← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 116

Sashe 70

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutane ne keta hada-hadan shiga da fice daga cikin asibitin.
Koda suka ƙaraso cikin asibitin ɗaki na musamman aka samawa Saifuddeen tare da taimakon Dr Acash prasat,   Dr.Adnan da Ahmad ne suka ɗaga Saifuddeen daga kan weelchair ɗin da suka turosa akai, kan faffaɗan gadon dake cikin ɗakin wanda yaji lallausan katifa suka shimfiɗesa, ahankali ya maida kyawawan idanunsa ya rufe tare da ɗan sauƙe ajiyar zuciya.  Kafaɗansa Dr.Adnan ya ɗan dafa a hankali, jin an dafa kafaɗansa ya sanyashi buɗe idanunsa ya sauƙesu akan laɓɓan Dr.Adnan,
Dr.Adnan kuwa ganin Saifuddeen na kallonsa ya sanyashi cewa.
"Yajikin naka?" 
Kyakkyawan murmushine ya bayyana akan kyakkyawar fuskarsa, kansa yaɗan jinjina alamar da sauƙi, tare dakai dubansa ga Hayatuddeen dake tsaye ya kafesa da ido, murmushinsa me kyau yayiwa Hayatuddeen tare da miƙo masa hannunsa, ganin haka yasa Hayatudden cikin tsananin ƙaunar da yake yiwa ɗan uwan nasa yataho garesa tare da miƙa masa hannu shima, damƙe hannun Hayatuddeen yayi acikin nasa hannunsa tare da lumshe idanunsa,  sosai yakejin son ƴan uwansa acikin rai da zuciyarsa, tabbas yasan Allah shine gatan kowani bawa, amma kuma yasan duk wani buri da fatan ƴan uwansa akanshi yake, shi musulmine da ya yarda da ƙaddara me kyau ko akasinta, haka kuma yayi imani cewa komai ya faru da bawa muƙaddarine daga Allah,
Sake rufe idanunsa yayi kirif yayinda zara zaran eye lashes ɗinsa suka kwanta luf aƙasan idanunsa, gashin giransa kuwa sai shinning yake kamar wanda aka shafawa mai, uwa uba ga tohon sabon gashi na tattausan sajen da ya fara yiwa fuskarsa k'awanya, sosai fuskarsa tayi fayau da ita hasken fatarsa yasake bayyana, haƙiƙa Saifuddeen kyakkyawane sosai, sannan duk da nakasar dake tare dashi komai nasa abun burgewa ne da so,  ganin kamar yayi bacci ne yasanya Dr.Adnan duban Ahmad da Hayatuddeen cikin kulawa yace.
"Yakamata ace kuje ku nemi masauƙi tunda Dr.Acash yayi mana komai ya kuma sama mana nurses ɗin da zasuna kula dashi, sannan gani ni zan zauna atare dashi."
Jinjina kai Ahmad yayi tare da duban hayatuddeen da har yanzun hanunsa ke cikin na Hamma Saifuddeen ɗinsa. "Mutafi ko Hayatuddeen, naga idanunsa arufe inaga yasamu bacci".
Ahmad yafaɗa yana me kallon Saifuddeen.

Kallon Hamma Saifuddeen ɗin hayatuddeen yayi,cike da tausayin ɗan uwan nasa ya soma yunƙurin zare hannunsa dake cikin nasa,  har acikin ransa yakejin tausayin Hamman nasa, tabbas shikam da ace ana sauya ƙaddara, to da tuni ya sauya ta hammanshi daga mummuna izuwa kyakkyawa.
  Haka Hayatuddeen da Ahmad suka baro cikin asibitin don nemawa kansu masauƙin da zasu zauna,  taxi suka shiga inda suka ce yakaisu hotel wanda yake mafi kusa.

Tafiya kad'an sukayi kana motar ta ratsa cikin Ƙofar katafaren hotel d'in.
Sahar International Mumbai,  mai taxi din ya sauƙesu, hotel ne ƙawatacce me kyaun gaske wanda yake ɗauke da dogon gine gine gwanin burgewa.
Kallon Ahmad Hayatudden yayi bayan sun sauƙa daga taxi ɗin sun biya me taxi ɗin kuɗinsa, cikin yanayi naɗan damuwa yace.
"Ya Ahmad baka ganin wannan hotel ɗin zaiyi tsada da yawa? ka duba kyawunsa fa".
Ɗan jim Ahmad yayi tare da ɗaga kansa yana ƙarewa hotel ɗin kallo, asanyaye yace.
"To Hayatuddeen ya zamuyi, dole haka zamu kama saboda shikaɗaine zai sauƙaƙa mana wahalan zuwa asibiti, kaga idan bashi ba ko ina muka kama sai munyi ta cacan kuɗin transport, kaga kuma wannan ma ƙarin ɗawainiya ne". 
Kai Hayatuddeen ya jinjina cike da gamsuwa da kalaman Ahmad, atare suka jera har zuwa cikin hotel ɗin inda suka tsaya a receiption.  saida sukayi duk wani abun daya dace kana suka biya kuɗi sannan aka basu makulli da kuma nomban ɗakin da suka kama,   tafiya suke suna me dudduba nambobin ɗakunan har suka iso ɗakin dayake da namba dai-dai da wanda aka basu, Ahmad ne yasanya key ya buɗe ƙofar ɗakin, Hayatuddeen na biye dashi abaya haka suka shiga cikin ɗakin, amatuƙar gajiye hayatudden ya faɗa kan faffaɗan gadon dake cikin ɗakin, wanda ke ɗauke da wata luntsumemiyar katifa me laushin gaske, lumshe idanunsa yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, kallonsa Ahmad yayi tare da girgiza kai aransa yana me cewa .
"Allah Ya shirya mana kai Auntan Ummi".
  kasancewar agajiye suke su dukansu, yasanya Ahmad soma ɗan rage kayan jikinsa kana ya wuce bathroom,  wanka yayi tare da ɗauro alwala don gabatar da sallan magriba wanda daf ake da cikar lokacinta, yana fitowa daga cikin bathroom ɗin yaci karo da wandon Hayatudden daya cire yayi wurgi dashi atsakiyan ɗakin, gefe kaɗan ma rigarsa ce wanda ya cire a yashe, cike da takaicin halin Hayatuddeen Ahmad ya girgiza kansa tare da ƙarasawa gaban mirror, don yasan idan yace da Hayatudden ya ɗauke kayan nasa daga ƙasan ma, wani sabon sakalci ne zai tashi, hakan yasa ya ƙyaleshi yashiga fito da kayansa dake cikin jaka don zaɓan wanda zai saka.
  Haka dai cike da sangarta Hayatuddeen ya wuce bathroom shima yayi wanka tare da ɗauro alwala,  koda ya fito awankan kamar yanda ya saba haka ya zazzage kayansu dake cikin jakan kaf akan gado, shidai Ahmad yana kallonsa bai kulasa ba, don yasan me hali baya taɓa fasa halinsa,  riga da wando na jeans Hayatuddeen yasanya cike da sakalci ya dubi Ahmad dake ƙoƙarin rufe kwalban turaren dake hannunsa, ɗan ɓata fuska yayi tare da shafa cikinsa cikin murya me ɗauke da gajiya yace.
"Yaya Ahmad nifa gaskiya yunwa nakeji, gashi bamu sayawa su Hamma Saifuddeen abinci ba!"

"To acici kai-dai baka da wani zance saina ci, yanzun idan mukayi sallah sai munemi waje mafi kusa musai abinci mukai musu, don tabbas nasan zuwa yanzu dole zasuji yunwa".
 Ahmad yafaɗa yana me ƙoƙarin saka takalmi aƙafarsa.
Shi kuwa Hayatuddeen bai sake cewa komai ba har Ahmad yagama kimtsa kansa suka fice daga cikin ɗakin, cikin harshen turanci Ahmad ya tambayi ma'aikatan dake aiki a hotel ɗin inda zai samu abinci,  dayake babu wani nisa tsakanin hotel ɗin da kuma inda ake sai da abincin hakan yasa ɗaya daga cikin ma aikatan yayi musu kwatance,  saida suka fara zuwa wani masallaci da ke nan kusa suka gabatar da sallan Magriba, daga Hayatudden har Ahmad babu wanda daya kafa goshinsa aƙasa ba tare da yayiwa Saifuddeen addu'ar samun lafiya ba, 
suna idar da addu'o'insu suka nufi inda zai sadasu da inda ake saida abinci. 
Koda suka ƙarisa wajen cin abincin, waje ne me kyau da tsabta sannan babu irin abincin da babu awajen,  cimar Nigeria sukaci, inda Ahmad yaci Fish roll and gas meat, shikuwa Hayatuddeen yaci roasted fish da kuma damammiyar madara me kaurin gaske, daganan takeaway sukayiwa su Dr.Adnan da Saifuddeen, kasancewar tsakanin hotel ɗin da asibitin babu wani nisa sosai hakan yasa da ƙafansu suka shiga takawa har zuwa privet hospital ɗin.
Kaitsaye inda su Hamma Saifuddeen din suke suka nufa,  abakin ƙofar ɗakin da Saifudden ɗin yake suka hango Dr.Adnan tare da Dr.Acash prasat, da alama magana suke mai mahimmanci, tsayawa sukayi daga gefe har saida suka kammala maganan kafun suka ƙaraso, kallon fuskan Dr. Adnan sukayi su duka, cikin yanayi naɗan damuwa Ahmad yace.
"Akwai matsala ne?"
Kai Dr.Adnan yagirgiza tare da cewa.
"No babu wata matsala, sai-dai bayanzu zamu samu ganin doctors ɗinba aƙalla sai munshare kwana biyu kafun mugansu,
  Dr.Anan Mehta, ƙwararren  likitane a ɓangaren  Orthopeadic surgeon, sai kuma  Dr.Mahesh Khurana, wanda shima ƙwararrene afannin neurosurgeon, muna da buƙatan ganin wad'annan likitotin don kuwa sune masu kula da irin lalurar Saifuddeen, fatanmu akullum dai shine Allah yabashi lafiya".
Da.
"Amin Amin". suka amsa su dukansu, ko wanne zuciyarsa cike da tausayin Saifuddeen. 
Ganin rauni nashirin bayyana akan fuskokinsu ne yasanya Dr.Adnan karɓan takeaway din hannunsu kana yace su koma masauƙinsu su huta sai kuma zuwa da safe idan Allah yakai rai,  bazasu musa masa ba domin dama agajiye suke, hakan yasa sukayi masa saida safe, koda Hayatuddeen ya buƙaci ganin Hamman nashi cewa dashi Dr.Adnan yayi yayi bacci sannan ba aso atasheshi, dole haka Hayatuddeen ya haƙura yabi Ahmad suka koma masauƙinsu.

Koda Dr.Adnan ya koma cikin ɗakin nan ya iske Saifuddeen kamar yanda yafita ya barshi wato idanunsa alumshe tamkar wanda yake bacci, shi kuwa Saifuddeen ba bacci yake ba, yayi nisa ne akan tunanin Zaliha, kyakkyawar fuskarta ne keyi masa gizo acikin ƙwayan idanunsa da zuciyarshi, tuno da yanda ta rungumesa ta baya tana me jansa akan su gudu alokacin da yaran Dalla suka kusa cimmasa  yasanya tsikar jikinsa tashi, lokaci guda ya tuno da taushin hannuwanta da kuma yanda daddaɗan ƙamshin turarenta ya zautar dashi,  yanayin da yakejin kansa aciki, ya sanya shi jin tamkar alokacin abun ke faruwa, sake lumshe idanunsa yayi alokacin da ya tuna da yanda bakinta ke motsawa alokacin da take cewa yazo su gudu kada su cutar dashi, wani irin yawu ya haɗiya wanda tuntuni ya tsaya masa amaƙoshi, gaba ɗaya jiyayi jikinsa yayi wani iri, yayinda yakejin wani irin sassanyan yanayi shauƙin sha'awa na musamman suka rufeshi dangane da ita.     "Saifuddeen!".
Dr Adnan yaƙira sunanshi yana me kamo hannunshi, tayanda zaiji ya buɗe ido, jin sauƙan hannu akan nasa hannun yasanyashi buɗe idanunsa ahankali, murmushi Dr Adnan yayi masa tare da cewa.
"Tashi kaci abinci, danajika shiru na ɗauka ma ai bacci kakeyi".
Ɗan murmusawa kawai Saifuddeen yayi, inda shi kuma Dr Adnan yaɗan ɗago saman gadon da Saifuddeen ɗin yake yayi sama, shida kansa ya gyara masa kwanciya inda yayi kamar azaune yake saidai kuma bayansa yana jingine ne da gadon, abinci Dr Adnan ya miƙo masa kana ya koma gefe shima ya soma cin nasa,   cikin nutsuwa haka Saifuddeen ya shiga cin abincin ahankali yake ɗan lumshe kyawawan idanunsa masu matuƙar ɗaukar hankali, haryanzu tunaninta ne kwance aƙasan zuciyarsa, ahaka dai har ya ɗanci abincin kaɗan ya ture sauran gefe, don shi ba mutum bane me yawan cin abinci sosai...

Gombe Nigeria
Chapter 70 · 0% Book details