← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 116

Sashe 83

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari.
Ƙarfe tara tuni yagama shirya kansa inda yayi kyau cikin riga da wandon jeans ɗin dake jikinsa, ahankali yake tafiya da keken nasa harya kawo bakin ƙofar fita daga ɗakin, hannunsa yakai jikin handle ɗin ƙofan ya buɗe,  yanzukam da kansa yake tuƙa keken nasa cikin nitsuwa da salonsa na k'in wahala inda ya dumfaro babban falonnasu.
Ummi, Hayatuddeen, da kuma Raihana su ya tarar zaune acikin falon,yayinda Raliya ke ta kaikawo tsakanin dinning area da kitchine tana shirya musu breakfast, shigowarsa cikin falon shi yabayyana murmushi akan gaba ɗaya fuskokin ƴan uwan nasa, ƙarasowa tsakiyan falon yayi tare da kai dubansa ga mahaifiyarsa wanda takasa ɗauke idanunta akansa, murmushi zallan ƙaunarsa ne kwance akan fuskarta,  murmushin daya bayyana kyawunsa yayi tare dayi mata alaman.
"Ina kwana"
"Lafiya ƙalau Saifuddeen ya jikin naka?".
Ummi tafaɗa cikin kulawa.
Da body language yayi mata alaman.
"Da sauƙi" nan Raihana ta gaidashi tare da tambayar jikinsa,  itama da body language ya amsa mata  fuskarsa ɗauke da murmushi tare da mik'o hannu ya shafan kan Affan dake kwance bisa jikin Ummi. Raliya da Hayatuddeen ne suka gaidashi, suɗinma amsa musu yayi cike da ƙaunar ƴan uwannasa.
 Raliya na gama shirya musu break fast shida kansa ya sarrafa kekensa har zuwa kan dinning table ɗin,  kujera ɗaya ya matsar gefe kana ya turo kekensa har wajen,  kasancewarsa bamai cin abinci da yawa bane hakan yasa tea kawai yasha sai kuma chips dayake ɗan tsakala yana sawa abakinsa kaɗan kaɗan, sosai zuciyar ƴan uwansa da Umminsa ke wanke fari ƙal, babu abun dake ɗawainiya dasu face farin ciki da jin daɗi, kasancewarsu da Saifuddeen awaje guda baƙaramin ƙara musu kuzari da karsashi yakeyi ba, basu jima da fara breakfast ɗinba Ahmad da  Saminu suka shigo, nan suma suka zauna aka shiga cin abincin tare dasu,  duk da cewa suɗin surukaine ga Ummi, amma su jin kansu suke matsayin ƴaƴa awajenta, don sunajin kamar yanda su Hayatuddeen ke ƴaƴa awajenta haka suma suke saboda haka babu batun wani nuƙu-nuƙu agabanta don mahaifiyace garesu a gabanta suka girma tun suna yara har zuwa samartansu sukanci abinci a gabanta a matsayinta na uwa a garesu shiyasa kuma, koda suka auri yaranta tafiyar bata sauya zani ba.
Suna kammala cin abincin ne dukansu suka koma falo suka zauna,  hira sosai sukeyi yayinda Saifuddeen ke binsu da idanu yana me karantar abun da kowannensu ke cewa, idan na dariyane yakan ɗan murmusawa, ana haka ne Ishaq da tawagar ƙungiyarsu ta Joint National  association of persons with disabilities (Jonapwd) Gombe State Chapter. All the best! Suka ƙaraso, nanfa falon Ummi yacika tam da mutane, makafi, guragu, kurame, duk zuƙatansu suka cika da murnar ganin Saifuddeen,  Ishaq kam ji yake kamar yamaida abokin nasa ciki saboda daɗi, duk da cewa baya gani amma zuciyarsa ta gamsar masa da cewa Saifuddeen ɗinsa aboki kuma ɗan'uwansa ya samu lafiya, haka Ummi tasa su Raihana suka ajiye abunci da abunsha ga kowanne daga cikinsu, baƙaramin daɗi Saifuddeen yaji azuciyarsa na ganinsu da yayi ba, haka suka kwashe tsawon awanni suna tare da juna, saida akayi Azahar ne Ishaq ya tattarasu duk suka koma.
Adda Rahama da Dr Adnan da Baba Bello haɗi da goggo mahaifiyarsa ne suka zo,  suna zuwa babu jimawa kuwa saiga mutanen dukku wanda suka kusa cika mota suma sunzo don duba jikin Saifuddeen ɗin da kuma taya Ummi murnar dawowarsa,  nanfa gida ya ƙara ɗinkewa da jama'a.

  Da yamma kuwa Alhaji Sani da Alhaji Kabiru da kuma Alhaji Sulaiman mahaifin Hisham da Alhaji Adamu yayan Jabeer sukazo duba jikin Saifuddeen ɗin, sosai ƙwarai yaji daɗin ganinsu, suma sunji daɗi sosai da suka tararda jikin nasa da sauƙi, nan suka ɗan taɓa hira inda kowanni magana da body language sukeyi idan basu gane ba kuma yakan rubuta musu awayansa sai ya basu su karanta, sosai suka ɗansha hira kafun daga bisani sukayi masa sallama, koda sukazo tafiya al'khairi me yawa suka bawa Ummi don sunsan idan suka bawa Saifuddeen to ko sama da ƙasa zasu haɗe bazai amsa ba,  awajen Ummin ma kuwa ba tsira sukayi ba don kafewa tayi tace bazasu amsa ba, da ƙyar Alhaji Sani yasanya Ummi ta amsa, inda yayi mata tuni da cewa bakyau maida hannun kyauta baya.  Badon Ummi tasoba haka ta amsa kana tayi musu godiya.  

Wayar Hayatuddeen dake aje kan kujeran falonne kete tsuwa alaman shigowar ƙira saidai hartayi ta katse ba'a ɗauka ba, wani ƙiranne ya kuma shigowa, Hayatuddeen dake cikin kitchine ne yafito da gudu hannunsa ɗauke da wani dogon tsinke wanda jikinsa ke saƙale da gasashshen nama sai tiriri yake da'alama yanzu aka gasa naman,  saura ƙiris wayan ta tsinke ya ɗauka tare da karawa akan kunnensa, cikin yanayi na ɗan faɗa tace.
"Saikuma kaga dama ne kafun ka amsa wayana?"
Dariya Hayatuddeen yayi  tare da cewa.
"Yi haƙuri Likita ina kitchine ne".

Murmushi Amina dake zaune akan kujera tayi tare da gyara zamanta cike da kulawa tace "Kwaɗayayye kawai, meya kaika kitchen?."
hyyy yayi dan zafin da yaji lokacin da ya kai bakinshi kan sokan nama daketa tiriri,
jin tana mishi dariya ne ya sashi cewa.
"Nama ne Ummina ta gasa min,
shine nake d'an tab'i."
Kwaffa tayi tare da cewa.
"Ni bawannan ba yajikin Hamma Saifuddeen?".

"Eh dai naji, jikin Hamma Saifuddeen da sauƙi sosai, don yanzu haka ma muna gida, da jiya kika ƙira ma wataƙila da kinzo kin dubashi don muna Abuja" 

Idanu Amina tazaro tare da cewa.
"Wai kana nufin ya tabbata kun dawo Nigeria? kuma ma wai har jiya kun sauƙa Abuja shine baka ƙirani kasanar dani ba?" 

Dariya Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Ga zahiri kuwa muna mgna da number ta na Nigeria."
Cikin jin haushi tace.
"Tun shekaran jiyan can nake kiran number ka ta Indian bata shiga,
sai kawai yanzu kamar da wasa nace bari in gwada mtn naka.
kuma sai ya shiga, gsky Hayatuddeen baka kyauta min ba wlh."
cikin tauna naman yace
"Tuba nake Likita, ai bansan kina da buƙatar ganin kyakkyawan Hamman nawa ba!"
Cikin haushin rashin sanin dawowarsu da batayi ba tace "Harsai na faɗa mane sannan zaka sani, nidai ba wani nan munyi faɗa".
Dariya sosai Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Kiyi haƙuri bokan turai!".
"Nidai ai nace maka munyi faɗa ko".
tana gama faɗan haka ta kashe wayarta, dariya sosai Hayatuddeen yayi, Ummi dake tsaye abayansa ne ta ƙaraso cikin falon, dubansa tayi tare da cewa.
"Kai kuma kaida waye kake waya haka?"
Murmushi yayi tare da cewa "Amina ce fa Ummi wannan nurse ɗin da ta kula da Hamma Saifuddeen lokacin da muke Abuja, to shinefa yanzu da ta ƙira nake shaida mata dawowar mu shine wai ita tayi fushi da har jiya muka sauƙa a Abuja ban gaya mata ba taje ta duba jikinshi".
Murmushi tayi cikin tsananin jin dad'i tana matuk'ar son duk wani maison Saifuddeen d'inta,
murmushin kawai Ummi ta kumayi tare da zama akan kujera kana ta maida hankalinta ga TV inda sunna tv ke haska wa'azin Malam Isah Ali Pantami.

Yau tunda tazo wajen aikin nasu fuskanta aɗaure yake tamau, sam takasa sakin fuska ga kowa wanda hakan ya matuƙar bawa abokan aikinta mamaki, don kuwa sunsan bahaka take ba ita takowace sannan itaɗin me yawan fara'a ce saɓanin yau da suka ga ta tsuke fuska, fitowarta daga ɗakin gabatar da shirye-shirye kenan inda ta gabatar da shirinta na mushaƙata, kaitsaye ɗakin hutawansu ta nufa inda anan tabar jakarta harma da wayarta.
Koda ta shiga cikin ɗakin kan wata kujera ta zauna tare da ɗaukan jakarta, zip ɗin ta zuge kana ta ciro wayarta, 4 missed call ta iske acikin wayar wanda kuma duk daga Abdussalam ne, tsuka tayi tare da kunna data'n wayarta ta shiga Instagram, Raveel ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, can ƙasan maƙoshi ta amsa masa sallaman batare da ta ɗago kanta ta kalleshi ba,
asanyaye ya tako ya ƙaraso zuwa inda take, kan wata baƙar kujera dake facing wanda take ya zauna murya asanyaye yaƙira sunanta "Zaleeha!"

Bata amsashi ba haka kuma bata ɗago kai ta kalleshi ba, ganin haka yasanyashi sauƙe ajiyar zuciya, kansa ya ɗan langwaɓar gefe guda cike da tsananin shauƙin mayen soyayyarta yace.
"Dan Allah M B S Dukku ki saurareni mana, ashe shikenan don zuciyata ta kamu da soyayyarki tayi laifi? Dan Allah Zaleeha kiyi haƙuri ki fahimci irin sonda nake miki, wallahi inasonki ina miki son da nikaina bansan adadinsa ba, rasaki dai-dai yake da daiɗaicewar tunanina Inasonki Zaleeha, dan Allah ki Amshi soyayyata!!"
Tsananin rauni da damuwar dayake cikine ya bayyana ƙarara akan muryarsa.
Chapter 83 · 0% Book details