Sashe 87
Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Waro idanun Ishaq yayi bayan yagama sauraran wayarsa inda ta karanta masa gaba ɗaya abun da Saifuddeen ɗin ya rubuta, cikin tsananin mamaki yace.
"Wai kana nufin Zaleeha?"
Still murmushi Saifuddeen yayi inda ya rubata cewa.
"Inasonta Ishaq, haƙiƙa ina tsananin sonta, harma inajin kowani bugu na zuciyata tare da zallan soyayyarta yake tafiya, Inaso na Aureta! Ishaq tun randa na fara ganinta sonta ya zame min abokin rayuwa,
shiyasa kullum mukayi mgna da kai sai na tambayeka ita da lfyarta".
Koda Ishaq yagama sauraran batun wani irin tsananin farin ciki ne ya lulluɓesa, haƙiƙa baya gani da ido amma yana gani da zuciya, kuma tuni zuciyarsa ta gama karanta masa kyawawan halayya da kuma nagarta irin na Zaleeha, tabbas zaisowa abokinsa Saifuddeen samun mace irin Zaleeha amatsayin mata, cikin jin daɗi tare da son ƙarfafawa Saifuddeen ɗin guiwa Ishaq yace.
"Naji daɗi Saifuddeen, kuma zanfi kowa so da muradin kasantuwar aurenku da Zaleeha, saidai kuma baza muyi gaban kanmu ba, zaifi kyau mu fara sanar da manya don baza muje haka kawai ba sai da ƙarfin mu, ma'ana sai munsamu amincewar manyanta, tabbas ayanda nasan Zaleeha nasan tanada nagarta, kuma zata soka".
Ya k'arishe mgnar cikin karsashi domin su basu sawa ransu cewa nakasarsu zata zame musu kasawa ba, bare ta hanasu neman duk wani abinda mai cikar halitta zai nema kuma ishaq bai san dakon son dake ran Zaleeha ba.
Wani irin ƙwarin guiwa kalaman Ishaq suka ƙarawa Saifuddeen, nan suka cigaba da tattauna hira atsakaninsu ta hanyar gudanar da text message.
Zaleeha kuwa daga Jomapwd kai tsaye gidan redionsu na vission FM. ta nufa, tundaga fitowarta acikin motarta gaba ɗaya kallo ya dawo kanta, haƙiƙa Zaleeha cikakkiyar mace ce dake iya ɗaukar hankalin kowani ɗa na miji, cikin takunta me ɗauke da nutsuwa ta ƙarasa babban ɗakin da suke tantance shirye shiryensu kafun su turashi izuwa ɗakin watsa shirye-shirye, saida aka tantance shirin nata na wannan rana kafun aka watsashi tayanda kowa zaijisa raɗau batare da wata matsala ba.
Zama tayi akan wata kujera wanda keda ƙafafun taya, ahankali take jujjuyawa yayinda ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, wayarta ta ciro tare da saƙala earpiece acikin kunnenta, cool music na Edsheeran ne ke tashi acikin earpiece ɗin nata, ahankali take jujjuya kanta alaman waƙan na taɓa zuciyarta sosai, luf tayi ajikin kujeran tare da kwantar da bayanta kana ta lumshe kyawawan idanunta, tunaninsa ne yayi mata tsaye acikin ranta, wani irin ƙauna haɗi da begensa ne suka cika zuciyarta, bazata taɓa cire rai da rabo ba akansa saba, haƙiƙa ita mai raunice hakanne ma yasanya soyayyarsa ke wahalar da zuciyarta, inama da ace wani zaiji abun da takeji, inama da ace ƴan uwanta zasu fuskanci mai takeji tabbas tasan da kowa sai ya jinjinawa girman soyayyar da takeyi masa, tanajin sonsa har cikin ƙashi da bargo, haka kuma tanajin soyayyarsa tamkar jinine dake gudana ajikinta ako yaushe, hawayene suka cika idanunta sakamakon rauni irin nata.
Ajiyar zuciya Raveel yasauƙe, wanda tun ɗazun yake tsaye yana kallonta, ayayinda tayi nisa cikin begen masoyinta, shikuma alokacin yakejin kamar zuciyarsa zata tarwatse saboda ƙaunarta, son Zaleeha yake da duka zuciyarsa, hawayene suka cika idanunsa, hango manager dake ƙoƙarin tahowa garesu da yayi yasanyashi saurin shanye hawayensa, tare da komawa cikin wani ɗan balcony ya tsaya don sam bayason manager ɗin ya gansa, saboda rauninsa ya bayyana sosai ta yanda bazai iya ɓoyewa ba.
Yana sako ƙafarsa cikin babban falon wanda yakasance kamar ɗakin hutu ga ma'aikata gidan radio'n vission FM ɗin wani irin walagigin ƙaunarta ne ya daki ƙahon zuciyarsa, yayinda ya lumshe idanunsa tare da shaƙan daddaɗan ƙamshin ta da ya cika ɗakin, ahankali ya buɗe idanunsa tare da sauƙesu akanta, sam batasan da zuwansa ba kasancewar haryanzu idanunta arufe suke, sannan zuciya da ƙwaƙwalwarta sunyi nisa wajen tunanin abincin ruhinta, ahankali yatako ya ƙaraso gareta, cikin kulawa yaƙira sunanta, sam bata jisaba don tayi nisa atunanin da takeyi, kujera yajawo tare da zama yana facing ɗinta, hannunsa yakai ya zare earpice ɗin dake kunnenta, da sauri ta ware idanunta da sukayi ja ta sauƙesu akansa, cikin mamakin ganinsa da kuma yanda ya cire mata earpiece ɗin kunnenta taɗa kallesa kana tayi ƙasa da idanunta.
Murmushi Manager yayi tare da cewa.
"Barkanki da hutawa gimbiyar mata".
Cikin takura ta amsa masa da yauwa acan ƙasan maƙoshinta, hakanan ganinsa yasanya taji ba daɗi acikin ranta, itafa yanzu hakanan ta tsani duk wani mahluƙin da zaizo mata da zancen soyayya, ayanzu mutum ɗaya kawai take muradi kuma tana nan tana jira ya taho mata da soyayyarsa,
"Zaleeha!" Manager yaƙira sunanta murya asanyaye.
Bata amsa masa ba bata kuma ɗago kanta ta kallesa ba, sam ayanzu batason damuwa, hutu da nutsuwa kawai take da buƙata.
Ganin cewa bata amsa shibane yasanyashi cewa "Kiyi haƙuri Zaleeha, bansan da yaushene kuma tayaya bane nakamu da sonki, amma tabbas inasonki sosai, ina fatan zamo warki mata agareni Zaleeha, nasan kina ganin girma ƙima da kuma mutumci na, amma banda yanda zanyi akan soyayyarki Zaleeha, inajin kaina tamkar ƙaramin yaro akan soyayyarki, bazan gaji da fallasa miki sirrin zuciyata ba, don ina fatan samun nasara agareki!".
Sai alokacin Zaleeha ta ɗago idanunta ta kalleshi, inama da ace shine zaune agabanta haka yake furta mata daɗaɗan kalaman soyayya? inama da ace zata kasance da masoyinta kasantuwa tahar abada, ajiyar zuciya ta sauƙe, tabbas tana ganin girman Manager acikin idanunta, saboda hakane ma batajin zata iya tafka masa yayyafin rashin mutumci, don ko bakomai shiɗin babban mutum ne, kanta ta kawar gefe cikin dauriya tace. "Tabbas kamar yanda kafaɗa ina ganin girma da ƙimarka acikin idanuna, saidai dan Allah naroƙeka Manager daka janye soyayyar da kakemin, inada wanda nakeso araina, banajin dagashi zanso wani aduniyar nan, dan Allah karabu dani naji da damuwar dake raina!". taƙare maganar tana me haɗe hannayenta biyu waje guda alaman roƙo.
Ajiyar zuciya manager ya sauƙe tare da ɗan rumtse idanunsa, idan yaji tana ambatan cewa tana da wanda takeso, ji yake tamkar kifiya take caka masa aƙahon zuciyarsa, cikin raunin daya bayyana akan fuskarsa yace. "Kamar yanda kike jinsa acikin zuciyarki haka nima nake jinki acikin tawa zuciyar, bansan taya zan fasalta miki irin tarin ƙaunar danakeyi miki ba Zaliha, dan Allah ki tausayawa zuciyar da ta jima tana dakon soyayyarki!"
Idanunta ta rumtse tare da cije laɓɓanta tana mejin kanta na wani irin sarawa tamkar zai fashe, sam bazata iya jurewa ba hakan yasa ta ɗauki hand bag ɗinta, tare da wayarta, ko kallon inda Manager yake bata sakeyi ba ta nufi hanyar fita daga cikin falo, da sauri Raveel dake tsaye yanajin duk abun da suke faɗa ya koma jikin gini ya tsaya, don sam bayaso sugansa harsusan yaji abun da ya wakana atsakaninsu, "Zaleeha! "Zaleeha!!" haka manager keta ƙiran sunanta, ko tsayawa batayi ba balle yasa ran zata juyo ta kallesa, hannayensa ya sanya ya dafe kansa, yayinda soyayyarta ke ƙara ninkuwa acikin zuciyarsa, itakuwa Zaleeha tuni hawaye sun cika idanunta, kaitsaye wajen motarta ta nufa, tanakai hannunta jikin murfin motar muryar Raveel ya daki dodon kunnenta.
Inda yaƙira sunanta, ƙoƙarin shanye hawayen dake cikin idanunta tayi tare da tsayawa cak, saidai bata juyo ba, ajiyar zuciya Raveel dake bayanta ya sauƙe tare da cewa.
"Dan Allah kijuyo ki fuskanceni!"
"Kafaɗi abun da kakeson faɗa danni sauri nakeyi!" Zaleeha ta faɗa cikin ƙosawa, don gaba ɗaya komai bayayi mata daɗi.
"Maganace akan SO Zaleeha, dan Allah Zaleeha ki bani dama, ashirye nake dana zama GARKUWA agareki, zan baki ingantaccen farin ciki me ɗorewa, sannan zan....."
"Ya isa haka Raveel, wai me kuka ɗaukenine kowa so! so!! So!!! maikuka maidani ne? shin wai ni kaɗaice mace aduniya? Dan Allah Raveel kafita arayuwata, ka tsaya amatsayinka na abokin aikina kadaina wannan ƙoƙarin na tura kanka inda baka da muhalli awajen!!". Zaleeha ta katseshi tare da faɗin maganan aɗan tsawace.
Bata jirayi me Raveel ɗin zai ƙara faɗi ba ta shige cikin motarta, azafafe ta murzawa motar key yayinda ta jata da wani irin speed, ko gama wangale mata gate ɗin bata bari maigadi yayi ba ta danna hancin motar tata waje ranta amatuƙar ɓace.
Raveel kuwa idanunsa da ke cike da hawaye ya rumtse tare da juyawa jiki asaluɓe shima yanufi wajen da motarsa take, don yanda yakejin ciwo azuciyarsa bayajin zai iya komawa cikin office ɗinnasu.
Ahankali take rage gudun da takeyi, kantane ke mata wani irin ciwo, gaba ɗaya damuwa yayi mata yawa, ɗan lumshe idanunta tayi tare da dafe saitin zuciyarta dakeyi mata zafi, kaitsaye Havilla tanufa, don ayanda takejin zuciyarta dole tana da buƙatar abun da zai sanyaya mata rai, tana shiga cikin wajen ta lumshe idanunta sakamakon wani irin daddaɗan sanyi daya ratsa jikinta, wani irin ni'imtaccen ƙamshin korayen shuke shuke dake wajenne ke ratsa cikin hancinta, sosai yanayin wajen yayi mata, cikin takunta mai ɗuke da nutsuwa taƙarasa can ciki, ƴan mata da samari ne suka kusa cika wajen, waƴanda kallo ɗaya zakayi musu batare da sai anfaɗa maka ba zaka gane cewa masoya ne, don kowanne dake cikin wajen fuskarsa ɗauke take da shauƙi, dayawan mazan dake wajen kallonsu ne ya dawo gareta, musamman wani kekyawan gaye dake zaune shi kaɗai akan table, cikin ajinta da sanin darajar kanta ta ƙarasa ga ma'aikatan dake cikin Havilla'n, nan ta basu order'n irin haɗin ice cream ɗin da takeso ayi mata, mintuna kaɗan wani saurayi ya kawo mata ice cream ɗin,zip ɗin hand bag ɗinta ta zuge inda ta ciro kuɗi ta bashi kana ta karɓi ice cream ɗin, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa ta juya ta fice, da sauri wannan saurayin ya rufa mata baya, don bayajin zai iya jure kasa furta mata soyayyarta da ta kamasa alokaci guda.