← Book details Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 116

Sashe 46

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kan hanyarsu ta zuwa Medical Center d'inne d'aya daga cikin police d'in yayi saurin zaro woyar dake al'jihun wondon Saifuddin
ganin tanata kawo haske alamun shigowar sak'o,
text ne aka turo kamar haka.
```"Babana Saifuddin Kana ina? ka dawo kayi bud'a baki mana, ka sani duk muna jiranka kasan hankali na bazai kontaba in baka ci abinci ba."```
shiru police d'in yayi yana jujjuya kalaman, a ranshi yake cewa.
"Bawan Allah azumi ma yakeyi kenan."
sai kuma ga wani sak'on da yaga suna no daya turo text d'in Hayatuddin inda yake cewa.
```"Slm Hamma Saifuddeen ka dawo gida muyi dinner yunwa nakeji kuma kasan bazamu iya cin abinci ba in baka nan please ka dawo da wurin shalelen Ummi kaga ta k'i kula kowa sai cekiyarka takeyi kamar kaine autanta."```
haka nan yaji tausayin ahlin wannan bawan Allah ya kamashi,
dai-dai lokacin suka shiga harabar Medical Center Gombe,
kasan cewar da jami'an tsarone lokaci d'aya aka karb'eshi, aka fara bashi taimakon gaggawa
d'aya daga cikin doctors da sukayi kanshi ne domin bashi taimakon gaggawa don ceto rayuqarshi yayi saurin matsoshi ido ya zazzaro woje Cikin tsananin kad'uwa da tarin tsoro da tausayawa yace.
"Saifuddeen!."
sai kuma yayi maza ya fara had'a na'urar dai-daita nufashi wato oksijin kana yayiwa sauran doctors guda biyun alama dasu fara aikinsu,
mazuk'in numfashin suka manna mishi,
kana suka kunna wani wuta mai tsananin haske sannan suka matso da dukkan abin buk'atan aikin suka fara, duddubashi ciki da woje sam babu wani yanka ko karta a sauran sashin jikinshi sai na bayan nashi kawai, sai kuma alamun duka da katako dake tsakiyar k'ugunshi da bayanshi.
Kana sai suka koma duba kwokwon kanshi inda suka samu buguwar guda uku, amman iya karsu woje basu shiga ciki yadda zasu shafi hankalinshi da tunaninshi ba.

Sosai suka duk'ufa dan ganin numfashi sa ya dai-dai ta,
amman abin yaci tura,
sosai suke aikinsu cikin iyawa da gwarewa da sanin makaman aikinsu,
shiru kakeji ba motsi sai body language da sukeyi a tsakanin su.
Tsawon awa biyu sukayi a kanshi kafin suka samu nasarar dai-dai tuwar numfashi sa,
canza mishi gado sukayi kana Doctor Adnan ya turo gadon da kanshi ya nufi I, C U inda nos guda biyu suke biye dasu,
bayan ya dai-dai ta mishi komai sai ya fito kai tsaye office nashi ya nufa.
Yana shiga ya zame bisa kujerar dake mazauninshi, idanunshi ya rumtse da azabar k'arfi yana jin wasu hawaye masu azabar zafi suna tsatsafo mishi cikin jijiyoyin idanunshi,
sai ya kuma mik'ewa da sauri kanshi ya kifa da jikin bongon office enshin yana mai zubda hawayen.
cikin rauni da tausayawa murya na rawa yake cewa.
"Astagfurillah Allah na tuna ya Allah nasan ka fini sanin waye Saifuddeen ya Allah nasan kafi ahlinshi sonshi, ya Allah ka sauk'ak'awa Ummi wannan jarrabawa dake shirin sauk'a gareta ya rabbil izzati ka duba larurar Saifuddeen ka yaye mishi ka bashi lfy."
sai ya kuma koma ya zauna kan kujerar kana ya kifa kanshi bisa babbn table dake gabanshi,
dai-dai lokacin Doctor Arabi ya shigo tare da police officer biyu,
da sauri ya matso wurin abokin aikin nashi ganin yana kuka cur-cur tamkar yaro,
cikin kad'uwa yace.
"Doctor Adnan meke faruwa?."
kai ya jijjiga jikin son tsaida hawayenshi yace.
"Dr Arabi wannan da aka kawofa k'anin abokina Nuruddeen ne."
cikin firgici Arabi yace.
"Innalillahi Saifuddeen! to kuma me yayi musu meya tsare musu, meyasa zasu cutar da bawan Allah shida baya mgna meyasa suke son sa ahlinshi a rana Allah sarki Ummi da Rahma wayyo Hayatuddeen wayyo Raliyya da Raihana."
cikin kad'uwa police d'in yace.
"Alhamdulillahi abu yazo da sauk'i tunda kun sanshi."
cikin rauni Arabi yace.
"officer kun kama wad'an da sukayi mishi dukan ne su waye ne ina suke me ya musu?."
cikin kauda kai officer d'in yace.
"Ina bamu kamasu ba asalima bamu san su waye bane,
domin kafin mujema shi kad'ai muka samu a wurin babu ko mutun d'aya,
itama wacce ta sanar damu cewa tayi wucewa tazoyi ta gefen sitadiyon d'in ne so sai taji ihu shiyasa ta kawo rahoto,
to ganin a firgice take yasa muka had'ata da d'aya daga cikinmu ya rakata gida don ta gaza yin draving dan tace itama sun biyota ne ganin ta d'an tsaya shiyasa har suka samu daman fasa mata glass d'in gaban mota, so kunga bamu da hanyar samun wata shaida, abu mafi sauk'i a bashi taimakon gaggawa kana ga woyarshi ku nemi yan uwanahi ku sanar dasu."
cikin rauni Dr Adnan ya rink'a jujjuya kai tare da cewa.
"Innalillahiwainna'ilaihirajiun wayyo ni Adnan ta yaya zan tinkari ahlin Saifuddeen da wannan mummunan lbri da wanne baki zancewa Ummi Saifuddeen d'inta na asibiti cikin d'ayan biyu mutuwa ko rayuwa taya zan sanarwa Rahma halinda k'aninta ke ciki?."
ganin haka Dr Arabi yayi saurin cewa.
"Please officer ga adireshin gidansu kuje ku sanar dasu kana ku d'aukosu ku kawosu nan d'in."
da wannan shawarar police d'in suka nufi federal lowcost
babu wuya ya gane kwatancen da Dr Adnan yayi mishi,
a k'ofar wani babban gida sukayi hon minti uku tsakani mai gadin ya lek'o, ganin motar jami'an tsarone ya sashi bud'e k'aramar k'ofar ya fito cikin hausarsa ta buzaye yace.
"Sannunku lfy kuwa?."
cikin saisaita fuska mai jan motar yace.
"Wurin masu gidan mukazo bud'e mana gate."
cikin sanyin jiki da d'an tsoro ya bud'e gate d'in kana ya rab'a gefe suka shigo,
bayan sunyi parking ne biyu daga ciki suka fito,
hannu suka bashi bayan sunyi musabaha ne police d'in yace.
"Kayi mana sallama da Hayatuddeen."
to yace jiki a mace har ya juya zai nufi cikin asalin gidan sai ya kuma juyowa tare da cewa.
"Dan Allah ku gaya min lfy dai ko?."
ganin alamun rashin gamsuwa a gareshi ya sasu ce mishi,
"Saifuddeen ne tsautsayi ya ritsa dashi so ana neman danginshi."
cikin tsananin firgici da tsoro buzun nan ya kama kai tare da cewa.
"Innalillahi! Saifuddeen meya sameshi ina yake?."
cikin mmkin waye Saifuddeen menene nagartarshi shi wayene da Doctors ma suke kuka kan cutarshi kana kalli yadda ma'aikatan gidansu ma suka firgita jin yana cikin matsala, jiki a mace yace.
"Kaga yi maza ka mana sallama da k'aninshi."
cikin rawan jiki ya kusa kai cikin gidan nan mai azabar kyau.
A cikin gidan kuwa Hayatuddeen ne da Ummi suke sauk'owa daga benen ,
cikin shek'iyanci Hayatuddeen ya zame ya zauna kan last step kana ya manna kanshi da k'afafun Ummi dake tsaye a gefenshi cikin shogwab'a ya kalli Raliyya kana yace.
"Yaseen yau a bedroom d'in Hamma Saifuddeen zan kwana, nine auta amman anfiji dashi, komai nashi na dabanne Ummi da kantafa take gyara mishi side nashi, ni kuma nawa ko oho."
cikin wasa sukayi mishi dariya, Ummi ce ta shafa kanshi tare da cewa.
"Yoh kaida kake cewa ka fini sonshi ni uwar data haifeshi ma."
ido ya lumshe tare da cewa. "In banso Hamma Saifunaba to waye zanso a duniyarnan?, amman dai duk da haka nima ina son a gyara min d'akina yayi ta shek'i da zuba k'amshi koda rabin na Hamma na ne."
dariya Raliya tayi tare da cewa..
"Hayatuddeen waya isa ya medaka irin Hamma Saifuddeen ko Allah ma bai halicceku iri d'aya ba Hamma Saifuddeee mutun ne mai tsabta, kaikuma irin kune ake cewa kai dai kaga gaye a titi karkaga ma koncinsa, kaida inda ka tub'e wondonka nan kake tsallakeshi."
dariya sukayi baki d'aya dan shima yasan halinshi kenan.
Raihana kuwa cikin dariya tace.
"Karka damu autan Ummi shalelen Hamma Saifuddeen daga yau zan rink'a share maka side d'inka."
Dariya yayi cikin jin dadi kana yayiwa Raliya gwalo,
cikin raha tace.
"Au nanda yaushe zata koma ka dawo kana min k'aramar murya."
dariya sukayi baki d'ayansu banda Ummi da zuciyarta ke yawan tsinkewa yana fad'uwa ras-ras.

Shi kuwa buzun nan
wata k'ofa ya bud'e tare da kusa kai cikin wannan corridor d'in, wucewa yayi ba tare daya tsayaba cikin wannan had'ed'd'en parlour mai azabar kyau ya kuma baiyana wanda yakeda tsananin girma da fad'i kana ga steps d'in da zai sadaka da sama, sallama yayi tare da duk'awa gefen Ummi kekkyawar mace wacce zata iya kai 49 years to 50 kekyawace wacce yawan shekarunta bai samu nasarar b'oye kyantaba, Ummi kenan sai wannan d'an matashi autan nata da banzai wuce 17 years da yan watanni ba, Hayatuddeen,
Raliyya matashiya yar duma-duma wacce zata iya kai 23 years.
Sai kuma Raihana da zata iya kai 26 year da d'anta Affan wanda bazai wuce shekara biyu ba.

Cikin maida hankali kan buzun Ummi ta juyo cikin wani yanayi da takeji tun da yammacin yau d'in tace.
"Baba ila ya akayi ne?."
cikin sanyin jiki yace.
"Wasune ke sallama da Hayatuddeen."
mik'ewa Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Muje wata k'il Zakariya ne."
kai ya jujjuya mishi cikin sanyi yace.
"A a bashi bane folisawa ne, sunce Saituddeeen ne ya samu d'an hatsari yana asibiti shine akeson yan uwanshi suje."
wata iriyar zabura Ummi tayi kana ta rumtse idonta da azaban k'arfi sabida wani irin duhu da jirin da ya rufe mata ido a take,
wani irin rawa jikinta ya fara har cikin hanjinta takeji suna hautsinewa zuciyarta kuwa tamkar zata faso k'irjinta ta fito fili sabida tsananin razana da kad'uwa lokaci d'aya wata zazzafar zufa ta yanko mata
hakama Raliyya da Raihana shi kuwa Hayatuddeen gaba d'aya idanunshi ya zazzaro woje.
kusan gaba d'aya a tare suka fito Ummi kam duk jikinta rawa yakeyi tamkar mazari.
Chapter 46 · 0% Book details