Ai munmafi gum Mama chumgum ai yana fita cikin Sauk'i "Pillown kujera Mama Halima ta d'auko tare da wulla mai tace wuce kaban wuri marar kunya so kake ka fitsarar mun da y'a" Dariya yayi ya kauce tare da Yin hanyar fita ya ce "y'artakice dai take son ta fitsarar dani" ya fad'a yana barin d'akin "Ja'iri ai zaka dawo ka sameni Mama Halima ta fad'a tare da wucewa Dakin da Aira take ita da Hafsat kwance ta tarar dasu Suna kallo a wayar Hafsa cikin fad'a Mama ta ce " Ke yanzu Mamana Dan gidanku haka ake hira kije ki lik'e jikin namiji Ko kunya gaku fitsararru'cikin shagwaba Aira ta ce "Mama yaya Arman ne fa " Arman din dan gidanku to wlh daga yau ki kama kanki kar in karaga kina shigemai jiki da da yanzu ba d'aya bane ki shiga hankalinki "To Mama yi hakuri Bazan sakeba" Yawwa y'ar kirki Mama ta fad'a tare da cewa ku fito ku d'ora mana abincin Dinner kunsan dai inada zakad'a zakad'an y'an mata kamarku bana shiga kitchen ba Dariya Aira da Hafsa sukayi Aira ta ce "Gaskiya ne big Mama muje ta fad'a tana kama hannun Hafsa suka sauko kan gadon.
Aira saida tayi sati biyu a Kaduna Tukwana Mama.Halima ta fara tunanin yanda zata kaita gida Mamy ta kira Bayan sun gaisa ta ce " ya ake ciki nan din Maman Aira Yaya ya huce kuwa"eh ko a a zance Dan Gaskiya bai sake maganar ta ba Kuma na fad'a masa tana wajenki baice komai ba "Ajiyar zuciya Mama Halima ta sauke ta ce " to kina ganin ba matsala gobe mu taho ko mu bari dai ya k'ara hucewa"Duk yanda kikace maman Hafsa Magana na wajenki "to bari muga gobe zamu shigo insha Allahu idan ya huce ni da sai ya bani ita ta zauna nan muga yanda hali zai bada" to Halima nagode sosai Allah dai ya bar Zumunci "ba komai ai yiwa Kaine ko na baki Airan ku gaisa" a a barta kawai sai anjima ngd "tukwana sukayi bankwana.
Washegari da safe Mama da su Aira sukayi shirin Tahowa kano Aira duk Inda hankalinta yayi dubu ya tashi sosai take fargabar haduwarta da Abba Wajen 10 suka fito Suna shirin shiga mota su tafi Airport motar Arman da danno dakatawa sukayi saida ya Iso kallonsu yayi ya ce " ina zuwa kuma Mama na ganku hada kaya"Kano zamu"Mama ta bashi amsa "Kano kuma Mama da kun bari ba yanzu ba" Yau mukayi niyyar zuwa ko zaka hanamu"Allah huci zuciyar big Mom Allah kiyaye amma nifa Gaskiya anshiga hakkina nan yafimun kusa ina ganin my cutie kullum ya fad'a yana tsare Aira da idanu sosai tayimai kyau cikin goduwar Riga Atamfa ta yafa gyale matching da kayan fuskar nan fayau sai hasken annuri "Itama Airan shi take kallo bako kyaftawa sosai yayi mata kyau cikin Shaddarshi da tasha aikin manyan mutane Fuskarnan tashi fayau ba ko Alamun damuwa a cikinta kafe juna sukayi da kallo bako k'iftawa Saida Arman yace karki cinyeni" Tukwana ta dawo daga duniyar tunanin da ta Lula "Hararar wasa ta aikamai cikin shagwaba ta ce " ba Kaine ka fara kallona ba "Murmushi yayi ya ce " To laifi ne Dan na kalli mata ta "Nima laifine Dan na kalli yaya na ta fad'a tana tsatsareshi da idanu irin ba wasan nan" Dariya yayi sosai ya ce "Keidai ki fad'i abunda ke ranki so kike kice laifine Dan na kalli mijina" ai tun kafin ki fad'a na shiga zuciyarki Naji abunda takeson furtawa"Uhm to ni ai bance ba Kaine kace haka"Kuma hakane ba Dan zuciyarki bazatayimun karyaba"Mama Halima ce ta ce "To marassa kunya a gaban nawa ma nafa lura kwata_kwata ku bakwamajin kunya ta ko " Murmushi Arman yayi ya ce "Wlhko Mama kamar kinsani " Bugu a baya Mama ta kaimashi ya kauce tace "ja iri da ka tsaya mana sannan ta kalli Aira ta ce " Saikishiga muje "Kallon Arman Aira tayi ta ce " yaya zamu wuce "Ai tare zamu tafi yaza ayi ku barni" Mama Halima ce ta ce "Wallahi baka isa ba Bazaka bimuba ka bari ma naje na samu na kashe gagarumar wutar da ka tada ba Inda zaka bimu ka k'ara tada mana wani bomb din" Dariya sosai Arman yayi ya ce "please Mama bansan cutie tayi nesa dani" tsaki Mama Halima taja ta ce "Saikayi kuma amma bazaka bimu ba Dan haka kama maza ka wuce Inda ka fito" Badan Arman ya soba yaki binsu ba ya koma Abuja su kuma suka kama hanyar kano Dan sunje Airport jirgin zai jima bai tashi ba hakan yasa kawai driver ya wuce da su kano.
K'arfe 12 da wani Abu tayi musu a Kano sosai Aira gabanta ya fad'i har suka isa gidansu addua take Dak'yal Mama Halima ta samu ta fito daga mota duk a tsorace take har suka isa Babban palourn gidan Mama da yaya Umar sai matarshi suka tarar a palour Ajiyar zuciya Aira ta sauke ganin basu tarar da Abba ba "Mama ce ta ce lale marhaban mutan kd sannunku da zuwa " Mama ta tarbesu Zaunawa sukayi aka gaggaisa Sannan ta kawo musu ruwa Aira duk ta rakube ta zama kamar wata bakuwa "Umar ne ya gaishe da Mama Sai kallon Hafsa yake khadija ko sai wani shashshan magani take a takaice ta gaida Mama Halima Aira ce ta ce " Yaya ina yini anzo lafiya "Lafiya qlau y'ar gidan Inna sannan ya kalli Hafsa ya ce " wai Mama Hafsa ce ta girma haka"Murmushi Mama tayi ta ce "Ai ka jima baka ganta ba shiyasa Mama Halima ta ce " Ai ganinka Babana wuya yake "Murmushi yayi ya ce " Mama yanayin Aiki ne sai a hankali yanzu ma Hutu ne muka Dan samu zuwanmu kenan"Allah ya taimaka yayi jagora "ameen " Hafsa ce ta ce "Ina yini ya Umar" Cike da Fara a ya ce "lafiya qlau Hafsa ya makarantar har Angama ko" Eh "to Allah ya taimaka " Ameen ta fada Sosai ta tsarugu da Kallon da ya Umar ke mata "Khady ko sai cika take tana batsewa tana Aika mata da harara Mamy ce ta shigo " zaunawa tayi suka gaisa da Mama Halima cikin mutuntawa Aira dai kanta a k'asa "dak'yal ta d'ago ta ce " Mamy ina yini"Lafiya qalau mutanen kd ke Kd dinma tafi amsarki harda k'iba"Murmushi Aira tayi Mama Halima ta ce "Nima haka nagani Ai shiyasa nazo mutafi da kayanta ni da kun bani ita ai sai Aure ya raba" Dariya Mamy tayi ta ce "nidai indai nice na baki halak malak sai ki hada kiyi twins Hankalina ma ni da yafi kwanciya" Dariya Mama Halima tayi ta ce "Kamar gaske " Sosai suka shiga hira cikin raha "Amma ce ta shigo Da gudu ta fad'a ta ta Rungume AIRA ta ce " oyoyoy sis Gaskiya nayi kewarki da yawa wlh gidan Duka baya yimun dadi da bakyanan"nima nayi kewarki sis daga ina kike"Amma bata kai ga Amsa mata ba Abba ya shigo sosai Aira ta tsure cikinta ya d'uri ruwa Cikin b'acin rai Abba ya nuna Aira da yatsa ya ce "........✍🏿

*Ni da yaya Arman na kud'ine ki biya #200 kachal to 07026166536 ki karanta cikin kwanciyar hankali karki fitarmun da Littafi kud'in karantawa kika biya ba na mallaka ba bazanyi Allah ya isa ba amma ki sani akwai hak'k'i*

*_Miss Hajo ce*_
[6/13, 08:16] Hajo hajo: 🅿️.......*39&40*
Chapter 24 · 0% Book details