← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 116

Sashe 21

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau jumma'a kana ana tsula zafin rana kowa ido yayi zuru-zuru sabida k'ishi da yunwa mazauna inuwama suna shan zafin azumin bare masu k'ananan sana'o'i irin Saifuddeen mai sai da leda da yan dako da yan garuwa da masu gonjo da kafintocin sama da kuma 'yan acab'a da direbobi.
Gashi yau shine azumi na 20,
Sosai Saifuddeen ke azabar jin k'ishi hakane yasa k'arfe hud'u dai-dai ya maida omo inda yauma ya samu riba sosai,
dama ya gama had'a ribar leda wanda yanzu masu sayan sun d'an k'ara sabida karatowan salla yasa cini kaiya k'aruwa.
Shagon ba miskila yaje yana isa Bello ya kalleshi cikin kula yace.
"Bingel yau ba omon ne?."
cikin gajiya ya lumshe ido tare da sharte zufar da yakeji da hankicib d'inshi cikin gajiya ya lumshe ido tare da mishi alamun akwai ya gajine yasa ya maida.
cikin kalato yawu Bello yace.
"Gsky kam bingel am azumin yau yanada dad'i."
murmushi sukayi baki d'aya kana Saifuddeen ya nunawa Bella d'anyar shinkafa da fulawa da sugar da geron
sai yaga kuma kamar bai fahimtaba hanne yasa shi zaro biro ya rubuta mishi cewa yana son d'anyar shinkafa da fulawa da sugar.
cikin kula ya auna mishi kana ya bashi kud'inshi shi kuma ya bashi ledodin daya zuba shinkafar a ciki.
Karb'a yayi sannan ya wuce ya sayo mai dasu yis, dan yana son a rink'a had'awa da masa a sadakan da ake kaiwa masallacin.
Sai kuma ya sai kayan marmarin daya saba saya, sannan yaje layin masu nama,
zabbi ya saya guda uku aka yanka aka fige aka gyarasu.
sannan ya fito bakin inda Salisu zai sameshi nan ya irga sauran kud'in inda ya samu ya shigesu sosai yau dubu uku zaisa a asusunshi,
yana zama ba jimawa Salisu yazo sauk'e wota mata kuma lokacin biyar saura aifa yace kawai su tafi gida,
to dama shima Salisu ya gaji kawai sai suka kama hanyar dukku.

Suna isa gida Hayatuddeen da Faruq suka tarbeshi,
da murnarsu bayan ya ajiye ledidin yayiwa Ummi alamun tayi musu ferfesun zabbin da asuba suci ko da biredi da tea
ai kam Raihana murna ta rink'a wai zata huta yin miyan asuba.
Shi kuwa gefen Rahma ya zauna sai ya kuma manna kanshi a kafad'arta cikin nuna tsantsar alamun gajiya domin Saifuddeen yana da tsoron wahala to kuma Allah ya jarab ceshi da ita,
cikin tausayawa ta shafa fuskarshi dan gaba d'aya jikinshi rawa yakeyi,
cikin tausayawa tace.
"D'an uwana sannu yau azumin da wuya anyi rana."
ido ya lumshe yana mai jin azabebben k'ishi,
a hankali ta kalli Ummi da tuni idonta sun cicciko da hawaye,
sai ta kuma kalli Raihana cikin sanyin murya tace.
"Raihana kai mishi ruwan wonka."
da sauri ta mik'e duk da tana jin wahalan azumi amman tasan dole ya fita shan zafin rana,
a randar tab'onsu ta d'iba saida ta cika mishi botiki sannan ta kai mishi bayan gida wanda yana wonke stab dan shi kad'ai ke amfani da bayan gidan tunda Nuruddeen da Abba suka rasu Hayatuddeen har yanzu bayan gidansu Ummi yake zuwa.
Tana kai ruwan taje ta d'auko mishi kondon sosonshi ta kai mishi sannan tace.
"Hamma na kai ruwan."
kai kawai ya iya gyad'a mata kana ya k'ara lafewa jikin Adda Rahmanshi,
jin hannun Ummi a kan gishinsa ne ya sashi d'ago kai ya zuba mata idanu,
ganin alamun zatayi kuka sai ya yunk'ura ya mik'e jiki na rawa,
cikin sanyi tace.
"Babana baka da lfy ko."
kai ya jujjuya mata a hankali kana yasa hannunshi kan cikinshi da yake a d'akale bafa irin d'akalellen cikin maceba a a irin nasu na maza,
sai ya kuma nuna mata mak'oshin sa alum k'ishi yakeji,
cikin kula tace.
"Je kayi wonka zakaji sanyi Babana."
Kai ya gyad'a mata sannan ya juya a hankali ya shiga kayan da zai sa ya d'auka sannan ya shiga bandakin,
yana shiga ya zare kayan jikinshi duka sannan yaje ya zauna bisa dutsen wonkan da yaketa shek'i da yake a inuwa yake baiyi zafiba,
surarshi ya k'arewa kallo idon ya zuba kan mararshi a ranshi yace.
"Hmmm yau kam kaji haza bayan baccinma har b'uya kayi ka koma cikin cikina ko?."
sai kuma ya fara watsa ruwan.

To Alhamdulillahi da yayi wonkan ya ji dama-dama gashi yana fitowa ana kiran salla,
al'wala yayi wanda tuni Ummi na gabanshi rik'e da dabino da surki mai d'umi,
dabinon ya amsa addu'a yayi kafin yaci guda uku,
da sauri ya jujjuya kanshi alamun shi bazai sha surkinba.
infa da sabo Ummi ta saba don haka yake ba komai yake ciba kuma zai tace maka yana jin yunwa kana kawo mishi abinci in ya tsakuri kad'an sai ya cire hannu wai ya k'oshi.
da sauri Hayatuddeen ya mik'o mishi pilet d'in su kankana to nan ya amshi fork a hannun Raihana sannan ya fara sokawa jikin kankanan da Rahma ta zuba mishi madara da sugar kad'an sabida ta sanshi da son zak'i,
ido kawai Ummi ta lumshe tana kallonshi sai yana tuno mata k'uruciyar Abbanshi,
bai shanye rabinshi bama yayi wani sassanyan gyatsa tare da mik'ewa wai ya k'oshi kenan,

jin ana tada kabbarane yasa Ummi bata hanashi fitaba,
shi kuwa kama hannun Hayatuddeen yayi suka fita zuwa masallacin.

Suma su Ummi sukayi haramar yin sallan.

Bayan an idar da salla, suna fitowa, Mudassir, Warisu, Salisu.
Suka nufi cikin gidansu Saifuddeen kai tsaye a babbar taburmar da Ummi ta saba shimfid'a musu suka zauna.
Rahma mace ta mik'e a hankali ta fara jero musu abin motsa baki, kankana da ayaba da dabinon suka fara ci, sunaci suna hira Rahma kuwa ita da kanta ta matso gefensu zama tayi tare da yi musu harara sannan ta jawo kulan dake gabanta cikin fidda numfashi tace.
"Daga yau bazan sake biye mukuba,
kun sani yi muku yambos wallahi ba k'aramar wuya na shaba kirba doyan nan wuya gareshi, gashi Raihana k'in tayani tayi wai ai nike biye muku."
Saminu da yanzu ya shigo tare da Saifuddeen ne ya harari Raihana tare da cewa.
"Yan ubanci zatayi mana shareta Adda Rahma ran salla ke kad'ai zamu bawa barka da salla."
tab'e baki Raihana tayi tare da cewa.
"Kada ku bani mana ni dama ban rok'aba."
Muddassir ne yayi d'an gyaran murya kana ya kalleta cikin tsuke fuska da bada umarni yace.
"Ni bazanma ci wannan yambos d'inba, yanzu ki d'an soya min dankali."
tura baki tayi tare da mik'ewa tana cewa.
"Ni wlh na gaji kuma yunwa nakeji."
Ummi ce ta d'anyi dariya kana tace.
"Zo Raihana taho nan ga dankalin dama na soyawa Bappa Alinku na kuma d'iba musu zoki basu nasan Mudassir so yake ya wahal min dake."
da sauri Saminu yace.
"To ni kuma indomi nakeso mai ruwa-ruwa yaji yaji da al'basa."
dariya sukayi baki d'aya dan sun san bazata iya musa mishiba,
sai kuma suka zuba musu ido jin tana ce mishi.
"Yanzu ne kakeso ko sai kun taso daga tabsir ne zan maka?."
ido ya lumshe kana ya zuba mata ido cikin sanyi yace.
"Ki huta sai mun dawo zamuyi aikin tare."
Ummi kam kauda ido tayi Warisu kuwa da Salisu tuni suketa hirarsu,
Mudassir kuma tuni ya zuba musu yambos d'in har ya fara ci Adda Rahma kuma tea tai ta had'a musu, nan suka fara ci sunaci suna hira.
Shi kuwa Saifuddeen gefen Ummin shi ya rab'a a hankali ya konta tare da d'ora kanshi a cinyarta, gyara zamanta tayi dan yaji dad'in konciyar,
kanshi ta d'an shafa cikin ido ta zuba mishi ganin sosai fa ya rame hancin shi zuwet har bisa baki idanunshi sun k'ara fitowa,
farinshi ya k'ara baiyana cikin kula ta kalleshi ganin ita yake kallo tace.
"Tashi mana Babana kaje kaci abinci da yan uwanka ai zakafi jin dad'in cin."
sanin in bai ciba hankalin ta bazai konta bane ya sashi yunk'urawa ya tashi zaune sannan ya amshi cup d'in da Adda Rahma ta cika da zazzafan tea mai k'auri sai k'amshi yake, gyara zamanshi yayi kana ya mik'awa Warisu hannunshi alamun ya bashi abinda suke ci d'in,
ganin Warisu zai kwatso mishi da yawane ya sashi nuna mishi yatsa d'aya alamun guda d'aya zai bashi,
kauda kai wWrisu yayi kana ya mik'o mishi guda biyu,
fuska ya d'an had'e dan shi cikinshi ya cika da ruwan da yaketa sha, ya kuma san Ummi zata sashi dole ya cinye biyun da ya sako mishi,
haka kuwa akayi dole ta sashi yaci sannan ta samishi soyayyan dankalin turawa, nanma yanaci yana d'an korawa da tea d'in a haka dai yaci kad'an.

Jin an fara kiran sallan isha yasa suka mik'e duka dan yin al'wala, dai-dai lokacin kuma Ahmad ya shigo shida Raliyya,
da sauri Rahma tace.
"Ke Raliyya meya kawoki a daren nan?."
kai ta d'an rausayar tare da gaida su Saifuddeen sannan ta zauna gaban Ummi cikin sanyi tace.
"Kai Adda Rahma ai nida Ya Ahmad ne muka zo nayi kewanku ne especially Hamma Saifuddeen, shiyasa nace yau mu taho tare kuma tare zamu koma."
Cikin fad'a Saifuddeen ya mata alamun da kada ta sake biyoshi gwara tazo da rana.
kai ta gyad'a mishi kana itama ta d'auki buta dan yin al'wala.

Su kuwa suna gamawa suka nufi masallaci koda akayi insha akayi asham, suna fitowa suka shiga cikin gida ruwa suka sha sannan suka nufi hanyar fita dan tafiya wurin tabsir kamar kullum,
har sunje bakin k'ofar fita Ummi tace.
"Ahmad ka dawo da wurifa ku tafi kasan Raliyya yanzu zatayi bacci anan."
juyawa yayi ya d'an kalli Raliyya cikin lumshe ido yace.
"Shike nan in tayi bacci sai in goyata mu tafi gida abinmu."
Warisu ne ya d'an bugeshi tare dayin k'asa da murya yace.
"Kai a gaban Ummin kake mata wannan kallon kamar wani tsohon maye."
ita kuwa Ummi cewa tai.
"Asheko yau sai dai ku kwana anan."
dariya sukayi kana suka fita,
Raihana kuwa da sauri ta isa gaban Saminu da shi yanzu yake shan ruwan,
cikin kauda kai ta mik'o mishi dabinon data ciko hannunta dashi guga bakwai ya tsinta kana yace.
"Ya isa sai mun dawo."
"To". tace dashi a sanyaye.

Daga nan suka fita suka tafi masallacin fad'an Dukku.
Chapter 21 · 0% Book details