Sashe 32
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 7 min read
abincin tana gamaci ta gyara wajen Wayarta ta d'auko ta hau what's app Ta fara chatting wajen la'asr Arman ya kirata ya ce " ki lek'o ina bakin gate"cikin Sauri Aira ta ce "To yaya ganin har yanzu y'an gidansu basu dawoba ya sanya hankalinta kwanciya ta ce " nasan kila ma ba yanxu ba zasu dawo"Fuskarta kawai ta gyara ta janyo doguwar Hijab d'inta tasa Tana fitowa Amir ya fara kuka yana mik'a mata hannu Alamun ta daukeshi tsaki taja tare da dungure mai kai ta ce "saikace cewa nayi zan barshi d'an rigima kawai" shiko shiru yayi tare da Lafewa jikinta yana tsotsar yatsa suna fitowa bakin gate ta nufa Baba mai gadi na zaune gaisheshi tayi ta ce "Baba zan gaisa da wani ba fita zanba ina bakin kofa yana waje " Baba mai gadi ya ce "To kiyi sauri dan Allah maman Alhaji karsu dawo su sameki" murmushi tayi ta ce "To Baba nagode" Tana lek'awa Ta Hango Arman a.mota yana hangota ya taho sosai yayi.mata kyau cikin shigar k'ana nan kaya Fuskarnan tashi sai shek'i take ga sajenshi lufluf dake zagaye da kyakyawar fuskarshi gashin kan nashi sai shek'i yake Dan yau baisa hula ba Alamun yana shan gyara"murmushi Aira tayi ta ce "Amma fa wankan nan ya tafi dani yaya" Haba my love ya fad'a yana karasowa bakin kofar"murmushi tayi ta ce "Ai.kaima ka sani sannan ta bata fuska ta ce " Allah sa wasu basu gama ganemun kai ba"Dariya yayi Kad'an dake k'ara mishi kyau cikin sigar zolaya ya ce "Ai kinsan babu wacce ta isa ma ta tsaya kalle miki miji kinsan kwarjini yake yiwa y'an mata basa iya kallona su k'ara "Uhm yaya kenan sarkin kod'a kai" Ai kema kinsan Gaskiya na fad'a "Sannan ya ce " Wai Amer ne ya girma haka masha Allah kawoshi mu gaisa"ya fad'a yana mik'a mata hannu "Mik'a mishi shi tayi daman Amer ba kiyiwa garai ba Sajen Arman ya kama ya dinga ja yana kyalkyalewa da dariya" Dariya Aira da Arman suma sukayi Arman ya ce "Ina son yara sosai my Aira nasan zaki Haifa mun yara kyawawa kamarki Allah yasa wataran d'anmu ne ni Dake na d'auka haka"Rufe fuska Aira tayi " Murmushi Arman yayi ya ce "bazakice Ameen ba" Dariya tayi ta ce "uhm To ameen my ya...muryartace ta sartse sakamakon Ganin motar su Abba da tayi a bakin gate din Alamun sun dawo suna Horn Cikin rudewa Aira ta amshe Ameer dake.hannun Arman ta Ruga ciki Kad'an Ya hana ta fad'i Arman ko Juyawa yayi yaga Inda take kallo" Girgiza kai yayi tare da Juyawa ya nufi Inda motarshi take Aira cikin tashin hankali ta shiga cikin gidan Tuni ta fara hawaye tace "Shikenan yau karyata ta k'are na shiga ukku " Batayi minti Ukku ba tsaye taji shigowar su Mamy Tare da su Mama hada Amma Cikin Sauri ta Aje Ameer Kasa tare da rugawa tayi cikin Dakinsu ta kulle sai hak'i take"Mamy ko d'anta ta d'auka tayi d'akinta Abba koda ya shigo bai tambayi Aira ba Kuma baice ina take ba bai nuna Alamun ko damuwa a fuskarshi ba Aira ko ta na Chan kulle Ranar bata fito ba Amma ma dak'yal ta bud'e mata ta shiga Washegari saida taga fitar Abba ta window tukwana ta sauke ajiyar zuciya ta fito palour Mamy ta tarar da Mama Gaishesu tayi suka Amsa Ya jikin na Aunty Aysha Mama"Aira ta fad'a tana kallon Mama"Aisha jiki da sauki Aira harma an sallamesu yanzu haka ta na gidan ta na maso nan sukayo da ita"Kamar zatayi kuka ta ce "Allah Kara sauki wlh inason ganinta Dan dai ba yanda zanyi ne" ita ma jiya ta na ta tambayarki idan taji sauk'i zatazo ai "To Allah Kara sauki " Satar kallon Mamy tayi taga harkarta take k'asa tayi da kanta ta ce "Mamy Dan Allah kiyi hakuri Allah bazan sakeba Jiyanma " juyowa Mamy tayi ta ce "Me kikamun " Shiru tayi saikuma ta ce "Jiya da Yaya Arman yazo Allah banzaci har zaku dawoba Nasan Abba ya k'ara fushi dani Dan Allah ki bashi hakuri" tsaki Mamy taja "Matsalarkice wannan tunda ke bazaki kiyaye umarninshi ba gashi gaki ba daidai yake dake ni ba ruwana " Abba ne ya shigo Sosai Aira ta tsorata sai kuma ta dake dak'yal ta iya d'aga baki ta gaisheshi ta ce "ina yini Abba"Lafiya" ya bata amsa sosai tayi mamakin ganin ko maganar Baiyi mata ba sannan ya amsa gaisuwarta Ajiyar zuciya ta sauke a ranta ta ce "Alhamdulilla k'ila Abba ya fara Saukowa " ta nan tsaye ta zaci zaiyi mata maganar amma shiru cike da murna ta koma Tare da cigaba da harkokinta.washegari wajen la'asr Arman ya koma Abuja basuyi bankwana ba da Aira sai a waya Bayan sati guda Ranar Juma'a Aira na palour ta na guga Mamy ta shigo kallonta tayi ta ce "Bar gugar nan Aira tashi mu shiga kitchen ki tayani Aiki Abbanku zaiyi bak'o sai yanzu yake fad'amun" bak'o kuma Mamy waye zaizo"Wai abokinshi ne tun suna secondary daga sokoto zaizo ni banma sanshiba amma Naji ance da yana zuwa kafin inzo gidan nice dai ban sanshiba badai wannan doguwar maganar ba yanzu tashi muje "to Mamy Aira ta fad'a tare da tashi a tare Mamy da Aira suka shirya duk wani Abu da ya kamata papper chicken, abinciccika, snacks karfe hud'u da wani Abu suka gama komai Aira duk ta gaji Dakinsu taje tayi wanka tana fitowa ta tada Sallah tana gamawa ta zira Atamfarfa blue da ratsin fari Riga da sicket sosai suka amsheta bata shafa komai a fuskarta ba Mamy ce ta shigo kallonta tayi ta ce " Bak'on Abbanku ya Iso kije ki d'auki kulolin ki kai palourn Abbanku saiki gaisheshi daga Chan kafin na shirya naje mu gaisa"Hakanan Aira batasan dalili ba Taji gabanta ya bada ras a hankali ta ce "To Mamy bari na kai gyale ta yafa ta fito taje kitchen ta dauki kulolin a basket ta tafi dasu da Sallama ta shiga palourn Abba zaune ta tarar dasu Suna fira sai Dariya suke a hankali ta k'arasa shiga kallon Bak'on Abba tayi dattijone bak'i mai kamala Wanda daga gani bazai wuce sa'annine Abba ba sanye yake cikin manyan kaya babbar Riga Tasha d'inkin manyan mutane k'atoto ne yana da k'iba sosai irin wannan manyan masu kud'in ne masu jiki da tumbi Aira saida taje gab dasu tukwana ta tsugunna cikin ladabi ta ce " Ina yini anzo lafiya"Tunda ta shigo Alhaji Yusuf madugu ya kafeta da idanu bako k'iftawa Wanda sosai kallon ya takura Aira baimaji gaisuwar da take mashi ba saida Abba ya ce "tana gaisheka fa" sai sannan ya dawo hayyacinshi cikin fara'a ya ce "Sorry banji ba lafiya qalau munsameku lafiya" Alhamdulilla "Aira ta fad'a har lokacin kanta kasa Aje basket d'in tayi ta ce " gashi Mamy ta ce a kawo maka"murmushi yayi ya ce "to nagode Beauty" Beauty Aira ta maimaita cikin ranta kallon Abba Alhaji Yusuf yayi ya ce "Yallab'ai y'arka ce ya akayi ban Santa ba" Eh ai ka daina zumunci shiyasa baka santa ba "haba ai zumunci ya na nan indai ba mutuwa akai ba ko y'ar Amarya ce dai naga bata kama da y'ay'an Zainab " Eh Abba ya bashi Amsa "Har lokaci Alhaji Yusuf idonshi na kan Aira ya ce"Masha Allah Ammafa tana da kyau sosai Alhaji Duka tafi Y'ay'anka kyau" Aira na jin Haka tayi saurin tashi duk saitaji mutumin Yama bata Haushi ta ce "Sai anjima " To ya sunanki y'an mata "Hajara ta bashi tare da Juyawa ta fice cikin Sauri ko sauraren me zaice batayi ba har ta isa part d'insu ta na Jan tsaki tana zuwa Mamy ta ce " ke kuma tsakin me kike "turo baki Aira tayi ta ce " nida wannan Bak'on na Abba mana karkiga irin kallon k'urullar da yakemun hada cewa wai wani beauty "tsaki Mamy ta ja ta ce " kede baki rabo da shirme me zai gani a jikinki zakizo kina wani famfamin yana kallon ki "Turo baki Aira tayi ta ce " Allah Mamy da gaske harna fito yana kallona kuma tunda na shiga yake kallona ni bansan kallo "hmm kede kika sani Mamy ta fad'a tana sanya hijab d'inta tare da ficewa taje su gaisa Aira ko zama tayi tana Jan tsaki ita kad'ai..........✍🏿