Sashe 99
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Daga Gidansu Zaleeha kai tsaye unguwar tudun wada suka nufa wato gidan Baba Bello, aƙofar ɗan madaidaicin gidan na Baba Bello Sule driver yayi parking motar, both ya buɗe inda ya cirowa Saifuddeen kekensa, buɗe murfin motar Saifuddeen yayi, inda dakansa ya yunƙuro ya hau kan keken nasa.
Yana gama dai-dai ta zamansa akan keken, Jafar almajirin Baba bello yafito daga cikin gida, ganin Saifuddeen yasanya Jafar sakin murmushi cikin kulawa yaɗan rusuna tare da cewa. "Hamma Saifuddeen sannu da zuwa."
Murmushi Saifuddeen yayi masa tare da jinjina masa kai alaman.
"Yauwa."
Cikin sauri Jafar yajuya ya koma cikin gida, nan ya iske Baba Bello dake zaune yasanar dashi zuwan Saifuddeen, cikin hanzari Baba Bello yazura takalma aƙafansa, inda kai tsaye yanufi hanyar fita daga cikin gidan.
Fuska ɗauke da fara'a Baba Bello ya tarbi Saifuddeen, nan yayiwa Saifudeen ɗin iso zuwa cikin ɗakinsa dake hanyar soro.
Bayan sun zauna ne Jafar ya kawowa Saifuddeen ɗin ruwa acikin wani babban plastic jug, kofin ruwan Saifudeen ya ɗauka tare da kaiwa bakinsa, tuno da yanda Zaleeha ta turs masa kayan fruits gabanshi ga kuma tsoronshi cikin ƙwayar idanunta tono hakan ne yasa yayi, yasanyashi sakin murmushi, ɗan kaɗan yasha ruwan gudun kada Baba Bello yaji ba daɗi, cikin kulawa Baba Bello ya dubeshi kana yace.
"Sam ban tsammaci zuwanka ba Saifuddeen, ai da nasanya Innar ku (Matar Baba Bello) tayi maka kwaɗon zogale da tumatur, gashi kuma yanzu batanan taje kitso."
Murmushi Saifuddeen yayi tare da sadda kansa ƙasa, cikin body language ɗinsa yayiwa Baba Bellon alamar cewa babu komai, nan suka shiga ɗan taɓa hira da Baba Bellon, inda Baba Bellon ya nuna jin daɗin zuwan Saifuddeen ɗin, domin kuwa tun ranan da suka dawo daga zuwa dubasa da sukayi, lokacin dawowarsa basu sake haɗuwa ba sai yau ɗin, hira sukeyi tsakanin magana da kuma body language, inda sosai Baba Bello ke gane yaren Saifuddeen, wato body language, cikin girmamawa haɗi da kulawa Saifuddeen ya labartawa Baba Bello maganan aurensa, kama daga farkon tura masa tambaya har kawo yanzu, cikin hikima yanemi shawarar Baba Bello agame da bikin.
Cikin jin daɗin yanda Saifuddeen ɗin ya karramasa, yakuma maidashi uba, yasanya Baba Bello gyara zama, nan yashiga bawa Saifuddeen ɗin shawarwari masu kyau, sosai kuwa Saifuddeen ya aminta da shawaran, inda ya yanke cewa jibi jibinna za akai masa lefe da kuma sadaki, sun ɗan jima suna hira daga bisani yayi wa Baba Bello sallama, kuɗi yaciro ƴan bandir ɗin ɗari biyar biyar sabbi ƙal ya ajewa Baba Bello agabansa, cikin dattako da halin kamala Baba Bello yace.
"Dan Allah Saifuddeen kada kasa kanka awahala, bayan ɗaukemin nauyin gidana da kayi gaba ɗaya kuma saika ƙara da sakanka a wata wahalan? kabar kuɗinka Saifuddeen nagode sosai bani da abinda zance maka sai dai addu'a, domin kuwa koda baka da lfy baka ƙasarma baka daina kulawa damu ba."
Fuska Saifuddeen ya kwaɓe cikin rashin jin daɗin dawo masa da kyautar tasa da Baba Bello yayi.
fuska ya marairaice, cikin body language ɗinsa yace.
"Dan Allah Baba Bello ka karɓa, kaifa matsayin Uba kake agareni, kamar yanda zanyiwa mahaifina kaima haka zanyi maka.!"
Jikin Baba Bello ne yayi sanyi, haƙiƙa Saifuddeen yaron ƙwarai ne, samun irinsa na da matuƙar wahala, tabbas Ummi tayi sa'ar haihuwa, domin samun Saifuddeen amatsayin ɗa babban nasara ce ga rayuwa, haka Baba Bello ya amshi kuɗin nan batare daya soba saidai sanin halin Saifuddeen yasanyashi karɓan kuɗin dole, nan ya rako Saifuddeen ɗin har bakin motarsa, saida Baba Bello yaga tashin motar tasu Saifuddeen kafun ya juya yakoma cikin gida.
Daga gidan Baba Bello kuwa kaitsaye ƙaramar kasuwa suka nufa, abakin kasuwan sule driver yayi parking motar, shida kansa ya buɗewa Saifuddeen murfin motar tare da gyara masa zaman kekensa, haka Saifuddeen da Sule driver suka kutsa cikin kasuwa, cikin nutsuwa Saifuddeen ke sarrafa kekensa, duk inda suka wuce ido ne ke binsu, yayinda mutane da yawa ke yaba tsantsar kyau irin na Saifuddeen, saidai ganinsa akan keken guragu shine abun dake ɗaure musu kai, kowa kallon cikakken balarabe yake yi masa, sam koda wasa babu wanda ya shaida kamannin Saifuddeen, duk acikin mutanen dake kallonsa babu wanda yakawo aransa cewa shine wannan matashin saurayin dake gararanban yawon raba leda, yake kuma yawon raba omo, kana harma da tallan fiyo wata (pure water), babu wanda zai gansa ayanzu yace shine wannan yaron da yasha gwagwarmayar rayuwa, yayi ta zagaye kasuwa koro-koro luggu da saƙo.
Fuskarsa ɗauke da annuri ya ƙarasa gaban wawakeken shagon wanda yake mallakinsu, Mudassir da Warisu naganinsa suka taso cikin tsananin farinciki suka tarbeshi, sam basu tsammaci ganinsa ba don ya matuƙar shammace su, yaɗan jima kaɗan ashagon nasu Warisu inda suka ɗan taɓa hira kaɗan, duban Mudassir da Wareesu yayi cikin body language ɗinsa yace.
"Kufara shiri tun yanzu don nanda ƴan sati kaɗan zakusha biki."
Mamakine ya bayyana akan fuskar Wareesu, daɗan ƙarfi yace.
"Biki kuma na waye?."
Murmushi Saifuddeen yayi tare da nuna kansa.
Cikin alamun ban mamaki Wareesu yace.
"Wow Surprise kenan! Kai amma naji daɗi sosai Allah yasa ayi damu, koya Mudassir, yakamata ne ma ai mufara gagarumin shiri."
Wareesu yafaɗa cike da farinciki.
Shiru Ahmad da ya shigo yanzu yayi tare da kafe Saifuddeen da idanu, kallonshi shima Saifuddeen ɗin yayi, yanayin yanda yaga fuskar Ahmad kaɗai yasayashi gane abun dake cikin zuciyarsa, murmushin daya bayyana kyawawan dimples ɗinsa yayi, cikin son ganar da Ahmad irin yanayin dayake ciki ya lumshe idanunsa, hannunsa yaɗaura adai-dai saitin zuciyarsa wacce ke beating.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ahmad ya sauƙe, tabbas ya gane hakan da Saufuddeen ɗin yayi me yake nufi, alamace dake nuna cewa Saifuddeen ɗin nasonta da duka zuciyarsa, tabbas yana matuƙar jin tausayin Saifuddeen domin kuwa shi tuni yajima da gano cewa Zaleeha ba matar aure bace, ba irinta Saifuddeen ke buƙata ba, Saifuddeen yana buƙatar kamilalliyar mace, nutsatstsiya, wacce ta yarda da ƙaddara tayi imani mai kyau ko akasinsa daga Allah Ne, amma ya zaiyi dolensa zai haƙura da ƙin Zaleeha da yake, sahoda yaga gaba ɗaya soyayyarta ta rufe idanun Saifudeen, ya fahimci cewa Saifuddeen Zaleeha kawai yake gani aciki da wajen idanunsa, saboda haka zaiyi ƙoƙari wajen manta abun da tayi musu, zai taya Saifuddeen ɗin ƙaunarta, nan yayiwa Saifuddeen ɗin Allah yasanya al'khairi, daga shagon nasu Warisu kaitsaye Saifuddeen shagonsa ya nufa, shida Ahmad masha Allah koda yaje yasamu nutane maƙil sun cika shagon, sayan kaya kawai suketayi, yayinda cikin shagon ke shaƙe da kaya tam na yara irin new designer ɗinnan masu kyau, Manyan Hajiyoyine keta business ɗinsu, wasu sayan dayawa sukazo wasu kuwa sayan ɗaɗɗaya , kasancewar shagon cike yake da mutane yasanya Saifuddeen baiwani zauna acikin shagon sosai ba ya tafi, Kaitsaye shagon Ba mishkila ya nufa, nan ya iske Ba mishkila yau shida kansa ne acikin shagon, ba ƙaramin farin ciki ba mishkila ya yiba dayaga Saifuddeen, nan yashiga tambayarsa jikinsa, inda ya amsa masa cewa "Dasauƙi sosai"
Daga shagon ba mishkila shagon Alhaji Ishaq baban abokinsa wato Ibrahim ya nufa, sosai Alhaji Ishaq yaji daɗin ganin Saifuddeen, shima sun ɗan taɓa hira inda yayi masa ƙarin ya jiki, daga shagon Alhaji Ishaq shagon Alhaji Kabiru Saifuddeen ya nufa, nan fa shima Alhaji Kabirun yacika da murnar ganin Saifuddeen, kasancewar hakan alamace dake nuna cewa sauƙi ya samu ga Saifuddeen ɗin. Sosai Saifuddeen yaɗan jima acikin kasuwan yayinda ya tsaya yagabatar da sallan Magriba cikin masallacin dake gefen kasuwan, yana idarwa suka kama hanyar dawowa gida.
Ahankali yake tuk'a kekensa haryakawo cikin falon na ummi inda ya iske Raliya, Hayatuddeen, da kuma Ummi wacce ke zaune akan kujera, Hayatuddeen na zaune aɗan gefe da ita yana latsa wayarsa, Raliya kuwa tsugune take agaban Ummin tana mammatsa mata ƙafa, murmushin dake kan fukar Ummi ne ya faɗaɗa sakamakon ganin yanda fuskar ɗan nata ke ɗauke da farin ciki, cikin kulawa tace.
"Saifuddeen kadawo?"
Kansa ya jinjina mata tare dayi mata alama, cikin body language ya sanar mata cewa daga kasuwa yake.
Murmushin jin daɗi Ummi tayi tare da cewa.
"Allah ya taimaka."
Duban Raliya tayi cikin kulawa tace.
"Bar matsamin ƙafannan haka jeki kawowa hamman naku ruwa mai ɗan sanyi yasha."
"To."
Raliya tace tare da miƙewa tsaye ta nufi hanyar kitchine ɗin dake cikin falon.
Hayatuddeen ne ya ɗago kansa, inda ya kalli Hamman nasa, cikin tausasawa yace.
"Hamma barka da dawo, dama kamar kasan naƙosa ka dawo wallahi."
Murmushi Saifuddeen yayi tare dayi masa alaman meke faruwa?
Gyara zama Hayatuddeen yayi cikin zumuɗin labarin dake cinsa yace.
"Ina wannan kyakkyawar mawaƙiyan da muka haɗu da ita a jirgi, lokacin da zamu dawo Nigeria, Hamma ka tuna ta Asma'u Ahmad Matawalle?."
Yaƙare maganan yana me tsatstsare Hamman nasa da ido.
Ɗan jim Saifuddeen yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, in few second ya hasasho fuskarta, duban Hayatuddeen yayi tare da gyaɗa masa kai alamar eh ya tunota.
Gyara zama Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Yauwa Hamma, wai kasan mene? tun ranan da takarb'i phone number na, kullum sai munyi chart, bata da wani labari sai naka, kullum maganarka take, shine yau tace nafaɗa maka wai tanasonka, zaka aureta?."