← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 116

Sashe 97

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da turarenta mai azababben ƙamshi ta feshe gaba ɗaya jikinta, wani ɗan siririn mayafi mai kalan kayanta ta yafa daga kan wuyanta zuwa ƙugunta, yanayin yanda dogon baƙin gashinta ya kwanto akan gefen wuyanta shi ya matuƙar ƙara ƙawata ado da kuma kyawunta, wani takalmi mai uban tsini ta sanya aƙafafunta, cikin takunta mai nuna tsantsar aji, ƙasaita, wayewa, da kuma jinkai tafito zuwa falo, nan ta iske Mama da kuma Zahira suna hira, duban tsab Mama tayi mata fuska shafe da toka tace.
"Sai ina?."

Zama tayi akan hannun kujera tare da ɗan turo bakinta gaba murya acushe tace.
"Makay zanjeni yin shooping".
Baki Mama ta taɓe tare da gyara zamanta ta fuskanci Zaleehan, fuskarnan tata sam babu alaman fara'a tace.
  "Ya kukayi da banzan gurgun da yazo wajenki jiyan?."

Lokaci guda yanayin fuskar Zaleeha ta sauya kala domin tunowa da baƙin cikinsa da tayi, cikin bayyana tsantsar tsanarsa da tayi tace.
  "Na musu bana sonshi." 
Ƙwafa tayi tare da ɗan gyara zamanta tacigaba da cewa.  "Wai harni wani banzan MUSAKI zaizo yace yana son ƴata hmm!."
Murmushin jin daɗi Mama tayi tare da ci gaba cewa. 
"Ae ni banga laifinsa bama, dama ni tuncan wannan ɗan iskan aikin naki na Babu maraya  ne, ko Nakasa ba kasawa bace ko mene yake da suna, sam ba ƙaunarsa nake ba, amma dayake ke uwar taurin kaine haka kike zuwa cikin nakasassu musakai kita washe haƙora kina naɗan muryarsu wai ke adole mai tausayi ƙaunarsu, to ai gashinan kin fara ganin sakamako tunda dai har Kurma kuma gurgu yasamu daman biyoki har gida da maganar soyayya.

Hannu Ya Aminu ya bawa Saifuddeen suka gaisa amutumce, nan Ya Aminu dakansa yayiwa Saifuddeen jagora zuwa BQ, shikam har acikin ransa ya yaba da nutsuwa da kuma haiba haɗi da kwarjini irinta Saifuddeen, koda Ya Aminu yayi masa jagora zuwa BQ cewa yayi dashi bari ya ƙira masa Zaleehan, cikin body language Saifuddeen yace "To."
Tare da yiwa Ya Aminu'n godiya.

Ɗan ƙaramin bakinta taƙara cunowa gaba, tare da gallawa Zahira dake ta dariya ƙasa ƙasa najin cewa wai kurma kuma gurgu yazo wajen yayartata da ƙoƙon barar soyayya, baki Zaleeha ta buɗe don kaftawa ƙanwartata rashin mutumci shigowan Ya Aminu ne yasanyata saurin haɗiye maganan dake ranta, dan da tayi niyan aunawa mayataccen gurgun zagine, kana daganan saita ci mutumcin Zahira dakeyi mata dariya.
Duban Zaleeha Aminu yayi fuskarnan tasa sam babu alaman annuri akanta, cikin tsare gida yace.  
"Ke Zaleeha kije kina da baƙo a Boys Quaters."

Wani irin faɗuwa gaban Zaleeha yayi, cikin sarƙewar murya tace.
"Ni...Ni kuma Ya Aminu?."
Harara Ya Aminu ya watsa mata cikin yanayinsa na rashin fara'a agaresu yace. "Da akwai wata Zaleehan agidannan ne bayan ke? ko kuma aduk gidannan akwai ƙatuwar gantsamemiyar budurwa sama dake? Maza tashi kije Saifuddeen ne yana jiranki banason shashanci!." 

Idanu Zaleeha ta zaro, lokaci guda jikinta yasoma ɓari kamar mai aljanu, sam ta manta da cewa Ya Aminu ne agabanta cikin tsananin ɓacin rai tace.
"What! Mayataccen gurgun nanne yaƙara dawowa, aikuwa saidai ya shekara don babu inda zanje!!".
Taƙirasa maganan cikin rufewar ido.

Cike da mamaki Ya Aminu ya matso inda take azafafe, cikin tsananin ɓacin rai yace "Me kikace? Maimaita nasakeji don banji da kyauba!".

Shiru Zaleeha tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, wani irin tafarfasa ranta keyi mata, ji take kamar ta kurma wani uban ihu ko zatasamu salama acikin rai da zuciyarta.

Jin tayi shiru batace komai bane yasanya Ya Aminu daka mata tsawa cikin faɗa yace "Kintashi kinjene ko saina ɓaɓɓallaki anan wajen shashashar yarinya da batasan ciwon kanta ba!!."

Jikin Zaleeha narawa ta-tashi da sauri har ƙafafunta na harɗewa haka ta nufi hanyar fita daga falon tuni wasu irin hawayen baƙin ciki sun cika idanunta, fuuuu haka Ya Aminu ya fice daga cikin falon,  tsuka mai ƙarfi Mama tayi cikin baƙin ciki da takaicin Mijin ƴartata Maryam wato Ya Aminu tace. "Wallahi indai akan Zaleeha ne babu wanda ya isa yayi mata dole, idan kuwa har dolennema za a mata tofa lallai saidai in akan Abdussalam, amma wallahi babu wani matsiyacin gurgu daya isa nahaifi ƴa kuma ya aure ta."
ƙwafa Mama tayi tare da cewa.
"Duk zanyi maganinku ne ae dani kuke zancen!."

Zaleeha kuwa ko gabanta bata gani da kyau saboda tsabar hawayen da suka cika idanunta, wani irin ɗaci na ɓacin rai takeji a maƙoshinta,  cikin ranta wata irin wutar masifa ne ke cinta, yayinda wutan tsanarsa ke ƙara ruruwa acikin zuciyarta,  tana kawowa bakin ƙofan da zai sadata da babban falon BQ ɗin ta tsaya cak,  ƙoƙarin shanye hawayen dake cikin idanunta tayi,  da wani irin ƙarfi ta bugi ƙofan falon, cikin takunta mai ɗauke da isa da kuma tsantsar rashin mutumci ta kutso kanta cikin falon.
Idanunsu ne suka sarƙe acikin najuna domin dama tuntuni idanunsa akan ƙofar shigowa falon suke.
Wata uwar harara mai ɗauke da tsantsar tsana, Zaleeha ta watsa masa, cikin takunta dake nuna tsantsar rashin mutumcin da takeji dashi ta ƙaraso cikin falon, ƙwas-ƙwas haka sautin takun takalminta ke amsa gaba ɗaya ilahirin falon, sam idanunta ya rufe da tsana, haɗi da masifar dake cinta arai, cike da son ƙuntata masa ta tsaya kusa dashi tare da sanya hannayenta ta kama ƙugunta,  amasifance tace.
  "Waikai wani irin maye ne? ina tunanin tun a jiya nasanar dakai cewa bana sonka na tsaneka!".
ɗan shiru tayi tare da dubansa sama da ƙasa da sauri ta janye idanunta daga nashi dan wani irin bugu da zuciyarta keyi a duk sanda suka had'a ido,
tabbas yayi kyau sosai acikin idanunta amma masifane kawai ke ɗawainia da ita, cikin gatsali tace.
"Oho wato kazone don ka nunamin naci da kafiya irintaku ta kurame ko?  to bari kaji duk bala'in nacinka bazan taɓa sonka ba, na tsaneka wallahi natsani ganin fuskarka, waima shin kai bakasan cewa kai nakasashshshe bane? gurgu, kurma, sannan kuma maye" ɗan numfasawa tayi tare da sake matsowa kusa dashi cikin son ƙunsa masa baƙinciki tace.
  "Kakalleni da kyau koda a iya fuskata aka tsaya kai kasan niba matar yara bace, bare kuma irinka wanda bazai taɓa amfanata da komai ba, ginannen taɓo mai kama da dutsi!".
Taƙare maganar tana jujjuya masa idanu tare da murguɗa baki, wai ita ala dole hakan masifa takeyi.
Tunda tashigo cikin falon yake kallonta har kawo yanzu, wani irin sanyine yaji yana ratsa zuciyarsa, sosai abubuwan Zaleehan ke bashi dariya, duk acikin abubuwan da ta faɗa babu ɗaya wanda bai fahimci me tace ba sai dai ya gane tana tsoron kwayar idanunshi, acikin ransa yace.
"Ginannen taɓo ko, hmmm zakisha mmki!."
Ƙawataccen murmushine ya bayyana akan fuskarsa,  cikin tsananin takaici Zaleeha ke kallonsa, zuwa yanzu kam yakaita bango don yagama ƙureta ahatsale tace. 
"Kayi dariya zama kayi kuka da waƴannan fitinannun idanun naka masu kama dana zuri'ar mayu, wallahi-wallahi, idan baka rabu dani ba nice nan ajalinka, me yasa bazaka gane cewa na tsaneka bane? Meyasa bazaka kalli wutar tsanarka dake ruruwa acikin idona ba? kaduba kaga na tsaneka nace, na tsaneka!!!".
Cikin tsananin ƙaraji take maganan yayinda hawaye suka cika idanunta, jitake kamar taje ta ɗauko wuƙa ta caccaka masa.
Dai-dai lokaci Sallaman Kaltume mai aikin gidan nasu ya ratsa kunnuwanta,  amatuƙar harzuƙe tajuyo tana kallon Kaltume,  ƙarasowa cikin falon Kaltume tayi hannunta ɗauke da wani babban tray wanda samansa ke ɗauke da bottle water dakuma kayan marmari dangin su Apple da Inibi, akan babban table ɗin dake tsakiyan ɗakin Kaltume ta ajiye tray ɗin, dubanta takai ga Saifuddeen wanda yake kallonta, aladafce tace dashi "Ina wuni ranka shi daɗe!".
Murmushin daya bayyana cikar haiba da ƙwarjininsa yayi inda ya gyaɗa mata kai alamar.
"Lafiya"
Nan Kaltume ta miƙe tafice daga cikin falon aranta tana me mamakin tsananin kyau irin nasa take cewa.
"Duk yanda akayi balarabe ne shiyasa banji ya amsa gaisuwata ba, dadukkan alama baisan ma menace ba, gsky Aunty Zaleeha tayi sa'an miji".
Chapter 97 · 0% Book details