← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 116

Sashe 80

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna shiga ta kalli Maryam cikin son jikar tata tace
"Ah Maryama dama kina cikine?."
cikin nitsuwa tace.
"Eh Hajja inna ina ciki salla nakeyi sanda Zakariyya yaje kiran Mama."
"Ayyah." tace da ita tare da kallon Zaleeha cikin yar tsamarsu tace.
"Rasa kunya berar tanka uwar kid'e-kid'e, ke ba abinda kika iya sai rawa da wak'a da kid'a ko."
Baki ta murguda mata tare da watsa mata harara.
cikin zaro ido tace.
"Iye ni kikewa wannan kallo lallai wannan yarinya in ba'a aurar da keba to tabbas zaki tashi gari,
hegiya mai zubin nasara."
Sai ta kuma juyo ta kalli Mama data tab'e fuska ko gaisheta batayi.
kwaffa tayi kana ta kalli d'an nata sannan tace.
"Kai Bashiru wlh infa kana son tsira da mutuncinka to ka aurar da wannan fitinenniyar yarinyar.
In ba haka zataci gaba da worwore maka tubkar da kakeyi.
Kullum kana kan hanyar zuwa gidan radio kana shirin tafarkin tsira al'ummar musulmai na k'aruwa da kai.
Abin takaici ana gama shirinka sai a sako shirin wannan dujaliyar yar taka wai mushak'ata,
haka zatayi ta zubawa wak'ok'i ka jita tanabin waken tamkar zabiya."
duk shiru parlour sukayi sai Zakariyya dake cewa.
"Ni dai da zata amshi shawarata ta dena bin wak'ok'in tana hanamu jin abu d'aya. Mu jita ko muji radio."
Da sauri ta gyad'a kai tare da cewa.
"Uhun ai dai kunji ko?."
shi kam Ahmad da Habu sai murmushin sukewa inna boris.
Ya Ameenu kuwa sai harara yake watsawa Zaleeha.
cikin muryar jin haushi Mama tace.
"Inna an wuni lfy?."
A hatsale Inna tace.
"Lau na wuni! gsky ce dai sai na fad'i ehe!."
Dariya sosai Ahmad yayi yayinda Baba malam ya murmusa.
ita kam Zaleeha ficewa tayi abinta,
ita kuwa inna sai cewa tayi.
"Dama iyayen yara sunfi son marasaji,
shiyasa take son Zaleeha kamar ranta bata son laifinta.
Kuma dole in fad'i dan ba yadda za'ayi in haifi d'ana malami ke kuma kizo ki haifa mishi zabiya, amara k'irjin biki."
Su duk dai ba wanda ya kuma mgn,
shigowa Mamy ne da kulan soyayyun kaji yasata washe baki tare da cewa.
"Allah dai ya miki al'barka Mamyn Ahmad."
Cikin sanyi Mamy tace.
" Amin Amin ." dan ita dai bata fiye son abinda inna kewa Zaleeha ba,
dan ita tana matuk'ar son Zaleeha kuma itama Zaleeha tana matuk'ar sonta.
Ido suka zuba mata ganin ta mik'e tare da cewa Zakariyya.
"Shalele na maza tashi mu tafi."
da sauri ya amshi kular sannan Suka fito,
suna zuwa parking lot nasu Baba malam yace.
"Inna muje in maidaki."
da sauri tace.
"Lalala bari a machine d'in Shalele na mukazo,
kuma a kanshi zamu koma."
Cikin tsoro baba malam yace.
"Inna a machine kuwa, to Ahmad ya maidaki ko Ameenu."
Kama hannun Zakariyya tayi tare da cewa.
"Muje ko Shalele yaro yana jin dad'in yau na hau machine d'insa kuma shine zaku hana."
Habu ne yayi dariya tare da cewa.
"Allah sarki watarana sunan hak'oranta babu."
Mamy ne tayi mushi dak'uwa su kuwa jikoki suka k'elk'ele da dariya.

Koda suka koma cikin gida Baba Malam da Ameenu da Ahmad da Habu mgnar Zaleeha sukaci gaba da d'an tattaunawa inda shi Ahmad yaje jaddada musu wai al'janine.

Jirgunsu na sauk'a a Abuja.
Ya Rabi'u da kanshi yazo ya d'aukeshi dan acan zasu kwana sai da safe zasu samu jirgin Gombe.

Sosai suka samu kulawa da karramawa ta musamman a wurin Aunty Mami.

Inda tayi tayiwa Hayatuddeen tsiya wai ya zama ba'indiye.

Washe gari k'arfe tara na safe jirginsu zai tashi.
So tun bakwai da rabi suka fito kai tsaye asibitin su Dr Aliyu sukaje.

Sosai fa Dr Aliyu yaji dad'in ganin Saifuddeen ya fara samun lfy,
Dr Batulu kuwa saida akayi mata kwatancenshi sannan ta tunoshi dan da fari tayi zaton ko ba indiye ne yazowa Dr Aliyu ziyara.

Karfe tara dai-dai jirginsu ya d'aga zuwa Gombe doma.

A hankali Hayatuddeen ke tura weelchair d'in da Saifuddeen ke zaune a kai,
cikin shiga ta alfarma,
wani dakekken yadine mai tsananin azabar kyau blue irin blue mai hasken nan sai ratsin d'igo-d'igo yellow irin yellow mai d'an duhun da za'a iya cemai ruwan k'asa.
Sai wata dakkeyar hukar damanga mai azabar kyau shina irin kalan kayanshin sai kuma takalminshi sau ciki suma kalar yellow mai d'an duhuwa,
sai agogon Gucci na fata shima kalan takalmansa,
ya kafa hular tayi ras a kanshi,
Sajenshi ya konta lib wanda hakan ya k'ara k'awata kekkyawar fuskarsa farar fatarshi ta k'ara baiyana red lips ɗinsa suka kara yin kyau cikin zagayen saje da kota million dake fuskarshi.
Shi kuwa Hayatuddeen wasu k'ananun kaya yasaka masu azabar kyau.
Tura weelchair d'in yakeyi a hankali da hannu d'aya,
yayinda d'aya hannun kuma ke janye da trollinsu.
a d'aya sashi kuwa ma'aikatan jirginne ke turo sauran kayan nasu wanda yake hade da wani weelchair d'in a ciki da dai sauran abun buk'a tunsu.

A hankali iska mai sanyi ke ratsa jiki da zuciyar Saifuddeen.
Tasbihi yakeyi ga ubangijin talikai daya sake nufarsa da dawowa k'asarsa jiharsa ta haihuwa wacce lokacin d'aya barta baisan inda yake bama tsawon shekara d'aya kenan dayawuce.

Isakar ya kuma shak'a tare da lumshe idanunshi yana maijin wani yanayi mai kashe jiki.

Suna isowa inda masu tarbarsu suke,
Kamar daga sana Hayatuddeen yaji an ruggumeshi ta baya,
da sauri ya juyo tare da sakin weelchair d'in ,
ganin Raliyya da Faruq ne ya sashi hadesu da jikinshi cikin tsananin jin dad'i,
jin sun sakeshi ne yasashi binsu da ido ganin inda suka nufa,
Adda Rahma ne sunkuye a gaban Saifuddeen dayi mishi wata iriyar rugguma ta yan uwa na jini,
madadin tayi mgna ina sai murmushi takeyi ga kuma hawaye nata kwaranya a idanunta.

Hakama Rainaha sarkin kuka tuni ta kasa isowa inda suke sai wani irin sark'ekk'en kuka da takeyi.
Ahmad kuwa wayarshi ya zaro yanata yi musu hoto a cikin duk motsin da sukayi,
ganin yadda Raihana ke kuka yasa Saifuddeen mik'o mata hannu,
aifa da gudu ta iso inda yake kawai sai ta durkusa dirsham har k'asa ta kafa guiwowinta kana ta kifa kanta bisa cinyarshi tare da yin zazzafan kuka,
kawai duk sai suka had'e kai a wurin.
Suna kukan farin ciki da tausayawa d'an uwansu.

Salisu ne yayi saurin isa inda suke ya janye Hayatuddeen da Faruq,
yayinda Ahmad kuwa ya janye Raliyya,
Ya Adnan kuwa ya gaza ce musu komai,
Ishaq kuwa, yana zuwa ya ruggume abokin nashi,
ganin airport d'in yayi musu kad'an wurin farin cikinsu yasa suka,
shiga motocin suka tafi,
Adda Rahma kam fir taki yin nesa da k'aninta a motar ya Adnan suke ita da Saifuddeen suna baya,
Ishaq kuma na gaba.

Hayatuddeen kuwa da Faruq da Raliya motar ya Ahmad suka shiga.

Salisu kuwa kuwa shi ya kwashi kayansu shida Raihana.

Daga airport zuwa cikin gombe akwai yar tazara,
so tafe suke suna hirarsu ta yan uwa shak'ik'ai.

Cikin tsananin mmki Hayatuddeen yake baza ido lokacin da suka shigo cikin gari sabida,
Sosai yaga sauye-sauye a garin.
Hakama da suka iso gida Saifuddeen da kanshi yayi mmkin ganin zubi da tsaruwar gidan,
Komai yayi shar tsirran da shuke-shuke sunyi lip-lip gwanin sha'awa.

Anayin parking Hayatuddeen ya fita da sauri, kai tsaye cikin gidan ya nufa a guje.
Ya Adnan kuwa yana fitowa ya bud'ewa Saifuddeen k'ofa kana ya bude but d'in motar ya fito da weelchair d'in.
A gab da kofar motar ya ajiye kujerar, yayinda tuni Adda Rahma da da Ishaq suka fito.
Hakama su Raihana ganin duk sun zagayeshi sun mishi zobene,
yasashi lumshe ido kana ya zuro k'afafunshi wojen tare dasa hannunshi ya dafa gefen motar sannan ya yunk'ura ya taso cid'ak cikin azama da jarumta da zafin nama ya zauna bisa weelchair d'in.
Wani irin nannauyan ajiyan zuciya Adda Rahma ta sauk'e da tsananin k'arfi dan da gani take kamar bazai iyaba.
Faruq kuwa da sauri ya tsuguna ya saita matakalar kujerar,
wani lallausan murmushi Saifuddeen yayi kana da taimakon Ahmad ya d'aura fararen sawunshi kan abin takawan.
Salisu kuwa tuni ya firfito da kayayyakinsu ya nufi cikin gida dasu.

Shiko Saifuddeen girarshi d'aya ya d'agawa Ahmad alamun tammayar ya dai ganin duk sun tsaya a kanshi.
Cikin tsananin tausayi da k'aunar d'an uwan nashi yace.
"Ai kaine jagoran."
lip inshi na k'asa ya d'an tauna ta gefe kana yasa hannunshi ya share hawayen dake bin fuskar Raihana sannan yasa d'aya hannunshi dai-dai wurin masarrafin weelchair d'in ya d'an daddana wasu madannai sai ga keken ya fara tafiya a hankali.
da sauri sukabi bayanshi.

Da sauri ya danna wani pin d'in sabida ganin Baba Ado mai gadinsu da Sule direbanshi sun rusuna gabanshi.
Sam sule ya gaza tsaida ruwan hawayenshi dan kamar yau yana tuna randa sukayi fitarsu ta k'arshe in da uban gidan nashi ya taka da sawunshi,
sai gashi cikin shekara d'aya ya zama bashi da damar tsayuwa.
kai ya d'an jujjuya musu alamun suyi hak'uri su bar kuka.
da kyar suka iya tsaida hawayensu kana suka mushi sannu da hanya da fatan samun lfy.

Hayatuddeen kuwa yana shiga parlour yayi tsalle ya fad'a kan kujera 3 str gefen Umminshi sai ya kuma ruggumota ta baya tare da cewa.
"Wayyo dad'i yau gani ga Ummi na."
Sosai Ummi ta ruggume autan nata tana maijin son yaran da begenshi.
Goggo Dada ce ta kalleshi cikin son yaran d'an uwan nata tace.
"Wato Umminka kawai ka gani ko?."
Da sauri ya juya zuwa gareta.
Dai-dai lokacin kuwa su Saifuddeen suka shigo,
wani irin farin cikine mara misaltuwa ya rufe Ummi wanda ta kasa koda motsa yar yatsarta,
sai bugawa da zuciyarta keyi da k'arfi-k'arfi.
Shikuwa Saifuddeen k'ara gudun weelchair d'inshi yayi ya saitata gaban Ummi.

Yana isa inda take gab da ita tayi saurin mik'o mishi hannu,
da sauri ya kamo hannun nata duka biyu kana ya tallabe fuskarshi dasu,
haka nan rauni zuciya suka rintsa mishi zuciya bai taba zubda k'walla akan wannan larura tashiba sai yau.
Kawai sai yaji wasu zafafan hawaye suna kwaranyo mishi,
da sauri ta mik'e tsaye ta matso gab dashi hakan ya bashi damar sahannunshi duka biyu ya ruggumeta tare da manna kanshi a cikinta,
wani sautin kuka mai cike da raunin d'a a gaban mahaifinshi ya sake.
Chapter 80 · 0% Book details