← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 127

Sashe 29

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 10 min read

*Ni da yaya arman Littafin kud'i ne ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa #200 Katin MTN to 07026166536*

*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[6/14, 18:32] Hajo hajo: 🅿️........*43&44*

Gaskiya kiyi hakuri Amma bazan bud'e maki ba idan har ba mai gidan bane da kansa ya ce na bud'e maki ba "jin abunda Baba mai gadi yace ya sanyata tashi ta Ruga ciki da gudu tana kuka tana zuwa ta fad'a kan Gado tare da fashewa da kuka saida tayi kukanta mai isarta Arman ne ya kira d'auka tayi cikin kuka ta ce " Yaya Baba mai gadi ya hanani fita wlh ba irin magiyar da ban mashi ba "daga dayan bangaren Arman sosai baiji dadi ba cewa yayi " ki kwantar da hankalinki kinsan bansan kukanki kuma ke baki tashi yi sai gabana"share hawayenta tayi tare da turo baki kamar yana gabanta ta ce "To ba dole nayi kuka ba kana gari amma anhanamu ganin juna" To sai kiyi shiru mu nemi mafita ko kukan shi zai zame mana mafita"a a yaya "Numfasawa yayi ya ce " matsala ta dake baki iya dabara ba ke a y'an farin ma shugabar faranta ce Wlh ko k'aramun yaro ya fiki wayau "ya fad'a da sigar zolaya " Kamar zatayi kuka ta ce "Ni wlh ba y'ar fari bace Kaine ma za a ce d'an fari kuma auta tunda baka da yaya baka da k'ani Niko ina da yayyu ina da k'anne" ta fad'a tana turo baki "Dariya Arman yayi ya ce " yau naja gori ko to ai ni bana abubuwan y'an fari keko ko maganarki ta y'an fari ce "Allah yaya ka bari zanyi kuka" ta fad'a cikin shagwaba "Dariya yayi ya ce " sorry my cutie kar ayi kuka ayi hakuri"turo baki tayi ta ce "Kai naga bama ka damu ba da Rashin haduwarmu ko" hmmm bazaki gane bane cutie wlh nafiki damuwa kawai taurin haline kinsan maza da dauriya"Uhm tace"kinsan me za ayi"a a saika fad'a "Yanzu bari zakiyi jibi saboda gobe idan Kikayi ganewa za ai kije ki kaiwa mai gadi kudi kice Mamy ta ce ya sayo mata wani abun kinsan dai abunda zakice ke kuma yana fita ki maza ki fito " tsalle Aira ta buga akan Gado ta ce "yesssssss wlh yaya wannan dabarar tayi kwata_kwata ni banma kawo hakan a kaina ba" Dariya yayi ya ce "to kindai yarda kece y'ar farin" Turo baki tayi ta ce "Uhm ban yarda ba Kaine dai Dan fari'" sun tab'a Hira cikin nishad'i tukwana suka kashe suna gama waya Hafsa ta kira tana d'auka ta zolayeta da "Matar yayaana" Dariya Hafsa tayi ta ce "Mrs Arman ake gaya muku" murmushi Aira tare da dafe saitin zuciyarta ta ce "wayyyyo har kinsa Naji wani sanyi a cikin zuciya kai Gaskiya kinci katin 1k " Dariya Hafsa tayi ta ce "Allah shiryeki" Ameeen indai akan Yaya Arman ne Kuyi tayimun Addu'ar ya ake ciki ne wai har yanzu yaya Umar na Kiranki"ke inaso na baki labari kullum fa sai yaya Umar ya kirani musha hira kawai jiya ingaya maki Matarshi ta kirani ta dinga surfamun zagi ta uwa ta uba hada cewa wai "na k'ara kira mata miji saita sa an sauyamun kamanni" Hafsa ta k'arasa fad'a tana fashewa da Dariya "Dariya Aira ta fashe da ita ta ce " wayyo Allah cikina amma Gaskiya abun nan ya bani nishad'i Ai daman Nasan Bazata barkiba shegiya y'ar wahala"Dariya tayi ta ce "Ai na dinga chusa mata Haushi kenan tunda mahaukaciya ce" cikin dariya Aira ta ce hhhh kici gaba da gasa mahaukaciya Wai yace yana sonki kuwa"Uhm ke wlh baice yana sona ba shifa kawai a zumunci yake kirana ita kuma ta d'auka sona yake"haba Hafsa Ai yaya Umar sonki yake kawai wlh kawai fad'a maki ne baiba"Uhm kawai Hafsa tace tukwana suka saki hirar suka koma wata sunjima suna waya tukwana sukayi bankwana.kamar yanda Arman ya fad'a ranar Da wajejen Ukku Aira ta shirya cikin doguwar Hijab d'inta purple me hannu sosai tayi mata kyau a palour ta tarar da Mamy tana kallo "Sannu da hutawa Mamy" ta fad'a tana zama kusa da ita"kallonta Mamy tayi ta ce "Yawwa " Mamy Dan Allah 1k zaki bani"me zakiyi da 1k"Sosa kai tayi tama rasa k'aryar da zatayi sai chan ta ce "Uhm Mamy awara zan bada a sayoman "hmm jeki jikin drawer kayan Amer akwai jakata ciki ki d'auka saiki maidoman chanjin" Cikin murna ta tashi ta ce "Thnks you my dear mom ta fad'a tare da shiga taje ta d'auko zata fita Mamy ta ce Ina kuma zaki keda Abbanki ya hanaki fita" kamar zatai kuka ta ce "Mamy Bafa wani waje ba zani Ba Bala mai bawa flower ruwa ne zanba ya sayoman"to dan Allah karkije ko ina" To Mamy ta fad'a tare da fita tana zuwa ta tarar da Baba me gadi zaune cewa tayi "ina yini Baba Sannu da hutawa " yawwa y'ar kirki "Baba gashi inji Mamy ta ce Ka amso mata kati Dan Allah " Amsa yayi yace "to bari a amso na nawa" na d'ari biyar "yana fita Aira tayi Sauri ta lek'a taga ya danyi nisa a guje ta fice tayi d'ayar center saida ta daina Hango gidansu tukwana ta tsaya tana hak'i kiran Arman tayi ta ce " yi Sauri yaya kazo ina daidai karshen layin gidanmu kwanar wannan ta biyu zaka ganni"To cutie ganinan "Huci kawai Aira take Dan tayi gudu ba ayi minti goma ba saiga Arman saboda gudu ya sharara tana ganin motarshi cikin Sauri tana waige ta shige gidan Gaba sai hak'i take" Ajiyar zuciya dukansu suka sauke a tare kallonta Arman yayi ya ce "Badai gudu kikai ba" haba yaya meye ma banba muje dai kar wani ya ganmu ta fad'a tana rufo kofa "Jan motar Arman yayi suka bar unguwar sai kallonta yake itama tana Kallonshi a hankali ya ce " kinyi missing Dina kuwa cutie"cikin shagwababbiyar murya ta ce "my yaya ai ko ban fad'a ba fuskata kanta ta isa ta shaida maka kalar missing dinka da nayi" murmushi yayi ya ce "kuma zuciyoyinmuma sun isa su shaidawa junansu kalar kewar juna da sukayi ko" Eh mana my yaya ai yau jina nake kamar salla fa"Dariya yayi ya ce "Nikuma ji nake kamar Anyimun Albishir an yafe mani Duka laifuka na" Dariya tayi ta ce "Yaya kenan "Shima cikin murmushi ya ce " cutie kenan ina sonki fa sosai"murmushi tayi ta ce "Nima ina sonka sosai yayana sonda bana kwatantashi da komai" d'ayan hannunshi ya mik'o ya kama lausassan hannunta kamar auduga murza hannun ta yake cikin wani irin salo ita kanta Aira jin sak'on nashi take Sunkai tsayin minti kusan Ukku ba Wanda yayi magana ji tayi Arman yayi parking tare da kallonta cikin Wace irin murya mai cike da kasala ya ce "Mu yiwa juna Alk'awarin bazamu rabu da juna ba duk rintsi duk wahala please cutie" Aira batasan lokacin da wasu ziraren hawaye suka fara zarya daga idanunta ba Cikin muryar dake shirin fashewa da kuka ta kalleshi ta ce "my yaya" juyowa yayi ya Kalleta idanunsu suka sartse Cikin na juna kafe juna sukayi da idanu bako k'iftawa kama d'ayan hannunshi tayi hawayen dake idanunta suka zubo a hannuwansu ta ce "Alk'awarin mu ya na nan yaya karkatab'a kawowa a ranka cewar zan manta dakai bazan tab'a iya rayuwa babu kai a tare dani ba kaid'in ka zamemun wani bangare na jikina kamar yanda mutum baya rayuwa ba tare da zuciya ba to kamar haka rayuwata take muddin idan babu kai a cikinta bata da amfani" ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka tare da Rungumeshi "daddab'a bayanta Arman ya fara tuni zuciyarshi ta karaya da jin kalamanta Shima jin yake da zai samu damar da yayi kuka cikin sigar lallashi ya ce " nima ta bangare na hakan take Aira kullum fad'a nake ina Kara fad'a. Sonki daga Allah ne na kasa iya misalta kalar son da nake maki a cikin raina Inajin a jikina duk ranar da su Abba sukayi sanadiyar rabamu to ranar ce ranar ajali na.."rufe mai baki Aira tayi cikin kuka ta ce "Ka daina fad'ar haka yaya bazasu iya rabamu ba banason kana maganar rabuwar nan tana tayarmun da hankali"daddab'a bayanta ya fara Dan son kwantar mata da hankali ya ce " Ai daman Nasan abunda bazai tab'a yiwa bane tashi ki yi shiru ki kalleni"kamar yanda ya fad'a tashi tayi daga kanshi tare da Kallonshi murmushinshi mai tsada ya sakar mata batasan lokacin da ta mayar mashi da kayataccen murmushin ta yake Kara mata kyau "mu yiwa juna alkawari" ya fad'a ya d'ora Hannunshi ya Aje itama ta d'ora nata a kan nashi tare suka ce " Alk'awarin mu na nan har abada"Goge hawayenta Aira tayi Ta ce "Yaya ina zamu" Gida kinsan Mummy ta dameni akan tana son ganinki"y'a fad'a yana tada mota"murmushi tayi ta ce "Allah sarki Mummy nah nima inason ganinta nayi kewarta" .
b'angaren gidan su Aira Baba mai gadi yana dawowa yaga wayam ba Aira sallama yayi cikin gidan Dan a tunaninshi ciki ta koma Mamy ce ta lek'o ta ce "Lafiya Baba" kati ya mik'a mata tare da chanji ya ce "gashi sak'on da kika Aiko maman Alhaji da yake haka cewa Aira na sayo" Cike da mamaki Mamy ta amshi katin ta ce "Ita Airar ta ce Na aikota ina take ita d'in" sosai mamaki ya kama Baba mai gadi ya ce "Hajiya yanzu fa ba jimawa ta zo ta ce kince na amso maki kati nikuma na tafi na barta a nan" tab'a hannu Mamy tayi tare da salati ta ce "Aiko wlh Baba wayau kawai tayi maka ta fita ba wani Aikenta da nayi sannan ta jinjina kai ta ce " Allah ya shiryeki Aira har kin iya dabarar fita "Sosai Baba mai gadi yayi mamaki ya ce " lallai yaran zamanin nan a gansu a kyale karamar yarinya tayimun wayau "Dariya mamy tayi ta ce " Allah dai ya shirya mana zuri'a kawai za ace ka koma kan aikinka kawai Baba "itama ciki ta koma tana mamakin Fitsarewa irin ta Aira ashe kudin da ta amsa duk shirine girgiza kai kawai tayi taci gaba da Al'amuranta.
suna isa Government house a tare suka fito security na Sara musu har suka isa Babban Palourn gidan Mummy ta taho da fara'arta ta ce "oyoyoyo ga y'ata ta fad'a tana Rungume Aira cike da farinciki ta kama hannunta ta ce " Sannu da zuwa tunda kika tafi kika barni da kewa"murmushi Aira tayi ta ce "Nima nayi kewarki sosai Mummy nah " Sosai Mummy ta dinga nan nan da Aira kamar zata maidata ciki sosai hakan yake yiwa Arman dadi yanda Mummy ke son Airanshi sai wajen magriba Aira ta fara tunanin Gida sai sannan ma ta tuna a yanda ta fito kallon Arman tayi ta ce "Yaya Mamy tace kar muyi magriba " ta fad'i hakane Dan Mummy tayi zaton da sanin Mamy ta fito "Mummy ce ta ce " Au har ina tunanin kwana zakimun "Murmushi Aira tayi ya ce " Mummy ai zandawo nayi maki kwana biyu"To shikenan Aiko da Naji dadi sannan ta tashi ta ce "jira ni ina fitowa Mummy na shiga Arman ya dawo kusa da ita ya ce " Yanzu sai yaushe zamu k'ara had'uwa"Turo baki tayi ta ce "Saina duba" Dariya yayi ya ce "irin wannan wulakancin na y'an mata ko" Dariya tayi ta ce "To me yafi son raina badai kace kana soba ai gwalaka ma fa zan fara"Dariya Arman yayi ya ce " Haba yarinya munga Wanda zai gwala wani cikinmu"ganin fitowar Mummy ya sanya Aira harararshi ta ce "To ka tashi sai Mummy ta ganmu" Meye Dan ta ganmu kefa har yanzu kink’ii ki waye saina wayar dake"harara Aira ta galla mai ta ce "Ai nice ma na wayar dakai ta fad'a tare da tsinkuninshi d'an Kara yayi tare da tashi yana Dariya " Mummy na isowa ta mik'awa Aira k'atuwar kwali bag mai d'auke da hoton Mummy da na Daddy ga alamu dai na siyasa ne ta ce "Amshi ki kaiwa maman naki kice ina gaishe ta sosai Dan Allah" Amsa Aira tayi ta ce "To Mummy zan fad'a mata nagode sosai " Tukwana sukayi bankwana lokacin da Suka isa unguwarsu Ana kiraye kirayen magriba a Inda ya d'auketa ya sauketa har ya wuce ta na Mashi bye bye saida taga wucewar motarshi tukwana ta nufi layinsu Tsit ba kowa unguwar Cikin Sauri take tafiya Harta isa gabanta na fad'uwa ta na zuwa Knoking tayi mai gadi ya fito ya na K'are mata kallo Aira bata Ko Kalleshi ba ta yi Sauri ta shige cikin Sauri har tuntube take ta nufi hanyar Part d'insu Daga bayanta taji muryar Abba na cewa "daga gidan uban wa kike"Shock Aira tayi a wajen ta kasa koda motsi gwalo idanu tayi ta ce " na shiga ukku "Abba ko tsawa ya k'ara daka mata daga Inda yake kan farar kujerar roba ya ce " ba dake nake ba".......✍🏿
Chapter 29 · 0% Book details