← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 116

Sashe 68

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can gida Nigeria kuwa dai-dai lokacin Raliya na zaune gaban Ummi da take ce mata.
"Tunda sukaje basu samu damar ganin Dr bama, ni gaba d'aya hankalin na a tashe yake."
da sauri Raliya tace.
"Yauwa Ummi dama abinda ya kawoni kenan fa yanzu mukayi mgna da Ya Ahmad yace min yau sun samu ganin Dr kuma Alhamdulillahi duk gwajin da ake buk'ata anyi, zuwa gobe sakamakon zai fito."
ajiyan zuciya tayi tare da cewa.
"Alhamdulillahi."
sai kuma tayi shiru jin Raliya na cewa yauwa gama Auta na kirana."
da sauri tace amsa kiran."
Da sauri tayi picking call d'in murmushi tayi ganin fuskar yan uwanta duk suma suna mata murmushi da sauri ta yunk'ura ta dawo gefen Ummi ta saita fuskarsu da fuskare wayar,
suna kallon junansu,
wani irin faffad'an murmushi Ummi tayi ganin fuskokin yaranta cikin happy tace.
"Alhamdulillahi babana ya jikin?."
kai ya d'an rausayar tare da yin yalwataccen murmushi,
Hayatuddeen kuwa cikin tankwara wuya yace.
"To wai ni kam bakuyi missing na bako kallifa Ummi ko ki kulani ninefa autanki."
dariya tayi har saida wushiryanta ya baiyana sannan tace.
"Nayi kewarka mana autana."
da sauri Raliya tace.
"Ni dai banyi kewarka ba dad'i ma nakeji na huta da tattaren kayanka yanzu gidanmu baya hargitsewa tunda ka tafi."
dariya yayi sosai sannan yace.
"Wayyo yarinya ai in ke kin huta mijinki bai hutaba yaseen watsar da komai nakeyi son raina Ya Ahmad ke tattaremin,
Yau da safe harda boxer na ya wonke min da zai wonke nashi."
da sauri yayi shiru tare dasa hannu yana shafa k'eyarshi da Ahmad ya bugi yana mai cewa.
"Wato kama maidamu bayinka nida matata."
cikin jin dad'i Raliya tace.
"Yauwa ya Ahmad buge minshi da kyau, kuma ka dena tattare mishi komatsanshi."
Saifuddeen kuwa hannu yasa ya jawo kan Hayatuddeen ya manna da kafad'arshi sannan yasa tafin hannunshi yana shafa mishi inda Ahmad ya d'an buge mishi.
murmushi yayi tare da cewa.
"Kada ya tattara mana ba sai muyi ta zama cikin dottiba."
cikin jin dad'i Ummi tace.
"Kai Autana ka fara girma fa ka rink'a womke guntayem wondunanka da kanka kaji ko?."
kai ya gyad'a mata sannan ya mik'awa Dr Adnan wayar cikin kauda kanshi yace.
"Barka da dare Ummi ya gida."
sunkuyar da kanta tayi cikin kunya irin ta surkai tace.
"Lfy lau Baban Adam ya mai jikin?."
A mutunce yace.
"Alhamdulillahi Ummi jiki da sauk'i yau mun samu munga likita,
nanda kwana biyu za'ayi aiki, ki kwantar da hankalin ki in sha Allah zai samu lfy."
cikin samun nitsuwa tace.
"Allah yasa."
Amin Amin sukace baki d'aya sai kuma tace.
"To ni kuma sai yaushe zan zo in dubashi?."
Da sauri Ahmad ya koma gefen Adnan d'in kana yace.
"Ummi ki kwantar da hankalin ki bari in an mishi aikin munga yanayin jikin sai kizo."
shiru tayi kamar dai bata gamsuba sai kuma Dr Adnan yace.
"Ki bari sai anyi aikin, dan nima in anyi aikin zan dawo,
in yaso in na dawo sai ki zo ko?."
a hankali tace.
"To ba matsala Allah ya bada sa'an aiki."
Amin Amin yace sannan ya kalli Raliya tare da cewa.
"Ina Faruq?." a hankali tace.
"Yana d'aki wurin Goggo Dada wai sai ta mishi tatsuniya daga nan duk sukayi bacci."
"Ki gaida min shi, gobe asabar yaje gida mana yayi hutun sati a wurin Mamanshi."
cikin nitsuwa tace.
"To ba matsala, ka gaida Hamma da jiki mun gode Allah ya saka ya bar zumunci."
Amin Amin yace sannan suka sallami juna.

Sosai Ummi ta samu nitsuwa da sukayi hirar.

Su kuwa suna gama woyar Ahmad ya gyarawa Saifuddeen konciyarshi,
dan ganin ya fara lumshe ido,
a hankali Ahmad ya kalli Dr Adnan tare da cewa.
"Ya Adnan kuje masauk'inmu kaida Hayatuddeen ku kwana bari ni in kwana dashi, kaje ka samu ka huta."
kasan cewar akwai gajiya a jikinshi yasa ya amince,
tare suka tafi shida Hayatuddeen shi kuwa Ahmad ya kwana nan wurin Saifuddeen.

D'aya gadon ya hau ya kwanta yana kwanciya Bappa Ali na kiranshi wanda shi kuma kawunshi ne yayan mahaifiyarshi da sauri ya amsa kiran.
"Salamu alaikum."

"Wa alaikassalam."

"Ina wuni Kawu Ali."

"Lfy lau Alhamdulillahi Ahmad ya jikin Saifuddeen?."

"Jiki da sauk'i Kawu yau mun samu munga Doctor."

"Eh haka dai Mudassir ke sanar min yanzu wai sunyi waya da Yayanshi Adnan."

gyara konciyarshi yayi tare da cewa.
"Na kira d'azu ai zan sanar maka to kuma sai naji layin naka baya tafiya."

"Eh lallai na rufe wayar ne, na tafi harami shiyasa."
Cikin nitsuwa yace.
"Kawu Ali sai yaushe ne dawowarku?."
"Saura mako guda, kuma in sha Allah ni daga nan saudia zan taho india".

"To Allah ya kaimu lokacin ya dawo daku lfy.
Kawu Ali a tayamu da Addu'a fa."
"In sha Allah, Ahmad zamuyi ta addu'a."

Daga nan sukayi sallama,
juyowar da zaiyi sai yaga Saifuddeen na rik'e da wayarshi,
a hankali ya tashi zaune kana ya mik'e ya taho gaban gadon,
lek'a fuskarshi wayar tashi yayi,
ido ya lumshe ganin karatun Qur'an yakeyi,
sai ya koma konta.

Shi kuwa Saifuddeen tunda Ahmad ya gyara mishi kinciyarshi,
ya lumshe ido ya fara bacci sai kuma ya fara mafarki inda yake ganin Zaleeha
tanata k'ok'arin son ganin fuskarshi daya rufe da tafin hannunshi,
shima kanshi ta tsakanin yatsunshi yake gane fuskarta,
ita kuwa sai tasa hannunta tana ta son ciro hannunshi daga fuskarshin amman ta kasa d'age hannun nashi,
ganin haka sai ta koma gefe ta zauna tanata kuka,
daga nan ya farka daga baccin.
To shiyasa kawai ya d'auki wayarshi ya fara karatu.

Shi kuwa Ahmad Warisu ya kira suka gaisa sannan sukayi saida safe.

Ya Adnan da Hayatuddeen kuwa da k'afa sukayi tattaki har cikin Hyatt kasan cewar ba nisa da asibitin.

Suna isa Ya Adnan yayi wonka,
yana fitowa Hayatudden ya mik'e ya shiga,
bayan sun gama shirin baccinsu ne,
Ya Adnan ya koma parlour ganin Hayatuddeen baiyi bacci ba, yanata charting da abokanshi da yawanci jikin Hammanshi suke tambaya.
Dan haka ya koma parlour dan yana son zaiyi waya da matarsa ya d'an kontar mata hankalin.
Sosai ya kontar mata da hankalin, sannan yayi bacci.

Washe gari bayan sun karya suka sayawa su Ahmad abinda zasuci sannan suka nufi asibitin.
Suna isa doctor na isowa, a tare suka d'anci abincin.
Tuni Dr Adnan kuwa ya kira Dr Acash prasat ya shaida musu suna kusa.

Suna gama woyar ya hangi Divia ta amsa kira sai kuma yaga ta nufi inda yake tare da ce mishi su shiga,
yana shiga suka tattauna da doctorn,
suna gamawa ya fita.

Yana dawowa wurinsu Ahmad yace.
"Har ka fito?."
"Eh na fito ya nuna min sakamakon gwajin da akayi ne,
ya kuma cemin gobe ne zasuyi aiki."

"To Allah ya kaimu." Ahmad ya fad'i yana gyara wuyan rigarshi,
Hayatuddeen kuwa Amin Amin yace tare da ajiye wayarshi kusa da kan Saifuddeen.

Washe gari kuwa k'arfe tara dai-dai na k'asar tasu.
Aka gama shirya Saifuddeen cikin shigar da akewa wad'anda za'ayiwa aiki,
tuni suma Doctors an gama shirya musu komai kayan aiki.

K'arfe goma dai-dai nurses suka shigo suka tura gadon Saifuddeen suka nufi wani corridor mai fad'i, a hankali Hayatuddeen ya bisu da ido da alamun karaya a idanunshi,
ganin haka yasa Ahmad ya jawoshi suka zauna kana ya d'an kontar mishi da hankalin.
Ganin ya d'an nitsune ya kira Ummi yace mishi tofa an shiga aiki ta tayasu da addu'a yana katsewa ya kira bappa Ali ya gaya mishi hakama su Salisu da Warisu duk ya gaya musu.

Shi kuwa Dr Adnan yana tare dasu Dr Acash dan shi a wurinshi kamar samun k'arin ilimi ne ace a gabanshi akayi aikin.

Suna isa d'akin da za'ayi aikin Saifuddeen yayi murmushi ganin Ya Adnan da irin shigar doctors d'insu,
shima Dr Adnan murmushi yayi dan yana jin k'arfin guiwa da karsashi daga ganin lafiyayyun kayayyakin aikinsu,
bugu da k'ari ga Dr Malik Khan shima dashi za'ayi aikin dashi.

Allurar bacci ko ince cire haiyaci sukayiwa Saifuddeen,
bayan sunga yayi lib alamun alluran sunyi aikinsu.

Nanfa suka fara aikinsu baji ba gani,
shiru kakeji ba magana ko tari basayi sai sautin AC da kuma d'an sautin injuna da d'an k'aran ajiye ababen aiki da sukeyi.

Surgery ba sauk'i kusan tsawon awa hud'u sukayi a kanshi,
sannan suka kammala komai,
canza mishi kayan jikinshi sukayi sannan suka canza mushi gado, kana aka turoshi tamkar gawa aka fito dashi,
ta gabansu Ahmad akazo aka wuce dashi,
mik'ewa sukayi suka fita daga wurin baki d'aya,
yayinda tuni su Ahmad suna biye dasu a d'aya,

Wani side dake can gefe suka shiga,
suna shiga wurin suka shiga wani babban parlour dake cike da kekunana da kuma d'an ma dai-daicin pharmacy kuma ga ma'aikata a cike da wurin.
Suna shaga wasu suka taso suka karb'eshi a hannun wad'an nan d'in,
wani d'aki suka shiga dashi dashi,
kuma basu hana su Ahmad shigaba sai dai suna shiga sukaga sun zuge wani k'ofa na glass sun shiga cikin d'an keb'an taccen wurin dake cike da,
na'urori.
Kontar dashi sukayi bisa gadon dake ciki sannan suka k'ara gudun AC tare da gyara mishi konciyarshi,
suna mgna amman su Ahmad bazasu jisuba.
suna gama kimtsashi sukayi d'aura mishi ruwa tare dasa ruwan allurai a ciki,
daga nan suka fito suka zo inda su Ahmad suke,
a nitse suka d'an musu bayanin cewar kada su yawaita hayaniya, kada kuma suce zasu shiga inda yake shida farkawa sai gobe iwar haka,
kada kuma su damu, su zauna na.
kai kawai suka gyad'a cikin gamsuwa da nitsuwa,
kana suka zauna a kujerun dake jere a wurin,
gaba d'aya Hayatuddeen ya kasa nitsuwa sai hawaye yaketa zubdawa da kyar dai Ahmad ke tausasa mishi zuciya.

A can kuwa ana fitar da Saifuddeen aka shigo da wani bature,
shima awa hud'u sukayi suna aiki a kanshi daga nan kuma,
suka firfito sai kuma gobe kasan cewar mutun biyu sukewa aiki kullum.
Chapter 68 · 0% Book details