← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 116

Sashe 3

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ranar da aka basu kud'i a ranar Bappa Ali ya shiga cikin birnin gombe ya sayowa Nuruddeen mashin d'in bajat sabuwa dal,
kana daga ranar suka fara cuku-cukun nemawa Saifuddeen gurbin karatu a makarantar kurame ta Gombe. Special education Gombe state,
cikin sa'a aka sama mishi takardar shaidar ya zama d'alibinsu zai ci gaba daga JSS two, kasancewar da sa hannun Malam Ashiru abokin Abbansu kuma Saifuddeen kanshi na ja sosai domin nakasarsama kamar k'ara zaburar dashi tayi.

Daga wannan ranar kullu yaumin fisha'i.
Nuruddeen zaiyi sammakon baro Dukku tare da Saifuddeen suna shiga gombe ya kaishi makaranta kana shi kuma ya shiga cikin gari yayi ta kabo-kabonshi tun baisan anguwaninba har yazo ya saba ya goge ya zama idon gari,
sai sun karya suke tahowa kana shabiyu nayi zai kaiwa Saifuddeen abinci duk da ana basu abinci a makarantar kasan cewar sashinta boarding school ne kana kuma akwai yan jeka ka dawo in har iyayenka zasu iya d'aukar dawainiyarka.
A ranar forko Saifuddeen ya had'u da abokinshi Is'haq makaho wanda suka shak'u sosai har yan uwan is'haq sun san Saifuddeen da Yayanshi Nuruddeen, hakama Nuruddeen yasan yan uwan is'haq dan har gidansu yana zuwa,
dan in an bada hutu Saufuddeen kan biyo Seyo gombe ya kawowa abokinshi ziyara su wuni suna hira da yake shi Is'haq iyayenshi a gombe suke cikin anguwar Fada,
shi Is'haq makahone kuma shima k'enda ce sila makantan shi dan ya bawa Saifuddeen lbri suna hira ta hanyar is'haq yayi Magna shi kuma Saifuddeen ya rubuta mishi amsa a wayarshi da yake iyayen is'haq sunada yar wadata sun saya mishi waya.

Haka rayuwa tai ta tafiya mashin d'innan ba k'aramin rufa asirinsu Ummi yayiba,
suna samun komai a wadace, shi kam Nuruddeen ya jingine batun nashi karatun dama dukkan buk'atun rayuwarshi burinshi ya gina rayuwar Saifuddeen.

Tuni rayuwa ta mik'e, sai dai kullum jikin Abba na yawan tashi,
Rahma ta haifin d'anta na fari mai suna Faruq, har ta kuma haifi na biyu mai suna Adam.

Tuni Saifuddeen ya tafi SS 3 shida abokinshi Is'haq da wasu sauran yan ajinsu karatu sukeyi sosai babu kama hannun yaro kuma. Alhamdulillahi kwakwalensu na ja.

Tuni Raihana ma ta fara zama yar budurwa hakama Raliyya Hayatuddeen ma tuni ya tafi primary 3.

Bappa Ali kuwa har yau Allah bai bashi haihuwa ba,
Kuma shike jan ragamar makarantar da mahaifinsu ya bari.
Goggo Dada kuwa tun haihuwanta na fari bata kumayin koda b'ariba tuni d'an nata Ahmad ya girma domin sa'an Saifuddeen ne shi.
Alhamdulillahi su Saifudddeen sun kammala makarantar especial education lfy,
har anyi bikin yaye d'aliban
kana yanzu sunata shirin zana jamb dan samun gurbi a jamir'ar G.S.U wanda shine burinsu.

Ana cikin haka Allah ya yiwa mijin Rahma rasuwa,
dole ta dawo gida da yan yaranta Faruq da Adam daga nan nauyin kula dasu ya dawo kan Nuruddeen,
abu ya had'e mishi gashi yanzu jikin Abba ya tsananta tsawon shekara guda kenan da abun ya tashi bai kuma sakeshi ba koda na dare biyu ne, duk ya rame ya lalace sai tsawonshi daya k'ara fitowa kana farinshi ya k'ara baiyyana
hancin nan nashi har kan baki,
gashi yanzu baifi gonaki shida bane ya rage musu, sai filayen cikin gari,
inda sunada fili a biyu a Sirinkiyo da katafila duk sunada fili anan,
sai kuma nan gidansu na gado da yake Dugge nan kusa da Fadan Dukku d'in .

dole ciwon Abba yasa aka saida gonaki biyu ya rage musu hud'u,
inda suka zuba kud'in wurin nema mishi mgnin.
Sukaje bauchi wurin wani Mlmi irin masu Islamic kemis innan,
nan duk kudaden suka k'are dan magungunansu da tsada,
Alhamdulillahi jikin ya d'anyi sauk'i sosai.
Sai kuma wani mak'ok'o ya fito mishi nanfa, suka fara jinyar asibiti kuma, amman ina abu sai gaba-gaba yakeyi,
ta kai matakin da ko tsawonshi baya iya mik'ewa.
Bappa Ali yace a kuma saida sauran gonakin amman Abba ya hana acewarshi kada su Kuma saida komai a kanshi dan yasan wannan ciwon ba barinshi zaiba kar yazo ya mutu bai barwa yaranshi komaiba,
sun so suk'i bin shawararshi amman sai yace bai yafe musuba in suka kuma saida wata kaddararshi dan jinyarshi,
su bari in ya rasu suyi duk yadda sukaga dama da kaddarorin da suka rage dole suka hak'ura, badon sun soba, haka yasa Nuruddeen zagewa da yin acaba don samo kud'in da za'a nema mishi mgni, wani lokacin sai k'arfe goma na dare yake baro gombe ya nufi Dukku.
Saifuddeen kuwa shike kula da Abban tunda yana gida,
bappa Ali ma yanzu bai fiye zamaba yana tafiye-tafiye dan yana bin kasuwannin k'auye yana aune-aunen kayan abinci. Still kuma dai yana kula da d'aliban sun, dan da safe baya tafiya sai ya karantar dasu na safe, kana in ya dawo da deddere bayan sallan isha za a hura wuta a tsakiyar tsangayar daliban su zazzauna kan itatuwan dake zagaye da wutan ayi ta karatu, sai k'arfe tara da rabi ake tashi,

Yau asabar da sanyin safiya Nuruddeen ya fara shirin tafiya gombe,
sai ya kuma fasa ya dawo ya zauna tsakiyar k'annenshi Raihana nayiwa su Faruq wonka dan Faruq ya fara zuwa makaranta, Abba kuwa yana zaune jingine da pillow,
kana Saifuddeen na gefenshi yana sa mishi sugar a cikin kunun koko da Ummi ta dama musu, kana Rahma kuma tana toya musu kosan da zasu had'a da kunun suyi karin kumallo dashi,
Raliyya kuwa wonke-wonke takeyi.
gefen Ummin shi ya zauna tare da tonkoshe kai irin yadda Saifuddeen keyi sannan yace.
"Na fasa tafiya yanzu yau sai azahar zan tafi."
cikin disashewar murya Abba yace.
"Meyasa?."
ajiyan zuciya yaja tare mik'e k'afafunshi kana ya yayi murmushi tare da cewa.
"Yau dai abincin Ummina zan ci."
Rahma ce ta juyo ta kallesu tare da cewa.
"Kuma dama d'an malele zamuyi yau Ya Seyo nasan kai kana son d'an malele,
ba irin Saifu ba da yake cewa muma mmki muke bashi wai shi baiga abin ciba a dan malele."
Hayatuddeen ne ya tura baki tare da cewa.
"Gskyan shi ai, dan malele fa abincin matane."
murmushi Ummin tayi tare cewa.
"Kada ku damu kowa zaici abinda yakeso, nasan Autana da Hamma Saifunshi da Abbanku suna son d'anwake, ni kuwa da sauran muna son d'an malale shiyasa nace ayi duka biyu kowa yaci abinda yake so."
murmushi sukayi baki d'aya kana sukaci gaba da hira,
sannan Rahma ta gama tuya ta kawo musu tsakiyarsu nan suka zauna sunaci suna hira,
saidai Ummi da Saifuddeen sam basuci wani mai yawa ba,
shi kuwa Nuruddeen sosai yaci kosan nan yana korawa da koko.
cikin kula Nuruddeen ya kalli Ummi tare da cewa.
"Lfy kuwa Ummi naga kinyi shiru da yawa, ko kokon baki shaba, gashi kin san Saifu bazai ciba muddin yaga kina cikin damuwa."
murmushi tayi sai kuma ga hawaye,
da sauri Saifuddeen ya zuba mata idanu lokaci d'aya idanunshi sukayi jazir.
shi kuwa Nuruddeen kasa had'iye abincin bakinshi yayi dan ji yayi ya mishi d'aci ranshi na suya,
tuni shima hawaye suka ciko mishi ido,
Rahma kuwa mik'ewa tayi ta shiga d'akinsu haka nan tausayin Umminsu da kanta da Saifuddeen yasata kuka tuno mijinta daya tafi ya barta, kana ga uba ba lfy. Kuka ne sosai ya rufeta tuno sam Umminsu tunda tayi aure take cikin k'uncin rayuwa.

Shi kuwa Nuruddeen cikin k'arfin zuciya ya sharce hawayenshi, kana ya d'ago kanshi ya kalli Ummi da ta zubawa Abba ido tana kuka,
cikin raunin murya yace.
"Ummi". kai ta juyo a hankali kana ta zuba mishi ido,
shi kuwa murmushi yayi still hawaye na zuba,
cikin k'arfin guiwa da yak'ini yace.
"Ummi ki kalleni, ki cewa k'annena su kalleni."
sai ya kuma share hawayenshi kana ya kalli Saifudden daya zuba mishi ido ko k'ibtawa bayayi sannan yaci gaba da cewa.
"Ummi na kada kiyi kuka, ki meda idanunki da buk'atun rayuwarki dana k'annena dana yaran k'anwata a kaina, dai zan iya kula daku, Ummi na kada kiyi kuka, kin ganniko ni d'innan nine farin cikinku, kin manta wanne suna kuka bani inkiya SEYO fa kike cemin to kuyi imani da Allah ku yarda da kaddara mai kyau ko akasinta, ku kalleni ni zan jure d'awainiya daku iya rai da mutuwa."
sai ya kuma kamo hannun Ummi da Abban su cikin rawan murya yace.
"In sha Allahu Ummi na ni d'innan sai na kaiku makka da madina birnin ma'aiki, insha Allah ni d'innan zan share hawayenku,
Ummi in dai fa ina raye to insha Allah bazakuyi kukaba."
sai ya kuma kalli Saifuddeen kana yace.
"Gamu Allah ya baku zaratan yara kyawawa muminai salihan bayin Allah,
ko ni na gaza zama gatanku in sha Allah Saifuddeen zai zama Garkuwar ku kuma zai saku farin ciki, zai kula daku ya ruggumi buk'atunku."
Raihana ce ta sharte hawayeta tare da cewa.
"Dan Allah ya Seyo kubar kukannan haka kallifa yadda kukasa Abba da Hamma Saifu kuka, please Ummi ki rink'a bamu k'arfin guiwa kada ki bari hawayenki suna zubowa."
jin haka yasa Ummi share hawayenta kana tasa hannu ta share na Saifuddeen da Seyo, shiko Saifuddeen ya share na Abbansu daya gaza cewa komai dan ya lura jikinsu ne ya fara basu zai mutu ya barsu da maraici.

Daga nan sai kuma suka d'an sake,
haka dai sukayi ta hira har Rahma ta gama musu abinci, kowa yaci abinda ransa keso.
Chapter 3 · 0% Book details